← Book details Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 95

Sashe 52

Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ai dama mun shirya Kawu, zuwanku kawai muke jira."
Watak'ila maganar ta bashi mamaki don saida ya d'an tsaya kamar kwakwalwarsa na gaya masa cewa da kunya ne fad'ar wad'annan maganganun wa yarinya k'arama kamar Bintu sa'ar 'yar cikinsa.

Kafin ya sake magana sai wayar hannunsa ta shiga kara don haka yayi amfani da damar ya fita daga d'akin.

"Idan su basu gaya miki ba, to akwai 'yan sanda k'ofar koda zaki sake tunanin guduwa." Cewar Kawu sulaiman kafin shima yabi bayansa.

"Kar ki saurari zancensu dan Allah deelah, ki barsu..."
"Basu da laifi Mami, ina tunanin ko waye a matsayinsu zaiyi hakan, mahaifiyarsu fa suke zargin na kashe, Uwa wadda ta kawo su duniya..."
Sai ta kasa k'arasawa saboda kukan da taji yana shirin kunyata dauriyarta.

"Deelah kin tuna wani a 'yanuwan mahaifinki wai Kawu Ibrahim?"
Ta d'aga kanta a lokaci guda.

"Na tuna kowa ai Mami, shi wa ne a wajen Babana amma ba nahaifiyarsu d'aya ba, a baya shi kad'ai ne mai tausayina a cikinsu, shi kad'ai ne nake samun sauk'i a wajensa."
"To a yanzun ma bai canja ba Fadeela, shi ya kira Daddy yace ya sama miki lauyan da zai kare ki, wallahi baki san yadda hankalina ya kwanta da hakan ba, saboda halayyarsu har tsoro take bani..

Wace irin k'iyayya ce wannan?"
"Mami tun asali basa sonmu dama..."
"Mairo ta riga ta gaya mana komai ba sai kin maimaita ba."
A lokaci d'aya taji azabar cikin kanta ta d'auke, ta d'ago ta kalli Mamin da tsantsar mamaki.

"Mairo?" Ta furta sunan da take jinsa bak'o a wajensa.

"Kwananta uku a asibitin nan Deelah tunda aka kawo ki a waiting area take kwana, sai a jiya ne kafin farkawarki ni da yaya Hadiza muka matsa mata kan taje gida ta d'an kintsa kanta, don baki ga yadda ta fita daga haiyacinta ba daga ita har mijin dake ta zarya..."
Sai ta d'ago da wayarta tana fad'in.

"Tun jiya ma da akace kin farka zan kira ta, Yaya Hadiza tace in kyaleta ta huta don ana fad'a zata taho, amma yanzu gwara a gaya mata tunda tafiya..."
Bata k'arasa ba Fadeelah ta mik'o hannunta dake d'aure da syringe da wani irin sauri ta damk'e wayar Mamin, a lokacin jinin dake cikin ledar ya k'are, k'arfin yadda ta rik'e wayar kuma yasa nata ya koma shiga ciki.

"Kar ki kirata Mami, Dan Allah kar ki kirata, bana son ganinta...

Wallahi har duniya ta k'are bana son sake ganinta.

Da tsananin mamaki Mamin ke kallon Fadeelah, ta san Mairo ta gaya musu cewa laifi tayi shi yasa su Kawu Yahyan da suka zo suka k'i kulata, to amma wane irin laifi ne da har a wannan halin ma Fadeelan da suke uwa d'aya uba d'aya zata juya mata baya?

Wai wani irin DANGI ne su Fadeelah haka?
______
3:43 PM.

Kawu Ibrahim na tsaye a harabar Babbar kotun cikin birnin Zariya yana tsumayin isowar motocin su Yahya da suka fad'a masa cewa suna dab da shigowa cikin garin.

Sai dai daga lokacin da suka yi wayar zuwa yanzu yaci ace sun iso, amma bai sani ba ko Yahyan k'arya yake masa tunda zuwa yanzu ya san sun samu labari abinda yayi daga wajen Kawu D'anjuman da suke bin umarninsa.

Ya jingina da wata mota dake ajiye a harabar wajen sanda kwakwalwarsa ta shiga tariyo masa maganganun Kawu D'anjuma lokacin da ya sake tunkararsa da zancen ya taimaka a janye shari'ar.

Ban yi mamaki ba da ka k'ara samuna da wannan zancen Ibrahim, Hajiya uwa ce a wajenka amma iya baki kawai, yau da ace ita ta tsugunna ta haife ka wallahi wannan tunanin ba zai tab'a zuwa kanka ba, amma baka san ciwonta ba balle ka san na mutuwarta.

Kai kaso ka auri uwar yarinyar nan tun kafin Abubakar marigayi yazo mana da zancenta, shi yasa baka tab'a ganin aibunta balle na 'ya'yan, shi yasa a baya har kayi kokarin had'a d'anka aure da 'yarta, ba don yarinyar ta nuna halinsu na 'yan tsintuwa ta gudu ba da yanzu yaro yana nan ka had'a shi baragurbi.

Sannan banyi tunanin cewa har zance mai girma irin wannan na kisan uwa a garemu zai zo ka d'auko tsohuwar soyayyarka ka d'ora akansa ba, ko ka manta Aminar ta mutu ne Ibrahim?

Idan don ita kake duk wad'annan abubuwan to yanzu bata nan, ya kamata ka bud'e idonka ka bari gaskiya tayi halinta, don gara ma ka sani, yau idan Sadiya da muke uwa d'aya ake zargi da kashe Hajiya, wallahi sai na saka an gurfanar da ita a kotu balle wannan yarinyar."
Ba zai manta kallon da Kawu Danjuman ya bishi dashi ba lokacin da ya furta.

"Na fahimci dukkan kalamanka Kawu, kuma banga laifinka ko kad'an ba don ra'ayinka ne, sai dai abinda zance shine ayi hakuri don Adamu ba zai samu damar karb'ar shari'arku ba, na riga na bashi umarnin cewa ya kare Bintu!"
Ba zai manta idanun Kawu D'anjuma a lokacin ba, ba zai manta kallon dake fitowa daga cikinsu ba, don sawa suka yi yaji kamar yasa gatari ne ya raba Babban gida b'ari biyu, ya d'auki wani b'arin daban da nasu, amma bai damu ba, don in har yayi iya k'ok'arinsa wajen kare Bintu koda kuwa babu nasara ya san cewa bai bagarar da yardar da yayansa marigayi ya bashi akan iyalansa ba, ya san kuma ko ba komai, bai bari jinin Amina ya wulak'anta a duniya ba.

Bayan k'arasowar su Yahya, a yanzu jiran Adam ne kawai ya rage masa, wanda ya bashi tabbacin cewa gobe da safe shima zai biyo jirgi ya taho tare da Sa'id, don sai ya k'arasa wani cike-cike da k'ungiyar da yake aiki ne sannan zai, Tunaninsa ya katse, sanda jerin motoci guda biyu suka shigo harabar kotun, ta ukunsu k'atuwar jeep ce ta 'yan sanda wanda ya tabbata a ciki Bintu take.

Motocin suka tsaya a gefe guda na wajen sannan mutane suka shiga fitowa daga cikinsu, ta farko wata tsohuwar golf ce dasu Yahyan ke ciki, wanda saurin fitowarsu ya shaida gajiya da kuma takurar da suka sha a cikinta, ta biyun kuma wata mulmulalliyar mota ce k'irar da Kawu Ibrahim d'in bai taba gani ba rufe ruf!

Cikin gilashin dake shaida ni'imar Ac dake cikinta, mata biyu ne suka fito daga baya, sai namiji d'aya da kuma wata matashiyar budurwa daga gaba.

Ba sai wani ya gaya masa ba ya fahimci sune marik'an Bintun da komai ke faruwa saboda ita.

Idon sa ya juya kan motar 'yan sandan da suka diro rik'e da bindigoginsu, a sannan ne yaga sanda d'aya daga cikin 'yan sandan ya bud'e gaban motar dake rufe da bak'in gilashi, a sannan ne kuma idanunsa suka hango masa Fatima Bintun dake zaune cikin bak'ar jallabiya da bak'in mayafe yafe a kanta.

Ya k'ifta idonsa ya sake bud'ewa amma ya kasa yarda wai Bintun da ya sani a baya yake gani a yanzu, wannan yarinyar dake shafe yinin ranarta a kullum cikin bautar Hajiya, wannan marainiyar data rasa duk wani gata da tallafin duniya bayan rasuwar iyayenta, wannan Bintun dai da ta bar gida da wannan cukurkud'adden hijabin da yayi mata gani na k'arshe a cikinsa.

Ta yaya Sadiya ta iya gane ta a wannan kammanin?

Ya san ita fara ce amma wannan farin nata ya zarce na Bintun daya sani, kamannin ma sun fik'e sun zarta na wannan yasasshiyar
marainiyar daya sani a Babban gida.

Ba don 'yansandan da kuma su Yahya ba, ya tabbata ba zai shaida cewa wannan ce Bintun da shari'a ke jiran zuwanta ba.
_____
4:06PM.

Ba'a bari Kawu Ibrahim ya samu ganinta ba har saida aka gama duk wasu cike-cike da tsare-tsare wanda Bintun tayi su babu musu kamar injin da aka saita akan hakan, daga nan aka bata cell a cikin kotun kuma aka umarce shi da sai yabi hanyar da mutum ke bi don ganin mai laifi.

A d'akin da ake ganin masu laifin ya zauna sannan mai tsaro guda d'aya ya fito da ita, ta k'araso ta zauna a kujerar dake fuskantarsa yayin da mai tsaron ya koma ya tsaya daga gefe.

Sai a yanzu da yake kusa da ita, sannan yaga kammanin Bintun daya sani a baya, ya d'an tsaya ya kalle ta
idanunsa cike taf da alhini, kafin ta gaishe shi da muryarta mai rawa, sai yace.

"Yaya jikin naki?

Ance yau aka sallamo ki koh?"
Sautin muryarsa ya dawowa da Fadeelah komai game dashi, zuciyarta ta tare ta kuma goge tsawon wannan lokacin data bar gida, taji a ranta cewa a jiya ne kawai komai ya faru, a jiya ne yazo ya tashe ta tsakar dare yake shaida mata cewa za'a kaita police station da safe, a yau kuma gari ya waye gasu a cikinsa, saboda haka maimakon ta amsa sai tace.

"Kawu kayi hak'uri, rashin mafita ne yasa na gudu na bar gida, amma wallahi bani na kashe Hajiya ba, ban kashe ta ba kuma ba zan tab'a iya kashe ta ba, na fad'a maka tun a wancan lokacin."
"Na sani Bintu, na fahimci komai ba sai kin maimaita ba, don komai ya riga ya wuce sai dai mu fuskanci abinda ke gabanmu a yanzu, na samo lauyan da zai kare ki, d'anuwanki ne ma, d'an k'anina Ahmadu da kike ji a baya ana cewa ya b'ata, shine ya nemo mu bayan bakya nan yazo har Babban gida a cikakken lauyansa, munyi maganar dashi kuma zai zo ya ganki gobe insha Allah, ina so ki fad'a masa duk wani abu da zaki iya tunawa don Allah."
Sai ta d'ago da idonta ta kalle shi, har sai an rok'e ta ma? ita da a yanzu take neman duk wata hanyar da zata iya samun nasara akan Habiba da kuma su Kawu D'anjuma, don ta karyata tunaninsu akanta ta kuma nuna musu darajarta na d'iyar 'yar gudun hijirar da suke gudu.

"Kawu, naga Mairo ma a can."
Ya gyad'a kansa sau d'aya.
Chapter 52 · 0% Book details