Sashe 13
Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya sake bud'e girman idonsa ya kalli fuskar tata sosai, yanayi kala-kala a jikinta, ba wanda zaka iya tsinta ya zama jigo musamman daga idanunta, Ya Allah! wad'annan idanun da suka hana shi sukuni tsawon kwanaki biyu.
Asabar, Lahadi... akan wani dalili da bai san shi ba.
Bai san cewa ya tsira mata ido ne ba sai sanda ta juyo daga kallon kujerar Mr.
David da take ta kalle shi, wani gefen zuciyarsa ya gaya masa cewa ya d'auke kansa kafin ta fahimci kallonta yake amma ita ta riga shi, ta juya ta sake kallon kujerar.
Ta san cewa an tashi daga makaranta ne a lokacin, don haka ba d'alibin da zata gani, amma mai zaman wajen fa? (Librarian) ya kamata ace shi yana zaune akan kujerarsa da take kallo fanko a gefenta.
"Mr.
David baya nan."
Muryarsa a hankali ta katse tunaninta, ba don ta san cewa haka take a baya ba, zata ce ya rage sautinsa ne don a d'akin karatu suke.
Ta juyo ta sake kallonsa, yana jingine da kujerar da yake kai yana kallonta ta k'asan lumsassun idanunsa.
Taji tana son ta waska masa mari yadda zai dad'e bai sake bud'e idanun ba.
Sai kawai ta d'auke nata idon gefe sannan ta k'araso wajen teburin, ba yadda zata yi dole ne ta tsaya wajen mutumin da ada, bata tab'a barin zuciyarta ta yarda cewa ma yana raye.
"Me ya tsaida ke har mintuna goma sha biyar?"
Lallausan turancinsa ya nad'o kalmomin cikin sautinsa, wannan sautin nasa data tsana kamar me.
Ya Allah ta tsani komai nasa ma.
"Naje sallah ne."
Muryarta ta fito kai tsaye babu gargada, a wayewar safiyar yau, ta furtawa kanta cewa 'zata iya' yafi sau cikin carbi, sannan ta nunawa su Melisaa dake ta sukar abin dauriyarta da kuma tabbacin cewa zata iya d'in, me yasa sai a gabansa zata k'aryata kanta?
"Na d'auka Sallar bata wuce minti biyar."
Ba tambaya yayi ba, fad'a yayi kamar kamar yana bata tabbaci ne.
A cikin shawarar da Melissa ta bata harda cewa tayi k'ok'arin b'oye addininta a gabansa, amma saboda me? ta tambayi zuciyarta, zata yi mu'amala dashi na tsawon lokacin da bata tantance ba kuma a daidai lokacin da sallar azahar ke shiga, toh saboda me zata b'oye kanta bayan ya riga ya san ko ita wace ce?
"Baka da hurumin da zaka yi magana akan addinina, don ba abinda ya kawo ni nan kenan ba."
Abinda ta koya a k'ungiyar 'Musulm Support' sanin hanyoyi ne na yadda zasu kare kansu daga mutane irinsa masu k'alubalantarsu, amma Allah ya sani, ko kad'an zuciyarta bata kwanta da wannan tsarin ba, saboda ta yarda cewa a lokacin da mutum ya nuna tsoronsa, a lokacin hanyoyin da za'a sami galaba akansa ke k'aruwa.
Ga mamakinta sai ya gyad'a kansa a hankali sannan ya nuna mata kujerar gefenta alamun ta zauna.
Ta dire jakarta akan table d'in dake tsakanin kujerar da tasa sannan ta zauna.
Ya mik'e zaune sosai.
"Yaya ma kika ce sunanki?"
"Fadeelah."
"Right, leelah..."
"It's Fadeelah." Ta katse shi da sauri.
"Fadlah?"
Sai ta juya idanunta kawai ba tare da ta kalle shi ba tace.
"Ka fad'a kawai yadda zaka iya."
Ya sake gyad'a kansa a hankali sannan ya juya jakarsa d'auko wani abin, sai a lokacin ta kalli fuskarsa sosai, fuskar dake b'oye halayyarsa a idanun mutane, fari ne sosai amma ba irin farin turawa ba Allah kad'ai ya san daga wace k'abila ya fito, dogon gashin idonsa ya kwanta akan na k'asa yabi saitin cikin jakar da kallo.
Zuciyarta ta matse da tunanin suna zaune a waje guda ne kuma suna shak'ar iska d'aya, daga yadda take jin k'amshin turarensa wanda ta haddace a gefen lokarta, k'amshin da tayi wa tambari da NASA.
Ya fito da tarin takardu fal! sannan ya d'ago ya kalleta, sai ta zame idanunta kan jakarta.
"Kafin mu fara komai, in kina da abin cewa, wannan ce damarki."
Kanta yaso ya d'aure, abin cewa kamar me? in ba addu'a yake nufin ta bud'e taron da ita ba ita bata san me yake nufi ba.
"Baki da wani abu da zaki fad'a min?"
Ya sake tambaya a hankali.
A can cikin kwakwalwarta ta rubuta cewa dole ne ta sabawa kanta da wannan sautin muryar tasa.
"Abinda zan fad'a maka kamar me? na d'auka nazo nan ne don ka koya min lissafin da ban iya ba, ba don na fad'a maka wani abu ba."
Ta fad'a a lokacin da ta d'ago tana kallonsa ta cikin glass d'in idonta.
"Eh na san abinda ya kawo ki ai, amma ina tunanin kafin mu fara komai akwai wani abu da ya kamata mu fara tattaunawa, don hakan ne kawai zai sa mu san irin hanyar da zamu bi."
Fadeelah ta hard'e hannayenta a kirji, zuciyarta cike da d'acin yadda yake maganarsa hankali a kwance alhalin ita dukkan nata tunanin a dagule yake.
"Bani da wani abu da zan tattauna da kai in ba lissafi ba, saboda haka ko ta wacce hanya ne ma ka bi."
A cikin kanta ta fassara kallon da yake mata da na rainin hankali, kamar yana kallon wata k'aramar yarinyar da bata iya kirga 'one plus one' ba.
Sai ya mik'o mata wata paper da babu komai a jiki, ta karb'a.
"Bari mu gwada wannan hanyar, ki rubuta min sunayen subject guda biyar a wanda na baki friday."
Bata ko kalle shi ba ta zaro biro a cikin jakarta ta shiga rubutu, sai da ta jero su guda ashirin da biyu sannan ta mik'o masa ba tare da ta d'ago da kanta.
"Kinyi k'okari." ya fad'a ganin ta rubuce su duka.
Sai ka fara gyara tunaninka akaina!
"Wanne kike ganin kinfi iyawa a ciki?"
Kamar ta zab'i wasu a cikinsu ta nuna, sai kuma taga meye amfanin zuwanta kenan, saboda haka kai tsaye tace.
"Kowanne ina da matsala dashi."
"Haka na gani a takardunki."
Ta d'ago da kanta lokacin da yake fito da gabad'aya papers d'in ayyukanta na Maths wanda Mr.
Hawkins ya tattaro masa, sai ta had'iye yawu sannan ta godewa zuciyarta da bata yi k'arya ba.
"Kin taba tambayar kanki me yasa bakya gane lissafi?"
Tambayar tasa ta d'ago da kanta a lokaci d'aya ta kalle shi, wani abu ya motsa a cikin kanta, kwakwalwarta ta maimata tambayar, Me yasa bata gane lissafi?_ Taji a jikinta cewar tambaya ce da ya kamata ace ta dad'e da yiwa kanta tun farko, me yasa take gane komai amma banda lissafi.
"Bud'a takardunki ki gani."
A hankali tasa hannunta ta janyo papers d'in dake kan table d'in, ta shiga bud'a su d'aya bayan d'aya, a jikin kowacce, a kan kowanne lissafi akwai iya wani waje da aka zagaye da jan biro.
"Duk inda kika ganshi a zagaye daidai kika amsa tambayar, daga k'asan sa ne kika kuskure wani wajen, saboda haka in kin kula zaki ga kowacce tambaya kin amsa rabinta daidai ne, rabi kuma yake fad'ar dake.
Saboda haka dole ne da akwai dalilin da yasa kike gane farkon kowanne lissafi kuma kike fad'uwa k'arshen kowanne."
Tayi shiru tana bin takardun da kallo, ita bata tab'a tunanin tana yin wani abu daidai ma a Maths ba, ta d'auka komai shirme take yi saboda data fara take jin kwakwalwarta ta cushe komai ya d'auke mata.
"Shi yasa na tambayeki idan akwai wani abu da zaki gaya min kafin mu fara."
"Ni bani da wani abun da zan fad'a maka, ban san komai ba."
"Kinga leelah..."
"Its Fadeelah..."
"Na kasa fad'ar hakan, kince zan iya fad'ar yadda zan iya."
Muryarsa da zurfi ta fad'a, sai ta gyad'a kanta kawai ba tare da tace komai ba.
"Idan muka ce zamu fara karatun nan a haka, baza a sami banbanci da yadda kike ganewa a aji ba, idan akwai matsala a abu dole ne sai an magance ta in ba haka ba, baza'a tab'a cigaba ba."
"Kana nufin akwai abinda ke hana ni ganewa kenan?"
"Haka nake nufi, kuma ke kin san kanki, idan kina da wata matsala ko yaya take, say it! zai taimaka miki sosai."
Tayi shiru tana murza yatsunta, bayan matsalar 'Memory loss' d'inta bata san wani abu dake damunta ba, sai dai in har ta bud'e baki a yanzu ta fad'i hakan, ta fad'a masa wani rauninta ne a matsayinsa na mak'iyinta.
Wani abu da baza ta tab'a bari ya faru ba, baza ta tab'a bari yaga gazawarta ta koina ba balle har ya samu damar danganta hakan ga sauran musulmai 'yan uwanta.
"Zan baki lokaci kiyi tunanin sosai, nan da zuwa kwana biyu."
"Kwana biyu?" Ta tambaya da mamaki.
"Subject ashirin da biyu nake dashi a cikin kwanakin da basu fi wata d'aya ba, amma har za'a sami kwana biyun kawai da zan zauna ina tunani?"
Ya cije gefen lebbensa na k'asa yana kallonta da idonsa a lumshe.
"Na fad'a miki baza mu iya fara komai ba sai mun san matsalarki, sauran karatun abu mai sauki ne da zamu iya gama shi in har ba matsalar."
Ta tsani yadda yake amfani da kalmar 'Mu' tsakanin shi da ita, kamar ta sake cewa wani abin sai zuciyarta ta gaya mata ai itama hutun ta ne baza taga fuskarsa har na kwanaki biyu ba, saboda haka ta mik'e tsaye ta d'auki jakarta.
"Ina ga ba amfanin zama na anan kenan."
Da haka ta juya ta fita daga cikin library d'in.
Ta isa daidai gate d'in makarantar sanda yazo ya wuce ta cikin motarsa.
"Hace tiempo que no te veo!"
(Na dad'e rabon da in ganki)
Direban Bus d'in ya fad'a sanda yake mik'o mata metro-card d'inta bayan ya d'auki kud'insa.
"Abubuwa ne suka d'an min yawa, amma ina nan..." Ta amsa masa cikin harshen turanci sanna ta k'ara da..
"...muchas gracias." Hakan na nufin ta gode sosai.
Sanda ta sauka daga cikin motar, kwakwalwarta na ta aunawa da tarawa ne akan maganar da ya fad'a mata, da ace akwai wani abu dake damunta bayan matsalar kwakwalwarta, da tun farkon zuwanta asibiti Dr.
Gibert ya fad'a mata ko kuma a yanzu da take ganin Dr.
Florence ta san da hakan.