← Book details Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 95

Sashe 83

Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"DANGi sune cikar zatin duk wani d'an adam a doron k'asa, sune wad'anda suke karb'ar mutum a kowanne irin yanayi na rayuwa, a cikinsu ne mutum ke samun tallafi da tausayawa koda kuwa duniya ta juya masa baya, amma mafi yawancinmu sai muka manta hakan, muka bari k'iyayyar da ba gaira ba dalili ta rinjaye mu muka cutar da yarinyar da bata da alhakin komai alhalin mai laifin yana cikinmu babu wanda ya tab'a zarginsa.

Don haka ina fatan wannan ya zama darasi a garemu kuma ina rok'on duk wanda muka d'auki alhakinsa da ya yafe mana don darajar ma'aikin Allah."
Daga nan ya jinjinawa Adam kan irin namijin k'okarin da yayi wajen baiyana gaskiya sannan shima ya rok'e shi da ya yafe masa akan wahalar daya bashi.

Hakan ya bud'e k'ofa ga su Kawu Yahya da sauran muk'arrabansa suma suka shoga neman yafiyarsa.

Ya wulkita idonsa kad'an tsakanin fuskokin da yake kalla, hankalinsa ya kwanta ganin Fadeelah ta d'ago kanta har tana magana da yayarta.

Bayan nan Kawu Ibrahim ya gabatar da marik'an Fadeelah ga jama'ar gidan, Kawu Danjuma yayi musu godiya sosai game da jinjina musu kan bajintar da suka yi.

Bayan haka Kawu Ibrahim yaso a tattauna matsalar Mairo amma a lokacin mijin nata da 'yanuwansa basu kai ga k'arasowa ba don haka ya yanke shawarar tafiya ga abinda suka riga suka gama shawararsa.

Ya kalli Daddy wanda ke zaune a hagun Kawu D'anjuma yace.

"Bayan wannan al'amarin ya natsa, dani 'yanuwana munyi shawara cewa a halin yanzu kai kafi cancanta da a kira ka da mahaifin Bintu, domin kai ka wahala da ita kuma kai ka d'auki duk wata d'awainiyarta, irin d'awainiyar da mu da muke 'yanuwan mahaifinta na jini ba muyi ba.

Don haka bisa shawarar da muka yanke a yanzu zamu nemi aurenta ne daga hannunka."
Kamar yadda madannin 'Pause' ke tsaida duk wani abu walau mai rai ko mara rai a cikin video, haka duniyar Fadeelah ta tsaya cak!

Lokacin da taji hakan, ta juyo daga sauraren maganar Mairo ta kalli Kawu Ibrahim daga inda take....

Zancen neman aure yake?

Aurenta kuma?

Dawa?

Wad'annan tambayoyin su suka dira a zukatan duk wasu mazaunan d'akin banda iya wad'anda Kawu Ibrahim ya tattauna zancen dasu.

Shi kansa Daddy tambayar daya bud'e baki yayi kenan.

"Aure kuma Kawu?

Auren Fadeelan?"
Kawu Bashir ne ya amsa masa wannan karon.

"Haka muke nufi Alhaji, in baka manta ba kun fad'a mana cewa ana tsaka da aurenta ne wannan al'amarin ya faru, kuma bayan haka kazo da 'yanuwanka ka gaya mana akasin da aka samu daga baya cewa auren ba zai yiwu ba, don haka muka yanke shawarar cewa a yanzu gwara ace ta tafi gidan mijinta ba wai don mun raina kulawarta karkashinka ba, a'a sai don dukkanmu munyi hasashen cewa hakan zaifi wajen wanke zuciyarta daga wannan al'amarin."
Fadeelah bata san sanda ta mik'a hannunta ta damk'e na Mami Saffiya dake d'aya gefenta ba, don gani take hakan ne kawai zai sa ta gane cewar ba'a tunaninta komai yake faruwa ba.

Daddy ya gyara zamansa kad'an sannan yace.

"Nagode da wannan matsayin kuma nima na goyi bayan shawararku don haka a shirye nake da ko YANZU in baku auren Fadeelah."
Babu b'ata lokaci kuwa muryar Kawu Ibrahim ta fad'i abinda ya girgiza tunanin mafi yawan mutanen d'akin.

"Idan haka ne, to a yanzun ina nemawa d'ana ADAM izinin auren 'yarka FADEELAH!!"
Idan ka d'auke su Kawu Danjuma da suka riga suka san zancen, a wannan lokacin kaftanin mutanen d'akin nan yanayin reaction d'in mutanen cikinsa iri d'aya ne sai dai na wasu yafi na wasu amma banda Sa'id, wanda yayi wani murmushi mai fad'i sannan ya juya ya kalli Adam d'in dake zaune a gefensa baki a bud'e kamar mutumin da aka sassak'a.

Sai yanzu ya fahimci kud'in da ya ciro a Atm na menene!
----
BAYAN NA MUTU!

AYSHA SHAFI'EE
BAYAN SATI BIYU, ABUJA
GIDAN MAMI SAFIYYA.

F A D E E L A H
....

Yau Amarya sunanki daina tsabar kuka_
Kin riga kin shiga k'ungiya ta manyan mata
Daga yau baki da izini da bin 'yanmata
Zaki bar Baba da Inna don dalilin aure
Zaki k'aura daga garesu don dalilin aure
Tunda ansa miki lalle, daga yau kin girma
Duniya komai naki lokaci ne na wani Gimbiya!

Fadeelah na sanye cikin wata doguwar riga kalar ja yayin da wata mace k'abila ke tsaye a kanta tana mata kitso cikin wani style mitsi-mitsi, Afrah na zaune daga gefensu rike da kwalbar mai wadda ake shafawa tsakanin kitson tana surutunta, tana shafawa a nata gashin itama.

Fadeelah ta rufe idonta a hankali tana k'ok'arin maida kwallar dake shirin fitowa daga idonta, inda za'a barta ta fad'i gaskiya kuma a saurareta, rok'o zata yi a cire wak'ar nan don ba abinda take k'ara mata sai sake dulmiyar da zuciyarta...

Sake dulmiyar da zuciyarta kan zagayen halin da take ciki.

Yau sati biyu kenan da d'aurin aurenta kuma yau d'in ake shirin d'auke ta daga gabansu Mami.

Ta dad'e da zama matar aure tun daga wannan larabar da akayi taro a Babban gida, don a la'asar d'in ranar su Kawu Ibrahim suka d'aura aurenta da Adam a masallacin unguwar ba tare da tuntub'ar d'aya daga cikinsu ba, kuma har cikin d'akin Aunty Hassanah Mami ta kawo mata sadakinta dubu d'ari cif ta nad'e su cikin tafin hannunta.

Tayi kuka sosai a wannan ranar, don kowanne aure yana da nasaba ne da abubuwa da dama tun kafin faruwarsa har zuwa yinsa d'in, amma ita babu d'aya data had'a da Adam don haka gani kawai tayi kamar su Daddy sunyi kyauta da ita ne.

Sai dai in ka d'auke 'yan k'alilan mutanen cikin Babban gida da suka saka ran Kawu Ibrahim zai had'a Adam da 'ya'yansu, kowa ya nuna murnarsa a wannan ranar ta yadda babu wanda zai shigo gidan a lokacin yayi tunanin cewa ba'a dad'e da mutuwa a cikinsa ba.

Hakazalika a daren wannan ranar, tasha tarin nasihohin daga mutane da yawa dake nuna jin dad'i da farin cikinsu, nasihohin da suka yi barazanar tsinka duk wani irin tunaninta akan auren, Kawu Ibrahim yace.

"...Wannan auren dana yi miki Bintu, riba biyu zai zame miki a rayuwa, ina ganin abinda daga ke har shi ba kwa hangowa a yanzu sai kun zauna da juna tukunna, Allah ne shaidata ina k'okarin gyara rayuwarki ne kan tafarki mai inganci, don haka a wannan lokacin babu abinda ya dace dake sai auren, don duk dad'in rayuwar da zaki samu a gaba ba zai rufe miki wani bak'in cikin ba, amma in har kina zaune ne a k'ak'ashin inuwar aure, wannan rahamar kad'ai zata yaye miki abubuwa da dama..."
Daddy yace.

"Abinda iyayenki suka yanke daidai ne Fadeelah, kuma kar kiga cewa nima ban tambayi ra'ayinki ba na biye musu, na san kina da hakki kan a nemi izininki tukunna, amma nayi abinda na san koda na tambaye kin ba zaki kunyata ni bane, na san ba zaki tab'a cewa A'ah ba Fadeelah, don haka ina miki fatan alkhairi a wannan sabuwar rayuwar da zaki fara..."
Kawu Bashir yace.

"...Adam shi yafi kowa dacewa dake Bintu, shi ya san duk wata matsalarki da kuma irin halin da kika shiga, don haka zaifi tausaya miki akan duk wanda zamu had'a ki dashi sab'anin shi d'in, mun hango wani abu ne da daga ke har shi ba zaku tab'a ganinsa a yanzu ba.."
Kawu Danjuma yace.

"...

Koda kin yafe min Bintu na san ni mai laifi ne a wajenki har abada, amma ina so ki sani cewa sanda Kawunki yazo min da wannan shawarar na had'a ki aure da Adamu naji dad'i mutuk'a sosai, naji kamar ana shirin yin gyara ne ga katangar da nayi yunk'urin rusawa a baya, don wallahi har cikin raina na yarda aurenki da Adamu babban ginshik'i ne da zai gyara zumuncin DANGINMU.."
Bayan wad'annan, akwai maganganun maganganun mutane da yawa da suka cakude akanta, a yanzu ba zata iya rarrabe kowannensu ba saboda kusan duk suna tafiya ne cikin siga d'aya, fatan alkhairi da kuma yak'inin cewa Aurenta da Adam ba matsala bane.

"Wai ba zaki fito bane tun d'azu muke zaune a mota, usman sai mita yake"
Muryar Rahma wadda ta lek'o cikin d'akin ta katse tunaninta tana kallon Asiya dake zaune a gefen gado tana shayar da 'yar jaririyarta Hanan.

Ta haihu ne a lokacin tana cikin rud'anin shari'ah don haka ba wanda ya gaya mata sai da ta dawo kawai ta ganta da baby.

"To ba sai ya tashi sama yana mitar ba ub*n 'yan azalzala, wallahi sai Hanan ta gama zan fito kuma ku tafi ku gani."
Cewar Asiyan, zasu je kai kaya ne can gidan da za'a kaita tare dasu Aunty Hassanah wad'anda su sun dad'e da tafiya ita kuma ta tsayar da motarsu ta dawo ciki saboda kukan da yarinyar ta dame ta dashi.

Rahma bata ko jira k'arashen maganarta ba ta juya fuu! tana fad'in.

"Tabd'ijan, to wallahi kuwa baza mu jira ba, mu mun tafi kya samu me kawo ki."
"Kar Allah yasa ku jira ni d'in dangin masifaffu." Taja tsaki sannan ta kalli Fadeelah tace.

"Yaya Saifuddeen ya d'ebowa kansa wallahi, nan da 'yan watanni rayuwarsa na cikin kwale-kwale."
Bata san lokacin da tayi murmushi ba don a irin wannan lokacin hirarsu Asiya ce kawai ke tuna mata cewa akwai murmushi a duniya musamman ace Fatima na nan, don su bidirinsu kawai suke kamar wancan lokacin bikin nata, tayi kewar su Zahra ma, wad'anda har yanzu ke Washington tun bayan bikin Al'ameen basu dawo ba, tayi kewar shige da ficensu da kuma tarin k'awayensu masu iyayi kamar yadda suka gaiyato su a wancan lokacin.

Wancan lokacin da take shirin zama matar Al'ameen...

Lokacin da duk tarin jama'ar da suka zo babu wani DANGINTA, kowa bare ne da bata had'a ko d'igon jini dashi ba, amma abain dad'in yanzu shibe ita d'in mai 'yanci ce, a yau itama ta zama kamar Asiya lokacin bikinta, tana cikin danginta ta kowanne b'angare, banbancin kawai shine a yanzu ba lallai duka nata dangin tsakani da Allah suka zo taya murna ba, amma duk da haka dai sune DANGINTA kuma sai da sunansu zata samu duk wata d'aukaka da nasarar duniya.
Chapter 83 · 0% Book details