Sashe 2
Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bayan rasuwarta sai rik'o na ya koma hannun Aunty saratu da tsawon shekara biyu kafin hatsarin mota ya zama sanadin rasuwar Babanmu, a lokacin ne kuma komai ya sake hargitsewa, aka raba gado sannan aka raba ni da Aunty Saratu, don ba yadda bata yi akan a bata ni ba, amma su Hajiya suka k'i yarda, wani zaice suna sona da gaske ne a lokacin, wani zaice suna k'okarin kare 'yancina ne na kar a kaini inda za'a dinga min kallon 'yar karo, sannan wani zaice zasu nuna min tarin gata ne sab'anin tulin bautar da nazo na tarar.
Gwaggo Lami da 'ya'yanta su suka cigaba da zama a gidanmu dake can bayan Babban gida saboda shi kansa gidan ma ya shiga cikin gadon 'ya'yanta maza, wanda ni nawa gadon ban ma san ina yake ba.
Dawowata Babban gida ya zama sanadiyar yankewar karatuna na boko da islamiyya saboda Hajiya mai iko kad'ai a gidan a matsayinta na matar Kakanmu guda d'aya data rage tace Mamana ma bata yi ko d'aya daga karatun ba don haka bata ga amfaninsa akaina ba nima.
Nayi kuka da jimami kamar an sake min sabuwar mutuwa a lokacin, don Allah ya sani ina mutuk'ar son makaranta amma ba yadda na iya, haka na cigaba da zama tsawon shekara d'aya da rabi ba wanda ke koya min ko alif, sai tarin bautar da nake yi safe da rana, wanda in na samu d'an lokacin hutu ne kawai zaka ganni zaune a can k'uryar d'akin don ko waje Hajiya bata tab'a barina na fita, sai in shafe wata guda a cikin gida.
Daga inda nake zaune ina wannan tunanin, ina iya ganin yadda Hajiya take shan kokonta a hankali bayan ta zuba shi a kofin murfin filas d'in, navsan cewa da ta gama wani aikin ne zai biyo baya don haka na kishingid'a kad'an na rufe idona, sannan tunanina ta gangara kan mamallakin wannan muryar, wannan sabuwar muryar da ta shigo cikin rayuwata a yanzu take shirin bani sabon fata irin wanda na dad'e ina sak'a mafarkansa a zuciyata.
Sai dai banyi nisa a tunanin ba wani irin tari mai k'arfi yasa na bud'e idanuna na kalli b'angaren da sautin ya taho, abinda na gani yasa zuciyata ta buga sau uku da wani irin k'arfi sannan naji jinin dake jijiyoyina yana zuk'ewa.
Hajiya kwance akan tabarmarta ta juyo tana kallona cikin ido yayin da jikinta ke girgizawa da k'arfi!
Bakinta yana fitar da wani irin farin yawu mai kauri sannan hannunta na hagu dunk'ule akan k'irjinta, d'ayan kuma yana baje akan tabarmar rik'e da kofin kokon nan.
Na janyo dukkan k'arfin jikina na mik'e da sauri na isa gareta.
"Hajiya....me...me ya sameki?" Muryata ta fito cikin rawa.
Idona yana kallo tana k'ok'arin bud'e bakinta amma ba sautin daya fito illa yawan yawun daya k'aru wajen fitowa.
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un..."
Na fad'a ina rufe bakina da duka hannayena, k'arar bugun zuciyata kamar zai fito waje, Idanunta sai faman k'iftawa da bud'ewa suke yi kwalla na zirarowa daga cikinsu, alamun tana cikin tsananin ciwo.
"Hajiya...Hajiya." Na shiga kiran sunanta da muryar da bata yi kama da tawa ba, amma bata iya amsawa.
Sai na mik'e da sauri na nufi k'ofa, amma wani tunani ya tsaida ni a daidai bakin k'ofar, ina zanje? wa zan kira? me zance ya faru? cewa kawai na bud'e ido na ganta a haka? hankali zai d'auka? ko kuwa wani zai yarda dani?
Na juyo na sake kallonta, idanunta na kallon rufin d'akin a yanzu, sannan fuskarta ta d'ashe, me hakan yake nufi? me ya faru kenan? ko dai alamar.... sai kuma nayi saurin katse kaina ban k'arasa ba, ba zan iya k'arasawa ba.
Na dawo da sauri na sake tsugunnawa a gabanta, a daidai hakan kuma k'arar shigowa b'angaren ta cika kunnuwana, sai na kasa banbance k'arar takun dana bugun zuciyata wanne yafi fitowa fili, Numfashi na ya tsaya cak! sanda murya tayi magana daga bayan labulen.
"Assalamu Alaikum, wannan 'yar tsohuwar tana nan?"
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un...!"
A zuciyata nayi niyyar fad'a amma sai naji bakina ya furta hakan da k'arfi.
D'agewar labulen d'akin ta nuna min fuskarsu tar! a cikin hasken safiyar, Salisu, Auwal, Sule, Yakubu da kuma wani da ban san sanshi ba.
A lokacin ne kuma na tuna da abinda Yaya Sule ya gaya mata jiya dadaddare.
"Salisu yazo gari jiya, watakila gobe ma zai shigo ya gaida ki."
Sai tayi dariya tace.
"Ai kuwa ina maraba da maigidana."
"Me ya same ta? me kika bata?" Yaya Salisun da a lokaci d'aya ya karaso cikin d'akin ya fad'a yana girgiza jikinta.
"Na rantse...
Na rantse da Allah ban sani ba kawai bud'e ido nayi na g..."
"Kamar yaya baki sani ba?
Tun yaushe take a haka?" Yaya Auwal ya daka min tsawa wadda tasa na zabura zan mik'e tsaye.
"Kawai, Kawai, kawai... bud'e idona nayi na ganta..."
"Ku kamata mu fita da ita!"
Yaya Sa'id ya katse k'ink'inata, suka ciccib'eta gabad'ayansu suka yi waje, ni kuma na cigaba da zama a wajen ba tare da wani katab'us ba, don dukkan tunanina a lokacin ya tattara ne ya rataye a iska.
Ba abinda nake iya yi sai kallon kofin kokon nan da kuma farin yawunta dake zube a k'asa.
Me kika bata?
Kalaman Yaya Salisun suka dawo cikin kaina.
Me kuwa na bata banda kokon nan? don in bashi ba na san ba abinda taci sai goronta na sanyin safiya, toh amma ta yaya koko kawai zai b'ata mata ciki haka?
Kafin in sake k'ok'arin wani tunanin, muryoyi suka shiga b'ulb'ulowa cikin d'akin sannan wani hannu ya cakumo ni ta wuyan rigata ya d'agoni sama, sanda kalla sai naga Aunty Sadiya ce bayanta fal da mutane.
"Me ya faru? me kika bawa Hajiya? nace don uw*rki me kika bata?"
"Na rantse da Allah Aunty, Wallahi Allah...."
Wani kyakykyawan mari mai zafi ya katse ni, naji zafinsa yana tafiya cikin kaina sannan a lokaci d'aya ya maida ganina dishi-dishi, na k'ifta idanuna da k'arfi amma ba abinda ya canja.
"Rantsuwa aka tambaye ki? cewa akayi me kika zuba a cikin kokonta?"
Muryar Ramatu ta fito daga wata siffa mai rawa.
Kokonta?
Suma tunanin da suke kenan?
Da sauri nace.
"Wallahi tallahi ban sani ba, bani ma na had'a kokon ba, Aunty Habiba ce ta had'a da nata, tace zata taya ni da ta ganni ina wanki, tace...."
"Laaahailah ha illallahu..." Muryar Aunty Habiban daga cikin mutanen nan ta katse tawa.
"Yaushe na ganki a safiyar nan bayan tashi na kenan yanzu naji ana hayaniya? ko kuwa wani ya taba ganina ma na damawa Hajiya koko a duk masu dama mata na cikin gidan nan? ba aikinki bane wannan? me nayi miki a duniyar nan Bintu da zaki kira sunana a wannan lamarin?" Sai kawai ta fashe da kuka.
Wani irin sanyi ya shiga bin kowacce jijiya ta jikina lokacin da na zare idona akanta, duk wata ma'ana ta mamaki da firgita shine halin da nake ciki, kafin inyi wata magana kuma wani marin ya taho daga Aunty Sadiya ya sake maida ganin nawa dishi-dishi.
"Ke kad'ai ce kika tsani Hajiya a gidan nan Bintu, wa zai cutar da ita haka in ba ke ba?
Innalillahi wa inna ilahir rajiun...." Sai ta sake ni muka sulale k'asa tare.
Amma Aunty Zainab ta finciko ni kafin in kai k'asa.
"Na rantse da Allah in baki fad'a mana gaskiya ba sai na kashe ki a wajen nan!"
Ta fad'a sanda ta janyo sandan dogoron Hajiya ta shiga dukana kota'ina, zafin dukan farko ya d'auke ni ya zagaya dani cikin duniya, na biyu kuma ya dawo dani cikin d'akin.
"Kar kiyi magana wallahi sai na kashe ki a d'akin nan koda kuwa hakan shine abu na k'arshe da zanyi."
Ta sake fad'a cikin kuka, kuma na tsinci muryoyi da yawa suna goyon bayanta.
"Aunty Sadiya!
Aunty Sadiya!" Ba zato muryar umar ta kwararo daga cikin dimbin mutanen da suka shak'e k'ofar d'akin.
"Hajiya ta mutu!" Ya fad'a cikin ihu.
"Ta mutu."
Ya sake fad'a sai dai wannan karon a hankali kamar cikin sheshshek'ar kuka.
A cikin sheshshek'ar muryar tasa, na hango yadda rayuwata take gangarawa cikin bala'i.
________
8:00 PM
Kusan awanni tara kenan da suka shud'e tun bayan da aka tabbatar da rasuwar Hajiya Balaraba, sannan awanni hud'u da gama jana'izar binneta.
Ta yaya ta mutu? ance wai an saka guba mai k'arfi ne a cikin kokonta wadda ta kasheta cikin 'yan mintuna k'alilan.
Ta yaya hakan ya faru?
Labarin ya gama zagaye kewayen garinmu kaf! cewa nice da alhakin kisan, tare da kawo wasu tarin dalilan da suka maida labarin irin wanda hankali zai d'auka.
Ni kuma fa? ina k'ulle a wani d'aki na b'angaren gidan yayin da zaman makokin ya cigaba da gudana a can b'angaren Hajiya, sai dai kafin a k'ulle ni su Yaya Salisu sunyi min d'an banzan dukan da yasa na fita daga haiyacina, kuma a cikin tarin jama'ar gidan kaf! ba wanda yayi yunk'urin cetona in banda tururuwar 'yan kallon da aka samu wand'anda ke k'ara masu dukan.
Kawu Ibrahim, wan Babana shi kad'ai da ya shigo gidan ya taimakeni, ya rik'e bulalar daga hannun Yaya Salisu sannan ya waska masa mari tare da fad'an cewa bai san bashi da hankali ba sai a lokacin.
Daga nan ya ja ni zuwa b'angaren Babban d'an Hajiya wato Kawu D'anjuma, anan ne na kula cewa gidan ya fara cika da d'imbin mutanen dake tunkud'owa don tabbatar da labarin da yaje musu, ta cikinsu na hango Gwaggo Lami kuma kamar kowa a wajen idanunta cike suke da tsana, wata irin tsana fiye da wadda na saba gani a wajenta tun tasowata.
Sanda muka shiga b'angaren sai Kawu Ibrahim yace in tsaya daga gefe shi kuma ya shiga cikin k'aton d'akin da nake hango maza fal a ciki, na fahimci yawancinsu manyan gidan ne sai kuma wasu 'yan uwa na kusa.
Daga inda nake tsaye jikina na d'agawar kuka, ina jiyo muryar Kawu Danjuma yana fad'in wad'anda zasu yiwa gawar wanka in an dawo da ita daga asibiti.