← Book details Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 95

Sashe 32

Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

In ya yarda me yasa bayan zuwansa kuma zai cigaba da kula dake?"
"Ba fa kula ni yake ba, tunda yazo ko gaisawa ba mayi, kawai dai ranar da bani da lafiya ne muka yi magana daga nan kuma muke gaisawa."
"Ba dai kuna gaisawa ba, saka ranki a ruwan sanyi, ni zan gaya miki hanyar da zaki bi yanzu ki tattaro hankalinsa kanki gabad'aya, yadda ko ita mahaifiyar tasa sai ya manta da lamarinta."
Mamaki ya kama Fadeelah ta zare ido tana kallonta.

"Anya Fatima Psiotherapy kuwa kike karantawa a makaranta?"
"Ke bar wannan zancen, yanzu bari mu fara tsara yadda zamu rik'e d'an bak'on balarabenku."
Gefen zuciyarta na farko yayi na'am da hakan, yayin da d'aya gefen ke gaya mata cewar in har ta amince da neman soyayyar Al'ameen, Adam fa? meye matsayin tunaninsa a ranta?

Adam fa?

Ta sake maimatawa kanta a ranar lokacin da tazo kwanciya.

A D A M
Wani farin dattijo dake zaune daga tsallaken teburin ya kalle shi cike da tsananin damuwa da kulawa yace.

"Ya kamata ka gaya mana sauran kwanakin da suka rage maka a duniya don mu fara shirin jana'izarka."
Ya tsaya cak! da rubutun da yake yi sannan ya d'ago ya kalle shi.

"Dama mutum yana sanin ranar da zai mutu ne?"
Ya tambaya da muryarsa mai fitowa kamar auduga saboda taushi.

"Abinda nake son in tambaye ka kenan, don naga kamar kai ka tsara taka mutuwar."
Ya tsuke baki kad'an sannan ya ajiye biron hannusa.

"Har yaushe zamu daina zancen nan ne wai?"
"Har zuwa lokacin da zaka ajiye komai, ka hak'ura ka dawo rayuwarka ta baya."
Sai ya koma da baya ya kwanta a kujerar da yake zaune yayin da dattijon ya cigaba da biya abinda shi dashi suka riga suka haddace.

"A shekara guda kawai ka fita daga haiyacinka, kammanninka sun canja,
ka daina komai banda aiki, awa ashirin da hud'u kullum cikin rubuce-rubuce kake, mu kanmu mun daina samun lokacinka, in ba yanzu da za'ayi gyara aka koro ka daga offfice d'inka ba ka gaya min yaushe rabon daka zauna a gida irin wannan lokacin?"
Adam yayi ajiyar zuciya a hankali sannan ya tura duka hannayensa cikin lallausan gashin kansa, yatsun suka nutse a ciki kafin ya lumshe idonsa.

"Abinda kake yi ko kad'an babu daidai a cikinsa, na san cewa munyi maka laifi mun b'oye abinda ya shafi rayuwarka, amma bai kamata ace ka dauki wannan hanyar ba, ka daina walwala da nishadi gabad'aya, bama ka da hanyar yin tunda ka rabu da abokanka tun farkon fara aikinka, ka d'auki damuwa ka d'orawa kanka akan abinda bai zama tashin hankali ba sannan ka hana mu sanin halin da kake ciki,
kana cutar damu kana cutar da kanka akan abinda ya riga ya wuce."
Abinda ya riga ya wuce! haka suke gani, shi yasa a kodayaushe suke binsa da maganganun da baza su tab'a tasiri akansa, sun manta cewa idan ya saita zuciyarsa akan abu guda to duk duniya babu wanda ya isa ya canja masa shi sai k'addara.

Kamar yadda a yanzu k'addarar ta canja masa tsari da kuma tanadinsa gabad'aya, ta tankwab'e guntuwar hanyar da yayi tanadin gyara rayuwarsa da ita,
ba zai taba manta ranar nan da hakan ya faru ba.

Bayan ya kammala case d'in malamin nan ne ya samu damar hutu na shekara guda kamar yadda shugabansu yayi masa alkawari, saboda haka ya gama duk wasu shirye-shiryensa ya sayi tikitin tafiya k'asar Ingila wajen Magareth don samun amsoshin da ya dade yana mafarki game da mahaifansa na asali, bai ko shaidawa iyayensa na nan ba yace dasu ne kawai zaiyi tafiya, kuma duk raunin alak'arsu a lokacin basu zargi komai ba don a lokacin suna ta kan kokarin yadda zasu wanke kansu ne a wajensa.

Ya shirya ya kuma tsara komai sannan zuciyarsa ma ta riga shi tashi
zuwa can, mafarkinsa da tunaninsa gabad'aya a lokacin ya koma na yadda yake hasko kansa a gaban Magareth kawai tana shaida masa komai dalla-dalla game da iyayensa na asali, sai dai ana gobe tashin jirginsa ne komai d'in ya rushe,
wata mata mai zak'in murya ta kira shi da nambar wayar gidan tsofaffin inda Magareth d'in take, ta shaida masa cewa tsohuwar ta mutu a safiyar ranar, don haka ya taimaka yazo jana'izarta sannan ya karb'i ragowar dukiyarta da suke d'iba wajen kula da ita, don suna ganin shi kad'ai ne d'anuwanta.

Kamar yadda kofin tangaran zai fad'o daga sama ya daki dandaryar siminti ya tarwatse haka tunani da kuma zuciyarsa suka yi a ranar nan, yaji komai ya tsaya masa cak!

Sannan komai yayi masa nisan da ba zai iya tattaro b'antarorinsu ya had'a waje d'aya ba, Uwar wahalar da yasha a shekarun baya tsakaninsa da gidan marayun da iyayensa suka karb'oshi da kuma ma'aikatu da asibitoci kafin ya iya samo sunan Magareth a matsayin wadda ta san ainihin mahaifiyarsa ta dinga nunawa tar cikin idonsa, ashe duk wannan fafutukar yayi tane kan abinda ba za
i masa amfani ba.

Duniyarsa ta hargitse,
kamar yadda ta yaro k'arami keyi a lokacin da ya siyo alawar da ya dad'e yana mafarki bayan lasa d'aya kawai ta fad'a cikin kwatami!

Tsawon wata guda a gida, ba irin k'okari da nacin da iyayensa basu yi ba amma ya daina komai, sai a rana d'aya kawai ya tashi koma office, ya soke hutunsa sannan ya karbi tarin ayyuka yasa hannu akai, wani abu da ya dad'a janyo masa k'iyayya daga masu adawa dashi a wajen aiki kenan, sannan kuma abinda ya dad'a janyo d'aukakar sunansa a wajen manyansu dama mutanen cikin gari da a da basu sanshi ba, yayi suna a garin washington da kewayensa, hatta makarantar da yayi aikin b'ad da kama sai da suka shirya masa taro na jinjina da kyaututtuka na yadda ya zauna cikinsu a matsayin d'alibi mai tashe ba tare da ko mutum d'aya ya san ainihin shi waye ba.

A hankali ya k'ara yin baya da kansa ya kwanta a kujerar, a wannan ranar Allah kad'ai ya san sau nawa yaga idon leelah ya masa gizo a cikin tarin d'aliban, idonta da ya riga ya zama wani b'angare na rayuwarsa a yanzu don tare dashi ya shiga cikin duk wata gwagwarmaya kuma ya fito, duk irin d'imbin aikin dake gabansa,
k'aryane a kowacce rana yazo kwanciya bai ga giftawarsu a nasa idon ba.

A ranar da akayi taron ya nemi k'awayenta kamar kwabon daya rasa amma matsalar shine ya manta sunayensu kuma bai san ta yaya zai banbance su cikin tarin d'aliban dake ta washe masa baki suna son d'aukan hoto dashi ba, Mr.

Hawkins kawai ya tambaya shima kuma ya gaya masa abinda ya riga ya sani cewa ta bar k'asar tare da 'yan gidansu, kuma kamar wancan karon bai tambayi sunan k'asar ba, don baiga amfanin hakan ba.

"Wannan ba rayuwarka bace Adam.."
Muryar dattijon nan ta katse tunaninsa, bai sani ba ko tun d'azu yake magana don in yana irin wannan tunanin baya fahimtar komai dake gabansa.

"...bamu zauna da kai tsawon shekarun nan don ka girma ka zama haka ba,
ko bamu haife ka ba ak'alla mun raineka ta hanyar da zaka bamu girman da muke..."
"Steve!

An kawo maka sak'o."
Muryar matar dake amsa sunan mahaifiyarsa ta kira daga can bakin kofar falon gidan,
hakan yasa Adam ya bud'e idonsa a hankali ya kalle shi.

"Na san cewa akwai abinda kake tsarawa a cikin kanka, dole duk wannan abinda kake yi yana da dalili,
na sanka..."
"Steve!

Yana buk'atar sa hannunka."
Muryarta ta sake katse shi, sai yaja guntun tsaki kafin ya mik'e ya nufi cikin falon,
daga inda Adam ke zaune,
yana hangota tsaye cikin shigar riga da wando dogon gashinta na reto a kowanne gefen kafad'unta yayin da mutumin daya kawo sak'on ke tsaye daga waje cikin uniform dinsa rik'e da wani k'aton kwali.

Kafin yayi wani tunani wayarsa da ta fad'i can k'asan wasu takrdu ta shiga ruri alamun shigowar kira, ya mik'a hannunsa ya d'auko ta, number sabuwar sakatariyar da aka bashi kwanan nan ce ta nuna akan screen d'in, saboda haka babu tantama ya amsa don ya san zancen aiki ne...

Sai dai abinda ta fad'a ya zama sab'anin tunaninsa.

"Yallab'ai na samu kira d'azu daga wata ma'aikatar kula da tsofaffi ta garin Leicestar a k'asar England, wai suna nemanka ne akan wani abu mai muhimmanci suna son in basu number wayarka ko adireshin email."
Ya rufe idonsa kad'an ya bud'e,
ya san zancen ba zai wuce na yazo ya karbi ragowar dukiyar Magareth da suke ta naci ba,
kamar yace mata ta rabu dasu sai kuma kalmar 'abu mai muhimmanci' ta d'auki hankalinsa,
saboda haka a gajarce yace.

"Ki tura musu da adireshin email d'in."
Ya rabu da layin da yake kiransu tun a da,
in suka san na yanzu zasu takura masa ne akan abinda ba zai taba zuwa ya karba ba,
tunda a baya yayi musu bayani amma sun kasa yarda cewa shi ba d'anuwanta bane hasali ma bai tab'aganinta ba ko a hoto.

Mintuna kad'an bayan hakan, shigowar sabon sak'o ya nuna akan computer da yake aiki da ita, ya riga ya san ko daga ina ne saboda haka bai bi ta kansa ba sai bayan awanni biyu daya kammala had'a evidence d'in da yake kan yi.

Ilai kuwa yana dubawa yaga wata doguwar wasik'a ce daga can gidan kula da tsofaffin.

A hankali ya koma baya kan kujerarsa sannan ya shiga jan idanunsa kan rubutun.

Dear Mr.

Steve
Bayan binciken da muka shafe muna yi akanka na tsawon shekara guda,
mun yarda cewa baka da alak'a da Magareth Whitford, kuma mun gode da baka karb'i dukiyarta ba.

Sannan muna farin cikin sanar da kai cewa abinda ka dad'e kana nema ya samu a yanzu, mun san cewa duk duk sanda ka kira waya kana neman Magareth ne da zummar son sanin wani abu game da iyayenka, to a farkon watan da ya wuce ne d'aya daga cikin ma'aikatanmu ta binciko wata tsohuwar wasika a cikin kayan marigayiyar, wadda aka buga ta da sunanka tun shekaru goma da suka wuce.
Chapter 32 · 0% Book details