← Book details Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 95

Sashe 11

Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kuma kin san munce zamu taya ki samo wani solution d'in bayan hakan koh? me yasa zaki yanke hukunci a lokaci d'aya, me ya canja ra'ayinki haka?"
"Duk abinda zamu samo ba zai wuce abu guda uku ba, na farko ko ku kuce zaku koya min, wanda wasu topics d'in kuma baku kware akansu ba, ko kuma in shiga summer classes da hutu, in zaku fahimta kuma duk abu d'aya ne da yanzun... kwakwalwata bata iya gane lissafi a cikin mutane, hanya ta k'arshe da zamu iya samowa shine muce zamu nemi wani a cikin makarantar nan ya koya min, amma ku kalla ku gani..."
Ta fad'a tana nuna wata poster a gefensu dake nuna b'atanci ga musulmai.

"Da wannan abin wa kuke tunanin zai b'ata lokacinsa don koya min karatu?"
Gabad'ayansu suka yi shiru cikin tunani kafin Melissa ta kalle ta tace.

"Kafin ki kira Adam a jiyan, kwakwalwarki tayi tunanin me yasa shi d'in ya yarda zai koya miki bayan yana daga cikin masu yad'a irin wannan abubuwan?"
Tunanin hakan ya dirar mata a lokaci d'aya, tabbas yaci ace tayi wannan hangen...

Me yasa duk fad'in makarantar shi kadai kaddara ta tsamo a matsayin wanda zai koya mata karatu? ita d'in da bata ko kai shekara guda a makarantar ba kuma ba kowa ne ya kai ga saninta ba... ko dai hakan yana daga cikin wani shirinsu ne? amma kuma sai tayi tunanin wane shiri zasu yi akanta ita kad'ai sab'anin sauran musulman dake makarantar.

Fuskarta ta nuna damuwa amma tayi saurin ture ta gefe, a yanzu ta riga ta saka kanta cewa zata yin kuma bata son ta bawa su Melissa damar da zasu raunana dauriyarta.

"Ban sani ba.." Ta fad'a tana d'aga kafad'unta, "..watakila don bai san ko ni wacece bace, kuma ina fatan in ya sanin yace ya fasa, Sai Mr.

Hawkins ya samo wani."
A haka hirarsu ta cigaba tana kare duk wata hanya da suke kawowa wajen sukar shawarar data yanke, ita kanta har mamaki tayi na yadda bakinta yake furta yak'ini akan abin, bayan can cikin zuciyarta fanko ne.

A lokacin da period ta uku ta shiga, Fadeelah ta samu kanta da yawan kallon screen d'in wayarta haka kawai, ta rasa gane dalilin da zai sata yin hakan, amma sai zuciyarta ta kare ta da cewar don wayarta na silent ne bata son tayi missing kiransa lokaci ya dad'a tafiya.

Tare take yin AP Biology da Melissa,
saboda haka tare suka tafi Ajin wanda ya kasance period na hudu a ranar,
kamar kowanne class d'in Biology, science lab ne mai d'auke sinks da kuma kujeru a tsakani.

Mrs Rease ta shigo rik'e da folder ta a hannu, dogon gashinta a yau nannad'e cikin bun.

"Good morning class, Today we will..."
Muryarta ta cigaba da karad'e ajin tsawon period d'in, kuma duk da cewa hankalin Fadeelah a rabe yake gida biyu ba abinda bata fahimta a topic d'in ba, Biology yana d'aya daga cikin subjects d'in da take mutuk'ar so kuma take ganewa, watakila kuma don malamar ta iya koyarwa ne kamar yadda kowa ke fad'i.

Daidai lokacin da aka kad'a kararrawar gama class d'in, daidai lokacin kararrawar vibration na wayarta ya kad'a, wayar ta shiga motsi akan table d'in gabanta yayin da Number jiya da k'arfe tara da rabi ta nu
na akan screen d'inta.

A hankali ta d'aga ta kara a kunnenta sanda hayaniyar ajin ta ragu saboda fita da ake tayi.

"Hellloo..."
Sai ta matsar da wayar kad'an saboda yadda muryar ta sulale cikin kunnenta, me ya same shi ne wai? yau ma baccin yake yi?"
"Kin shigo makaranta?" Nadadden turancinsa ya tambaya kafin ta iya cewa wani abin.

"Eh." ta amsa a takaice.

"Okay." Ya fad'a sannan kiran ya katse.

Ta sauke wayar a hankali tana kallon yadda kiran ya b'ace daga fuskar wayar.

"Kin san cewa daga yanzu kin sa kanki cikin masifa ko?"
Melissa ta fad'a daga gefenta, sai ta gyad'a kanta a hankali ba tare da ta kalleta ba.

"Na sani."
Melissa tana da wani class d'in, saboda haka ita da Romilda ne kad'ai a cafteria suna cin abinci, a hankali take tauna abincinta tana saurarar mitar da Romildan keta nanatawa akan zancen Adam.

Wayarta tayi k'ara alamun shigowar sak'o.

Ki same ni a bayan makaranta.

Alhamdlilah, ta ayyana a ranta, in har baya son a gansu tare hakan yayi mata daidai, don itama abu na k'arshe da zata so a rayuwarta shine wani ya san da alaqar dake shirin faruwa a tsakaninsu.

A hankali hannayenta suka shiga cikin message d'in, ta rubuta.

I'm a freshman (ni sabuwar d'aliba ce) ba'a barinmu mu fita bayan makaranta.

Sakan d'aya, wani k'arar message d'in ya shigo.

Ki same ni a wajen store.

Wata mab'oyar, yayi daidai! abu na farko da baza su sami matsala akansa ba kenan.

Sai da ta gama cin abincinta tsaf! sannan tace da Romilda zata je lokarta, ta fad'i hakan ne saboda bakinta ba zai iya furta cewa zata je wajen Adam ne ba.

A jikin wata k'ofa dake fuskantar Store d'in ta hange shi, yana tsaye ya juya bayansa yana kallon can bangon ginin da baya b'ullewa.

Zuciyarta ta dagule a take, ta lumshe idanunta sannan ta kalli k'afafunta dake tafiya, k'arya zata yiwa kanta in har tace wannan ba shine abu mafi muni daya tab'a faruwa da ita tun da ta fara sabuwar rayuwarta ba.

Ya juyo da fuskarsa jin takunta.

"Kin san dad'ewar da nayi ina jiranki?"
Sai yanzu ta tabbatarwa kanta cewa a baya bata tab'a jin muryasa ba, don yanzu ma bata canja ba, kamar yadda taji ta a waya ne ta zata bacci yake... a lalace kamar baya cikin haiyacinsa sosai.

Ta tsuke bakinta kawai ba tare da ta amsa ba, idanunta na k'asa.

Shima bai nemi amsar ba, sai ya d'age hannunsa zuwa sama, alamun ya cusa shi cikin gashinsa ne yayin da d'ayan ke rik'e da wata folder, sai ya mik'o mata kafin tayi tunanin meye a ciki.

"Nayi magana da Mr.

Hawkins, zamu fara ranar monday, awa d'aya bayan an tashi kullum, a Library.

Wannan Topics d'inku ne watannin da akayi, ki duba su kafin monday."
Ta karb'i Folder ta bud'a ta, paper d'aya ce a ciki mai d'auke da jerin sunayen topics d'in.

"Sai na ganki."
Sautinsa ya sake fad'a a hankali sannan ya gifta ta ya wuce.

Kwakwalwar Fadeelah ta tsaya cak! da aiki yayin da k'afafunta suka manne a wajen, me ya d'auke ta?

Dak'ik'iyar da har baza ta iya rik'e sunayen topics ba?

Idonta ya sauka akan wasu daga cikin sunayen.

Pythagoras_
Numeric and Geometric Patterns_
Functions and Relationships_
Algebraic Expressions_
Algebraic Equations_
Geometry of Straight Lines...._
Ta cije lebb'enta na k'asa a hankali, ranar monday zata fara kwance wannan d'aurin data tanada!
*BAYAN NA MUTU!*
AYSHA SHAFI'EE
*05*
RANAR ASABAR.

"Lokacin yarintata a tsakanin shekarun 1980's zuwa 1990's, ni da yayyena biyu ne kad'ai musulmai a makarantarmu, kuma nasha had'uwa da k'alubale da yawa a lokacin saboda ni kad'aice macen dake saka dogon wando a maimakon k'aramin da ake sakawa na wasanni, ni kad'aice wadda bata zuwa fati irin na rawa da makaranta ke had'awa, sannan sunana yasha jawo min habaici da izgilanci ba'a wajen d'alibai kad'ai ba har da malamai.

Shi yasa a yanzu nake k'ok'arin cusawa 'ya'yana alfaharin kasancewarsu musulmai da kuma juriyar dogaro da kansu a lokaci irin wannan.

A watannin baya ne 'yata ta biyu ta shaida min cewa yara da yawa a makaranta na mata kallon kyama saboda hijaabinta amma bata tab'a basu damar da zasu tunkareta ba saboda bata damu da sanin gurb'ataccen tunaninsu game da addinita ba, a wannan lokacin nayi mutuk'ar farin ciki akan karfin hali da kuma juriyar dana hango a cikin idanunta, na san cewa tarbiyar dana ke mata ta fara tasiri akanta."
Sarah Muhammad, wata dattijuwar mace ta fad'a zaune a jerin zagayen kujerun sanda layi yazo kanta.

Fadeelah ta k'ifta idonta a hankali daga inda take zaune tana kallonta, suna zaune ne a cikin fad'ed'en d'akin taron dake cikin ginin wajen 'MUSLIM SUPPORT GROUP' (k'ungiyar tallafi ta musulmai.)
A watan baya daya wuce ne Mami Saffiya ta samu labari daga k'awarta cewa k'ungiyar ta bud'e zauren tattaunawa tsakanin mata da yaransu game da k'alubalen da suke fuskanta a yanzu, wanda ake saka ran haka zai taimaka wajen k'arfafa zuciyar yaran da wasu masu rauni wajen fuskantar duk irin k'alubalen da zai zo musu.

Zahra ta motsa kujerarta a gefen Fadeelah alamun gajiyawa sanda matar dake gaba ta shiga nata bayanin.

"Dani da k'anwata mu kad'ai ne ke azumi a cikin watan Ramadan, k'awayenmu sai suyi ta tambaya 'Yanzu baza ku ci komai ba tun daga safe har fad'uwar rana? ko ruwa baza ku sha ba?', duk sanda lokacin cin abinci yayi sai mu tafi can d'akin karatu mu k'are lokacinmu."
"Saura awa nawa lokacin ya k'are...?" Muryar Zahra ta rad'a a cikin kunnenta.

"...

Na gaji wallahi."
Fadeelah ta d'aga kafad'unta.

"Ban sani ba amma watakila nan da
wasu awannin biyun."
"Ya salaam ya Allah!" Ta fad'a tana jefa kanta saman kujerar.

Sarai Fadeelah ta san me Zahra ke kewa, Wayarta.

A tsawon wata gudan da suka fara zuwa wajen nan, suna barin gabad'aya wayoyinsu ne a mota, kamar yadda tsarin Mami ya tanadar.

"...

Ni da iyayena munsha mutuk'ar wahala wajen wayar da kan hukumar makarantar dana ke a lokacin su san cewa hijaabin da nake sakawa yasha banbanci da tsarinsu na cewar ba'a yarda d'alibai su saka hula a makarantar ba, da kyar suka fahimci cewa hijaabin yana daga cikin 'yancina kuma ba zai zama watarana na saka watarana na cire ba kamar yadda hula take.

Amma duk da haka nasha fuskantar k'alubale daga wajen d'aliban, k'alubalen da bana son 'ya'yana su fuskance shi, shi yasa a yanzu na tura 'yata wata makarantar musulmai mai zaman kanta dake West Valley City."
"Kinyi hukunci mai kyau Zeena..."
Shugabar k'ungiyar, Amani Omar ta fad'a, da yawansu suka gyad'a kansu kafin ta cigaba.

"...

Abune mai kyau yadda kowannenmu ke fitowa yana fad'ar irin nasa k'alubalen da kuma tsoronsa, na yarda cewa hakan hanya ce mai b'ullewa da zata sa mu yak'e su.
Chapter 11 · 0% Book details