Sashe 8
Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Asibiti ne ta tabbata kuma muryar farko ta Namijin nan tayi mata kama da Dr.
Gilbert, amma mamakinta shine me yasa ta tsinci damuwa irin wadda ta daina gani a wajensa? tayi zaton matsalarta tafi k'arfinsa da har ya daina d'orawa kansa damuwa akanta.
Ta biyun kuma tabbata Dr.
Florence ce, wata babbar likita da ba kowa ke iya ganinta a asibitin ba sai in har cutar mutum tayi k'arfi da yawa, kenan abinda ya faru da ita har yayi k'arfin da Dr.
Florence ce zata iya dubata?
Bata fahimci komai a cikin zancensu ba amma ta san dole ne bayan farkawarta tayi magana akan abinda ya same ta don haka dole ne ta shirya,
ta san amsar da zata bawa dukkan tambayoyin dake jiranta, tayi ajiyar zuciya a hankali, k'arar monitor d'in dake gefe ya shaida cewa yayi registering hakan.
Tsoro ya shige ta kad'an don ta san in har zata nemo abinda Dr.
Florence zata tambaya dole ne ta dawo da abinda ya faru cikin kanta, abinda ya sanya ta fita daga haiyacinta, tunaninta ya dulmiya cikin kanta, a
yanzu bata iya hasaso komai sosai, abinda ya faru na shirin b'acewa daga cikin kanta, kamar yadda mutum ke hasashen mafarki bayan ya farka.
Ta sake yin ajiyar zuciya a hankali... monitor dake gefe ya sake shaida cewa ya d'auki hakan.
Tunaninta ya nutsa cikin kanta, ta shiga lalube cikin
duk wani tunani daya tab'a zama a kanta, wad'anda ta sansu tun lokacin da sabuwar rayuwarta ta fara, komai daidai yake, komai yana nan kamar yadda ta san shi.
Sai dai daga can karshe ta lalubo wani sabon tunanin da bata san dashi ba, a cikinsa ta hangi wata yarinya tana tafiya cikin duhu, bata iya ganin fuskarta amma tana iya kwatanto gajiyar da take ji a lokacin don tayi tafiya mai nisa ta cikin duhun titunan dake bayanta, jikinta na rawa ta cikin cukurkudadden hijabinta.
Ta kasa gane wacece yarinyar da kuma inda ta ganta, a ina ta ganta da har zata shiga cikin tunaninta?kwakwalwarta ta shiga lalube amma tunaninta ya kasa nemo amsar hakan, ta sake tafiya wani b'angaren a cikin kanta amma sai ta daki bango.
Anan tunanin ya k'are kuma babu komai sai abinda ta wuce a baya, kamar ansa wani abu ne an goge sauransa don ta san ba nan ne k'arshe ba, kamar kwakwalwarta ta lalace ne daga nan.
Taji ranta na shirin b'aci, zuciyarta ta shi bugawa da k'arfi sannan hannayenta suka damk'e cikin tafinsu.
Monitor dake gefe ya nuna rahoton haka k'arara akan screen dinsa, a lokacin taji alamun taku na tahowa wajenta sannan muryar Dr.
Florence ta kira sunata a hankali.
Fadeelah.
****
"Kina buk'atar a kashe fitulun?" Dr.
Florence ta tambaya tana kallon yadda ta kasa bude idanunta sosai tun bayan lokacin da ta farka.
"A'ah a barsu, ina son hasken." Muryarta ta fito kai tsaye babu alamun wani ciwo ko rikicewa.
"Na san kinyi mamakin ganina a maimakon likitan da kika saba gani Dr.
Gilbert, ba wai hakan na nufin ciwonki yafi karfinsa bane, kawai ya d'an d'auki hutu ne ni kuma zan maye gurbinsa."
K'arya take, ciwona yafi k'arfinsa ne.
Fadeelah ta ayyana a ranta, wane hutu Dr.
Gilbert ya d'auka bayan yanzu ta gama jin muryarsa cike da damuwa anan? ta fadi hakan ne don kawai ta d'auke hankalinta kar ta damu akan abinda suke tunanin babban al'amari ne.
Bata san cewa rikicewar data tayi na farko ya wuce ba, kuma tunda ta bud'e idonta ta ayyana cewa hakan ba zai sake faruwa ba da ita ba.
Don irin wannan ciwon kan yafi duk wanda ta taba fuskanta a baya shi yasa ta kasa tsaida rikicewarta, amma kamar yadda suka fad'a ne, a baya ta karb'i ciwonta da hannu biyu ta tallafi kanta, a yanzu kuma data fahimci ciwon nata na sake k'aruwa ne zata gayawa b'arin kwakwalwarta mai lafiya haka, ba zata sake yarda ciwon yayi galaba a kanta ba, ta daure a baya kuma zata daure ma yanzu, zata daure ta fuskanci dukkan matsalolinta a yadda rayuwa ta kawo mata, ita ba mai rauni bace!
"Na fahimta." Ta amsawa likitar tunda ta nuna alamun tana jiran amsarta ne.
Sai ta gyada kanta sannan tace.
"Na san zaiyi miki wuya ki tuna abinda ya faru dake a kwanakin baya, amma..."
Kalmar kwanakin baya ta d'auki hankalinta.
"Kwana na nawa anan?" Cikin sauri ta katse ta.
"Kwananki uku kawai cikin kulawar da kwakwalwarki ke buk'ata, kuma da alama'yanuwanki na mutuk'ar sonki, don duk da mun hana kowa ganinki basu daina sintiri zuwa da kuma jero addu'oinsu ba."
Ta k'arasa tana kallon gefe, Fadeelah tabi idanunta da kallo, ganinta ya sauka akan wani d'an k'aramin table dake cike taf da tarin flowers da kuma katina masu d'auke da rubutun addu'a da fatan samun sauk'i, a gefen wani mai rubuce da sunan Iman ta hango, akwai na kawayenta ma Romilda da Melissa daga gefe, sai sauran data san bayan 'yan gidansu na tarin 'yan uwan Daddy ne.
"So muna magana..." Dr.
Florence ta katse ta, ta juyo ta kalle ta.
"...
In akwai wani abu da zaki iya fad'a min na abinda kika tuna zai taimaka sosai wajen bamu sanin ainihin abinda ya same ki."
Jin cewa har a lokacin basu san ainihin abinda ya same ta ba yasa ta ture tunanin 'yan uwanta a gefe.
"Bana tuna komai banda irin azababben ciwon da naji a cikin kaina."
"Na fahimci hakan, zaki iya gaya min me kike yi kafin farawar ciwon?"
Ta rufe idonta a hankali.
"Muna zaune da k'anwata ne a lokacin, tana gaya min wani labari data karanta daya dangaci k'asarmu Nigeria, ta fada min cewa sunan yarinyar ciki BINTU, a lokacin sai naji sunan kamar a irin mafarkaina yake, kamar na sanshi ne a wani wajen daban, wajen k'okarin tuna inda na san sunan sai ciwon ya fara."
"Fadeelah..." Dr.
Florence Ta kira sunanta da kyar cikin murd'adden turancinta.
"Bari mu koma baya kad'an game da ciwon ki, kin samu matsalar kwakwalwa dalilin wani abu daya faru dake a baya, bamu san me ya faru ba saboda ba zaki iya tunawa ba amma muna hasashen kin samu damewar kwakwalwa ne ta hanyar buguwar kai, wanda ya haddasa miki ciwon 'Retrograde amnesia.'
Kalar Amnesia data saka kika manta rayuwar data faru dake kafin faruwar ciwon, tunaninki na baya duk ya mutu, sai sababbi kawai kike iya rik'ewa, I'm i right? kina sane da hakan?"
Fadeelah ta d'aga kanta ba tare da ta kalleta ba.
Zancenta ya nuna mata ta karanci file d'inta ne tas! koma ta haddace shi.
"Kuma bayan anyi haka kwakwalwarki tana hargitsewa a wani lokacin ki manta komai na kewayenki, haka ne?"
Ta sake gyad'a kanta.
"Amma cikin shekara d'aya, sanda kika fara zuwa wajen Dr.
Gilbert ciwonki yayi sauki, abubuwa sun fara daidaita har kin shiga makaranta rayuwarki ta fara tafiya cikin tsari.
A watannin baya kuma sai kika fara mafarkai masu yawa da tsoratarwa, murya da siffofin mutane na binki suna maganar da ba kya iya ganewa.
Haka ne?"
Maimakon ta amsa sai ta kalli yatsunta tace.
"A lokacin Dr.
Gilbert yace gajiyar makaranta da kuma yawan karatun dake shiga kwakwalwata ne suka jawo min ba wani abu ba, amma daga sanda na fara mafarkan nan, kwakwalwarta da duk wani abu mai hankali a jikina ya bani alamar cewa wani babban al'amari ne ke shirin faruwa dani."
"Tabbas hakan ne." Dr.
Florence ta fad'a kamar mai k'arashe mata zancen, sai kuma ta d'anyi shiru zuwa wani lokaci kafin ta sake magana.
"Yanzu ina son kiyi k'ok'arin tuna wani abu game da mafarkanki na baya, ina son ki bincika cikin muryoyin nan na mafarkinki ki gani zaki iya tsinto wani abu da suke cewa... ko meye kuwa, ko bashi da ma'ana zai zama shirme a bakinki just say it, ni zan nemo ma'anarsa."
Kin kashe ta!
Kalaman mafarkin da tayi na k'arshe
suka amsa rangadadau a cikin kanta, a baya ta b'oyewa Dr.
Gilbert don tana ganin hakan babban abu ne amma a yanzu da abubuwa suke cakud'ewa dole ne ta hak'ura ta yaye shi, dole ne ta fad'awa Dr.
Florence don a yanzu ta yarda cewa a irin ciwonta babu wani abu wai shi Sirri.
Ta d'ago a hankali ta kalli likitar da yanayin fuskarta ya nuna alamun jiran amsa.
"Mafarkin da nayi na k'arshe akwai wata murya dana tsinci tana cewa na kashe wata a yayin da nake gudun."
Ta fad'a kamar wadda aka tursasa ta fad'i kalaman.
Dr.
Florence ta kamo hannunta a hankali cikin sigar jan hankalinta.
"Fadeelah zan gaya miki wani abu da yake gaskiya kuma wani abu da kowa muke gayawa ba sai irin wad'anda suka karaso matakinki...
Dr.
Gilbert ya taba fad'a miki cewa ciwonki ba mai d'orewa bane koh? ya gaya miki cewa akwai lokacin da kwakwalwarki zata warke har ki iya tuna wacece ke a baya koh?
Ta gyada kanta tana saurare.
"Toh zan gaya miki gaskiya a yanzu, ciwon irin na damewar kwakwalwa bashi da wani takamaimai magani duk duniyar nan... bau wata kwaya da za'a baki ya zama rana d'aya kin tashi kin warke.
A baya sanda kika fara zuwa asibitin nan, treatment d'inki yana tafiya ne akan kokarin tallafar kwakwalwarki a saita ta ta karb'i sabuwar rayuwar dake kewayenki, kuma hankali muka samu akayi yi sa'ar hakan.
A yanzu kuma da kwakwalwar take jin alamun cewa ta daidaita kanta sai wani b'angarenta ya fara kokarin tattaro abubuwan da suka faru dake a baya da ciwon naki ya k'ulle.
Don haka a yanzu kina wani mataki ne da ake kira 'Memory Retrival'.
Daga yanzu kwakwalwarki zata dinga d'aukan duk wani abu da zaki ci karo dashi wanda kika sanshi a rayuwarki ta baya, kuma a matakin farko na Memory retival akwai 'Creative Reimagination, wanda shine abinda kika fara experiencing a yanzu.
Shi yana faruwa ne a lokacin da tunanin baya ya had'e dana zahiri, shine halin da kwakwalwa ke fara shiga kafin ta iya sanin yadda zata banbance abinda ya faru a bayan da kuma sabo da ya shiga cikinta, Sai abubuwa da yawa su cakud'e waje d'aya su fidda wani abu daban da zai iya shallake tunanin d'an adam.