Sashe 43
Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Harabar gidan Mami na d'auke da mutane tsilla-tsilla yayin da wajen yake yab'e da wani tsantsareren decoration mai d'aukan hankali, mazaunin kujeru kad'ai da zagayen teburinsu abin kallon ne, don tun kafin wajen ya fara cika da mutane akwai robobin lemu na ruwa da kuma kayan marmari fal wanda suka fi k'arfin duk mutanen da zasu zauna a kowanne tebur.
Idan ka kalli mazaunin amarya kuwa, ba zaka tab'a son d'auke idonka da wuri ba don adon al'adar gargajiyar dake jikinsa abin sha'awa da zai ka shagala wajen kallinsa, ga tsofaffi ma har hakan ya tuna musu da lokacin k'uruciyarsu a doron duniya.
Daga saman rumfar kuma wani rubutu ne mai kyalli dake haska harafan...
'Barka da zuwa Kamu da Walimar Fadeelah Ahmad Malik!'
A harabar wajen ba mutane sosai sai tsilla-tsilla,
amma cikin gidan dank'am yake da tarin jama'ar dake ta fafutukar shiryawa wasu kuma na k'arasa packaging kayan souvenirs d'in da za'a raba, ga 'yan aiki birjik har da na gidan Hajiya Amarya da Aunty hadiza ta tattaro sai faman aikin wanke-wanke suke da kuma d'ora abinci bayan wanda akayi ordering da za'
a raba a wajen.
Mami kam! bama ka ganin inda take,
don minti d'aya ne ka ganta minti d'aya kuma duk gidan sai a nemeta a rasa.
Usman na ta bin Fatima yana rokon wai sun gaiyato abokansu ta taimaka in abincin yazo akai musu can boys quaters d'in Faruk, su Zahra kuwa d'akinsu guda suka cika da k'awayensu da suka fara zuwa, in banda kwalliya,
hira da kuma waya da samarin da aka had'a agenda dasu ba abinda ke wanzuwa a d'akin.
Fadeelah bata da dangi amma wallahi a ranar nan ba mai gane hakan, don kowa daga b'angarensa yayo gayya daidai gwargwado ta mutanensa.
Sai dai duk wannan bidirin da akeyi a cikin gidan, ita Amaryar na can band'akin dake cikin d'akin Daddy inda shi kad'ai ne ba mutane ta k'ulle kanta, ta rufe 'basin' na zama sannan ta hau ta dunk'ule jikinta akai, idonta a tsaye suke kyam! kan wayarta tana kallon zunzurutun adadin kud'in da suka shigo account d'inta na banki daga account d'in Mami.
"Fadeelah kud'in kayan d'aki ne wannan, in kinje duk abinda yayi miki ki siya kiyi amfani dashi, tunda kinga baza'a d'ebi kaya har can ba."
CAN! can yana nufin k'asar America,
inda dai ta baro take murnar ta dawo tushe ta inda rayuwarta zata gyaru ta inganta watakila ma har ta samu waraka daga ciwonta, ashe wannan burin zance ne a iska kawai!
Tarihi ne zai sake maimaita kansa kamar yadda ya faru ga Mami, da aure ya d'auke ta cak! ya tsame ta daga cikin 'yanuwa zuwa wata nahiya ta duniya.
A baya gani take Mami tayi mutuk'ar k'ok'ari data iya zaman can d'in,
sai yanzu ta gane ashe ba kokari tayi ba, abu ne da ba yadda zaka yi dashi....
Ba zaka iya sa k'afa ka ture ba ko kasa hannu ka tsige shi, manne yake cikin k'addararka da ba mai iya canja hakan sai ubangiji!
Allah ya sani ta riga ta gama fahimta a yanzu auren ne kwata-kwata bata so, shi yasa take jin kamar zata mutu, amma kuma tana son Al'ameen, irin son da take ganin tsananin kirkinsa da kuma tsananin kyawunsa, bayan haka bata jin komai a ranta game dashi amma ta yarda cewa iya wad'annan abubuwan kad'ai zasu saka taji dad'in zama dashi,
sai dai inda ta baro zata koma fa?
Wajen da a yanzu bata da kowa sai nasa DANGIN, wanda yake k'unshe da mahaifiyarsa da har yanzu bata san matsayinta a wajenta ba.
Ya dai ce mata yau zasu taho, amma bata san 'SU' wa da wa ya k'unsa ba, abinda tafi rik'ewa kawai shine zasu zo su tafi da ita, CAN inda sabon DANGIN data samu a yanzu ma zata yi musu nisa.
Tasa bayan hannunta ta share kwalla mai d'umin data taru a idonta, ita haka ubangiji ya kaddaro mata rayuwarta, daga nan sai can, daga wuya sai dad'i daga dad'in kuma a koma wuyar, fatanta d'aya a yanzu shine ta samu farin ciki tare da Al'ameen, farin cikin da zai d'ebe mata wasu abubuwan.
K'ofar band'akin ta shiga bugawa da karfi sannan muryar Aunty Hadiza maman Rahma ta biyo baya.
"Fadeelah bud'e k'ofar mana,
me kike yi?
Ga mutane har sun fara zuwa baki shirya ba."
Sai ta kashe wayarta a hankali sannan ta d'ora saman sink, bata da yadda zata yi fa, bata da zab'i babu ma mai bata zab'in...
Komai tafiya yake kawai kamar yadda ubangiji ya tsara, ita nata kallo ne kawai!
A hankali ta bud'e k'ofar.
"Ga mai kwalliya nan tun d'azu muke neman..."
Sai maganarta ta katse ganin hawaye shab'e-shab'e a fuskarta.
"Haba 'yanmatan Mami, kukan ne tun safe har yanzu?
Girma ne fa ya hau kanki meye abin masa kuka?"
Sai ta jawota ta rungume ta a faffad'an jikinta, kamar dama hakan Fadeelah ke jira sai ta dunk'ule kanta cikin kafad'unta ta shiga rera shi a hankali, irin mai zurfin nan dake tasowa tun daga k'asan zuciya.
"Haka kowa ke ji Fadeelah, ba ke kadai ce ba kowacce mace irin wannan zafin rabuwar sai ya hau kanta, amma komai yana wucewa ne a d'an kankanin lokaci, da kanki watarana in kinzo ma zaki tashi ki tafi gidanki..."
Maganganu masu taushi da kwantar da hankali Aunty Hadiza tayi ta rad'a mata a kunne har da kyar ta samu ta shawo kanta, ta tsaida kukan nata da kyar sauran ya koma k'asan zuciyarta ya shiga jiran wani lokacin.
Sannan ta saka ta ta koma band'akin ta wanke fuskarta kafin ta zauna gaban mai kwalliyar dake jiranta da k'aton akwatinta, ba yadda ta iya haka ta d'anyi mata murmushi sannan ta fuskance ta, sai daga baya kuma tayi tunanin meye amfanin ma murmushin bayan ta ganta ta gama kuka yanzu.
"Bari inje in turo miki Fatima da kayan da zaki saka."
Aunty Hadiza ta fad'a sannan ta bud'e k'ofar d'akin ta fita, da kyar ta samu Fatiman a cikin taron jama'ar gidan ta bata muk'ullin wardrobe din Mami da cewar taje ta d'auko kayan Fadeelah ta kai mata.
Daga nan ta nufi masaukin k'awayenta da suka fara taruwa a lokacin, ta tarar wata Nafisa daga cikin k'awayen nata tana ta bada labarin sabuwar 'yar aikin da tayi da bata gajiya kamar inji.
"Ke nifa yanzu tiles d'in barandar wajen gidana ma fa sai ki kalli fuskarki kamar mudubi saboda tsabar yawan mopping."
Wata Jamila tace.
"Dan Allah daga ina take nima insa a samo min 'yar garinsu?"
"Daga Ikara take wai, sunanta Sadiya kuma bazawara ce wallahi ba yarinya ba."
"Ina ne Ikara?"
Aunty Hadiza ta tambaya tana zama cikinsu.
"Can wajen hanyar Zariya ne inji ta."
Daidai lokacin da Sadiyan ta k'araso rik'e da d'an matar, ta gaishe su d'aya bayan d'aya sannan ta karb'i jakar kayansa ta shiga canja masa rigar daya b'ata.
Basu cigaba da hirarta ba sai suka canja wata,
amma kasancewar ita Sadiyan taji su tun farko,
sai tayi kwafa a hankali sannan ta maimaita abinda ta kudirtawa ranta tun farkon zuwanta gidan.
Kaina nake gyarawa waje baiwar Allah, zamanki a gidan nan ya kusa k'arewa!
Fatima ta k'araso a daidai lokacin nan d'auke da manyan ledoji na kayan Fadeelah, ta mik'awa Aunty Hadiza muk'ullin sannan tace.
"Aunty ba mai taya ni dan Allah,
wallahi kayan da nauyi."
Caraf!
Nafisa ta kalli 'yar aikinta Sadiya tace.
"Bar saka masa kayan nan ki mik'o min shi, taya ta ku kai kayan nan sai ki dawo."
Sadiya ta mik'e da sauri ta mik'e ta mik'a mata yaron da jakar
sannan ta kinkimi duka ledojin hannun Fatima tabi bayanta dasu zuwa d'akin da ake shirya Amarya Fadeelah!
BAYAN NA MUTU!
AYSHA SHAFI'EE
RANAR DAYA GA FARKON WATA.
ASOKORO, ABUJA.
Ta juya miyar dake zab'alb'ala kan gas d'in gabanta a hankali yayin da gwalantun d'anta Muhammad dake zaune a island na kitchen d'in ya cika wajen, d'aure yake cikin kujerarsa ta yara amma yana ta mik'a hannu yana k'okarin tab'o plate d'in yayarsa Afra dake zaune a
gefensa tana ta kanannad'e indomie d'inta cikin fork maimakon ci.
"Mommy Muhd zai zubar min."
Yarinyar ta fad'a cikin shagwab'a tana ture yala-yalan kitson kalabarta daga fuska, sai dai mahaifiyar tasu bata ko juyo ba balle ta nuna alamun taji me tace, cigaba da juya miyarta kawai take yi a hankali idanunta na tsaye kyam akan taswirar siffarta dake nunawa a jikin murfin gas d'in.
Watak'ila ruhinta yayi nisa ya bar doron duniya ma a lokacin, don tunani take yi mai zurfi, irin tunanin da tsawon shekaru bata tab'a yin irinsa ba, bai tab'a zuwa kanta ba don a kwakwalwarta kaf babu muhallin irinsa, Tun bayan lokacin da idanunta suka gano mata k'anwarta Bintu a wajen bikin nan, bata sake tunawa da ita ba sai a yanzu, a yanzun da take jin ba iya tunanin k'anwar tata ba ma, abubuwa ne da yawa ke ta taruwa suna kwancewa a cikin kanta, kamar a da an k'ulle su ne can wani wuri guda, sai yanzu suka sami 'yancinsu na fitowa.
A hankali taji hannu ya ziro ta gefen k'ugunta ya kashe wutar gas d'in dake shirin k'one miyar, sannan ya zuro kansa cikin wuyanta ya rad'a a cikin kunnenta.
"Tunanin me kike yi?"
Mairo ta rufe idanunta a hankali sannan ta kwance hannayensa daya nad'e a jikinta ta juyo ta kalle shi, ta kalli fuskar da tun a kwanaki biyu ta canja mata zuwa wani iri duk da cewa kammaninsa basu canja ba don shine dai mijinta, wannan Sadiq d'in da take so fiye da komai a rayuwarta, wanda har ta baro gida saboda shi, d'an kyakkyawan bafulatanin nan da tun gani na farko da tayi masa a bakin rijiyar da suke zuwa d'ebo ruwa taji zuciyarta ta fad'a duniyarsa.
To me yasa a yanzu take ganinsa wani iri?
"Me ya same ki?" Ya tambaya hankalinsa kwance yana maida wani dogon gashinta daya fito cikin hular kanta.
Ta san yana yin hakan ne saboda miyar bayanta dake bud'e, yana son gashi amma baya sonsa a harkar abinci.
Sai ta zame hannayenta daga cikin nasa daya rik'e sannan ta kalle shi sosai.