Sashe 78
Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Wannan rashin jituwar ita tasa tun a baya kika yi yunk'urin kawar da ita ta hanyoyi da dama amma hakan bai yiwu ba har saida kika yanke shawarar neman guba ki zuba mata a abinsha don a lokacin kina son cimma wani abu da kika san in dai tana nan to baza ta bari ki samu ba.
Haka ne?"
Gaban habiba ya had'e waje d'aya sannan yayi k'undunbala ya fado daga wata sama mai nisa, ya akayi ya san wannan abin?
Ya akayi ya san wannan sirrin nata?
Ya akayi ya binciko abinda ta b'oye daga idon duniya?
Daga ita sai aminiyarta Salame take kashewa ta binne irin wannan sirrin da ita...
Salame!
Sunan ya tsaya cak!
Akanta, ta bar zuwa kotun nan tun kwanaki data tazo ta kawo mata ziyara ta k'arshe a inda take tsare, zuwan data kula da canji sosai a tare da ita don bata wani dad'e ba ta d'auki jakarta ta tafi da cewar ciwon k'afarta ya ishe ta da wari.
Ai kuwa Tabbas! ta hanyarta ya samo wannan zancen kenan, Salame ta sayar da ita a idon duniya, tayi mata hali irin na d'an Adam, Butulu!
Sai ta had'iye yawu a mak'ogwaronta ta kuma had'iyewa sannan ta amsa.
"Haka ne yallab'ai."
Take kotun ta rud'e da hayaniyar 'yan Babban gida, a yau Habiba ta fito da zaton kowa da kuma zargin da ake mata gaban duniya ta gaskata shi.
Salati da maganganu suka cika wajen ba tsayawa, kowa na fad'in albarkacin bakinsa.
Habiba ta kawar da kai gefe, ta yarda dole ne a yanzu ta ture komai ta amshi laifinta, don alhaki kwikwiyo ne baya tab'a daina bibiyar d'an Adam, kuma a yanzu haka ma bata hango wani dad'i nan gaba a rayuwarta, 'ya'yanta maza uku da tun farko bata jasu a jikinta ba yanzu haka duk sun yar da ita, matansu sun janye su ba mai zuwa wajenta sai autanta dashi baiyi aure ba, wanda tafi sharewa a baya da tunanin ya b'ata lokacinsa wajen neman ilimin addini maimakon ya fita kasuwa ya nemi kud'i, shi kad'ai ne a yanzu ke ta d'awainiya da ita da kuma ciwonta.
Sannan dukiyar da take tarawa ma yanzu babu ita, zuwanta Niger kwanakin baya ya cinye mata komai, ragowar kud'inta na gida yanzu baza su doshi dubu d'ari biyar ba, don a baya ma filayenta ta siyar tayi gyaran d'aki, bata da wani kwakkwaran d'an'uwa sannan bata da wani mai sonta a Babban gida, to 'ya'yanta ma sun guje ta balle wani?
Dole ne a yanzu ta sauke komai ta karb'i laifinta...
Lokaci yayi da Bintu zata fita daga sharrinta!
Da kyar aka samu surutun wajen ya lafa, Adam ya gyara tsayuwarsa yace.
"Kenan a yanzu kin yarda da zargin da ake miki na farko?"
Tasa hannu ta d'auke kwalla a gefen idonta sannan tace.
"Na yarda, kuma duk abinda na fad'a wancan karon dana tsaya a nan k'arya ne, waccan yarinyar Bintu bata da laifin komai, k'awata Salame ce ta bani shawarar muyi amfani da ita don kar a zarge mu, duk abinda ta fad'a gaskiya ne, ni nayi kokon a wannan ranar kuma na zuba gubar dana samo a wajen Malam Salisu a ciki, Bintu tazo ta d'auka ne bayan ta gama wankin da Hajiyar ta saka ta.
Ina rok'on kotu dama duk wanda na d'auki alhakinsa ya yafe min."
Wannan karon da kyar aka samu kowa ya saurara saboda tsabar yadda wajen ya rud'e da hayaniya, har sai da Alkali yayi gargad'i ga kowannensu ya kuma karanto wasu daga cikin sharad'an karya dokar kotu sannan kowa ya shiga hankalinsa aka nutsu.
Tambayar da Adam yayi mata ta gaba shine ta baiyanawa kotu inda ta samo gubar da tayi amfani da ita.
Muryarta na rawar kuka kuwa ta shiga bayani tiryan-tiryan yadda taje wajen Malam Salisu kamar yadda Adam yaji daga bakinsa a k'auyen Mimbiri, Habiba bata b'oye komai ba don har jayayyar da suka yi akan ba zai bata ba sai da ta fad'a, da kuma yadda daga baya yazo har gida ya kawo matan.
A yanzu da babu damar hayaniya, kotun ta d'auki wani irin shiru daya wuce hankali, ba abinda ke haskawa a fuskokin mutane sai mamaki da rud'ani tsantsarsu!
Da mamaki kaci karo da abinda baka tab'a zatonsa ba...
Da mamaki yadda wannan gaskiyar ke fitowa tar! daga bakin Habiba.
Sab'anin yadda mamakin kowa ya ta'allak'a akan Habiba, Kutama nasa akan Adam yake, yayi shiru kawai dunk'ule da hannu akan bakinsa, a iya saninsa da kuma shekarun daya d'iba akan aiki, bai tab'a ganin lauya irinsa ba... ta yaya a rana d'aya kawai da ya karb'i shari'ar zai fito da wannan bayanan?
Wata nawa shi ya d'iba yana gabatar da nasa shaidun da basu tab'a tasiri irin haka ba?
Wace irin hazak'a ce dashi da zai fito da komai a wannan d'an k'ankanin lokacin?
Ya had'iye wani dunk'ulen yawu a mak'ogwaronsa, fargabarsa a yanzu ba ta fad'uwa shari'ar nan bace don ya riga ya gama cin kud'insa, fargabarsa d'aya ce, in har Adam zai kasance a Nigeria, dole ne hanyar samun abincinsa zata k'aranta.
Habiba bata tsaya ba sai da ta dire gaskiyar komai har zuwa sanda ta gama had'a koko mai gubar, da sanda Bintu tazo ta d'auka ta tafi, da sanda akayi shelar mutuwar Hajiya, da sanda Bintun ta gudu aka neme ta har Kano aka rasa wanda hakan yasa shari'ar ta mutu, ita kuma ta bud'e nata babin cin duniyar daga nan.
Hannayen Kawu yahaya in banda rawa ba abinda suke yi, ji yake dama yana da ikon tashi ya fita ya kira Kawu Danjuma ya shaida masa duk abinda ke faruwa, wannan wace irin kunya ce suka jawowa kansu haka?
Tuntuni suna tare da wadda ta kashe mahafiyarsu amma suke ta bulayin neman yarinyar da bata da laifi, bata da alhakin komai? suka aikata abinda ya raba kan DANGINSU alhali baren data shigo cikinsu ita ta aikata komai...
Don a yanzu babu wani b'oye-b'oye komai ya fito fili cewa Habiba ce tayi kisan.
Sai dai me?
Kalaman da suka fito daga bakin Adam suka sake daskarar dashi a mazauninsa.
Ya d'ago da idonsa ya kalle shi, ya juya gaban alk'alin yana magana.
"Na san kotu ta saurari duk bayanan Habiba wanda babu k'arya a cikinsu, kuma na san kotu ta fara d'aukar wani b'angare na cewar Habiba tana da laifi a ciki, sai dai ina son kotu ta fahimci cewa ba haka al'amarin yake ba,
gubar da Habiba take zaton ta dama kokon Hajiya da ita ba guba bace face wani sassak'en magani da bashi da tasiri ko kad'an a jikun mutum, don haka Habiba bata da alhakin kashe Hajiya, daga ita har yarinyar sun fad'a tarkon wani mai sharrin ne, anyi amfani dasu a cimma wani burin."
A wannan karon kowa manta gargad'in Alkali yayi, waje ya sake rud'ewa da hayaniya wadda bata lafa ba har sanda Alk'alin ya kalli Adam yace.
"Wace shaida zaka bayar akan haka?"
Adam yace.
"Kamar yadda kotu taji a cikin bayanan Habiba, ta samo abinda take tunani guba ne a wajen wani mai sayar da magungunan gargajiya Malam Salisu, wanda a yanzu haka ya dad'e da barin garin ikara.
Sai dai naje har k'auyen da ya koma a yanzu kuma na same shi mun taytauna, ya gaya min gaskiyar komai kuma na gamsu da bayanansa, naso ace ya samu halartar wannan zaman da kansa amma yana cikin rashin lafiya irin ta tsufa kuma ya rasa k'afafunsa a dalilin hatsari, amma na samuna d'auko maganganunsa a lokacin da yake min bayanin.
Yana rufe baki Jabir ya taso rik'e da wata 'yar karamar recorder, ya mik'awa wani ma'aikaci dake zaune a teburin dake k'asan zungureran teburin Alkalin, mutumin ya k'arb'a ya jona a jikin speaker da wayar AUX, tak'e muryoyi suka shiga fitowa tar a kunnen kowa dake wajen.
Ni na san shari'ar nan baza ta tab'a mutuwa ba sai anyi ta, an samu yarinyar da ta gudu ne?
Eh ta dawo.
Muryar Adam ta ciki ta amsa.
Daga Habiba har yarinyar sun fad'a tarkon wani mai sharrin ne, anyi amfani dasu a cimma wani burin
Ban gane abinda kake nufi ba.
Ko waye ya turo ka kaje ka gaya masa ba Habiba ce ta kashe Hajiya Balaraba ba.
Tiryan-Tiryan hirarsa da Malam, Salisu ta shiga fitowa daga speaker har zuwa iya inda ya sanya a ciki, iya inda yake so ji.
"K'orafi ya mai shari'ah!"
Kutama ya mik'e a lokaci guda da muryoyin suka k'are.
"Kotu bata da tabbaci cewa wannan muryar ta wanda aka kira da Malam Salisu ce, za'a iya amfani da muryar wani a matsayin tasa."
Alkali ya juyo ya kalli Adam.
"Me zaka iya cewa game da haka?"
Muryarsa a nutse tana sulalowa kamar tafiyar tsutsa ya amsa.
"Ya mai girma mai shari'ah, bayan 'yan cikin babban gida akwai mutanen cikin Ikara da yawa a nan, kuma na tabbata duk a cikinsu babu wanda bai san Malam Salisu ba saboda shaharar da yayi a lokacinsa, na bawa lauya Kutama dama, zai iya zab'ar ko waye ya nemi tabbaci."
Alkali ya juya ya bawa kutama dama.
Mutum uku kuwa ya zab'o daga cikin 'yan kallo, biyu mutanen gari ne, d'aya kuma Saminu ne, d'an gidan gwaggo lami wa a wajen Bintu, dukkaninsu kuma suka fito suka tabbatar cewa muryar da aka kunna ta Malam Salisu ce, don haka ba wani kuzari kutama ya nemi waje ya zauna.
"Kotu ta gamsu da dukkan bayanan da aka gabatar don haka lauya zai iya kiran shaida ta gaba."
Alkalin ya fad'a cikin muryar dake nuna cewa shi kansa yana jin dad'in yadda shari'ar ke tafiya.
Habiba bata san me take ji ba har lokacin da wata mai tsaro ta taimaka ta fita da ita daga cikin akwatin wajen, ba wai an tabbatar bane amma zata shallake gaban mamaki in har akace ba ita ta kashe Hajiya ba, duk k'ok'arin da take ganin a baya wayonta ya shirya a banza ya tashi kenan... hukuncin Allah ya danne nata.