← Book details Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 95

Sashe 4

Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Burina shine inyi nisa da babban gida, inyi nisa da duk wanda ya san ni, inje wani wajen da mutane baza su lura dani ba, wajen da damuwar kowa ke kan rayuwarsa ba ta wani ba, zan iya rayuwa cikin duniya amma banda nan.

Tunani da yawa ya cika kaina akan wajen da zanje kafin fitowar rana wani tunanin yace in samu waje in b'oye amma na ture shi, wani
zai iya fitowa ya ganni duk da cewa guduwa shine abu na k'arshe da kowa ke ganin zanyi.

Abinda yafi kawai shine in tafi wajen da zuciyata ke hank'oro, saboda haka na cigaba da mik'ar titin yayin da kukan karnuka ya cika kunnuwana.
______
06:20 AM.

Na sunkuyar da kaina a jikin tagar motar sanda direban ya tada injinta tayoyin suka shiga motsawa.

"Allah ya kaimu lafiya." kwandastan motar ya fad'a yana rufe k'ofar, muryoyi da yawa suka amsa da Ameen.

"Allah ya kiyaye oga!" wani mai talla ya fad'a yaana d'agowa direban hannu.

"Allah ya kaiku KANO lafiya."
maigadin tashar motocin Ikara ya fad'a yana dukan bayan motar, naji zuciyata ta buga tare da k'arar.

Na sunkuyar da kaina lokacin da muka hau titi gudun hangen idon sani, na tuna lokacin dana iso cikin tashar bayan tafiyar kusan awa biyu a k'afa mai cike da 'yar b'uya duk sanda naji motsin wani abun, na hango Hamza daga cikin tashar wani abokin Yaya Sani, hakan yasa nayi saurin b'uya a k'asan wani karyayyen tebur.

A lokacin tashar ba mutane sosai saboda haka anan nayi ta zama har sai da wajen ya cika da hayaniya.

"Kano!

Kano!!" Wani mutumi nata ihu sanda na fito.

"K'anwata Kano zaki je? taho nan, motocin suna can."
Ya fad'a sanda ya k'arasowa wajena, ba tare da musu ba nabi bayansa, don bani da tunanin inda zanje, abinda nake nema kawai taya ce da zata gangara dani na bar cikin garin Ikara.

"Subhaanal-lathee sakhkhara lanaa haathaa..."
Na jiyo muryar wata mata a gefe na tana biyawa 'yarta yayin da yarinyar ke maimaitawa cikin gwarancinta.

"....wa 'innaa'ilaa Rabbinaa lamunqaliboon." Tawa zuciyar ta k'arashe sanda na hango shafin hisnul muslim d'ina.

A take kuma tunani na ya gangara kan kayana dake d'akin Hajiya, Ya salam! kwata-kwata na manta da zancensu sai yanzu, ta yaya zan iya rayuwa da kaya d'aya kawai... sai na tuna ma ai ba ko takalmi a k'afata saboda haka na ajiye wannan tunanin a gefe, Kaya ba sune abinda ya kamata ya dame ni yanzu ba.

Na juya fuskata jikin tagar, ina kallon yadda hoton waje ke sulalewa cikin gudun motar, korayen bishiyu, k'auyuka da kuma digon mutane na yawo cikin safiyar.

Naji zuciyata na washewa da kowanne hoto dana kalla, dukkan tsoro da damuwata suka dinga bajewa da kowanne motsi da tayar motar ke yi.

Bayan awa d'aya da rabi, zuciyata nata yawo cikin gajemaren tunani, na tsinci muryar wani yana k'orafi game da gyaran hanya da kuma bin titi d'aya.

A wannan lokacin kuma naso da dukkan fatana direban nan bai juyo yayi magana ba.

Motar ta tarwatse, k'arfin shigowar gingimarin dake d'auke da itace ya haddasa wata k'ara kamar ta tashin bam, k'ofofin motor suka yage daga jikin bodin, gaba wajen zaman direba ya fita ta taga, injin motar ma yayi tsalle wani wajen.

Ka'ra mai yawa ta cika iska, yadda k'arfe ke had'uwa da d'an uwansa, yadda k'arfe ke datsa bishiyoyin gefe da kuma yadda karfe ke k'onewa.
_______
FIKRAH WRITERS ASSOCIATION.

BAYAN NA MUTU..!

AYSHA SHAFI'EE
BAYAN SHEKARU BIYAR!

WASHINGTON, AMERICA.

"Zaki iya tuna me kika gani bayan hakan?"
"Zan iya..."
Fadeelah ta amsa a hankali tana rufe idanunta, hotunan mafarkin da tayi a daren jiya ya haska tar cikin ganinsu.

"Ina gudu, a cikin wani daji mai yawan bishiyu, ganyen bishiyun suna da siffar fuskoki munana, bana iya jin me suke cewa amma suna ta ihu akaina... bana iya gani sosai amma na cigaba da gudun zuwa wajen wani abu, zuwa cikin duhun dake gabana, ban san me..."
Sai ta tsaya a da
idai nan, kalaman suka gutsire a iska.

"All through the way, a voice was shouting 'kin kashe ta!"
"A cikin gudun na tsinci wata murya na fad'in 'kin kashe ta!"
"Me abinda kika fad'a na k'arshe yake nufi?"
Dr.

Gilbert ya tambaya cikin harshen turanci yana kallonta.

Hakan yana nufin na kashe ta, nayi kisa a cikin wata rayuwar da ban santa ba, na kashe wata a can d'aya duniyar da idona ke nuna min, wata da ban san wacece ba.

A cikin kanta tayi wannan tunanin yayin da Dr.

Gilbert ya cigaba da kallonta yana jiran amsa.

"Miss Malik?"
"Me?

Oh yi hak'uri, hakan na nufin kamar in gudu kenan."
Tayi k'arya cikin harshen turancin da suke magana, Dr.

Gibert likitanta ne tsawon shekara guda, wanda ke bata tallafin warkar da ciwon kwakwalwarta, (Psyiotherapist.)
Saboda haka bata tab'a b'oye masa wani abu da ya shafi ciwon nata, amma abinda ta gani jiya a mafarkinta wani abu ne da bata tunanin akwai mahalukin da zata iya shaidawa, babu wanda zata iya tunkara tace mafarkanta na kwanan nan suna nuna mata ita mai kisa ce a wata rayuwar!

Tana iya jin yadda idanunsa ke nazarinta kafin yace.

"Wancan mafarkin da kika yi shima wani abu ne ya biyo ki koh?"
"Yes, wannan karon kuma muryoyi ne, Dr.

Gilbert ban san ya zan maka bayani ba amma ina ganin abin k'aruwa yake, a baya ina dad'ewa kafin mafarkin yazo sai dai na zahiri kawai, amma wannan shine kusan na sha biyar fa a wata d'aya."
"Well, bari mu gwada wasu tambayoyi toh." Ya fad'a yana ajiye biron hannunsa akan k'aton littafin dake gabansa.

Sai ta kwantar da kanta kad'an a jikin kujerar da take zaune, wata kujera mai taushi da dad'i, kamar yadda komai na ofishin yake mai kyau, don shi kansa ginin a wani waje yake da zuwansa kad'ai zai sa maka nutsuwa.

"Tunda aka fara hayaniyar nan game da addininku, kin fuskanci wani k'alubale?"
Ta girgiza kanta.

"In banda kallon da mutane ke bina dashi duk sanda na fita, ban fuskanci komai ba."
"Wani na kusa dake fa?"
Ta d'an had'iye yawu kafin ta amsa wannan.

"Wancan satin an kori Mami Saffiya daga aiki akan tace baza ta daina zuwa da hijaab d'inta ba."
"A lokacin kin saka abin a ranki sosai?"
"Zuwa kwana biyu ne kawai na damu, amma yanzu Alhmdlilah mun manta shi, ya wuce kuma tana neman wani aikin."
Ya rubuta wani dogon layi cikin littafin kafin ya sake d'agowa ya kalle ta.

"Yaushe kika yi bacci jiya?"
"Ban tabbatar ba amma zai kai kusan sha d'aya da rabi."
"Me kika yi kafin ki kwanta?"
"Na k'arasa wani zane dana fara ne."
"Har yanzu kina gidan yayanki?"
"Eh."
"Akwai wani abu... ina nufin kina d'an takura ko yaya ne da hakan?"
Da sauri ta sake girgiza kanta.

"No, I'm Okay."
"Kina da matsala a makaranta?"
"A'ah na fara sabawa da komai, sai dai karatun kawai da yake min yawa."
"Fassara min kalmar 'yawa'"
"Yawa sosai, da sai in kai dare ina assignment."
"Kina ciwon kai?"
"Wani lokacin."
"Kina shan magani?"
"Sosai, yadda wata rana ma zan tashi cikin dare ne in sha."
"Kina--"
Wasu tambayoyin da yawa akan makaranta kafin ya fad'i abinda tayi hasashensa.

"Daga yadda na fahimta Miss Malik, yawan mafarkan yana faruwa ne saboda wata damuwa--"
Abinda yake shirin fad'a min shine gajiyar makaranta da kuma yawan karatun dake shiga kwakwalwata ne suka jawo min yawan mafarkan ba wai wani abu ba, saboda haka in ragewa kaina abubuwa sannan---"
"Kuma ki dinga hutawa, sai na ganki a wani appointment d'in."
Ya k'arashe tare da tata zuciyar.

"Thank you, zan k'okarta."
Ba wani taimako daya bani yau.

Zuciyarta ta ayyana sanda ta rataya jakarta ta nufi hanyar fita, sai dai kafin ta tura k'ofar wani dogon mudubi daga gefe ya d'auki hankalinta, ta juyo a hankali ta kalle shi, ta kalli kanta, sannan ta kalli siffarta dake tsaye sanda hoton wata 'yar siririyar matashiya ya kallota ta ciki.

Fuskarta d'auke take da kamanni irin na fulanin k'asar Nigeria da take gani a hoto, sai dai tata fes! babu irin tsagun fuskarsu da internet ke nuna mata.

Ta cikin kalar ruwan k'asar idon tana iya hango damuwa fal da kuma rashin kwanciyar hankali a k'asan su, a kowacce rana dake wucewa, fuskarta na k'ara zama bak'uwa a wajenta ne, tana jin kamar wani ne daban yake son kwace jiki da zuciyarta, ya ture nata ruhin gefe.

A ranakun data fara zuwa wajen nan, lokacin da Daddy ya kawo ta da kansa ranar appointment d'inta na farko, zuciyarta na rike da wani fata ne, fatan cewa damuwarta zata yaye, rayuwarta zata haska kamar yadda komai na wajen yake cikin kala mai kyau, Amma a yanzu bayan shekara d'aya da watanni ta sarewa wannan fatan kamar yadda ta lura Dr.

Gilbert ma ya fara sarewa al'amarinta... ya rage yi mata yawan murmushi da bata fatan warkewa.

Watakila matsalarta tafi k'arfinsa ne.

Nayi sirranta da yawa.

Zuciyarta ta rad'a mata.

Dole ne in dinga cin abinci da yawa.

Tana fita daga office d'in, wata tsohuwar Baturiyar dake zaune ita kad'ai a waiting area ta mik'e ta shiga rik'e da sandar dogaronta, a lokaci d'aya kanta ya sara sanda ta kalli sandan, saboda haka tayi hanyar waje da sauri bata ko tsaya kiran da receptionist ke mata ba na tayi booking wani appointment kafin ta wuce.

Daga Clinic d'in zuwa Bus stop mafi kusa tafiyar minti goma ce, haka tayi ta bin hanyar idonta a k'asa, hannunta na dama damk'e da jakar ratayenta kamar hakan ne zai kare abinda take gudu kar ya faru.

Bai fi mutane sha biyu ba a Bus Stop d'in saboda haka ta sami damar tsayawa daga cikin 'yar rumfar, sai dai ta gefen idonta tana iya ganin yadda baturen dake tsaye a kusa da ita ke kallonta, wani tsoho ma ya kyallaro da idonsa ta saman jaridar da yake karantawa sannan wata mata ta sak'e damk'e hannun d'anta.

Kamar ita d'in bomb ce dake shirin tashi a kowanne lokaci.
Chapter 4 · 0% Book details