Sashe 18
Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shima ya d'ago da kansa jin an bud'e k'ofa, yana sanye cikin wata doguwar jacket light brown da gashinsa cikin wani style kamar an barbaza shi wajen goshinsa, k'arya zata yiwa kanta in har tace bai yi kyau ba.
Ya k'ifta idonsa a hankali kafin yace.
"Kin kyauta yau da baki makara ba."
Ya salam! taji kamar ya rad'a mata maganar a cikin kunnenta ne saboda yadda muryar ta fito cike da laziness.
"Bani da lokacin b'atawa yau, idan har ka san zaka sake cewa sai gobe ne, ka fad'a min tun yanzu in juya."
Kamar bai jita ba sai ya turo leda d'aya gaban teburin.
"Kizo ki duba, ina ga kamar na siyo komai daidai, in kuma akwai abinda baiyi ba gobe sai a sake siyowa."
Ba yadda ta iya, haka ta k'araso ciki zuciyarta cike da mamakin me ya siyo, Ledar farko data fara bud'ewa kayan painting ne na kaloli da kuma brushes d'in shafawarsu, ta biyu kuma tarin tarkace ne fal da suka tabbatar mata da abinda kwakwalwarta ke tunani... abubuwan da take so ne gabad'aya a cikin ledar! ma'ana duk abubuwan da suka shafi hobbies d'inta wanda ta rubuta masa jiya.
Ta shiga fiddo su d'aya bayan d'aya zuciyarta na juyawa cike da mamaki, har zuwa kan wata hadaddiyar MP3 dake d'auke da complete karatun alqur'ani... ta tuna cewar ta rubuta harda sauraren alk'ur'ani don hakan ma ya dad'a k'ona ransa, sai gashi da hannunsa yaje ya siyo ya kawo mata.
Ta kasa daure mamakin don haka sai ta d'ago ta kalle shi, ya sake lumshe idonsa kad'an sannan ya gyad'a mata kai.
"Yau zamu fara Maths, ta hanyar da kwakwalwarki zata karb'e shi."
Ya lura bakinta ya k'ulle gabad'aya, ta rasa me zata ce ko kuma abinda ya kamata tace d'in.
A daidai wannan lokacin ne kuma wayarsa tayi k'ara, ganin number dake kira yasa ya mik'e da sauri ya nufi can d'aya b'arin library d'in, wajen da dogwayen durowuyin littattafai ke jere.
"Barka da aiki yallab'ai." Ya fad'a muryarsa cike da girmamawa.
Daga d'aya b'angaren wayar aka amsa.
"Barka dai Adam, komai lafiya?"
"Lafiya k'alau, komai yana tafiya daidai."
"Babu wani suspect?"
"Babu ranka ya dad'e daga malaman har d'aliban babu mai zargin wani abu har yanzu."
Da alamun gamsuwa a muryarsa ya sake tambaya.
"Ka kusa gamawa?"
"Duk da ya amince dani a yanzu, wasu abubuwan baya sakin jiki akansu sosai, amma dai a yanzu ma akwai evidence da yawa."
"That's good, kuma babu wata matsala data k'aru?"
Wannan maganar tasa ya juya a hankali ya kalli Fadeelah dake tsaye tana ta juya kayayyakin nan
har yanzu, bayanta kawai yake iya gani daga nan, amma zuciyarsa na iya karanto labarin kan fuskarta, musamman daga cikin wad'annan idanun nata...
Sai ya girgiza kansa kawai, ita d'in kamar nauyinsa ce a yanzu ba zai tab'a sanyata cikin lissafinsu ba.
A hankali muryarsa mai taushi tace.
"Babu wata matasala ranka ya dad'e, kuma ina k'okarin kare duk wata hanya da zata fito da cewar ni LAWYER ne!"
BAYAN NA MUTU!
AYSHA SHAFI'EE
"Mu fara?"
Muryarsa ta tambaya bayan ya dawo daga wayar daya amsa.
Ta juyo da idonta t
a kalle shi, me yasa ne wai yau yayi kyau a idanunta?
Har yanzu bakinta ya k'ulle ta rasa me zata ce, don haka sai ta d'aga kanta kawai sanda yaja kujerarsa ya zauna, tana shirin zama a ta gabanta ya tsaida ita ta hanyar d'ago mata zara-zaran yatsun hannunsa.
"Wane irin lenses kike amfani da shi a glass d'inki?"
"Aspheric."
Ya gyad'a kansa a hankali.
"Yana nuna rubutu a juye ne?"
"Kamar yaya?"
"Ina nufin idan nayi rubutu anan, zaki ganshi a daidai daga nan?"
Ta gane me yake nufi amma bata da niyyar magana saboda haka ya nuna mata kujerar dake gefe da d'an allinsa, wadda dama kamar ya tanade ta ne saboda ita.
Bayan d'an gajeren tunani taga cewa bata da zab'i saboda haka ta saki kujerar ta zagayo a hankali ta zauna a gefensa.
Sassanyan k'amshin turerensa kuwa ya nemi k'ofofin hancinta yayi masauki, sai ta runtse idonta kad'an jin k'amshin da kwakwalwarta ta yiwa tambari da NASA.
Ya jawo ledar farko mai d'auke da kalolin zane, ya b'are su daga cikin ledojinsu sannan ya d'auko wata farar cardboard paper a gefe.
"Abu na farko da kika fara rubutawa jiya shine kina son zane (painting), don haka dashi zamu fara."
Yanzu da take kusa dashi, sai taji kamar ya lalubi kunnenta ne yana rad'a mata maganar, saboda haka sai ta karkatar da kanta kad'an.
Ya bud'e robobin kaloli guda goma sha biyu.
"Daga 0 zuwa 9, kowacce number zan zana ta da kala daban, sai ki rik'e kalolinsu yadda idan muka fara amsa tambayoyin, kwakwalwarki zata karbi kowacce number da irin kalarta, za'a samu saukin hargitsewarta wajen gane nambobin."
Bata ce komai ba ya cigaba.
"0 - green, 1- blue, 2 - orange, 3- yellow, 4- red, 5-...."
"Kayi d'aga muryarka bana ji sosai."
Ta katse shi.
Ya juyo a hankali ya kalleta.
"I'm sorry haka muryana yake, ina damunki ne?"
Kamar yaya yana damunta? yana tunanin muryarsa tana da wani tasiri akanta ne?
Ta girgiza kanta da sauri.
"Ta yaya zaka dame ni, ka cigaba kawai ina jinka."
Bayan ya juya tasa yatsanta d'aya ta k'asan glass d'inta, ta duba kwarmin idonta da tunanin ko kwantsa ya gani a ciki, don ta lura duk sanda zai kalle ta cikin idonta sosai yake kalla kamar mai son lalubo wani abu nasa da ya tab'a rasawa.
Da wata tambaya guda d'aya a topic na farko 'Pythagoras' suka fara, kamar wasa ko wani abu ma majigi, sai gashi
a hankali Fadeelah ta fara gane abinda yake yi, saboda yadda yake bin kowanne step na lissafin daki-daki cikin rubutunsa mai tsananin kyau da kuma yadda raunanniyar muryarsa ma ke mata bayanin kamar ana zirara ruwa cikin roba a hankali.
Sannan dad'in dad'awa da taimakon yadda kowacce number ke fitowa cikin nau'in kalarta daban, sanda suka gama tambaya ta farko sai yayi kama da draft d'in zane, ta dinga gani a idanunta yadda zata ja kowacce kala zuwa 'yaruwarta har su had'u su fitar da wani hoton.
Lissafin da ake yinsa a aji tana ganinsa kamar wani tashin duniya sai ya zama kamar d'an uwan zanenta a yanzu har taji ta k'agu a tafi wata tambayar don ta samu a sake fitar da wani abun.
Wasa-wasa, a cikin awa guda kawai sai ta suka amsa tambayoyi hud'u, wanda babu wanda bata fahimta ba a cikinsu, Allah ya sani kwarai ta jinjina masa yadda ya iya mata bayanin cikin nutsuwa, sai yanzu ta fahimci zancensa da yace zasu iya gama gabad'aya topics d'in cikin lokaci.
A wannan daren bayan ta gama dukkan harkokinta na ranar, tayi sallah sannan tayi wanka, ta saka wata 'yar k'aramar riga armless iya gwiwa, sannan ta d'ago cardboard paper da ta amsa question guda d'aya da yace in ta koma gida tayi, rana ta farko a rayuwarta data amsa lissafin Maths kuma tayi daidai, don ya rubuta mata final answer a bayan paper yace in har tayi daidai amsar da zata samu kenan, kuma bayan ta dawo gidan ta kasa ko cin abinci sai da ta zauna tayi, haka tayi ta zagaye gidan da murna
rik'e da paper su Mami ma na taya ta.
Ta rufe idonta a hankali, sanda fuskarsa ta ranar ta haska a cikin su, tana son kalar brown sosai watakila shi yasa shigarsa ta yau tayi mata kyan da har ta kasa manta ta.
Ta hango yadda gashin idonsa ke kwantawa akan na k'asansa duk sanda yake rubutu, sai kaga kamar ya rufe idon ne gabad'aya.
Me ya same ta ne wai? ya kamata tayi wa kanta fad'a, Adam d'in data tsana kamar me shine tun ba'a je koina ba take b'ata lokacinta wajen tunaninsa? don kawai ya koya mata maths ta gane? wannan ma ai shirme ne.
Ta ja tsaki a hankali sannan ta ninke paper ta ta ajiye akan bedside drawer, daidai sanda wayarta dake gefe tayi haske alamun shigowar message.
Memory loss girl kin kwanta?
Ta karanta sak'on da muryar Al'ameen kamar yadda number ta nuna shi ya aiko, a cikin kwana biyu ta fara sabawa da Al'ameen sosai ta hanyar chatting d'in da ta koya ta dalilinsa, don kullum zai aiko mata da text lokacin da zata kwanta wani lokacin ma har da safe kafin tafiyarta makaranta, sai dai bai k'ara zuwa ba don kullum yana gaya mata abubuwan sun masa yawa, don harkar settling d'insu a garin da komai yana hannunsa.
Da murmushi a fuskarta hannayenta suka rubuta.
Beeem!
Wani sak'on ya shigo a take.
Thank god ban tashe ki ba, kin yini lpya?
Lafiya k'alau.
And you?
Dama baki tambaya ba, don nasha wahala sosai yau, in na fara gaya miki zaki tausaya min.
Ta sake wani murmushi sannan ta rubuta.
Me kayi?
Intrested? ya tambaya.
Yes.
Ta tura sak'on da ya haddasa doguwar hira a tsakaninsu, doguwar hirar data shafe ta kuma wanke tunanin Adam a kanta!
Adam ya rufe idonsa a hankali yana hasko nata daga ciki, idanun dake hana masa sukuni a kowacce bullowar rana zuwa fad'uwarta, musamman a kowanne dare lokacin da zai zo kwanciya.
Ya lullub'e jikinsa da bargo baki d'aya kamar hakan ne zai hana shi tunanin idanun nata kafin bacci ya d'auke shi.
A baya inda zai karanta cewa wani abu zai zo ya dami kwakwalwarsa bayan burin da yake dashi, zai k'aryata koma meye ne kuma yayi sanadin dakatar dashi.
Sai dai sanin gaibu baya hannun d'an adam, a yanzu ya tabbata koda wani zai kawo masa hanyar da zai cire tunaninta daga kansa ba zai tab'a karb'a ba, don watak'ila ya saba koma yana jin dad'in hakan.
A hankali tunaninsa ya gangara can baya zuwa wani lokaci baya kad'an...
*WANI LOKACI BAYA KAD'AN.*
K'arfe takwas da rabi na safiyar ranar talata, had'addiyar motarsa tayi parking cikin jerin gwanon motocin dake harabar ma'aikatar kotun.