← Book details Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 95

Sashe 54

Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai dai kamar yadda ya samu amsarsa itama ta samu tata da kalaman Kawu Ibrahim na jiya.
...na samo lauyan da zai kare ki, d'anuwanki ne ma, d'an k'anina Ahmadu da kike ji a baya ana cewa ya b'ata, shine ya nemo mu bayan bakya nan yazo har Babban gida a cikakken lauyansa...

Kanta ya sara, ciwonsa kuma ya shiga kokarin dawowa, abun yayi mata yawa, bayan duk wannan ace kuma Adam d'in da ta baro a can America d'anuwanta ne?

Kuma shi zai karb'i shari'arta?

Ganin bata da niyyar motsawa, sai shi ya k'araso gabanta ya tsaya, a lokacin k'amshinsa ya ziyarci hancinta, wannan k'amshin da tun a baya ta yiwa tambari da NASA.

"Sunana Adam, nine lauyan da zai kare ki."
Muryarsa tana nan yadda take, mai taushi tana bi ta kan fatar ta a hankali, amma ba hakan ne ya bata mamaki ba, da hausa fa yayi maganar...

Da hausa, hausa yarenta, anya Adam d'in data sani ne kuwa?

"Nazo ne inyi miki wasu tambayoyi kafin ranar da za'a fara shari'ar."
Ya sake fada' yana kallonta, me yake nufi?

Bai gane ta bane ko me?

Ta yaya zai kasa gane ta?

"Zaki iya zama sai muyi maganar?"
Da gaske yake?

Da gaske yake ba zai ce ya gane ta ba?

Ba zai kira sunanta da leelah ba?

Tabi hannunsa da kallo sanda ya janyo mata wata kujera a gefe, sannan ta dawo da idonta kansa sanda yace.

"Ga waje ki zauna."
Ya Allah!

Hausa yake yi har yanzu..

Ta yaya ya iya hausa?

Ta kasa yi masa musu saboda haka ta matsa ta zauna, mamaki na cinyeta a kowacce gab'a ta jikinta.

Shima ya zauna a wata kujerar yana fuskantar ta.

"Kafin in tambayeki komai, ina son ki sani cewa duk abinda zamu tattauna yanzu taimako zaki yiwa kanki, kuma zai tsaya ne tsakanina dake kawai, amma ina son ki fada min gaskiyar duk abinda zaki iya tunawa a wancan lokacin."
Da turanci yayi maganar yanzu, hakan na nufin ya gane ta kenan?

Ya san tana jin turanci, to me yasa ba zai ce ya gane tan ba?

Sai kuma kwakwalwarta ta tuna mata da mai tsaron nan dake bayansu, watakila don shi yake yi baya son ya san akwai sanayya a tsakaninsu.

Sai ta yanke shawarar biye masa itama, amma Allah ya sani akwai tarin tambayoyi fal!

A bakinta, Me ya faru?

Ta yaya yazo nan?

Da gaske Id card din nan ke fad'a dama shi lauya ne?

To me yaje yi makarantarsu a lokacin?

Ya akayi ya zama d'an uwanta kuma yanzu?

Ya musulunta kenan?

Yaushe ya musulunta...

Ya bud'e wata 'yar k'aramar jotter a hannunsa sannan ya zaro biro yace.

"Zaki iya gaya min wace alak'a ce tsakaninki da Hajiya Balaraba?"
Ta kasa yarda wai da abinda zasu fara kenan, ta kasa yarda ba zai fara gaya mata duk abubuwan da suka faru dashi bayan rabuwarsu ba, sannan ta kasa yarda itama ba zai tambayeta komai ba zasu d'auki yau ne a matsayin had'uwarsu ta farko.

"Hajiya kakata ce wadda ta haifi mahaifina."
Da kowanne harafi, muryarta na shaida ba abinda take son fada kenan ba.

"Ke kika kashe ta?"
"A'a..." Muryarta ta fito da tsantsar yak'ini.

"Bani na kashe ta ba."
"Lokacin da take raye akwai rashin jituwa tsakaninku?"
Kai tsaye tace.

"Hajiya bata k'aunar mahaifiyata wanda hakan ne nima ya shafe ni tun tasowata, amma ban ban damu ba saboda ba'a wajenta nake ba sai bayan iyayena sun rasu ne na koma wajenta da zama."
"Saboda bata sonki shi yasa kika kashe ta?"
Sa ta ware dara-daran idanunta akansa cike da mamaki.

"Na gaya maka bani na kashe ta ba, babu wani dalilin da zai sa in kashe ta."
Sai ya koma da baya ya d'an jingina da kujera da yake kai.

"Zaki iya fad'a min wani abu da kika sani game da mutuwar tata?"
Ta gyara zamanta kad'an, sannan ta shiga zayyana masa duk abinda zata iya tunawa a ranar da Hajiya ta rasu, sai dai hakan ba abu ne mai sauki ba, don tana bayanin tana jin tension d'in dake tsakaninsu na k'ara yawa, tana jin ba haka ya kamata ya zancen ya fara zama ba.

Kallonsa kawai take yi da tsantsar mamaki wanda tsaf!

Ta san ya fahimci hakan amma ya cigaba da yi mata tambayoyinsa hankali kwance, saboda haka a k'arshe itama ta dake tata zuciyar ta zuba masa ido kawai don taga iya gudun ruwansa, wanda kuma ta gani d'in don har bayan kusan awa d'aya da ya gama tattara duk wasu bayanai da yake nema daga gare ta, bai bada ko alama d'aya da ta sake nuna mata cewa shine Adam d'in data sani a America ba, in ka d'auke wannan k'amshin nasa da sautin muryarsa da baya tab'a canjawa.

Da kowacce kalma data fad'a, Adam ya tace ta tsaf a cikin kansa kuma ya yarda cewa bata da laifi kuma bata wayo, bata da wayo da har yanzu da bata iya gano ainhin wadda tayi kisan ba, sai zargi da take kamar kowa.

"Kin tabbata iyaka abinda kika sani kenan?"
Muryarsa a hankali ta tambayeta bayan kusa awa d'aya yana
tattara bayanan dake fitowa daga bakinta.

Ta d'aga kanta ba tare da kallonsa ba.

"Bintu.."
Muryar tasa ta kira sunan a tsaye, kuma kowanne harafi ya fito dalla-dalla kamar dama ya saba fad'a ne, sai ta d'ago ta kalle shi, idanunta na shaida karyewar da zuciyarta tayi tun daga can k'asa, don a lokacin ta gama tabbatar da cewar da gaske yake ba zai nuna ya santa ba, itama kuma ta yanke shawarar baza ta tab'a fara nuna cewa ta sanshi d'in ba.

"Ina so ki fahimci cewa zanyi dukkan iya kokarina in taimake ki a lamarin nan, amma akwai wata 'yar matsalar da muke da ita a yanzu, wad'anda suka shigar da k'arar nan sun riga sun tanadi isassun hujjojin da in kotu ta gamsu za'a iya yanke miki hukunci a d'an k'ankanin lokaci, shi yasa nake so ki tabbata duk abinda kika gaya min yanzu daidai ne kuma babu k'arya a cikinsa."
Nazarinsa kawai take kuma idanunta basu d'auke daga kansa ba har kusan sakanni talatin kafin tayi magana da wani irin sauti mara amo.

"Kawu Ibrahim yazo nan jiya kuma ya riga ya fad'a min cewa in gaya maka duk abinda na sani dasu zaka yi amfaninka fitar dani daga nan wajen, don haka duk abinda na gaya maka gaskiya ne Lauya, kuma babu wani abu da zan k'ara akai!"
Lokacin da Adam ya koma makwancinsa (Temporary gidan da Sa'id ya kama musu) a ranar, ya tabbatarwa kansa cewa shawarar daya d'aukarwa kansa tayi daidai, ba zai tab'a nunawa kowa cewa ya sa Fadeelah a baya ba, har ita kanta kuwa, in ba haka ba aikinsa ba zai tab'a tafiya daidai ba, zai bari zuciya da kuma feelings d'insa su jagorance shi akan case d'in, ya samu raunin da zai dakushe shi ta wani b'angaren, abinda bai tab'a ba kuma baya son a fara da yanzu, yanzun da yake rik'e da shari'ar da zata nuna yadda alak'ar DANGINSU zata kasance a gaba.

Ya hasko yadda take kallonsa da wad'annan idanun nata masu tasiri akansa, ya san tana cike da mamakin abinda yayi amma kuma yaji dadin yadda itama ta rik'e sanin da tayi masa sannan ta biye masa suka yi komai kamar yadda yake faruwa tsakanin kowanne lauya da client d'insa.

A yanzu ya san komai game da ita amma akwai tarin tambayoyin da bakinsa ke son furtawa game da wasu abubuwan da basu shafi case d'in ba.

Yasa hannu ya murd'a ruwan shower dake zuba a kansa ya koma na sanyi kalau, so yake sanyinsa ya k'arfafa shi, ya daskarar da kwakwalwarsa wajen tunaninta amma yak'i yiwuwa, ganinta a yau bayan tsawon lokaci ya bud'e komai, ya fallasawa kansa cewa yayi kewarta a baya, musammam wad'annan idanun nata...

Ya Allah! shi fa ba yaro bane, idan a baya ya bari har zuciyarsa tayi abubuwa irin na matasa to ai komai ya wuce kuma ya canja a yanzu, ya zama cikakken mutum mai d'imbin ayyuka a gabansa, bai kamata ya bari wani shirme ya dame shi ba.

Dole ne ma ya kange zuciyarsa, ba zai k'ara zuwa ganinta ba sai hakan ta kama!

A cikin kwanaki hud'u kawai Adam ya tattara duk wasu isassun bayanan da zasu ishe shi ya fara tunkarar shari'ar, sannan bayan duk wasu tare-tsare na kotun ya samu kira daga alkalin da zai jagorancin shari'ar yaje ya had'u dashi da kuma lauyan da su Kawu d'anjuma suka d'auko mai suna Bashir Kutama.

A lokacin ya k'ara fahimtar yadda su Kawu D'anjuma suka d'auki shari'ar nan da zafi, don Bashir Kutama babban lauya ne daya shahara a garuruwa daban-daban na arewacin Nigeria, bai san nawa suka narkar don d'auko shi ba, amma ya san cewa sunyi hakan ne da fushin abinda Kawu Ibrahim yayi musu kuma sun narkar da kud'insu akansa ne da tunanin kwarewarsa zata yi tasiri a shari'ar.

Yaje Ikara har sau biyu, bayan kuma bayan Kawu D'anjuma da yaga canjin fuska daga gare shi, babu wanda yaga wani abu daga wajensa, kowa ya sakar masa fuska sosai, har zancen shari'ar sai da suka yi dasu Kawu Bashir inda anan yaji cewa Kawu D'anjuman ya hana kowa daga Babban gida zuwa wajen Fadeelah.

Hakan ya tabbatar masa da cewa za'a cika a kotun kenan ranar fara shari'ar, don ya san hatta mutanen gari zasu nik'i gari ne su taho har cikin birnin Zariya.

A kusa da kotun da za'ayi shari'ar ya samu wani office mai kyau yayi hayarsa inda zai dinga ganawa da duk mutanen da zasu shafi bincikensa hankali kwance.

Sai dai bayan tsare-tsaren shari'ar, office d'in ya zama kamar wani waje dake kange shi daga komawa wajen Fadeelah, don ranar daya sake komawa kotun ma yayi magana da marik'anta, bai nemi ganinta ba.

Ya sake magana da Kawu Ibrahim, kuma ya k'ara samun duk wani sauran bayanin da yake nema daga gare shi, sai dai kamar yadda ya b'oyewa kansa shima bai shaida masa cewa ya san Fadeelah a America ba.
Chapter 54 · 0% Book details