Sashe 44
Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Bibty akwai maganar da nake son na fad'a maka wadda ni kaina ban tabbatar da ita ba."
Watakila ba'a idanunta kad'ai ba, har a wajen wasu ma fuskarsa zata nuna cewa hankalinsa a kwance yake,
amma daga shi sai ubangijinsa suka san irin rud'ani da kuma tashin hankalin da yake ciki tun dawowarsa daga k'auyen 'Talfa'.
Ya san cewa a baya ya shigo da Maryam cikin rayuwarsa ne saboda burinsa da yake son cimma, amma tun kafin ma ya kammala samun burin nasa kyautatawarta a gareshi tasa ya kamu da son ta, bayan samun burin nasa kuma sai ya yarda cewa rayuwarsa baza ta tab'a tafiya daidai ba in har babu ita, ta riga ta zama kamar wani b'angare na jikinsa da ba zai iya yankewa ya yar ba, saboda haka sai ya ajiye komai shima ya biyewa wannan hasashen da shi da ita suka d'ora iyayensa cewa bata da DANGI, sai iya wata mata kad'ai daya kaita wajenta bayan sun gudo daga garinsu, inda yasa iyayensa suka nema masa aurenta a gurinta.
Hankalinsa a kwance yake da hakan tsawon shekaru, amma daga lokacin da tazo haihuwar d'ansu na biyu tasha wata irin wahala kamar zata mutu, daga wannan lokacin nadamar abinda yayi mata ta fara kama shi,
don kusan kwananta biyu cikin matsananciyar nak'uda kafin ta iya haihuwa saboda likitocin sunce gwara ta haihu da kanta, a sannan ne kuma daya duba yaga wata yayar mahaifiyarsa ce kad'ai tare da ita a asibitin sai tausayinta ya kamashi, ya ayyano da mutuwa zata yi kenan haka zata tafi babu kowa nata a kusa, saboda yasa an hana ta tuna duk wasu DANGINTA a duniya.
Nadamar abinda yayi ta fara kama shi har zuwa ranar da suka tsaya wajen bikin nan yaga alamun kwalla a idanunta, tunaninsa ya bashi cewa watakila taga wani ne data sani a baya kuma ta kasa gaya masa saboda ya riga yasa an k'ulle kwakwalwarta daga son tuna 'yanuwanta.
Amma a yanzu ya shiryawa komai, ya shirya masa da dukkan dauriya da kuma k'arfin hali, zai amsa tambayoyinta ya kuma karb'i laifinsa hannu biyu... abu d'aya da har yanzu bai shirya masa ba shine rabuwarsa da ita.
"Daddyn Afra ranar da muka tsaya a wajen bikin nan bayan mun dawo daga park..."
"Mommy Muhd ya zubar."
Muryar Afra ta katse ta sanda k'arar plate d'in abincinta ya tarwatse a k'asa.
Shikenan!
Sadiq ya ayyana a ransa sanda ta janye idanunta daga nasa ta tafi wajen yaran, daga yanzu komai zai fara, zai fara girbar k'addarar abinda ya shuka.
Yana kallonta ta kwashe abincin ta zuba a shara sannan ta bud'e k'asan fridge inda ba sanyi sosai ta d'auko madarar kwali, ta zubawa Afra a kofi sannan ta zubawa Muhd a feedersa mai straw, ta bawa kowannensu sannan ta sake dawowa ta d'ora idanunta akan nasa.
"Bibty ka tuna ranar?
Har na juya ka tambayeni me nake kallo?"
Bata bari ya amsa ba ta cigaba.
"Wata na gani kamar k'anwata Bintu ta can Ikara kuma tun daga lokacin sai na kasa mantawa da ita, kullum sai na tuna fuskarta don na tabbata ita d'in na gani."
Tirk'ashi!
Gabad'aya abin yazo kenan,
wato k'anwarta ma ta gani ba wai wani na nesa ba, k'anwarta da ya san ita kad'ai take da ita a duniya, to amma ta yaya hakan ta kasance?
Aikatau ne ya kawo ta Abuja ko me?
Don zai iya tuna yarinyar k'arama ce sosai a wancan lokacin da yake zuwa Ikara, don samun Maryam kawai!
"Ka tuna ta?" Muryarta ta katse tunaninsa, sai ya kamo duka hannayenta biyu ya matso da ita gabansa sosai.
"Ta yaya zan manta 'yaruwarki Sweetum, na gane Bintu sosai."
Ta shiga motsi da yatsun nata cikin hannunsa a hankali.
"Ban san ina zamu same ta yanzu ba,
amma da gaske ina son ganinta Daddy, jikina yana bani cewa bayan duk wad'annan shekarun 'yanuwana zasu manta da komai."
Da gaske ne yaje Talfa, da gaske ne ya tone kabarin nan kuma da gaske ne ya k'ona layar mutum-mutumin data zama silar arzikinsa, in ba haka ba tsawon shekarun nan yaushe Maryam ta tab'a zancen 'yanuwanta, yaushe ma ta iya tuna su balle har tayi tunanin komawarta wajensu?
Sai dai godiyarsa d'aya a lokacin shine bata yi tunanin ya akayi ta manta su a baya ba, ya akayi shima bai tab'a yi mata zancensu ba sannan ya akayi ma har ta iya gudowa daga gare su...
Don wad'annan tambayoyin su zasu canja akalar rayuwarsa.
"Kin shirya a yanzu kina son komawa wajensu kenan?"
Yayi tambayar ne da ma'ana biyu,
farko in har da gaske ta shirya tunkarar k'alubalen da daga ita har shi zasu fuskanta, sannan na biyu don ya maida abun kamar itace a baya bata neme su ba.
Ta d'aga kanta a hankali.
"Na shirya Daddy, ina ganin lokaci yayi da zan neme su...
Ko don su Afra."
Ya gyad'a kansa a hankali shima sannan ya fad'i abinda ya shirya masa
tun farkon bayaninta.
"Kije ki shirya yanzu mu fara da neman Bintunki Maryam."
Idanunta suka zare a lokaci guda.
"Yanzu?
Yau?"
"Ko zamu bari sai gobe?"
Sai ta saki hannunsa sannan ta shiga girgiza kai.
"Da gaske kake?"
"Da gaske nake, kije ki shirya."
"To amma ina zamu ganta? ranar ma.."
"Ssshhh..."
Ya matso a lokaci d'aya ya d'ora yatsansa akan lebb'enta.
"Kar kice komai, kije ki shirya mu fara gwadawa."
Mamaki ya kusa had'iye ta inda take a tsaye, anya daidai komai yake faruwa kuwa?
Ta yaya zai yarda da ita a lokaci d'aya haka?
Ta bud'e baki kamar zata sake yin magana kuma sai ta fasa ta d'auki Muhammad da sauri tayi hanyar d'aki da niyyar shiryawar tun kafin ma ya canja shawara.
Ya bi bayanta da kallo tare da godewa Allah data fasa maganar data yi niyya, don ya san in har godiya zata yi masa,
daga baya zata zo tayi dana sanin hakan fiye da tunaninta.
****
"Alhaji kace ranar shida ga wata ko?"
Habibu, mai kula da harkar wajen biki ya fad'a yana fitowa daga wani d'aki mai cike da takardu a cikin office d'insa.
"Kwarai ranar shida ga wata ne."
Sadiq ya amsa daga kan kujerar tsallaken teburin da yake zaune.
"To ai ba'a ma tafi da nisa ba, shi yasa da nayi tunanin sai mun duba sannan ka dawo, amma wata biyu ai record d'in yana kusa."
Ya karaso ya zauna akan kujerarsa sannan ya d'ora yatsansa d'aya kan wani layi a cikin littafin.
"Gashi nan bikin wata Aseeyah akayi daga yamma har zuwa Magariba."
"Washe gari fa?" Ya tambaya kai tsaye.
"Bikin wata Aminah Salihu Mu'azzam."
Kwarai!
Itace 'yar shugabansu a office da aka gaiyace shi suka zo bayan fitar da suka yi a ranar akace ba ranar ne bikin ba.
"Ranar bikin Aseeyan, an samu wad'anda suke zuwa neman bikin Amina?"
Habibu ya danyi murmushi sannan yace.
"Yallab'ai ai ni harkata ta masu zuwa neman hayar wajen ne da kuma biya kud'i, wannan sai dai a kira securities din wajen su zasu san wannan."
"A'a barshi kawai, yanzu zaka iya bani address din wadanda suka nemi hayar wajen?"
"Na bikin Aminan?" Habibu ya tambaya.
"A'a na ita Aseeya d'in."
"Eh to yallab'ai, ai ka san irin wannan abin ne da d'an matsala, kazo ka bada bayanin mutum kuma wani abu ya faru ace..."
"Kaga..." Sadiq ya tsaida shi.
"Babu wani abu da zai faru, bayani kawai nake nema daga wajensu ba wani abu ba, ko kaga nayi maka kama da wanda zai aikata wani abu mara kyau ne?"
Fatan Sadiq a lokacin, Habibu ya amsa da 'Eh' don da gaske ne shi mai aikata abu mara kyau d'in ne, banbancin kawai,
a bad'ini ba zahiri ba.
"Shikenan to, Allah ya kare bari na samo takarda na rubata maka address d'in matar da ta karbi hayar wajen."
Sanda Sadiq ya tashi fita daga office d'in, ya ajiye masa rafa na takardun 'yan d'ari biyu sababbi.
"Bibty address d'in waye wannan?"
Mairo ta tambaya sanda ya fita ya same ta tsaye a jikin motar daya barta a cikinta, da alama ta kasa zaman ciki ne saboda d'okin dawowarsa.
"Mutanen dacsuka karbi hayar wajen."
Sai ta d'ago ta kalle shi da wani sabon mamakin a fuskarta.
"Me address d'in zaiyi mana?"
Bai amsa ba Muhd ya fara kuka daga cikin motar saboda haka ta bud'e ta d'auko shi, a take shima ya matso ya karb'e shi ya shiga jijijiga shi.
"Ina jin kwarewa yayi,
shi yasa bana son tsotson hannunsa, ta fada tana shafa bayansa sanda yake jijjiga shin.
Daga can gefensu wata budurwa na zaune a cikin mota tana jiran yayanta ta hango su, a lokaci d'aya taji zuciyarta ta murmushe da sha'awarsu, taji dama itace Mairo da wannan kyakkyawan mijin da kuma kyawawan yaran don tana iya hango Afra dake dukan glass na windon motar alamun tana son fitowa, gani take Mairo ta gama samun sa'ar duniya, bata san cewa itace take cikin sa'a ba da take cikin DANGINTA, da mahaifiyarta bata mutu da bak'in cikinta ba, da bata kasance matar mutum dake rayuwa cikin haramun ba, da kuma bata had'a zuri'a da wanda yake cutar da ita tsawon lokaci ba.
D'an Adam baya taba kallon wani yace 'yayi sa'a',
kowanne mutum da irin damuwarsa a duniya.
****
K'amshi k'amshi yana tashi...
'Yan mata zamu je kamun amarya!
Wak'ar dake ta tashi a wajen kenan yayin da mutane suka dabaibaye rumfar zaman amarya da ake gudanar da kamun amarya Fadeelah.
Sadiya dake gefe taja tsaki a k'asan ranta, ita tun d'azu taso ganin amaryar,
amma wadda ta d'aukarwa kayan nan ta hana ta fon suna zuwa k'ofar d'akin ta juyo ta karb'i kayan sannan ta sallameta, yanzu kuma an shigo da ita fuska a rufe wai sai anyi kamun za'a yaye tukunna.
"Wannan fa duk shirme ne walkahi ba haka ake ainihin Kamu ba, a garinmu ranar kamu amarya ko kwalli bata sawa balle tayi kwalliya."
Wata a gefen Sadiya ta fad'a a inda suke zaune,
daga can gefen filin ne inda kusan tawagar 'yan aiki ne da kuma wasu 'yanuwan masu gidan na k'auye da basu da wayewa sosai.