← Book details Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 95

Sashe 22

Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai taji ta zama wata 'yar mitsitsiya a gabansa, tunaninta ya shiga kwancewa d'aya bayan d'aya, kuma ta rasa wanne zata fara tattarowa don amsa tarin tambayoyin dake take hango kyallinsu a cikin idanunsa.

Daga can jikin tagar falo, Aunty Miryaamah ta damk'e labulen data yaye tana hangen d'anta a gaban wannan mahaukaciyar yarinyar!

BAYAN NA MUTU!

AYSHA SHAFI'EE
Ya k'ank'ance idonsa a hankali yana kallon ta, yaluwar doguwar riga, shudi'yar hula, ga fuskarta a kumbure sannan gashinta ta kowanne gefe ya fito, sai ta k'ara yi mishi wani irin kyau a take... yaga ta koma kamar wata 'yar Bebi ta wasan yara da ko babba zai so ya d'auke ya b'oye don ta kasance tare dashi kullum.

Sai dai kuma a kowanne lungu da sak'o na fuskar tata, alamun damuwa ne fal da kuma wani abun da bai sanshi ba, wani abu da yayi masa kama da yanayin da mutum ke shiga lokacin da zuciya ta karye, ka rasa wani abu da ka saka rai akansa (Heartbreak).

Allah ya sani zuciyarsa ta fara sonta tun daga ranar daya fara ganinta, sai dai ra'ayin mahaifiyarsa akanta yasa yayi tunani ko tana da wani aibun ne, shi yasa yayi ta bibiyarta a hankali har ya fahimci halayyarta wadda a kullum ke k'ara adadin sonta a zuciyarsa.

Shi kansa bai so sanar da ita hakan ta waya ba a jiya, ya san a yanayin ciwonta hakan zai iya damunta ta wani b'angaren, amma ba yadda ya iya... zancen wani Adam da take masa a kullum ya sanya bakinsa ya sub'uce
ya fad'i abinda bai tanadi fada mata a yanzu ba.

Har ya bud'e baki da niyyar magana gefen idonsa ya hango masa d'agewar labule daga can jikin windon falo, bai lura da wanda ke tsaye a wajen ba amma jikinsa ya bashi ko waye bai cancanci ganinsu a haka ba, saboda haka ya zare hannunsa daga kan igiyar a hankali sannan yace.

"Ki kunna wayarki dan Allah."
Da haka yayi gaba ya wuceta, fuskarsa ba alamun ita yayi wa magana.

"Al'ameen kayi hakuri, ni da kai bamu dace ba, mun bari zuciya tafi karfinmu ne har aka zo wannan matakin, watakila kuma ni na ja ka, na biye maka muka fara alak'ar da har kake tunanin zata kaimu wani matakin, ina
da tarin abubuwan da nake kokarin saita kwakwalwata akansu yanzu, ba zan iya k'ara mata wani sabon al'amarin irin wannan ba, na d'auke ka ne kawai a matsayin d'anuwa na ko wani aboki da nake samun tallafi a wajensa.

Sannan ga al'amarin mahaifiyarka, ni da kai mun sani abu ne da ba zata tab'a bari ya faru ba, na yarda nayi kuskure tun farko da na bari sabo ya shiga tsakaninmu ba tare da hangen nesa ba, don in har aka cigaba a haka dole ne sab'ani ya shiga cikin zumuncinku... kayi hak'uri Al'ameen amma kasancewata da kai ba alkhairi bane."
Ta fad'i hakan ne duka a tsaye gaban dogon mudubin d'akinsu da take kallon kanta ta cikin dim hasken fitila guda d'aya dake ci a d'akin, ta riga ta tsara wad'annan kalaman kuma ta yanke hukuncin yanke alak'arta dashi tun komai yana tsakaninsu a yanzu, kafin ma na ukunsu yaji.

A hankali ta jawo wayarta dake kan bedside drawer, ta danne power button d'in ta kunna ta, ba tare da wani b'ata lokaci ba messages suka shiga tururuwar shigowa wanda mafi yawancinsu daga number Al'ameen ne, number da ada hannunta har rawa yake wajen bud'e sak'onsa, amma a yanzu bata ko bi ta kansu ba, ta shiga cikin wajen sabon rubuta sak'o, ta rubuta abinda ya gajarta zancenta...

Kayi hak'uri Al'ameen, abinda kake tunani ba zai tab'a faruwa ba, kuma ina ganin ya kamata mu tsaya da koma meye hakan, tun kafin abubuwa su fara tab'uwa!

Sak'on na nuna mata cewar ya isa, ta lalubi makunnin ta sake kashe wayar, ta d'auki zuwan wannan sak'on a matsayin almakashin daya datse alak'arsu, tayi wa kanta alkawarin daga yanzu tsakaninta da Al'ameen gaisuwa ce kawai, gwara tayi wa kanta katanga dashi tun kafin al'amarin ya had'o da mahaifiyarsa.

Su Zahra sun dad'e da kwanciya a lokacin saboda haka ta lalubi gadonta ta kwanta a hankali itama, idonta na kallon wayar sannan kwakwalwarta na gaya mata cewa ta hak'ura da ita kenan har abada, abada wadda Al'ameen zai gaji ya daina nemanta.

Kwanaki biyu bayan nan, yazo gidan sau d'aya amma bata bari ya ganta ba, ta shige toilet har lokacin da ya gaji yayi tafiyarsa, don ta yarda babu wata sauran alak'a tsakaninsu yanzu bayan text d'in data tura masa, haka take yini a kullum da jiki mai nauyi babu walwala ko kad'an, ta riga ta saba dashi, ta saba da hirarsa mai shiga rai, shi yasa take jin kamar rayuwarta bata da wata sauran ma'ana ne a yanzu da ta yakice shi daga ranta.

We should'nt have talked, watak'ila kyawunka ne ya rud'e ni har nayi nisa da tunani na amma insha Allahu komai ya k'are yanzu.

Da zata iya maida hannun agogo baya, zuwa ranar data fara ganinsa a tsakiyar kitchen d'insu, da ta daure zuciyarta akansa, da bata sake fad'awa tarkon sa ba!

A tunaninta, Al'ameen ya zama tarihi kenan cikin rayuwarta, sai dai ashe wata k'addarar bata ma fara ba!

Kamal matashi ne amma kuma babban lauya dake b'angaren Corporate law (lauyan kamfani) a wata sananniyar k'ungiya dake garin, asalinsa iyayensa mutanen k'asar Somali ne, amma a garin washington aka haife shi har yayi girma da karatunsa anan, lokacin da Al'ameen yake shekara ta hud'u a karatunsa ne k'ungiyar su Kamal suka kai ziyara makarantarsu akan wayar da kan d'aliban dake karatun law kan harkar shariah, anan suka had'u da Al'ameen kuma abota mai k'arfi ta shiga tsakaninsu.

Hakan yana d'aya daga cikin dalilan da yasa Al'ameen yayi farin cikin dawowarsu washington bayan gama karatunsa, don shi ya sama masa gurbi a ma'aikatarsu kasancewar shima abinda ya karanta a birnin london kenan, shekara shida yana practising CORPORATE LAW.

Saboda haka a d'an lokacin nan na samun aikin Al'ameen a ma'aikatarsu sai ya zama kusan komai tare suke yi duk da banbancin matsayinsu, tun dama Kamal ya dad'e yana maraicin d'anuwa musulmi a ma'aikatar.

Lokacin da ya shiga office d'insa a safiyar laraba, Kamal ya d'ago ya kalle shi yace.

"Yanzu nake nemanka, Philiph yana buk'atar wannan file din da kayi assessing patnership da kamfanin beauty products d'in nan."
Bai ko saurareshi ba ya zube files d'in da ya shigo dasu sannan ya nemi kujera ya zauna ya dafe kansa.

"Meye yake damunka? ba dai aikin ne ya sami matsala ba?"
"Forget about the damn case Kamal, rayuwata ce ke neman birkicewa."
Sai ya ajiye biron hannunsa da yake rubutu dashi ya gyara zama yana kallonsa sosai.

"Me ya faru?" ya tambaya cikin nutsuwa.

Al'ameen ya d'ago da kansa ya d'ora yatsu biyu kan lebbensa sannan ya huro iska ta tsakaninsu, wani abu ne mai kama da guguwa a cikin kansa duk sanda idanunsa suka hasko masa text din da Fadeelah ta turo masa, kwata-kwata kwakwalwarsa ta kasa karb'ar kalaman balle ma ya yarda dasu, gashi ta kashe wayarta kuma yaje gidan yafi sau a k'irga amma ta hana shi damar da zasu yi magana, in har zai ganta to zata gaishe shi ne kawai a tsakiyar su Mami daga nan kuma ta b'acewa ganinsa, sau da yawa ma haka zai je ya dawo bai ganta d'in ba.

Tunaninsa a yanzu gabad'aya ya tafi wajen lissafawa da neman hanyar da zai iya samunta ne suyi magana, tunda da alama ta yanke shawarar daina amfani da waya a rayuwarta.

"Na tab'a gaya maka zancen wata yarinya dana gani a gidan Mami kwanaki ko?" Ya fad'a kai tsaye.

"Yes, wadda ta sami matsalar memory loss."
"Right, to ni da ita a kwanakin bayan da suka wuce kusan mun saba sosai har ta kai ina yawan zuwa gidan Mami bayan na tashi daga aiki saboda ita."
"Na fahimta."
"Ban san me ya kaini ba, amma ba tare da na tsara komai ba bakina ya gaya mata cewa ina sonta, tun daga lokacin kuma sai komai ya rikice ta daina d'aukan kirana ta kashe wayarta ma gabad'aya, daga baya ta turo min da sak'on cewa inyi hak'uri ba zai yiwu ba saboda wasu shirmen dalilai da take tunani, naje gidan yafi cikin k'irga amma bata bari na ganta ko ta bani damar yi mata magana kamar da, idan na tambayi Mami ita sai tace min wai bata da lafiya ne, bayan na san ba hakan bane.

Da har na yanke shawarar fadawa Mami abinda ke tsakannmu, amma tsorona d'aya ne Kamal, kar in gayawa Mami kuma ita tazo ta k'aryatani tunda har bata riga ta amince dani ba, kuma na san in har na fad'a Mami sai ta tambayeta tukunna."
Kamaal ya gyara zamansa a hankali alamun ya fahimci dukkan zancensa.

"What's the point yanzu? me kake so?"
"So nake in ganta, in tabbatar mata wad'annan shirmen dalilan da take tunani basu da tasiri don wallahi da gaske nake ina sonta, sannan kuma
inji irin tunanin da take akai na, amma na rasa ta yaya hakan zai yiwu."
"To ka same ta a wani waje mana, me yasa dole sai a gida?"
"Ban san wajajen da take son zuwa ba, kuma idan har na cika bibiyarta Mami zata zarge ni, ya zamo har Mommy (yana nufin Aunty Miryamah) ma tazo ta sani tun kafin in san matsayina a zuciyarta."
"Ajiye zancen su Mami a gefe, kana nufin ita yarinyar kullum tana gida bata fita koina?"
Ya d'anyi shiru bai amsa ba.

"Bata fita makaranta?"
"Tana zuwa." Bakinsa ya furta a hankali.

"To ka same ta a can, na tabbata zata saurareka in har taga cewa ka bita har wani wajen."
Ya gyad'a kansa a hankali sanda tunanin hakan ya gifta cikin kansa, da
wani d'an guntun murmushi ya shiga d'agawa Kamal babban yatsansa guda d'aya, kwakwalwarsa na gaya masa cewa babu abinda zai hana shi ganin Fadeelah a gobe, ko da kuwa mitar Auny Miryaamah ce wadda kusan kullum yake shan ta duk sanda ya koma gida.
Chapter 22 · 0% Book details