← Book details Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 95

Sashe 23

Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Al'ameen da kai fa nake magana, ko baka jina ne?"
Aunty Miryaman ta fad'a zaune a kujerar kan dining da take fuskantarsa lokacin da yake cin abinci bayan ya koma gida a ranar, K'annensa mata na daga can tangamemen falo dake bayansu suna harkokinsu.

"Mommy me zan ce to, sau nawa ina gaya miki ni ba kula ta nake ba, na manta handkerchief d'ina ne wancan zuwan da nayi shine naje dubawa a wajen da suke shanya."
Ya fad'a hankalinsa na kan abincin, don yunwa yake ji sosai saboda tarin aikin da yasha a office, a matsayinsa na sabon ma'aikaci, kullum aiki yake na kusan awanni goma a kowacce rana, wanda a kwanakin baya a hakan yake matse lokacinsa yaje gidan Mami don kawai ya ganta!

"Ka san Allah Al'ameen, ka shiga hankalinka akan duk abinda kake shirin yi, don ka san sarai abinda zan d'auka da wanda ba zan tab'a lamunta ba."
"To."
Ya amsa kawai da lumsassun idanunsa masu cike fal! da damuwa, don kwata-kwata ba fahimtar abinda take cewa yake ba.

"Sannan ko ita Saffiyan bata fad'a min kai tsaye ba, na fahimci kana yawan zuwa gidan nan, kuma tun a baya na gaya maka bana so, ga sauran duka gidajen 'yan uwana da suke anan wadanda suka fisu kudi me yasa sai gidan zaka je?

Ko ni da kaga muna shiri da ita saboda tana da wayewa ne a wasu harkokin da nake son sani ba wai don komai ba, saboda haka kar ka sake in sake ganin ka cigaba da zirga-zirga a gidan nan balle har na sake ganinka tare da wannan mahaukaciyar yarinyar."
Ta k'arashe cike da zafin rai, ya sake d'aga mata kai kawai ba tare da ya fahimci abinda ta fad'a ba don washegari Alhamis, k'arfe bakwai da rabi na safe a k'ofar gidan Mami tayi masa.

Sai dai ba shiga yayi ba, yana tsaye daga cikin wata motar da ba wanda ya sanshi da ita a 'yan gidan, ya zuge gabad'aya tinted glasses d'inta yana sauraren cool music d'in dake fitowa daga cikin rediyon motar, idonsa na kallon yadda mutane daga kowanne gida ke ta fitowa suna tafiya wajen harkokinsu, har sanda k'ofar gidan ta bud'e, Farouq da Daddy suka fito, bayan wani lokaci kuma Zahra ta biyo bayansu sannan ita, ita d'in data hana zuciyarsa runtsawa a 'yan kwanakin, ta birkita tunaninsa ta kuma tsaida da yawa daga cikin harkokinsa.

Tana rik'e da hannun Iman sanye cikin kaya kalar shade d'in milk mai kama da light yellow, fuskarta nad'e cikin rolling d'in mayafinta a kullum, ya lumshe idonsa a hankali lokacin da ta bud'e k'ofar motar ta shiga.

A hankali ya tada tasa motar shima yabi bayansu, tiryan-tiryan har aka je makarantarsu Zahra aka sauke su, sannan ya cigaba da binsu har zuwa makarantar su inda suka sauka ita da Farouq, sannan Daddy yaja motar ya tafi wajen aikinsa.

A parking lot na makarantar yayi parking sannan ya fito, yabi ta cikin jerin d'aliban ya shiga ciki.

Abinda ya faru a wannan ranar, shi yayi sanadin guntule alak'arsa da Fadeelah, alak'ar data faru ta kuma k'are cikin abinda bai wuce wata guda ba, a tunaninsa kuma ya rabu da ita kenan har abada, don hatta ziyararsa gidan Mami ta ragu sosai wanda hakan ya sanya Aunty Miryamah cikin farin ciki da tunanin yayi mata biyayya ne yabi shawarta...

Sai dai daga ita har shi basu san cewa wata k'addarar bata ma fara ba!
*BAYAN WATA DAYA.*
"Na zata a rana ta k'arshe baza ki saka ni jiranki ba."
Muryar Adam ta fad'a a hankali sanda yake jingine jikin motarsa a harabar parking lot na wani k'aton amusement park (wajen shak'atawa) dake gabansu.

Bata san da wani irin yanayi mai dad'i ya tashi a yau ba wanda ya saka shi saka wata doguwar jacket ta cotton mai tsananin kyau kalar ruwan toka mai haske, gashinsa kansa a barbaje sannan yanayin fuskarsa a nutse, haka kurum sai taji kamar wani b'angare na zuciyarta itama ya samu nutsuwa da kallonsa.

A yau shine rana ta k'arshe da zasu k'are lesson d'insu, zasu kammala topic na ashirin da biyu a jerin wad'annan topic din daya fara bata da cewar ta haddace.

Abubuwa da yawa sun faru a cikin tsukin lokacin wanda muhimmi shine Daddy ya samu aiki a wani Babban asibiti dake Nigeria a birnin Abuja kuma suna ta shirye-shiyen tafiya ta kowanne b'angare.

Burin Mami ya cika don a yanzu kusan kullum sai sunyi waya da 'yan uwanta na gida akan shirin tafiyar, ta fahimci ba ita kad'ai ba dukkan 'yan uwanta irin murnarta suke yi don ita kad'ai ce take nesa dasu, don ma iyayenta duk sun rasu ne sai kishiyar mamanta ce kad'ai ta rage musu.

Jarabawar da taci burin yi don ta samu ta tsallake ajin gaba a yanzu ba zata tab'a yinta ba, sai dai karatunta da Adam wani babban nasara ne da baza ta tab'a manta shi ba a rayuwarta, ya bata alkhairin gane lissafi ta hanyoyi kala-kala da take ganin in za'a tara mutane dubu baza su iya ba sai an sami guda d'aya irinsa.

Shi yasa a yanzu take mutuk'ar ganin girma da kuma darajarsa, gashi kuma sunyi sabon da ta dad'e da ajiye dukkan wata gadarar da take masa a gefe, sannan yadda yake nuna sha'awarsa ga son sanin abubuwa game da addininta yasa ta rage kusan kashi saba'in na tsanarsa a cikin ranta, sauran talatin d'in yana jingine da cewar shi d'in ba musulmi bane har a lokacin.

"Kayi hakuri sai da nayi bayani a gida na fito that's why." Ta amsa a hankali.

Ya ciji gefen lebbensa kad'an sannan ya gyada kansa.

"You should'nt have done this, da baka wahalar da kanka ba, ba dole ne sai mun bi dukkan abinda na rubuta ba."
Ta fad'a tana nuna k'ofar shiga wajen, a jerin hobbies d'inta data rubuta harda zuwa irin parks d'in nan masu wadatar fili da bishiyu, wanda sanyin iskar wajen kan sa mutum ya manta da matsaloli da yawa na rayuwarsa.

Bata tab'a tunanin cewa kamar yadda suka bi dukkan abinda ta rubuta shima zasu zo kansa ba musamman ganin shine na k'arshe a jerin, sai a yau da ya same ta a makaranta ya bata ticket d'in wajen da cewar a can zasu yi lesson d'insu na k'arshe da misalin k'arfe hudu.

Sannan bata tab'a tunanin cewa Mami zata barta ba shi yasa ma bata tambaya da wuri ba, sai da ta nemi numbersa a wayarta ta rasa sannan ta yanke shawarar tambayar tunda babu ta hanyar da zata gaya masa cewar ba zata iya zuwa ba.

Dalilin makarar ta kenan don da alama hankalin Mami gabad'aya ya tattara wajen shirye-shiryen komawarsu Nigeria, shi yasa har ta iya barinta ta fito.

Lokacin da suka yi nisa a karatunsu daga cikin park d'in inda suka sami waje mara yawan mutane, Fadeelah ta kasa daure kanta wajen kallon fuskar Adam, wadda tayi tsananin kyau da wani fresh a lumshin yammar, dogon gashin idonsa daya kwanta akan na k'asa ya k'ara fito da cikar zatinsa, ance wai wanda yake ba musulmi ba a fuskarsa ake ganin cewa babu alamun rahma, amma ba don kar tayi sab'o ba, zata iya cewa a yanzu da ta san kammanin Adam sosai, zata iya kwatanta yanayinsa dana masu tsantsar Imani ma, a share zancen rashin musuluncin gefe.

Wani lokacin zai d'ago ya kalleta idan yaji shirun nata yayi yawa, bata san me yasa ba, haka kawai taji wani gefen zuciyarta na tunanin cewa daga yau shikenan karatu tsakaninta dashi ya k'are, watakila kuma ba zata sake ganinsa ba kenan, tunda akalar rayuwarta zata koma wani b'angaren daban, can tushenta gida Nigeria, inda sanadin komai ya fara daga nan!

"Ciwonki yayi sauki yanzu?"
Muryarsa ta tambaya a hankali lokacin da suka gama karatun dake shirin dasa aya a mu'amalarsu.

Da mamaki ta juyo ta kalle shi domin tun bayan ranar daya fad'a mata ya san wani abu game da ciwonta, bai sake sako zancen hakan ba sai a
yanzu.

Tunaninta ya gangara kan yadda ta soke zancen zuwanta asibiti itama a tsawon lokacin nan, tun sanda suka fara karatun ta wad'annan hanyoyin taji bata da bukatar ganin wani likita, zamanta dashi yasa ta koyi cewa ba sai mutum ya dogara da likita ba sannan zai iya samun sauki a ciwonsa, akwai hanyoyin da kai da kanka zaka nemowa kanka waraka.

Dr.

Florence ta dawo har sunyi kiranta sun gaji bata tab'a reporting apointment d'inta ba.

Al'amarin Al'ameen na kwanakin baya ne kawai ya saka ta cikin damuwar da taji tana buk'atar shawar wani, amma shima ta daure zuciyarta a tallafi kanta da kanta, tunda a lokacin da ta sanya shi cikin rayuwarta bata nemi shawarar kowa ba.

"Akwai abinda nake son in fad'a maka."
Ta fad'a ganin wannan ce damar da ya kamata tayi masa sallama.

"... watak'ila ba zaka ji dad'i ba amma ba yadda zanyi ne... a cikin watan nan zamu koma k'asarmu, don haka jarabawar da muke ta wannan tanadin don ita ba zan sami damar yi ba."
Kamar yadda mutum zai ji idan guduma ta fad'o masa a tsakar kai ba tare da zato ba, haka Adam yaji saukar maganarta amma sai ya b'oye ta hanyar tankwashe k'afarsa akan dardumar da suke zaune sannan ya lumshe idanunsa a hankali.

"Kina tunanin ba zan ji dad'i ba?"
Idanunta na kan yatsunta ta d'aga kai.

"Na sani babu dad'i ace duk abin nan da muke yi babu amfaninsa..."
"Amfaninsa yana tare dake har abada leelah kuma na koya miki karatun nan bane don kici jarabawar makarantar kawai ba, na koya miki ne don kici jarabawar Maths a koina cikin fadin duniya."
Ta d'ago ta kalle shi sannan ta gyad'a kanta a hankali.

"Nagode, ka taimake ni sosai ina fatan kaima Allah ya taimake ka ta hanyar data fi kowacce."
Sai ya mik'e tsaye rike da jakarsa, yayi murmushi kad'an wanda ya k'ara wa fuskarsa kyau, ya riga ya san me take nufi don haka yace.
Chapter 23 · 0% Book details