Sashe 79
Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ya mai girma mai shari'a, zanso in gabatarwa da kotu Maryam Idris Musa, wadda aka fi sani da Anna."
Idanun kowa ya juya kan k'ofar shigowa sanda aka shigo da Anna wadda take a tsaftace sab'anin yadda 'yan babban gida suka santa, sanye cikin dogon hijabinta.
A cikin 'yan sakanni kawai Adam ya tuno irin wahalar da ya sha kafin ya samu Anna ta bishi su tafi Asibiti, daga k'arshe sai da aka had'a da matar Kawu Ibrahim da kuma yayar Bintu wanda suka rik'eta har zuwa asibitin, inda bayan an gama bincikar ta ne kuma suka kaita wajen gyaran jiki aka tsaftace ta, sai bayan nan sannan ya sami zantawa da ita, a lokacin ya dawo daga police station wajen SULE.
Jabir ya sake mik'ewa ya kawo masa wani file, shi kuma ya k'arasa ya sake bawa wannan ma'aikacin da ya tashi yaje ya mik'awa Alkalin.
"Ya mai shari'ah wannan sakamakon gwaji ne daga kwararren asibitin gwamnati, munje tare da wakilin da aka bamu daga wannan kotun inda aka auna kwakwalwar Maryam kuma aka tabbatar cewa babu ciwo a cikin kwakwalwarta kamar yadda result d'in yake nunawa.
Ta sami matalar shafar Aljanu kawai tun lokacin aurenta na farko wanda har hakan ya hana ta zaman auren, mutane suna yi mata kallon mara hankali ne sakamakon rashin kulawa data samu bayan ta dawo gida, amma kamar yadda sakamako ya nuna lafiyarta k'alau kawai tana da matsalar saka shirme a zancenta ne saboda shafar aljanun amma mun sami gamsassun bayanai daga wajenta.
Idan kotu ta amince zan so ta tsaya a matsayin shaidata ta gaba."
Bayan wasu 'yan mintuna Alkalin ya gama karanta dukkan results d'in dake cikin file d'in ya d'ago ya kalle shi.
"Maryam Idris zata iya tsayawa a matsayin shaida."
Adam ya gyada kansa alamun godiya sannan ya juya ga Anna wadda aka gama rantsar da ita.
Sanin halinta da yadda ya sami amsa daga wajenta a jiya yasa kai tsaye ya tambaye ta.
"Me kika sani game da shari'ar nan?"
Anna ta girgiza kai tana kallonsa.
"Ni babu abinda na sani game da shari'ar nan, babu wanda yake fad'a min me ake ciki, na gaya maka hakan tun ranar da ka tambayeni, ko ka manta ne d'an bature?"
Da yawan mazauna wajen suka murmusa jin sunan da ta kira shi, Adam ya girgiza kansa muryarsa a hankali yace.
"Ban manta ba na sake tambayarki ne kawai ko kin samu wani abin."
"Ban san komai ba..." Tana magana tana yin alama da hannayenta.
".... iya hirar Sule da mahaifiyarsa da na gaya maka tun wancan lokacin ita kawai na sani."
"Ko zaki iya yiwa kotu bayani kamar yadda kika yi min?"
Ta d'aga kanta.
"Me zai hana?
Ai dole ne ma in fad'a."
Sai ta juya ta kalli Alkalin.
"Zan fad'a maka komai yanzun nan kotu, shekaru 'yan kad'an da suka wuce kafin Hajiya ta rasu ku fara wannan shari'ar, Yaya Danjuma ya bani wani d'aki a jikin katangar b'angarensu Sule, to ina nan zaune a ciki kullum, sai wani gefe na d'akin ya rufta har ina iya lek'o d'akin mahaifiyar Sule daga nan, kuma kullum ina jin zancenta dana 'ya'yanta.
Amma zancen dana fi ji shine in Sule ya shigo wajenta sai tayi ta masa fad'a tana cewa ya zama bawa a Babban gida, yana ganin kowa yana da abinyi amma shi yana zaune kawai ya kasa magana a basu gadonsu suma su sami kud'i, shi kuma yace mata ai ba zai iya bijirewa umarnin Hajiya ba, kullum-kullum suke ta yin wannan zancen har Hajiya tazo ta mutu..."
Sai ta had'e tafukan hannayenta biyu ta kwanta akansu alamun bacci.
Adam ya juyo daga wajenta ya kalli Alkali yace.
"Ya mai girma mai shari'ah, Tun a farko munji daga shaida ta biyu cewa mahaifin Sule ya rasu amma Hajiya ta hana a raba musu gado kuma saboda irin biyayyar da yake mata baice komai.
Idan muka yi la'akari da wannan bayanin zamu ga cewa bayan anyi hakan mahaifiyarsa ta shiga tursasa shi cewa bai kamata ya yarda da hakan ba."
Yana gama fad'in haka ya juya wajen Kutama ya bashi izinin nasa tambayoyi, amma ga mamakin kowa sai ya girgiza kansa kawai alamun bashi da tambaya akanta.
Ya yarda cewa a wannan gab'ar, babu wani abu da kokarinsa zai canja, Adam ya riga ya tunkari shari'ar baki d'ayanta ba tare da wani kewaye-kewaye ba irin nasa kuma yana baiyana komai ne a ainihin gaskiyarsa, don haka kudirin daya dauka a baya nana ganin ya toshe duk wata hanyar samun nasararsu ba zai tab'a tabbata ba, a yanzu haka ma shi ba ta wannan shari'ar yake ba, tunaninsa hange kawai yake na yadda zai kare tauraruwarsa daga dusashewa.
Adam ya d'anyi shiru sanda ya lura da rubutun da Alkalin yake yi, bai sake cewa komai ba har ya sai da ya k'arasa ya d'ago ya kalle shi sannan yayi magana.
"Ina neman kotu ta bani damar kiran shaidata ta k'arshe."
Babu shiri Kutama ya had'iye yawu cikin mak'ogwaronsa yayin da Alkalin ya zare gilashinsa ya kare masa kallo daga inda yake zaune.
"Shaida ta k'arshe? kana nufin daga wannan shaidar ka rufe shari'ar daga b'angarenka?"
Adam ya gyad'a kai gami da lumshe ido.
"Haka nake nufi ya mai shari'ah."
Sai ya maida gilashinsa sannan ya ware hannunsa a iska.
"Kotu ta baka dama."
Ya amsa hakan ta hanyar cewa.
"Zanso in kira Sulaiman Muhammad Idris a matsayin shaida ta ta k'arshe."
Babu b'ata lokaci kuwa aka shigo da Sulaiman wanda kowa yafi sani da SULE cikin wajen, biye dashi d'ansanda d'aya ne wanda ke nuna cewa a hannun hukuma yake, idanunsa sunyi zuru-zuru alamun tashin hankalin k'arara a cikinsu, kuma kamar yadda idanun suke haka ma muryarsa ke fita sanda ake rantsar dashi.
"Ina so ka yiwa kotu bayanin abinda ya faru bayan rasuwar mahaifinka."
Wannan itace tambayar da Adam yayi masa bayan ya gama amsa dukkan wasu tambayoyin da suka shaida matsayinsa a cikin zuri'ar da kuma irin alak'arsa da Hajiya Balaraba.
Sai ya kawar da kansa ga barin kallon 'yan Babban gida, tun daga ranar da mahaifiyarsa ta fad'i ta mutu yake jiran wannan ranar, ya riga ya san zata zo kamar yadda yake kwana da sanin cewa ranar mutuwarsa zata zo.
Shi yasa a baya ranar da aka fara bud'e shari'ar nan, da kyar ya yarda ya tsaya a matsayin shaidar Kutama, don sai da Kawu Danjuma yasa baki tukunna sannan ya yarda yazo, tun a lokacin gani yake kamar daya bud'e baki zai fad'i gaskiyar komai ne, amma sai talalarsa ta k'aru..
Ubangiji ya k'ara masa lokaci Adam bai zarge shi ba a sannan.
Amma a yanzu daya riga ya gama nemawa k'annensa mafita, ya yarda komai yazo k'arshe, shi yasa lokacin da 'yan sanda suka zo tafiya dashi baiyi musu ba yabi su, kuma baiyi wani musun ba a lokacin da Adam ya tsare shi da tambayoyin da kullum suke haskawa a cikin mafarkinsa.
Ya bashi amsa tiryan-tiryan kamar yadda yake maimaitawa a yanzu.
"Hajiya ta hana a raba gado bayan mahaifinmu ya rasu, saboda bashi da wani kud'i ajiyayye sai gidaje kawai guda biyu wad'anda 'yan haya ke ciki, saboda haka tace baza a sayar da muhalli ba sai dai a cigaba da karb'ar kud'in hayar kawai wanda shi kuma ba wani abu ne mai yawa ba kasancewar tun farko mahaifinmu bai d'auki gidajen da muhimmanci ba yafi maida hankali kan sana'arsa.
Bayan wani lokaci sai kud'ad'en dake hanunmu suka k'are ni kuma ba wata sana'a nake yi ba gashi auren k'anwata dake bina ya taso kuma babu wani tallafi da muke samu, saboda haka mahaifiyata ta matsa cewa dole ne mu samarwa kanmu mafita ba zai yiwu muyi ta zama a haka ba.
Babu irin bayanin da banyi mata ba akan girman abinda take son mu aikata amma ta tursasa ni cewa idan muka kawar da Hajiya daga duniya komai zai bud'e mana don in babu ita, ba wanda ya isa yayi magana akan gidajen muna da damar sayar da abinmu.
Ita ta tsara komai da cewar mu saka mata guba a abinci ta yadda baza a zarge mu ba, sai dai a zargi wanda ke da alhaki da abincin, babu yadda na na iya, dole na yarda da ita kuma na bada shawarar mu d'orawa Bintu hakan tunda ita ke kula da abincin safen Hajiya kuma kowa ya riga ya san yadda Hajiya bata sonta, sai ayi tunanin ta kashe ta ne saboda hakan.
Ko kad'an bamu san shirin Habiba na son kashe Hajiya itama a wannan ranar ba, don haka ban san cewa ba Bintu ce tayi kokon ba kamar yadda ta fad'a, abinda na sani kawai shine a wannan safiyar na sami filas d'in Hajiya wanda na san ana zuba mata koko a ciki, na zuba garin gubar da mahaifiyata ta bani yadda in an zuba kokon zai had'e da ita sannan naje na sami Bintu wadda ke wanki a lokacin..."
Duk wannan bayanin da yake yi, idanun Fadeelah na sunkuye tana kallon teburin gabanta, sai da yazo daidai nan sannan ta d'ago ta kalle shi, take komai na wajen ya janye daga idanunta lokaci ya d'auke ta daga cikin kotun zuwa wani zamani can baya.
"Ke!"
Wata k'atuwar murya a gefe ta janyo ta daga cikin tunaninta, ta zabura da sauri sanda atamfar rigar da take wankewa ta sub'uce cikin bokitin kafin ta d'aga idonta akan siffarsa, Yaya Sule.!
Wani mutum guda d'aya da baya tab'a barin tayi yini guda a rayuwarta ba tare da hargitsi ba, a lokuta da yawa da tunaninta ke tafiya rubutun wasik'ar jaki, tasha hasko cewa rayuwarta a cikin gidan zata fi sauk'i in har zai matsa wani wajen, don shi ba mutum ne mai yawan fita ba, saboda haka kusan kullum yana gefen Hajiya yana k'ara b'antare ragowar rusashshiyar alak'ar dake tsakaninsu.
"Me kike yi anan?"
Ya tambaya yana kallon bokitin dake gabanta.
Me? na zata kana zaune a wajen lokacin da Hajiya ta jefo min tarin kayan wankinta da sanyin safiyar da ba kowa ya gama tashi ba taje inje in wanke.
Taso ace zata iya gaya masa hakan ba tare da ta jawowa kanta wani abun ba.
"Kayan Hajiya nake wankewa." Ba yadda ta iya, ta amsa a hankali.