← Book details Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 87 OF 95

Sashe 87

Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Na gaya miki ki bari ko zuwa nan da next week ne sai ki tambaye shi tukunna, amma ko gidan Mami kika je yanzu sai ta miki magana."
Gidan Mami.

Ta maimaita kalaman a cikin kanta, a da nan take kira da gida, amma yanzu saboda tasirin wasu kalamai da kuma 'yar walima, kalmar 'Gida' a wajenta ta canja daga wajen su Mami zuwa nan...

Gidan Adam!

Ta shiga gyara gashinta da yatsun hannunta don Mairo bata san komai game da yadda zaman shirun nan d'in ya fara damunta bane, a yadda kowa ya sani su biyu suke rayuwa a gidan, amma a zahiri ita kad'ai take dabdalarta a cikinsa, don hatta washegarin ranar da aka kawo ta lahadi, Adam bai yini a gidan ba sai dare ta ganshi.

Ita dashi a yanzu kamar wasu makwabta ne kawai dake rayuwa a kusa da juna, ta san dai kullum zasu gaisa idan ya dawo daga aiki ko kuma wani lokacin da safe in zai fita harma ya tambayeta wani abun amma bayan nan bata fiye ganinsa sosai ba, don bata zama a inda zata ganshi d'in ko yana gida, sai dai ta jiyo motsinsa kawai daga nan cikin d'akinta.

Alkawarin daya d'auka yana nan rataye a cikin zuciyarta yana reto, don haka ta zab'i bin wannan hanyar ne saboda tana ganin itace maslaha game da irin zaman da zasu yi, ta yarda in har ta nesanta kanta dashi rabuwarsu zata zo mata sauki a duk ranar daya tsayar zai sallameta.

Domin bata so tarihi ya maimaita kansa, wancan karon a makarata kawai suke had'uwa amma data bari zuciyarta ta saba dashi, ba k'aramar wahala tazo tasha ba wajen kewarsa.

Bayan haka kuma akwai wasu banzayen sak'e-sak'e da zuciyarta keyi in har tana gabansa, shi yasa ma dole ta kaucewa ganinsa tun kafin ta makara wajen ceto zuciyar tata.

Dad'in da take ji d'aya ne, duk irin sak'e sak'enta bata tab'a tunanin Al'amin ba, don taji nasihar da Mami tayi mata akan hakan shi yasa ta d'auki tunaninsa ta kai zuwa can wani sak'o a zuciyarta kamar yadda take fata shima ya manta da ita ya karb'i zab'in mahaifiyarshi hannu biyu.

Bayan gaisuwa kuma abinda kad'ai ke had'a ta da Adam shine abinci, don a
cikin wancan satin data gaji da kame-kamen abin ci a gidan ne tayi girki ta had'a dashi, kuma wannan ma gani tayi rashin kyautatawa ce k'iri-k'iri ace shi da gidansa da kuma kayan abincin daya kawo amma ta dafa ta barshi da neman na siyarwa, don hatta Awwal d'in da yazo yayi mata siyayya ma shi ya turo shi, saboda haka sai ta k'udirce a ranta cewa zata yi ko don ta samarwa kanta lada kafin damar ta sub'uce mata, tunda Allah ba ruwansa da tsarinsu, a wajensa shi mijinta ne da in ta kyautata masa zata samu ladanta.

Kuma taji dad'i da shima ya karb'i hakan a matsayin kyautatawa kawai, baiyi tunanin cewa tana neman cusa kanta ne wajensa ba.

Watak'ila kuma wannan yanayin zaman nasu yana d'aya daga cikin abinda ya dad'a kwantar da hankalinta ta samu nutsuwa a cikin 'yan kwanakin nan. amma kuma yanzu kad'aicin ya fara so ya dameta don haka take son ta d'an fita, kuma ta san in dai ta tambaye shi zai barta, matsalarta kawai shine kowa sai yayi magana in yaji ta fitan, don ga Mairo nan ma ta fara.

Sai ta koma da baya ta sake kwanciya akan gadon sanda Mairo ta cigaba da cewa.

"Bintu abinda nake so ki fahimta shine daga ke har shi wannan shine aurenku na farko, kuma kowa ya san a yadda auren yazo don haka ki bari hankalin mutane ya d'an d'auke daga kanku tukunna, zuwa wani lokaci ba wanda zaice wani abu don kin fita."
Zuwa wani lokaci. shima haka yace mata, zuwa wani lokaci zai rabu da ita, to ta yaya kuwa zata yi ta zama babu abinyi har 'Zuwa wani lokaci?'
Sai dai har ta bud'e baki zata yi magana, ta tsinci k'arar knocking a jikin k'ofar d'akin, babu shiri ta mik'e zaune idanunta d'auke da mamaki.

"Waye?" Tambayar ta fito daga bakinta tun kafin ma ta san ta ma ta fad'a, kuma a take taga wautarta k'arara, waye zai mata knocking da safe in ba wanda suka kwana suka tashi tare ba?

To bai tafi aiki ba dama?

Sai ta juyo da fuskar wayarta ta kalla, a lokacin wayar da suke yi da Mairo ta katse...

Abinda ta gani ya k'ara sawa ta zare idanu, yau asabar!

Hutun k'arshen sati! yana gida!

Ya salam kwata-kwata ta manta don a wancan k'arshen satin yayi tafiya Katsina ne tsawon kwanaki uku wanda ya had'a har da litinin.

Ba shiri tayi wulli da wayar ta lalubi ribbon akan gadon ta d'aure gashinta, sannan ta jawo hijabin sallarta ta zura, ta kalli fuskarta a mudubi kafin ta wuce bud'e k'ofar, babu kwantsa a idonta amma ta sake murje shi sannan ta kwantar da gashin girarta.

Yana tsaye kuwa sanda ta bud'e k'ofar, sanye cikin farar T-shirt da wando 3-quater, sannan gashin kansa a barbaje, zuciyarta ta matse don rabon da ta ganshi a haka tun lokacin da suna America, wai baya jin sanyi ne?

Shima ita d'in yake kallo, sai dai shi ba kallon nazari yake mata ba, kallo ne kamar na wanda ya kama mai laifi, taji zuciyarta ta matso cikin mak'ogwaronta sannan iska tayi mata wuyar shak'a, ko dai tayi masa laifin ne?

"Kin tashi lafiya?" Muryarsa mai zurfi ta gaisheta kafin ta gama tunanin, nata hankalin gaisuwar yazo.

Kunya ta ratsa ta, sai tayi saurin sakin hannun k'ofar sannan ta gaishe shi.

"I'm sorry na tashe ki ne?" Ya furta a hankali cikin sigar damuwa wanda ya cakud'e da taushin muryarsa.

Watakila d'azu ta manta bata fad'i cewar muryarsa ma na d'aya daga cikin abinda yasa take k'ok'arin kauce masa ba, don har yanzu duk sanda zai mata magana ji take kamar yana rad'a mata ne a kunne, bata san kuma yaya zata ji ba in har da zai lalubi kunnen nata ne ya rad'a mata.

Wata murya a cikin kanta ta rafka salati, kina da hankali kuwa Fadeelah? wane irin tunani kike yi haka alhali yana tsaye a gabanki? amma wata muryar ta kare ta da cewa to meye?

Ai ba haramun bane don kinyi wannan tunanin akansa.

A wajen kanta kuma, lallausar muryarsa ta sake maimata mata tambayar da yayi.

"Na tashe ki daga bacci ko?"
Sai tayi saurin girgiza kanta cikin riba biyu, ta bashi amsa kuma ta kad'e wad'ancan muryoyin biyu.

"A'a na tashi dama, kawai dai ban fito bane."
Ta k'ara da cewar.

"Na manta yau saturday, ban san kana gida ba."
"Nima banso na fito dake yanzu ba, wasu ne suka zo wai bak'in ki ne daga mak'ota."
Da turanci yayi maganar, watakila bai san yadda zai fad'i kalmar 'mak'otan' bane don har yanzu hausarsa bata zauna sosai ba don ma dai yana kokari ne, amma wad'anne irin mak'ota ne zasu shigo mata da safe haka?

Ta san dai mata biyu dake mak'otaka dasu a gefen gidan sun shigo mata kwanakin baya,
amma yanzu kuma bata san waye ba...

Bari dai taje ta gani koma su waye d'in, bari ta fincike kanta daga wannan yanayin mara kyau da take shirin fad'awa, saboda haka ta gyad'a kanta kawai tace bari taje su gaisa, amma maimakon ya bata hanya, sai ya k'ara matsowa dab da ita ya tsaya, hannayensa sunk'e cikin aljihun wandonsa.

"I want to ask you something. (Ina so in tambaye ki wani abu)"
Bata kalle shi ba, amma tana iya jin tsawonsa kamar na dutsen zuma a gabanta, don haka ba shiri zuciyarta ta shiga tsere, me kuma zai ce mata bayan yace bak'i suna jiranta? wani abu yayi girma a cikin mak'ogwaronta saboda tana iya jin tasirin kallon da yake mata a jikinta, hakan yasa ta dunk'ule yatsun k'afarta.

"Me yasa kike guduna?"
Bata san lokacin data saki k'afar tata ba sannan ta d'ago da idonta ta zare su akansa,
Me?

Ta ina ina wannan tambayar ta taho?

Ya akayi ya gane?

Waye ya bashi shawarar ya tambaye ta?

Saboda me ma zai tambaye tan?

Sai ta girgiza kanta.

"Ni ba gudunka nake yi ba, ina ganinka kullum, ta yaya zan guje ka."
Kusan gaskiya ta fad'a, don tana da hujjar kare kanta, shi kansa ya sani babu ranar da ba zasu ba kuma inda zai bata dama ma, tsaf zata lissafo masa kowanne kaya daya saka tun bayan tarewarta gidan, a jere ba tare da tsallaken koda rana guda ba.

Ta had'iye yawu kad'an tana aikawa zuciyarta kallon mamaki, don ko ita kanta bata san ta rik'e hakan ba sai yanzu.

Ga mamakinta sai yayi murmushi sannan ya gyad'a kansa kamar ya fahimta ko ya yarda da ita kafin yace.

"In kin gama da bak'in naki, akwai maganar da nake son muyi."
Ya k'ara jefa mata wani kallon kafin ya juya ya tafi.

Tabi bayansa da kallo sannan ta rufe idanunta alamun Allah ya kawo mata agaji, don bata san wane irin yak'i zata yi da zuciyarta ba in har suka zauna yin maganar.

Adam ya lumshe idanunsa sanda yake zaune a wani side falo dake hanyar zuwa kitchen, waya ya gama yi yanzu da abokin aikinsa Nasir akan wani case da suke yi tare, Nasir d'in ya nemi daya shigo ne don su fitar da sakamakon wani sauti da aka tace musu game da shari'ar da suke yi ta wani saurayi daya kashe k'anin mahaifinsa, amma kai tsaye ya shaida masa cewa ba zai iya fitowa ba, don a ko k'ofar gida baya son fita, hutu yake buk'ata irin wanda ya dad'e rabonsa dashi.

Ya kurb'i coffe d'in daya had'a a hankali sannan ya koma da baya ya jingina da kujerar, yau sati biyu kenan da tarewarsu a gidan, kuma a cikin wad'annan kwanakin yana tunanin ya cimma tsarinsa na bawa Fadeelah isashshen lokacin da hankalinta zai kwanta, don a yanzu ya lura fatarta tayi haske
kamar yadda take a baya sannan idanunta sun washe kamar madara, babu wannan d'ashewar, babu firgici a cikinsu balle kuma wani tunani.
Chapter 87 · 0% Book details