Sashe 25
Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A tsawon shekara guda da dawowarsu Nigeria kuma cikin 'yan uwan Mami, har yanzu ta kasa sabawa da hirar 'yan matan wadanda suke 'yayan yayyen Mami, saboda duk sanda suka had'u kafin tayi magana d'aya su sunyi biyar, ga salon magana kala-kala a bakinsu da kuma yadda suke mu'amalarsu na harkar k'awaye, biki da samari duk bak'on abu ne a wajenta, wani abu da bata tab'a fuskanta ba a sabuwar rayuwarta.
Shi yasa a duk ranakun k'arshen mako ko kuma juma'a irin wannan da suke zuwa Family house d'in a had'u gabad'aya, sai dai tayi ta sauraren su, in ta gaji kuma ta d'auko aikinta na makaranta tayi, duk da cewar suna iya kokarinsu wajen sako ta cikin harkokinsu amma ta kasa sabawa har yanzu.
Yanzun da take cikin wata irin nutsuwa fiye da duk lokacin daya wuce na baya, lakacin da suke rayuwa cikin k'asar turawa don ta yarda da karin maganar da Mami ke fad'a a kullum 'Kowa ya bar gida, gida ya barshi.' babu ta yadda zaka hada rayuwa a cikin mutane masu irin jinsi da kuma yarenka da mutanen da komai nasu daban ne da naka, ko da kuwa akwai alak'a wajen addini, dole ne ka jika a gefe a yanayin mu'amala yadda suke tafi da rayuwarsu.
A yanzu ba k'aramin k'okarin Mami take gani ba, yadda ta iya barin wannan rayuwar da tarin 'yan uwanta ta koma inda bata da kowa sai 'yanuwan miji wanda suma a cikinsu kusan kowa yarensa daban, ta tabbata in ba aure ba babu abinda zai saka mata wannan juriyar.
Hatta ciwonta yayi sauki yanzu, don kusan a kodayaushe suna da abin yi, al'amarin 'yan uwa da struggles na Nigeria yasa babu ranar banza da zata zo babu wani abin yi, ba kamar a America ba da komai gashi nan cikin sauki.
Sai dai kuma kowannensu na mutuk'ar jin dadin hakan don al'adarmu Hausa-Fulani abu ne mai mutuk'ar kyau da burgewa.
Farouq wanda yafi kowa nuna damuwarsa lokacin tahowarsu, a yanzu yafi kowa sakewa cikin cousins d'insa da ya saba dasu wanda kullum suna kan hanyar yawon harkoki kala-kala tunda anan ya samu 'yanci har driving yake.
Zahra ma ta samu su Sameera da Sahla 'yan uwan iyayinta sun had'u sun cigaba daga inda kowannensu ya tsaya.
Daddy ne kad'ai baya jin dadin zaman Nigeria sosai, don kullum cikin complain yake na yadda aiki yayi masa yawa ga kuma rashin wadatar kayan aikin sosai kamar yadda ya saba, sai dai Mami tace ya riga ya sawa ransa hakan ne tunda can ne tushensa don haka shima yanzu ya d'and'ana irin hak'urin da tayi daya d'auketa daga nata tushen.
Amma baya d'and'anawar don duk sanda ya samu saukin aiki ko yaya yake, zai tafi ne can wajen 'yan uwa da abokansa, don a yanzu haka ma baya nan satinsa guda kenan a can Washington.
Gidansu mai kyau anan cikin Abuja, sannan makarantar da su Zahra suke zuwa mai kyau ce ta kud'i, tunda a yanzu abubuwa sunyi musu sauk'i ba kamar America ba, ita da Farouq kuma sun fara zuwa University of Abuja inda mafi yawancin jikokin gidansu Mami ke yi.
Iyayen Mami gabad'aya sun rasu sai kishiyar mamansu guda d'aya, dattijuwa da suke kira da Hajiya Amarya, wadda ita 'ya'yanta uku ne a gidan, amma mahaifiyarsu Mami ita 'ya'yanta biyar.
Babban cikinsu, Baba Habibu 'ya'yansa biyar shima da matarsa Haj.
Halima, dukkaninsu maza ne, Sadiq, Ibrahim, Aminu, Salim, da kuma Saifuddeen, Ukun farko sunyi aure sai biyu ne suka rage kuma dukkaninsu sun gama karatu suna aiki.
Daga shi sai Baba Sani, yana da mata Haj.
Saddik'a amma Allah bai tab'a basu haihuwa ba har zuwa yanzu da suka manyanta.
Mama Balaraba itace ta uku, mijinta Soja ne kuma tana da 'ya'ya shida.
Yusuf, Maryam, Asiya, Fatima, Sameera da kuma Mukhtar, Yusuf da Maryam duk sunyi aure, sai Asiya da Fatima dake jami'a, sannan Sameerah sa'ar Zahra da kuma Mukhtar duk 'yan secondary.
Daga ita sai Aunty Hadiza, wadda Rahma ce Babbar 'yarta, itama tare da mai bi mata Abdul suna jami'a, sannan Adnan da Sahla 'yan secondary.
Babansu ma'aikacin Banki ne anan cikin Abuja.
Sai Mami Safiyya autarsu wadda karatu ya kaita America gidan
'yaruwar mahaifinsu ta had'u da Daddy a can ya aureta.
'Ya'yan Hajiya Amarya uku ne, Mami Hauwa, sa'ar Baba sani ce, amma ita a kaduna take zaune 'ya'yanta uku ita, Sulaiman, Abdulmalik da macenta d'aya Salma sa'ar su Asiya, sai dai basu fiye zuwa ba don gabad'aya yaran ma suna k'asashen waje karatu, mijinta professor ne kuma rik'akken d'an boko.
Daga ita sai Kawu Isma'il, wanda shima 'ya'yansa duk maza ne su uku, Abdullahi, Aliyu da Anas.
Abdullahi ya fara aiki amma Aliyu da Anas duk suna jami'a.
Sai autarsu, Aunty Iyami asalin sunanta Aisha, Shekaru biyu kenan da aurenta wanda shine zuwan su Mami Nigeria na k'arshe.
Ta haifi 'yan biyu wanda shekararsu d'aya yanzu, Hanifa da Hanif.
Wani abun burgewa a zuri'arsu Mami shine suna da mutuk'ar had'in kai 'yan gidan, mutum d'aya ce ta fita zakka wato Mami Hauwa, don kafin tazo ganin Mahaifiyarta ma aiki ne balle ta tuna da 'yan uwanta, gashi mijinta yana da kud'i sosai amma bata da taimako, ko 'ya'yanta ma haka suke, Shi yasa a abubuwa da yawa kowa ma mantawa yake dasu.
Maza sun fi yawa a jikokin gidan, hud'u ne suka yi aure, uku 'ya'yan Baba Habibu sai d'aya d'an Mama Balaraba sannan mace d'aya Maryam da ita kad'aice tayi aure a cikin matan.
Lokacin da Fadeelah ta sauka k'asa da niyyar zuwa kitchen, Su Mami na zaune su shida a falo suna hira, da Haj.
Saddika matar Baba Sani, kasancewar ita a gidan b'angarensu yake sai Mama Balaraba, Aunty Hadiza da kuma Aunty iyami, sai 'yar tsohuwa Hajiya Amarya.
Ranar Asabar ce, kuma kamar kowanne k'arshen mako a sabon tsarin da aka fara su Mami na zuwa gidan mahaifiyar tasu ne gabad'aya da 'ya'yansu don sada zumunci, sai dai kusan matan ne kawai suke zama, don mazan ko sun zo, 'yan mintuna kad'an ne kawai zasu tafi harkokinsu, Baba habibu ne kad'ai wani lokacin zai kai har magariba yana zaune ana hira, sai dai yau baya nan yayi tafiya Lagos.
Kafin Fadeelah ta shiga kitchen tana jiyo dariyar da suke tayi wa Mami Safiyya kan wani abu data fad'a, har Aunty iyami na cewa anya baza su tattara su koma k'asarsu ba kuwa don wai ko su Faruq ma har yanzu basa iya fad'ar wani abin a hausa.
A cikinsu gabad'aya, daga Mama Balaraba sai matar Baba Habibu sune kad'ai basa sakar mata fuska sosai, amma su Aunty Hadiza babu ruwansu sun karb'eta kamar yadda Mami ta karbeta cikin rayuwarsu da farko, musamman Hajiya Amarya, yadda take mata baya banbantuwa dana jikokinta ko kad'an, kuma kullum ta ganta sai ta tuna da mai sunan da aka saka mata... k'anwar hajiyan Daddy, wadda taji a bakinta cewar hatsari tayi ana dab da bikinta ta rasu.
A kitchen d'in, ta tarar da Saifudden d'an gidan Baba Habibu yana sirka lemo da ruwa, bata tab'a ganin mutum mara son sanyi irinsa ba amma duk da haka kullum cikin mura yake, watakila yanzu babu lemon ne sai a fridge shi kuma yaga ba zai iya hak'ura ba, ta gaishe shi a hankali sannan ya matsa mata ta d'auki ruwan, har taje bakin k'ofa ya tsaida ita cikin dusashiyar muryarsa ta alamun mai mura.
"Rahma tana nan?"
Ta d'aga kanta.
"Eh, tana nan."
Yayi shiru kamar zai bata sak'o sai kuma yace.
"Shikenan kawai."
Sanda ta fito daga kitchen d'in, ta tsinci muryar Abdullahi, d'an gidan kawu Isma'il yana magana zaune a gabansu Hajiya, su Zahra, Sameera da Sahla na gefensa kowaccensu fuskarsu tasha kwalliya d'al da ita ga kayayyaki da takardu kamar na
certificate a hannunsu.
"Wallahi fa Mama, kawai Nasir ne yace inzo muje zai d'auko mamanshi daga wajen bikin yaye wasu masu koyon kwalliya da akayi wanda har da k'anwarsa a ciki, shine fa muna zuwa naga yaran nan a wajen wai suma har dasu aka yaye, sai d'aukan hotuna ake yi dasu, wai ita Zahra ma har wata kyauta aka bata don tafi su sanin wasu tips d'in kwalliyar.
Ashe har watansu biyu suna zuwa babu wanda ya sani."
Cikin tsananin fushi Mami Safiyya ta kalle su tace.
"Waye ya baku kud'in da kuka je kuka biya su?"
Zahra tafi su sanin halin Mami, don haka kai tsaye tace.
"Abbansu Sahla muka tambaya."
"Ai dama wallahi sai da na kawo a raina, in ba Abba ba wa zai basu kud'in nan."
Cewar Aunty Hadiza, don sarai ta san halin mijinta wajen shagwab'a yara.
"Yanzu Audullahi tunda kaga wajen, d'aukarsu ka maida su kuce musu ba'a san sun biya daga gida ba, su maido muku da kud'in."
"Hajiya kud'i fa sun riga sun tafi tunda har an gama ba mai dawo dasu, sannan dan girman Allah sunana Abdullahi, haba dan Allah."
Haj.
Saddika tace.
"Babana kaima ka san fa haka ta iya fad'a ba yadda zaka yi."
Yace.
"Wa?
Hajiya a da kenan, amma ranar da kunne na ni da Salim muka ji tace Abdullahi sak!, don baya nan ne da ya tabbatar muku wallahi."
"Ai dama akwai randa za'ayi sa'a ta fadi hakan." cewar Mama Balaraba.
"Kai ku kyale ni dashi nace Audullahin, je ka kaini kotun k'oli a tsire ni."
"To ba gwara kai bama tana k'arasawa..." cewar Aunty iyami.
"Abdul da take kira da Auduwa fa."
Sai dukkaninsu suka kyalkyale da dariya har da su Zahran da aka tasa a gaba da farko.
Wata ranar Laraba, Farkon azumin watan Ramadan kuma ana saura kwana biyu dawowar Daddy daga Washington, Rahma da Fatima suka zo gidan Mami da niyyar d'aukar Fadeelah suje siyayyar kayan Sallah wanda Baba Habibu ya ba basu kudi gabada'ya har da ita, wannan itace sallarsu da zasu yi ta farko a Nigeria, bayan zuwansu.
"Wai har wata siyayya ake yi da yawa? ni nayi zaton kayan da za'a saka ranar idi ne kawai."
"A k'auyenku na k'asar turawa kenan, anan garin activities ake had'awa har sai kin gaji, don ma bamu da sarki ne da kinga hawan doki na kwana da kwanaki."
"Eh acan ma ana activities d'in amma baya wuce ranar idi dai."
Fatima tace.