Sashe 55
Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A daren da ya zama washegari za'a fara shari'ar, Adam ya kasa wani bacci cikakke, tunani fal ke yawo akansa game dayadda komai zai kasance, shari'ar Nigeria daban ce da wadda ya saba a America, yaga hakan akan case biyu daya k'alubalanta bayn dawowarsa, ba daga alk'alan kad'ai ba, mutanen nan suna da wani irin taurin kai da sai sunga abu k'iri da muzuru sannan zasu yarda, amma a America in har akwai shaidu na gaske da suka tabbatar da abu to shari'a zata iya yadda dasu ba sai anja da nisa ba.
Amman Nigeria, sai kowa yaga komai dalla-dalla tukunna, shi yasa tunaninsa ya kasa tsayawa waje d'aya,
lalube kawai yake yi a cikin kansa ta yadda zai fito da komai ya baiyana bayan tsawon shekaru da faruwarsa.
Idanunsa biyu tar ya kwana!
BAYAN NA MUTU!
AYSHA SHAFI'EE
K'arfe goma na safiyar laraba sha biyar ga wata za'a shiga shari'ar, amma tun kafin takwas mutane suka fara tururuwar zuwa don samun wuri kafin ya cika, 'yan Babban gida kaf matansu da samarin 'yayansu, hannu kawai d'aya zai d'ebe wad'anda basu zo ba, sannan banda 'yanuwa ga jama'ar gari dama wad'anda suka tsinci zancen a titi, kowa yazo cike da zumud'in d'aukar rahoton yadda shari'ar zata kaya, musamman da jita-jita ta zaga koina cewa ai lauyan da zai kare yarinyar ma musamman daga America aka d'auko shi.
Sadiya.
Tana daga cikin wannan cincirindon mutanen sai fara'a take sanye da wani leshi irin kwancen data samo a Abuja, wani zaice taron wani abin alkhairi daya same ta ake yi ganin yadda take ta zubar surutu tana k'ara nanata zancen da zata bayar a matsayin shaida daga gare ta.
"Gabana fad'uwa yake Salame, kin tabbatar kuwa da malam yayi aikin nan?"
Habiba data iso wajen bisa tattagowar da Kawu D'anjuma yayi mata ta fad'a tana duban k'awarta Salame.
"Na rantse da kabarin ubana Habi bani da shakka akan malamin nan, ni ban san sau nawa zan gaya miki hakan ba ki yarda, kin riga kin sawa zuciyarki k'ulafucin sai aikin na Kadunan nan ne zai ci, bayan da bakinki kika ce ai ko'ina ma sa'a ake samu kawai."
"Dole inyi shakka Salame, tunda har Kawu D'anjuma nace dake a k'ulle bakinsa daga zancena a lamarin nan bayan ita an kashe tan amma har yanzu yarinya na raye, kuma kina gani yadda aka sa Mudan ya tattago ni har nan a haka."
Ta fad'a tana kallon karyayyiyar k'afarta d'aya da kuma sandan da take dogarawa, a ranar da suka kama hanya zuwa Kaduna ne motar da suka shiga tayi hatsari, kuma wani abu na tsautsayi Salame ta fita babu ko kwarzane yayin da ita ta samu karaya a k'afa harda kuma gocewar k'ashi.
Hakan ne yasa ta tattara kud'in da ta dad'e tana tarawa dubu d'ari da hamsin cif!
Ta bawa Salame da tayi mata zancen wani sabon bokan da aikinsa ke ci kamar yankan wuka a nan gaba dasu kad'an.
"To me akayi da maza?
Yanzu fa za'a fara shari'ar nan ko shiga bamu yi kinji me za'a ce ba, kar kiyi saurin yanke hukunci, don dama saida ya fad'a, aikin kisa da d'aure baki a lokaci d'aya abu ne mai wahala, don haka ki bari mu saurara dai mu gani."
Da wannan zancen Salame ta rufe bakin Habiba daga sake wani k'orafi amma daga ita sai ubangijinta suka san irin fargabar dake dukan zuciyarta.
Lokacin da lauya Bashir Kutama ya iso harabar cikin kotun, wasu ma'aikatan gidan jarida da kuma na rediyo da suka sami labarin abin suka tare shi tun daga wajen motarsa.
Bayan sun sanar dashi abinda ke tafe dasu ne d'aya daga cikin 'yan jaridan ya tambaye shi.
"Yallab'ai me zaka iya gaya mana game da wannan case d'in?
Yaya kake ganin shari'ar zata kasance?
Kutama ya kalli camerar da aka saita don d'ukarsa hoto da murmushi sannan yace.
"Wannan shari'a ce mai sauki, a duk case d'in da na tab'a yi ban ma tab'a cin karo da mai sauki wanda komai yake a fili irin wannan ba, saboda haka abinda zan iya cewa shine zamu yi nasara nan da k'ankanin lokaci insha Allah."
"To yallab'ai me zaka iya cewa game da abokin takararka wanda akace kwararre ne tun daga k'asar America."
Ya sake wani murmushin mai kama da dariya sannan yace.
"Kow sarki ne a garinsu, don haka abinda zance fili nan ga mai doki, Allah ya bawa mai rabo sa'a!"
A wannan safiyar ta laraba dai, idanun Adam suka sami abincin da suka yi yunwarsa tsawon kwanaki, don dole ce tasa shi ya sake neman ganin Fadeelah kafin a fara zaman kotun, a cikin kwanaki hud'u kawai, kammaninta sun fara canjawa daga yadda ya ganta da farko, hasken farinta ya ragu sannan idanunta sun fara zurmawa cikin raminsu.
"Ki cire damuwa a ranki, komai zai tafi daidai da yardar Allah, zamu fuskance su kuma zamu yi nasara kinji?"
Babu yadda ya iya dole ya fad'a mata hakan cikin sigar lallashi, don ta fahimci duk irin k'arfin halin mutum akwai taraddadi ranar da zai fara shiga kotu a matsayin wanda ake zargi da kisa.
Bata kalle shi ba tace.
"Habiba tazo?"
Sai ya ya lumshe idonsa yana kallon yadda gashin idonta ya had'e dana k'asansa kamar a rufe suke, hakan ne kad'ai ya bashi damar iya kallonta hankali kwance.
"Kawu Ibrahim yace tazo, amma ban ganta ba."
Sai ta gyad'a kanta kawai alamun ta fahimta, sannan tayi shiru bata k'ara cewa komai ba.
Har ya mik'e tsaye sai kuma ya juyo ya kalle ta yace.
"Ina so ki yarda dani, kar ki bari duk abinda zaki ji daga bakin mutane ya raunana fatanki na samun nasara, baki da laifi don haka insha Allah zaki kub'uta."
Bata d'ago da kanta ba kuma bata ce komai ba haka ya juya ya fita, sannan mai tsaron da ya rako ta ya bata umarnin tashi don ana dab da fara zaman shari'ar a lokacin...
Shari'ar data gujewa a baya, shari'ar dake shirin canja akalar rayuwarta.
Kotun ta cika ta kuma tunbatsa don har saida aka rufe k'ofa da wasu mutanen a waje.
Zaune daga jerin wajen masu saurare, Kawu Ibrahim ne a gaba sai daga gefensa wasu daga cikin 'yan Babban gida masu irin ra'ayinsa a ciki har da Abdullahi daya zo tare dasu Mami, layi biyu bayansu kuma muk'arraban Kawu D'anjuma ne su Yahya, sulaimaman, da sauransu.
Su Mami na daga bayansu ita da Aunty Hadiza da kuma Fatima wadda tayi tsuru-tsuru don har ga Allah ta shiga damuwar ganin Fadeelah a wannan matakin.
A layi na k'arshe kuma, Nasir abokin aikin Adam ne daga can ma'aikatarsu wanda yazo a daren jiya a matsayin wakilin ma'aikatar.
Daga nan kuma duk mutanen Babban gida ne da kuma cikin Ikara mazansu da matansu kowa da irin abinda ke k'ulle a zuciyarsa.
Daga gaba teburin masu shari'ar kuma lauya Kutama ne zaune a gefensa da wasu k'ananan lauyoyin biyu masu taimaka masa.
Adam na zaune, daga gefensa kuma wani k'aramin lauyan gwamnati ne da kotun ta bashi don ya taimaka masa ta hanyar rubutu mai suna Jabir.
Adam sanye yake cikin kaya na kowanne irin lauya amma sai ya fita daban da kowanne lauya dake cikin wajen, saboda yadda kalar hular ta kwanta akan fatarsa ta kuma fito da duk wata ilhama da kwarjininsa.
Zuciyarsa tayi nauyi ta kuma tsaida bugunta na wasu dakikai lokacin da aka shigo da Fadeelah cikin wajen, irin abinda yake gudu kenan gashi ya fara faruwa tun ba'a je koina ba, ina ga kuma ya bari sun fahimci juna?
Alkali Bashir Uba Ali (mai jagorantar shari'ar) ya shigo cikin kotun a daidai wannan lokacin, mai sanarwa ya d'aga muryarsa ya bada umarnin a mik'e da cewar zaman kotu ya fara kuma alk'ali ya zauna.
Bayan zamansa ne kuma, Alkalin yayi gyaran murya yace.
"Za'a iya zama, wannan shari'ar zata fara ne tsakanin masu shigar da k'ara da suka taru akan hakan da kuma wadda ake zargi Bintu Abubakar.
Zamu iya farawa."
Bayan kowa ya zauna, Alk'ali ya juya ga Kutama yace.
"Shin masu shigar da k'ara suna da abinda zasu ce?"
Kutama ya mik'e tsaye a take.
"Kwarai ya maigirma mai shari'ah, kamar yadda kowa ya samu labari an shigar da wannan k'arar ne shekaru hud'u da suka wuce bisa zargin yarinyar dake zaune anan Bintu Abubakar wadda a lokacin shekarunta sun kai sha takwas akan kisan kakarta, ta hanyar sanya mata guba a cikin kokon da take dama mata a kullum safiya.
Amma k'arar bata kai ga isa mataki na gaba ba, sai yarinyar ta tsere a washegarin ranar da tayi kisan, anyi nemanta har zuwa garin Kano inda bayan bincike aka tabbatar da inda ta nufa kenan, kuma motar data hau d'in tayi hatsari a lokacin, amma aka samu
sab'ani kafin hukuma ta isa ma'aikatan asibitin suka sallameta bisa rashin sanin ainhin dalilin rabuwarta da gida.
Kuma tun daga wannan lokacin bata k'ara waiwayar gida ba, saida a bisa fad'in marik'anta, sunce ta samu gushewar tunani ne a dalilin gatsarin nata wanda babu wata kwakwakwarar shaida data nuna hakan, don a lokacin da aka ganta, da bakinta ta furta cewa ta gane kowa kuma ta san laifin da ake zarginta dashi."
Ya juyo da idonsa kad'an ya kalli Adam fuskarsa d'auke da murmushi.
"Hakan na nuna cewa tana sane da laifinta kenan, kuma tana guje masa ne tsawon wannan lokacin, ya mai girma mai shari'a, akwai tarin hujjojin dake tabbatar da aikatuwar laifin nata wanda zasu zo a gaba kad'an.
Nagode."
Ya koma ya zauna, Alkali ya juyo kan Adam dake nazarin komai da dukkan wata kafa ta fuskarsa yace.
"Masu karewa suna da abinda zasu fad'a?"
A hankali Adam ya mik'e tsaye sannan muryarsa mai taushi ta shiga kunnen duk wani mahaluki dake wajen cikin nutsuwa.