Sashe 67
Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sauran matan biyun suna zaune a k'asan sauran gadajen suna kallonsu, ko kuma tace mace d'aya kawai, wadda ta zame hannun rigarta d'aya tana shan iska, amma ta bayanta babu marabar kammaninta dana maza, jikinta mai tsawo ne da girma sannan babu wani alamun tsari irin na jikin mace, komai nata ihun fad'i yake yi.
Ta katse nazarinta ta hanyar washe bakinta sannan tace.
"Barkanku da zuwa, bak'inmu."
Fadeelah ta lumshe idanunta cike da rud'ani.
Ashe da mai yi mata Barka da zuwa.
BAYAN NA MUTU!
AYSHA SHAFI'EE
Watak'ila tafi minti biyu a tsaye tana kallon 'yan kananan kwarukan dake layi suna bin gefen yamusashshiyar katifar da aka nuna mata a matsayin gadonta, sama ne amma bashi da maraba da k'asa don tsalle d'aya kawai mutum zai yi ya haye.
"Mun gama gaisawa da 'yaruwarki, ke yaya sunanki?"
Wannan mai siffar mazan ta fad'a sanda ta tsaya a gefen gadon.
Kallo d'aya kawai Fadeelah tayi mata sannan ta fad'i sunan dake rubuce jikin form d'inta.
"Bintu."
Ba zata tab'a bari wajen nan ya amsa sunan Fadeelah ba, Fadeelah mai wankakkiyar zuciyar ce da ko k'uda bai tab'a mata sharri ba, zata kare martabar wannan sunan daga samun gurbi a k'azamin waje irin wannan, duk kuwa da cewar sunan ya fara sulalewa daga gareta, Bintu ta riga ta dawo tayi kane-kane da komai na rayuwarta...
Banda su Mami da kuma Adam da ta sani a America watakila da ita kanta ma ta fara manta cewa ta tab'a zama Fadeelan.
"Sunana Kenken..." Matar ta cigaba sannan ta juya ta nuna d'ayar nan mai cirarriyar hannun riga.
"Waccan sunanta Gheto..." Sai ta nuna wannan Babbar da har yanzu ke kallon Fadeelah tana washe baki.
"Wannan itace shugabarmu a d'akin nan, sunanta Lalita, sannan Zazu..." Ta nuna mai kama da k'abilar nan ta saman gado.
Yanayin fuskar Fadeelah ya shaidawa Kenken cewa sunayen basu bada ma'ana a kwakwalwarta ba, saboda haka tayi wani karkataccen murmushi wanda daga gani ta saba yinsa sannan tace.
"Ba sunayenmu na gaskiya bane, inkiya ce muke kiran kanmu da ita don mu manta da rayuwarmu ta waje,
duk wanda kika gani a wajen nan yana da sabon suna don haka kema kwanan nan zaki samu naki, "
Bata ce komai ba Kenken ta cigaba da cewa.
"Karki damu kowa anan ya shiga irin halin da kike ji zaki ware nan da lokaci kad'an, kin riga kin shigo cikinmu yanzu, zamu zama 'yanuwa kuma abokai mu taimaka miki ki fara sabuwar rayuwa, ki manta da komai ki kuma samu duk irin dad'in da kika baro a waje."
Ta k'arashe da murmushi tana k'ok'arin dafa kafad'unta, amma sai ta matsa baya da sauri sannan ta juyar da kanta, haka kurum zuciyarta bata amince da kenken ba ko d'aya daga cikin sauran 'yanuwanta.
Hakan da tayi kuma bai b'ata ran matar mai kama da maza ba, sai ma murmushi da ta sake yi sannan ta d'auke hannunta daga iska.
"Kar ki damu Binbi, muna da isashshen lokaci ai."
Taji sunan da ta kira ta, amma bata so ma ta yardarwa kanta cewa ta jin, saboda haka ba tare da ta k'ara kallon kowaccensu ba ta janyo katifar kan gadon ta karkad'e ta.
Zan zauna zuwa wani lokaci,ta ayyana a ranta.
Zata daurewa zama da mutanen nan kafin lokacin da za'a sanar dasu Kawu Ibrahim yazo yasa a bata cell ita kad'ai, Kafin kuma dawowar Adam yazo ya fitar da ita gabad'aya.
A lokacin wata iska ta kad'o ta tsakanin k'arafan k'ofar cell d'in, wani tsami ya taho ya kuma kwaso warin toilet d'in cikin cell d'in ya baza shi a iska, Fadeelah ta saka duka hannayenta biyu ta rufe hancinta da bakinta, don ta raba kanta da warin don kuma ta hana kanta ihun dake shirin fasowa daga k'irjinta.
"Wai baki da lafiya ne?" Muryar wadda Kenken ta kira da Zazu ta tambaya daga saman gadonta.
Bata bata amsa ba, haka bata juya ba har saida ta tabbatar ta kwantar da kukan dake neman 'yancinsa sannan ta maida katifar ta hau gadon, ta d'ora kanta akan kayan da aka bata sannan ta duk'ule duka jikinta.
Ta daurewa abubuwa da yawa a baya, don haka wannan ma zata daure masa.
Zata daure.
Zata daure.
Bayan kwana biyu.
Ba mafarki bane, tunani ne kawai cikin bacci, don babu abu d'aya da ya canja na wancan lokacin.
A wannan d'akin ne....
Cikin kotun da suka baro, inda d'aurarru ke ganawa da baki, Lokacin da Adam ke bacci a gabanta....
Wani irin tausayinsa ne ya dirar mata a sannan, don bayan sajen da taga ya tara, wannan baccin shine abu na biyu daya tabbatar mata cewa baya samun isashshen hutu a kwanakin nan...
Duk saboda shari'arta.
Ta lumshe idanunta a hankali tana cigaba da kallonsa.
Shine wanda ta tsana a wancan lokacin da zuciyarta bata fahimce shi ba.
Shine wanda bata ko son inuwarsa da tata su kasance waje d'aya.
Sannan shine wanda a baya take ganin kamar yana rik'e da makamin tarwatsa rayuwarta.
Sai dai wannan bayan ta riga ta wuce, ta dad'e da shud'ewa tun farkon lokacin da k'addarar koyon karatu ta had'a su, wani b'ari na zuciyarta ya bud'e har ta fahimci b'oyayyun halayen da yake binnewa a bayan fuskarsa...
Wannan fuskar dake gigita d'aukacin matan makarantarsu tana saka musu yardar cewa shine k'ololuwar duk wani fatansu.
Ta sake lumshe idonta tana kallon yadda yake baccinsa tsakani da Allah, zuciyarta cike take da hasashen wace irin k'addara ce ta cillo shi Nigeria kuma kan hanyarta.
Ta cije gefen lebb'enta kad'an tana hasko ma'anar K'addara a cikin kanta...
Hukuncin Allah ne da babu tunanin wani d'an adam d'in da ya isa ya kai gejinsa, ta yarda da wannan har cikin ranta don in a yanzu in ba hukuncin Allah ba ta yaya shi d'in data baro a can wata nahiyar duniya zai tsallake koina yazo ya same ta har cikin 'yanuwanta anan?
Kuma sab'anin a baya, yanzu ya zama mai fafutukar ceto rayuwarta?
Duk da baccin da yake yi, mai kallonsa zai iya tsinto zallar halayen da kowanne cikakken Namiji ya kamata ya tara, dogaro da kai, juriya, jajircewa, sanin ya kamata da kuma zurfin tunanin da zai zarta na tarin mutane....
Kyawunsa mai sanyi ne ba kamar Al'ameen ba mai manyan kyau.
Al'ameen.
Tuna sunansa da tayi ya dawo mata da zagayen rayuwarta da tasa, ta tuna cewa har ta fara taka matakin zama Amarya.
Amaryar shi d'in da a yanzu bata san wane hali yake ciki ba, Mami ta gaya mata komai ya tsaya saboda rasuwar mahaifinsa amma ta san ta fadi hakan ne don ta lullub'e ta daga ainihin gaskiyar...
Gaskiyar itace komai ya cakud'e saboda abinda ya faru da ita da kuma rasuwar mahaifin nasa.
Zuciyarta na tausayinsa kuma tana kewarsa, kewar cewa da tuni suna tare yanzu, da ta dad'e da zama mallakinsa a can k'asar da zuciyarta bata marari, k'asar da komai kud'inka babu wani sakewa a matsayinka na musulmi kuma mai banbanci da kalar fatarsu, sannan k'asar da zata nesanta ta da duk wasu danginta sai nasa kawai, nasan dake d'auke da mahaifiyarsa wadda ta kwana da sanin cewa bata k'aunarta...
Amma banda wad'annan abubuwan zuciyarta ta san cewa zamanta da Al'ameen zaiyi dad'i, don Allah ya sani ko a yanzu da komai na rayuwarta ta baya ya dawo mata ba zata iya kwatanta kowa dashi a kyautatawar mu'amala ba.
A sannan ne k'ofar wajen ta bud'e, mai tsaron nan Musa, da Adam ya umarci ya basu waje ya lek'o da kansa alamun iya lokacin da aka d'iba musu yayi.
Da sauri ta janye idonta daga fuskar Adam ta kalle shi.
"Yallab'ai inaga kamar lokacin da aka d'iba ya k'arato." Ya fad'a yana kallon bayan Adam d'in, kasancewar ita take fuskantarsa.
"Yi hakuri Malam Musa..." Zancen ya fito cikin hardaddiyar hausar Adam.
"...yanzu muke shirin kammalawa."
Da tsananin mamaki tayi saurin juyowa daga kan Malam Musa ta kalle shi, dama ba bacci yake ba? dama idonsa biyu yayi shiru ya barta tana ta kallonsa?
Malam Musa ya gyad'a kansa sannan ya koma ya maida k'ofar ya rufe, Sai tayi sai ta d'auke kanta sannan ta mik'e tsaye tana sake cukwuikwuye ledar hannunta.
"Kin gama?
Zan iya tafiya?" Taji muryarsa ta fito kamar had'e da murmushi.
Ya ubangiji ya Allah!
Ta gama me?
Kallon nasa?
Ko me?
Dame zata kare kanta tace ba haka bane, watakila kawai idan k'asa ta tsage ta shige komai zai fi sauk'i, amma simintin dake k'asa yak'i bud'ewar.
Ya taso rik'e da waya da kuma tarkacen su jotter ya tsaya a gabanta, taji girmansa kamar na wata katuwar bishiya a kusa da ita, cikinta ya yamutse sannan yawu ya shiga zaryar shigewa mak'ogwaranta, ta gagara ko motsa kafafunta.
A hankali taji yace.
"Zan yi tafiya jibi..."
Ta dago da sauri ta kalle shi.
"...
Na gaya miki a zama na gaba mu zamu fara gabatar da shaidu, to zanje wani bincike ne akan abinda nake tarawa saboda haka ba lallai ki k'ara gani na ba a cikon kwanakin nan, may be sai ranar da za'a zauna."
K'arar kiran wayarsa a wancan lokacin yayi daidai da k'arar k'ararrawar da ta karad'e d'akin....
K'ararrawar data tashe ta daga tunanin rabuwarta da Adam na k'arshe.
Ta kalli yanayin lokacin, wajen k'arfe uku ne na rana, wanda ya kama lokacin da kowa zai tafi yin aikinsa kamar yadda yake tsare a jadawalin tsarin wajen da ta riga ta haddace.
5:00 A.M
Za'a kad'a k'ararrawar tashi.
5:15 A.M wanka da alwala
5:30 A.M Za'a fito sallar Asuba.
5:40 A.M Za'a koma cikin cell.
6:00 A.M Za'a fito kowa ya tafi gurin aikinsa.
10:00 A.M Za'a tafi wajen cin abinci.
10:30 A.M Za'a tafi wajen motsa jiki.
11:00 A.M Za'a koma gurin aiki.
02:00 P.M Za'a tafi yin sallar Azahar.
02:30 P.M Za'a koma cell.
03:00 P.M Za'a koma wajen aiki.
04:00 P.M Sallar la'asar.
04:30 P.M
Za'a tafi wajen koyon sana'o'i.
06:00 P.M Sallar Magriba.
06:30 P.M Za'a tafi cin abincin dare.
07:00 P.M Za'a koma cell.
08:00 P.M Sallar Isha'i.
08:50 P.M K'ararrawar shirin kwanciya.
09:00 Za'a kashe fitila kowa ya kwanta.