Sashe 92
Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ita ba mutum ce mai yarda da mafarki ba, amma da ace jiya bayan tafiyar Adam an samu wani ya mintsene ta, kuma ta farka ta ganta a wani lokacin daban ba wanda Adam ke gaya mata cewar ba zai iya rabuwa da ita ba don zuciyarsa na k'aunarta, tsaf zata oya yarda cewa mafarkin tayi saboda hakan abu ne da tab'a tunanin kwatankwacinsa ba balle har ya fito a zahiri ya zama gaskiya, a baya ta d'auka cewa Adam mutum ne da bai damu da komai ba face harkar aikinsa kawai, sai ko Kawu Ibrahim da yake wa kallon uba.
Don haka ta d'auka ita a wajensa ba komai bace sab'anin d'aya daga cikin tarin matan daya tab'a sani a America kuma sabuwar 'yar uwarsa daya taimakawa saboda Kawu Ibrahim kawai.
Ashe ba haka bane, ashe ta dad'e da shiga cikin zuciyarsa, ashe ta dad'e da zama abu mai muhimmanci a wajensa, ashe shima yana son cigaba da zama da ita shi yasa ya canja akalar zamansu, ashe yana sonta...
Yana sonta!
To amma ita kuma fa?
Yaya sunan abinda take ji game dashi...
Shin tuntuninsa a baya daya kasa barin zuciyarta a baya so ne?
Ko matsayinsa daya k'aru a zuciyarta bayan ya taimake ta shima so ne?
Ko kuma yanzu da take son cigaba da zama dashi hakan na nufin tana son sa ne?
A baya Fatima ta tabbatar mata cewa tana son Al'ameen ne saboda tunaninsa da zuciyarta ke yi, amma kuma in har wancan shine so, to baza ta tab'a had'a shi da abinda take ji game da Adam ba tuntuni kuwa, don in har tunani shine so, to tayi tunanin Adam fiye da sau d'ari kafin na Al'ameen, don shi sai tana ganinsa tukunna sannan kyawunsa da kyautatawarsa ke narka zuciyarta ta kasa mantawa dashi amma Adam....
Har tsawon bayan shekara guda rabuwarta dashi tunaninsa bai tab'a barin ranta ba duk da cewa kuwa bata k'ara ganinsa ba.
Amma duk da haka a jiya taji tana neman k'arin bayanin wani wanda zai taimaka ya faiyace mata ma'anar abinda take ji don haka ba shiri ta lalubo waya ta kira malamarta.
"Fatee yaya ma kika ce ana ganewa idan mutum yana son wani?" Ta tambaya bayan bugu d'aya kawai da
Fatiman ta d'auki wayar
kasancewarta ba mai saurin bacci ba.
"La'ilaha ilallahu! tsaya mana, Deelah wa kike so da aurenki?" Muryarta ta fito da sauri.
"Babu kowa, kawai ki gaya min."
"Fadeelah kwantar da hankalinki dan Allah
ki fad'a min komai a nutse yadda zan fahimta, kuma kiyi k'asa da muryarki don wannan al'amarin babba ne, amma zamu san yadda zamu yi maganin ko wane irin d'*n iska ne wannan kafin ma aje da nisa, ki gaya min waye shi?
A ina kuka had'u?
Bai san kina da aure bane yasa kika fara son sa?"
Da mamakin me Fatin ta d'auke ta tace.
"Fatee ba wani fa nake so ba, Adam ne."
Sai ta d'anyi shiru kafin tace.
"Adam kike so?
Ban gane ba?
Shine kuma kike fad'a min?"
Sai da Fatiman ta fad'i haka ne sannan ta fahimci abinda ta fad'a, sannan ta fahimci amsar da take nema, zuciyarta ta riga ta dad'e da son Adam, kawai rashin samun isashshiyar dama da kuma tarin abubuwan dake kanta a baya ne suka danne hakan, amma a yanzu da komai ya kauce rayuwarta ya zama daga shi sai ita, ba abinda ya isa ya kore hakan.
Ta bud'e idanunta a hankali tana kallon kalar kayan dake hannunta, fari da ja...
Jan mai haskawa kamar an watsa masa jini.
Tun a jiya ta yanke shawarar cewa itama zata fad'awa Adam gaskiyar zuciyarta, idan har zai iya ajiye duk wani matsayinsa ya gaya mata wad'annan kalaman, me zai hana ita kuma ta kasa? dole ta cire dukkan wata kunya ta fad'a masa cewa tana sonsa fiye da yadda yake tunani.
A rayuwarta ta fuskanci nau'i kala-kala na ma'anar k'unci don haka bata jin a yanzu kuma tana da karfin da zata iya fuskantar wani.
Maganganun Kawu Ibrahim suka haska cikin kanta.
"Wannan auren dana yi miki Bintu, riba biyu zai zame miki a rayuwa, ina ganin abinda daga ke har shi ba kwa hangowa a yanzu sai kun zauna da juna tukunna, Allah ne shaidata ina k'okarin gyara rayuwarki ne kan tafarki mai inganci, don haka a wannan lokacin babu abinda ya dace dake sai auren, don duk dad'in rayuwar da zaki samu a gaba ba zai rufe miki wani bak'in cikin ba, amma in har kina zaune ne a k'ak'ashin inuwar aure, wannan rahamar kad'ai zata yaye miki abubuwa da dama..."
Sai yanzu take fahimtar ma'anar kowacce kalma daya fad'a, sai yanzu ta hango irin rahamar da yake fad'a, to don me yasa kuwa zata kasa ajiye komai tak'i karbar wannan rahamar?
Matsalar shine zuciyarta tace zata iya, amma bata san ta yaya bakinta zai iya bud'ewa ya fad'a masa cewa itama tana son sa ba...
Don gashi tun ba'aje koina ba kayan da zata saka ma sun mata wuyar zab'a.
BAYAN NA MUTU!
AYSHA SHAFI'EE
BABI NA K'ARSHE!
"Barka da safiya."
Muryarta ta kutsa cikin tunaninsa, d'auke da d'umin da yafi na coffee d'in da yake sha a lokacin, yana zaune ne a falo cikin lallausan carpet d'in dake tsakiya mai kalar ruwan toka yana danne-danne a computersa, ya d'ago ya kalle ta, kallon da a lokaci guda yaji zuciyarsa ta tsaya cak na wasu 'yan sakanni kafin kuma ta cigaba da bugawa da k'arfin da yayi barazanar girgiza kofin hannunsa.
Tana sanye ne cikin wata doguwar riga ta material fara k'al, amma kuma an watsa mata adon wasu jajayen fulawowi masu haske akanta! haske sosai kamar an sirka su ne da kalar jini, daga inda yake zaune kuma yana iya jiyo k'amshin nan nata dake tsima zuciyarsa.
A baiyane yake cikin idanunta cewa taci baccinta ta gode Allah, alhalin shi sam bai samu baccin ba sai wajen hud'u na dare don har yaso ya makara sallar Asuba, kuma da ace zai je wajen aiki ma da ya dad'e da makara, a yanzu haka k'okarin turawa Nasir dake jiransa ayyukan da zasu yi yau yake, ya yanke shawarar ba zai fita yau bane, don ko yaje office d'in ba lallai ne ya tab'uka wani abun azo a gani ba, hankalinsa ba zai kwanta ba sai in har yaji amsar da Fadeelah zata bashi, amsar da zata baiyana masa matsayinsa a wajenta.
Ya san ya gaya mata ne cewa tana da damar da zata yi tunani daga yanzu zuwa tsawon lokaci, amma ba zai iya ba, a yadda yake jin kansa yanzu ba zai iya jiran hakan, don a daren jiya zuciyarsa ta sake jaddada masa cewa ba zai iya cigaba da zama da ita a irin tsarin da suka d'auko ba, in ba haka ba zai aikata abinda daga ita har shi zasu zo suna nadamarsa ne, don in zuciyarsa ta fad'i abu to da gaske take hakan ne.
Maimakon ya amsa gaisuwar tata, sai ya mik'o mata hannunsa alamun ta k'araso, yana ganin yadda ta kalli hannun kamar mai shawara da zuciyarta kafin ta mik'o masa natan, kuma a take ya nutse cikin taushinsu yayin da wani abu kamar zugi ya shiga bin jijiyoyinsa.
Ya matso da ita gabansa, ta durk'ushe cikin carpet d'in idanunta a k'asa, a cikin abu guda biyu bai san wanne yafi burge shi ba, kawalliyarta ko kuma ladabinta.
Ba tare da ya saki hannun
nata ba yace.
"Kin tashi lafiya?"
"Alhamdlilah."
Sai ya d'auko plate d'in sandwich d'in da yake ci, ya saka a tsakiyarsu, rabi akan k'afarta rabi a tasa.
"Bismillah, mu ci."
Ta girgiza kanta a hankali sannan tace.
"A'a, Thank you." Ya gyad'a kansa sannan shima yace.
"Thank you too for wearing this dress."
Maganar tasa ta d'ago da idonta ta kalle shi, ya d'aga mata duk girarsa biyu yace.
"Nayi zaton 'yar godiya muke yi ne."
Sai tayi d'an guntun murmushi tana kallon gefe.
Yace.
"Me yasa baza ki ci ba?"
"Bana iya cin abinci da sassafe."
Ya sake gyad'a kansa.
"Okay, ni kam tun d'azu nake ci ina jiran fitowarki kuma."
Ya lura tayi tunanin wani abu daban kafin ya d'ebe hakan da cewa.
"So nake ki fad'a min meye wannan abin don na san dai Sandwich ba haka yake da dad'i ba."
Baiyi mamaki ba sanda ta juyo da idonta ta sake kallonsa, don sun dad'e da saba irin wannan hirar, sabon abu shine yadda take zaune kusa dashi da kuma hannunta dake cikin nasa.
Tace.
"Kuma sunanshi kenan, don ance ba'a canjawa tuwo suna."
Ya k'ara kaishi bakinsa sannan yace.
"Na fahimta, amma kuma meye tuwon?"
Ta d'anyi shiru alamun mamaki kafin tace.
"Oh! na manta fa kai ba bahaushe bane, amma dai duk da haka zaka san tuwon ai, tunda kana zuwa Ikara."
Ya d'age gira d'aya cike da jin dad'in sakewarta.
"Waye yace ni ba bahaushe bane, bayan jininsu na yawo a jikina?"
"Jini daban, amma a magana dai ba wanda zai kira ka bahaushe balle kuma al'ada."
Sanyin muryarta ya shiga aika masa da sak'onni kala-kala cikin kansa, bai sanda ya ajiye kofin hannunsa ba tare da ture batun Nasir dake jiransa, ya k'ara gyara zamansa a gabanta yace.
"Kin san kuwa nine top kuwa a class d'inmu?"
Girarta biyu ta had'e.
"Wane class d'in?"
ayan dawowata Nigeria nayi joining wani online class da ake koya hausa ne a cikin 'yan watanni kawai, kuma nine mai highest grade a class d'in"
"Kuma an koya muku komai?"
"Komai." Ya tabbatar mata.
"To shi kanshi mai koyarwar yana buk'atar guidence gaskiya, don ina jin a al'adar bahaushe tuwo yana zuwa ne a saman abubuwa da yawa."
"Na fa san tuwo leelah, kawai dai ban gane a sentence d'in da kika saka shi bane."
Ta cije gefen lebb'enta na k'asa tana kallonsa.
"Kenan ba'a koya muku komai ba tunda baku san karin magana ba."
"Na san karin magana mana, akwai littafi guda ma dana tab'a karantawa akansa."
"Zaka iya tuna d'aya?"