Sashe 81
Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kwata-kwata ta manta da hakan don a lokacin ta k'okarin farfad'owa take, sai kuma rasuwar Sadiya da zancen rashin lafiyar Adam tazo ta danne maganar a zuciyarta.
Saboda haka yanzu ta fahimci zancen na Mami, k'okarin shirya tafiyar su Zahra can Washington take yi saboda bikin nasa yazo.
A lokaci guda taji kwarin jikinta na neman guduwa kamar an zare mata laka, amma bata ga dalilin da zai sa taji hakan ba don ana shirin bikin Al'ameen... mutumin daya yaudareta, ya kuma tilastawa Mami akan ta taya shi b'oye cewa zai aure ta ne ba da izinin mahaifiyarsa ba, Allah ya sani bata ji haushin Mami na yin hakan ba ko kad'an, saboda ta san irin yadda ta d'auki Al'ameen kuma watak'ila a lokacin ta fahimci itama tana son shi.
Sai ta mik'e daga wajen gabada'ya ta koma cikin d'akin Aunty Hassanan ta kwanta.
Tunaninta ya gangara kan maganar da ta tab'a gayawa Al'ameen a America, lokacin daya fara cewa yana sonta.
Zuciyarka ta gaya maka tana sona, saboda haka kana k'okarin bata abinda kake so ne kawai ba tare da tunanin halin da ni zan shiga ba.
Na gaya miki...
Baka gaya min komai ba Al'ameen sai son zuciyarka kuma na fahimce ka sarai saboda haka nima ka fahimce ni ka fita daga rayuwata, na fad'a maka bana sonka kuma bana sonka a cikin rayuwata.
A yanzu ta kuma yarda Al'ameen son zuciyarsa kawai ya sani, baya tab'a duba halin da waninsa zai shiga illa tabbatuwar abinda yake so kawai, sanda ake shirin bikinsu, bai damu da yaya mahaifiyarsa zata ji ba in har ya aureta ko kuma ita kanta ta yaya zata iya rayuwa a inuwar wadda bata k'aunarta.
Duk abinda ta gaya masa a wancan karon gaskiya ne, abu d'aya kawai da tayi k'aryarsa shine da tace bata sonsa, wannan k'arya ne, ta so shi a wancan karon kuma ta so shi a lokaci baya kad'an saboda iya mu'amala da kuma kyawunsa, amma banda yanzu...
Yanzu data shiga duk wani nau'i na kalar rayuwa ta fito harda kuwa wanda ya sata a ciki.
Ta ja guntun tsaki kafin ta janyo hijabin Mairo dake gefe ta rufe fuskarta dashi.
Alak'arta da yayarta ta gyaru tun daga ranar da aka sallame ta daga kotu, a ranar data fahimci cewa ba wai abinda kake dashi ne a rayuwa mai muhimmanci ba, illa wanda kake dashi a rayuwarka.
Don haka a yanzu kullum tare suke kwana suke tashi cikin tarin labaran da basa yankewa akan abubuwan da kowannensu ya shiga bayan zamanin da suka rabu, sai dai hirar bata tab'a gangarawa kan shari'ar da aka gama da kuma d'an zaman kurkukun da tayi, ta fahimci Mairo na k'ok'arin tallafota ne don ganin ta farfad'o ta saki jikinta sosai, saboda ko zancen fasa aurenta sau d'aya ta tab'a yi mata shi da fatan Allah yasa hakan shine mafi alkhairi ya kuma bata wanda yafi shi.
Sannan itama bata fiye yi mata zancen mijinta ba illa na 'ya'yanta kawai, kuma hakan ya taimaka sosai wajen wanke zuciyar kowannensu daga uk'ubar da suka fito.
Kawu Ibrahim yace zata koma wajensu Mami in al'amura sun natsa amma ita gani take yanzu ba zata iya tafiya tayi nisa da Mairo ba.
Aunty Hassanah ta gaya mata dukkan irin abinda ya faru da mijinta da kuma irin zirga-zirgar wahalar da yake yi na ganin ta koma, wanda har yanzu bai samu kwakwakwaran mutum d'aya da zai tunkara a Babban gida ba hatta kuwa shi Kawu Ibrahim d'in, daga shi sai su Saminu masu taimaka masa ke ta bulayinsu har yanzu.
Ita kanta bata son Mairo ta koma wajen mutumin daya cuce ta, amma Aunty Hassanah tace komawar tata shi yafi ko don k'ananan 'ya'yanta da ba'a san hannun wa zasu fad'a ba in har ta dage dole sai ta rabu dashi.
Zuciyarta ta cigaba da sak'e-sake cikin duhun hijabin da yayi mata dad'i a fuska kafin a yaye shi.
"Tunanin me kike yi?"
Mairo ta tambaya tana zama a gefen gadon.
Ta d'ago da idonta ta kalle ta daga kwancen, bata san yaushe tayi wanka ba amma ta canja hijabin jikinta zuwa wani sea green daya k'ara haskata, Allah ya sani dole ne mijinta ya nace da bibiyar ta koma gidansa don Mairo tana da kyau, irin kyawun da ta tabbata koina zata shiga a fad'in duniya babu wanda zaiyi mata kallon daban, saboda irin wannan kyan ne da d'aid'aikun mutane kawai Allah ke zab'a cikin jinsi ya azurta su dashi..
"Wai nace tunanin me kike yi?"
Ta sake katse ta da alamun damuwa a fuskarta.
"Ba komai..." Ta amsa tana k'ok'arin cire wani guntun farce a yatsanta na hagu.
"...
Kawai tunaninsu Afran ki nake, ina son in gansu ko suna kama dake."
Da jin haka sai ta janyo hijabin da ta cire a fuskarta ta shiga ninkewa.
"Kar ki wani damu kanki da wannan tunanin, d'azu Saminu yazo yake ce min Babansu yace zasu zo tare da 'yanuwansu suyi gaisuwa."
Sai ta tsaya daga k'ok'arin cire farcen.
"Da gaske?
Yaushe zasu zo?"
"Ban sani ba gaskiya, zancen da nazo gaya miki ma daban ne, Saminun yace min wai an sallami Adam daga asibiti, an maida shi gida yanzu."
Adam.
Asibiti.
Kalaman suka yi nauyi a cikin zuciyar Fadeelah, yau kwanaki uku kenan, tun ranar da aka sami labarin rasuwar Sadiya, Sa'id yayi waya cewar Adam ma ya tashi da wani irin zazzab'i har asibitin da suka je sun rik'e shi, don haka tun wannan ranar mutane ke zarya daga wajen makokin zuwa cikin Zariyan dubo shi.
Bata samu tayi magana dashi a ranar da aka sallame ta ba don bata ma k'ara ganinsa ba tun bayan da aka gama zaman kotun, tayi tunanin zuwa dubo shi itama amma ta san Kawu Ibrahim ba zai bari ba.
Don tun sanda suka shigo b'angaren Aunty Hassana a daren da k'afarta ta tako cikin Babban gida bayan tsawon wasu shekaru, bata lek'a koina ba, ko mutanen dake zuwa ganinta ma kad'an ne saboda rasuwar Sadiya data d'auke hankalin kowa, kuma hatta manyan babu wanda yayi wata magana har yanzu.
"Ya warke kenan?" Ta tambaya a hankali tana kallon Mairon wadda ta girgiza kanta.
"Saminu yace a yadda ya ganshi jiya dai yana jin jiki, watakila saboda zirga-zirgar dubo shin da ake yi ne ya matsa sai ya koma gida.
Kin san wanda ba bahaushe ba ba lallai yaso wannan jelan na mutane ba."
Sai ta gyad'a kanta a hankali tana k'ara tuno gutsirarrun labarin Adam wanda Mairo ta tsinta itama ta gaya mata.
Komai ya bada ma'ana a cikin labarin, abinda kawai bai bada ma'ana a cikin kanta ba shine me yasa daya ganta yak'i nuna ya santa?
Don ko sama da k'asa zata had'e baza ta tab'a yarda cewa ba shine Adam d'in data sani a America ba.
"Wallahi da Kawu zai yarda, da gobe Saminun ya kaimu munje mun dubo shi, mutumin da yayi maka babban taimako ai ya wuce irin wannan uzurin ya hana ka dubo shi."
Cewar Mairo, ta cigaba da cewa.
"Bawan Allan nan yana da kirki Bintu, d'an zamana a gidan nan baki gayadda yake hidima da mutane ba, yanzu haka fa komai na d'awainiyar b'angaren nan shi yake yi, sannan Aunty Hassana tace min yanzu duk mai wata buk'ata a Babban gida Sa'id kawai ake samu a fad'awa, da ya gaya masa shikenan wallahi ko nawa ne zai bada, shi kansa Kawu D'anjuman ba k'aramin sauk'in abubuwa ya samu ba da zuwansa, bashi da kyashi ko kad'an irin na al'adarmu."
Tana rufe baki Mami ta shigo d'akin.
"Har kin fito daga wankan?
Banga wucewarki ba." Ta tambayi Mairo kafin ta sami bakin gadon itama ta zauna.
"Na fito Mami, kuna ta magana da Aunty Saratu na wuce."
Mairo ta amsa da murmushi.
"Sannu Fadeelah, ya gajiyar jikin naki?"
"Da sauki sosai, Aunty Saratu tayi min gashi jiya naji dad'in jikina."
"Toh Allah ya sawwak'e, d'azu dana shigo Kawu Ibrahim yake ce min ya kira Daddy a waya cewar muzo wani satin akwai zama da za'ayi, ya gaya muku?"
Mairo ta girgiza kai.
"Wallahi bamu sani ba, kuma jiyan nan ma muke zancen komawar tata."
"To watakila sai ranar in munzo zamu tafi tare, Deelah na d'ebo miki wasu kayan sakawar, Hassanah ta tura yaranta su karb'o miki daga wajen Farouk."
"Toh Mami, Madallah."
"Yanzu zamu tafi kuma, Farouk yace jirgin da zamu bi k'arfe uku zai tashi, kina ganin zaki iya fitowa soro ku gaisa dashi?
Nayi nayi ya shigo yace wai mutane sunyi yawa."
A Babban soron shigowa cikin gidan suka sami Farouk bayan Aunty Hassanah da Aunty Saratu duk sun amince cewa taje d'in, Fadeelah ta cika da mamakin ganin yadda ya fara ajiye k'asumba a 'yan watanni kawai da ta rabu da ganinsa.
Taso ta tambayeshi su Usman da harkar makaranta amma ta lura kallon da yake mata na tsantsar tausayawa ne don haka ta bar zancen sai ta koma gida tukunna.
Motar da suka d'auko ta kawo su Ikara daga airpot d'in Kaduna na tsaye a gefen hagu na k'ofar gidan kasancewar rumfunan zaman makokin daga dama suke, don haka ita da Mairon data rako ta suka lek'a kad'an har zuwa tashinsu.
Sai dai me?
Motar tasu na tashi wata k'erarriyar mota k'irar Ford ta maye gurbinta, kuma kafin tayoyin motar su kai ga gama tsayawa ko kuma kafin su Fadeelan su kai ga juyawa cikin gida..
Wanda ke zaune a mazaunin direba ya bud'e k'ofarsa da wani irin sauri ya fito.
Wucewar 'yan sakanni kawai kafin idanun Mairo su daukar mata siffar Sadiq tsaye yana kallonta, bata k'ara ganinsa ba tun bayan ranar daya kawo ta saboda a haka kamar yadda yake kallonta da mamaki itama mamakin ne ya tsayar da k'afafunta daga juyawa ta koma ciki, sai da sauran k'ofofin motar suka shiga bud'ewa ne sannan komai ya tarwatse, ta juya da sauri tayi cikin gidan.
Fadeelah ta bita da kallo kafin ta dawo ta sake kallon mutumin dake tsaye a gefen bud'add'iyar k'ofar motarsa, da farko bata gane shi ba sai a yanzu data juya sannan taga kamar an saka wani abu daya zabge shekarun fuskarsa ya hasko mata shi a sanda ta sanshi...