Sashe 34
Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ba ranar da zata fito ta fad'i ba'a binne gawa wajen ba, har sai da ta kai saboda k'arancin waje sai an tara gawarwaki da yawa sannan a binne su a rami d'aya, kuma kamar yadda ake k'aro sojojin a kodayaushe haka muma 'yan aikin ake k'aro mu da zarar adadin yayi k'asa.
Tun zuwanmu wajen babu abinda muke yi sai aiki, aiki irin wanda lokacin magana da na kusa da kai ma babu shi,
gashi kusan kullum ruwa ake yi amma ba ga mu 'yan aikin ba hatta sojojin nan duk k'arfin ruwa baya tsaida al'amura.
Bamu dad'e a wajen ba muka fahimci cewa kusan rabin sojojin wajen da wanda ake k'arowa
asalinsu ba 'yan k'asar america bane,
wasu sojojin haya ne daga wasu k'asashen, wasu kuma masu laifi ne daga gidan yari irin wanda aka yanke musu hukuncin d'aurin rai da rai,
daga baya aka basu zabin shiga aikin sojan ko kuma su k'are rayuwarsu a d'aure.
A cikin irin wad'annan fursunonin Mahaifinka yake, Sunansa
AHMAD,
musulmi ne, dan wata k'asa mai suna NIGERIA.
Bamu san laifin da yayi yazo nan ba,
amma kowa a wajen ya sanshi akan mutum mara magana da hayaniya wanda koda yak'i ya tsagaita a wasu ranakun, baya tab'a sakin jikinsa kamar yadda sauran su kanyi, abu na farko daya fara jan ra'ayin Maria akansa kenan.
Hanya guda d'aya da muke ganin sojojin nan shine,
a ranakun da yaki yayi sauki suka dawo nan cikin sansanin su ci abinci, mu kuma zamu je mu kwashe kwanukansu mu wanke, sai dai
hakan ba sosai yake faruwa ba don wani lokacin sai a fi k'arfin kwanaki arba'in babu irin wannan ranar,
amma duk da k'arancin hakan Maria ta fara lura da Ahmad a irin wannan lokacin.
Sai tace dani.
"Gashi can yau ma zaune, ba tare da kowa ba."
Tun ina biye mata muna yin hirarsa lokaci-lokaci, har na fahimci abin nata yayi yawa na rabu da ita.
Amma Maria bata daina ba, ta cigaba da bibiyar al'amuran Ahmad har ya kai duk sanda aka samu irin wannan ranar in zamu je kwashe kwanuka, da wuri zata fita don ta riga kowa d'auke na gabansa, ta wannan hanyar ya fara lura da ita har suka karya dokar da ake jaddada mana a kullum cewar kar mu yadda wata alak'a ta had'a mu da sojojin, don bana mantawa bamu fi wata d'aya da zuwanmu wajen ba aka kashe wani soja tare da wata 'yar aiki da ya yiwa fyad'e, basu ko duba cewa babu laifinta a ciki ba aka harbeta da harsashi d'aya a zuciya kamar yadda aka yiwa sojan.
Maria tana da hikimar zance,
watakila maganar harshenta ce yasa ta ja hankalin Ahmad har ya san sunanta, don a watarana mun je don kwashe kwanukan, sai ya taso ya tsaya a gabanmu ya miko mata nasa kwanon kuma ya kirata da mai sunan 'yan garinsu, watakila ba don na janye hannunta mun bar wajen ba, tun a wannan lokacin k'addara zata datse komai tsakaninsu ba tare da an samar da kai ba.
Na san cewa Maria kyakkyawa ce 'yar k'abilar mutanen turkiya, amma a wannan halin da muke ciki kullum jage-jage ban san abinda yaja ra'ayin Ahmad ya fara sonta ba, Na fahimci hakan ne ta yadda duk ranar da aka samu sauk'in yak'i, Maria ke cika da mutuk'ar d'okin tafiya kwasar kwanuka don kawai ta ganshi, sannan idan mun je shi kuma baya tab'a iya janye idonsa daga kanta har mu gama komai mu tafi, na dad'a tabbatar da abinda ke tsakaninsu ne ranar da Maria ta sulale da duhun Asuba ta bar aikin da muke yi ta fita ta baya, ana kwara matsanancin ruwa wannan lokacin saboda haka mamakin abinda zata yi yasa nabi bayanta.
Daga can nesa na hangeta tsaye ita dashi, sunyi kusa da juna sosai sannan ya rik'e hannayenta duka biyu kamar yana mata sallama don a lokacin koina ya cika da k'arar takun sojojin dake ta fita suna tafiya gab'ar yak'in.
Nabi duk wasu hanyoyi da na sani don in nusar da ita ta daina shiga al'amarin Ahmad amma bata fahimce ni ba Saboda a wannan komawar da suka yi ne yak'i ya rincab'e,
aka kashe mutanen cikinsu masu d'imbin yawa, ya zamana
kullum cikin dawo da gawarwaki ake ana binnewa, wasu ma ance a can ake barinsu kawai.
A lokacin Maria ta daina bacci ta daina komai, kullum idonta na kan 'yar k'aramar tagar dake kallon hanyar da ake shigo da gawarwakin, tun ban damu ba har nima nazo na fara fatan dawowarsa, don daga yadda naga yanayin k'awata a wannan lokacin na tabbata zata iya kashe kanta a duk ranar da aka shigo da gawar Ahmad.
BAYAN NA MUTU!
AYSHA SHAFI'EE
Fatanmu mu duka ya karb'u a ranar da yak'in ya tsagaita, duk da anyi musu mummunar ta'asa amma sun taho da murnar cewa abinda suka yiwa wad'ancan yafi nasu muni,
don har mu 'yan aiki a wannan ranar munyi farin ciki.
Ahmad ya dawo shima, a cikin cincirindon sojojin dake dawowa a wahalce kuma Maria bata yi wani tunani sau biyu a kwakwalwarta ba ta tafi ta rungumeshi!
Ubangiji yaso kowa yana ta kansa ne a lokacin saboda haka ba'a sami wad'anda suka lura dasu ba, a sannan ne kuma na fahimci cewa duk wani bayanina ba zai tab'a tasiri akan Maria ba, ta riga ta had'e zuciyarta da ta Ahmad kuma ban isa in raba su ba, saboda haka na zura ido kawai na kalli abinda k'addara ta tanadar tsakaninsu.
Don kamar had'in baki a wannan lokacin sai sojojin suka shafe kusan kwanaki ashirin basu koma fagen yak'i ba, saboda haka alak'ar Maria da Ahmad sai ta samu bigiren yad'uwa,
har ta kai nima na sauko daga tunanina ina jin dad'in kasancewarta dashi,
saboda wata irin tsantsar kulawa da yake bata ta hanyoyi da dama, har saida ta kai yanayinta dama shigarta sun fara banbanta da namu, duk da cewar albarkacinta nima na canja sutura a irin kayayyakin da yake bata wanda yake yin aike ga masu gadin wajen su siyo mata.
Kuma cikin ikon ubangiji babu wanda ya tab'a zargin komai daga gare ta balle har alak'arsu ta tonu.
A wannan lokacin ne kuma Maria ta same ni da zancen cewa ta canja addini ta koma na Ahmad, kuma ya gaya mata zai aure ta su koma can k'asar su bayan an gama yak'in, bance mata komai ba don bana iya hanata komai d'in daya dangance shi.
Sai dai Ahmad bai samu damar koya mata komai game da addinin ba yak'i ya sake dawowa suka tafi barmu cikin jiran tsammani, kuma a cikin wannan jiran ne wani babban al'amari ya faru.
Wanda shine samun cikinka, yazo a lokacin da muka shekara d'aya da rabi a sansanin, lokacin da muka riga muka saba da rayuwar wajen muka zama mutanen daji na k'arfi da yaji, har a sannan kuma su Ahmad basu dawo daga gab'ar yak'in ba.
Ni na fara ganewa Maria tana da ciki kafin ma ita, kuma bayan mun tabbatar da hakan na shiga bata shawarar hanyar da zamu bi mu gudu tunda muna d'aya daga cikin manya da ba'a takura musu sosai amma Maria tak'i yarda, tace min baza ta tafi ta bar Ahmad ba alhali baima san da cikinta ba.
Kamar yadda na sani, itama ta san a wannan lokacin in sojojin dake gadinmu suka fahimci ciki ne da ita ba abinda zai hana su kashe ta amma soyayyar da take wa Ahmad ya rufe idonta gam da hangen hakan, saboda haka na rabu da ita muka cigaba da zaman jiran tsammanin da muke ciki a kodayaushe.
Wanda k'arshensa ya haifar da abubuwa da dama, na farko dawowar sojojin nan ba tare da Ahmad ba ko gawarsa, gashi ba wanda zamu je mu tambaya ace meye alak'armu dashi?
Nayi iya kokarina in nusar da Maria ta hak'aura cewa Ahmad ya mutu amma ta kasa fahimtata, tace ai ba dukkaninsu ne suka dawo ba mu dai zauna zamu ganshi.
Na biyu komawar sojojin da sake dawowarsu bayan watanni biyu babu Ahmad, na uku sauran ma'aikatan da muke tare suka fahimta cewar Maria na da ciki,
na hudu, ganewar d'aya daga cikin sojoji matan dake gadinmu da k'ulleta da suka yi a wani d'aki wanda kowa ya san duk aka saka a ciki to baya wuce kwanaki biyu ba'a harbe shi ba, na biyar...
Fito da ita nayi da kuma guduwarmu!
Na samu taimakon wata abokiyar aikunmu ne muka sato muk'ullin d'akin da aka kulle Maria cikin dare, daga nan muka bi ta wata hanya ta cikin k'arkashin k'asa da suka yi inda shima muka samo mukullinsa, matar nan ita ta taimake mu ta kulle k'ofar daga waje bayan mun shiga, amma duk da abinda ya faru da kyar na samu Maria ta yarda ta bini muka gadu daga wajen, tunaninta gabad'aya ya ta'allak'a ne cewa zamu tafi mu bar inda Ahmad zai dawo nemanta, don bata yarda cewa ya mutu ba har a sannan.
Allah ya taimake mu har muka yi kwanaki biyu muna tafiya cikin dajin da bamu san kansa ba sannan sojojin suka farga da guduwarmu suka bazama neman mu, mun gane hakan ne ta yawan harbin bindiga da muke ji a kusa damu da kuma hango motocinsu da muka fara yi a can nesa damu, a lokacin tunanimu ya tafi kan me yasa zasu tada hankalinsu don mu 'yan aiki biyu sun gudu kawai,
amma muka kasa sanin dalili.
Bama taba tsayawa a waje d'aya
kullum cikin tafiya muke sai idan mun samu ruwa a waje ne kawai muke d'an tsayawa mu huta gajiyarmu, ubangiji ya sani daga ni har Maria bamu yi tunanin zamu tsallake dajin nan ba tare da an kama mu ba, amma cikin sa'a sai gashi har muka isa wani k'aramin gari basu ganmu ba, anan muka zauna tsawon wata guda muna aiki a wani k'aramin gidan cin abinci, inda da kyar suka bamu wajen kwana cikin sitonsu.