← Book details Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 95

Sashe 45

Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ai kin san abin al'ada-al'ada ne, mu a namu b'angaren ruwan turare ma ake wanke amaryar dashi."
Cewar wata kuma a gefe.

Wata daga can hausarta cakud'e da yare tace.

"Mu namu duk wanda yazo kudi zai je ya dank'a a hannun amaryar kafin ma ya nemi wurin zama."
Suka kyalkyale da dariya, wata tace.

"Ashe duk amarya kud'i take yi da bikinta."
"Ko kad'an ake bata kuwa ai ta tara."
Haka suka yi tayi Sadiya na jinsu bata ko ce uffan ba, don ita tunaninta na can wajen hangen abinci da kuma son ganin amaryar, tana son ta tashi amma ta san da hajiyarta ta ganta zata dank'a mata wannan fitinannen d'an nata,
a cikin ranta ta kudirce cewa duk randa ta kori mahaifiyarsa daga gidan shi zai fi kowa shan azabarta kamar yadda ta bauta masa fiye da kowa.

"Yawwa kinga zo ki taya ni dan Allah."
Muryar wannan yarinyar data taya d'aukan kaya d'azu ta yafito ta daga gefe,
Fatima take ko wa?

Da saurinta kuwa ta mik'e tayi wajenta don daman neman hanyar tashi daga wajen take.

Buhu ne na jakunkuna masu d'auke kayan amfani kitchen dama na gida kala-kala a ciki.

Lallai kud'i na inda suke!

Ta ayyana hakan a ranta sanda ta hango rayuwarta ta Ikara shekara da shekaru,
musamman a gidan mijin ta na biyu data sha mutuk'ar wahala.

Amma ba komai ita zata yi abinda yafi haka ma ranar da ta tashi aurar da 'yar da zasu haifa da Alhajin hajiyarta da take shirin aura.

Can gefen rumfar amaryar yarinyar tasa ta ajiye buhun,
ashe da sauran wasu ma don sai da suka koma ta d'ebo kai uku banda wasu ma da suka taya ta d'ebowar.

Mutane sun ragu sosai a rumfar saboda haka sanda ta ajiye na k'arshe ta juyo ne idonta ya hango mata abinda take nema tun farkon zuwanta wajen...

Cikin rumfar amaryar da mutane suka ragu a yanzu sannan amaryar dake zaune fuskarta shab'e-shab'e da hawaye.

Yadda tsawa ke fad'owa kan wani abu walau tsirrai ko dutse ta tarwatsa shi ya tashi daga kammanninsa, haka Sadiya taji a lokacin da kammanin fuskarta suka juya take cikin tsananin mamaki da rud'ewa sanda fuskar amaryar ta haska cikin idonta, ba wai don tsananin kyan da tayi ba ko don darajar fararen kayan jikinta da ta san sunfi kadarar data mallaka gaba d'aya a Ikara...

A'a sai don tsaf idanun nata sula gane mata kammanin d'iyar d'anuwanta marigayi, d'iyar da ta kashe mahaifiyarta har lahira kuma ta gudo!

Bintunsu dai a matsayin amarya!

BINTUN IKARA!

"Kana tunanin zamu iya samun wani abu ne a wajenta?"
Mairo ta tambaya sanda suka shawo kan kwanar adireshin dake hannunta.

"Sweetum kince sanda kika ganta ankon bikin ne a jikinta,
kinga kenan dole tana da kusanci dasu masu bikin,
in ma basu gane ta ba ko a hotunansu za'a iya samunta."
"Haka ne." Ta fad'a tana damk'e takardar a hannunta sannan ta saki ajiyar zuciya mai nauyi.

A hankali Sadiq ya ziro hannunsa ya d'ora akan nata.

"Komai zai tafi daidai Insha Allah Maryam."
Da sauri ta kyallo fararen idanunta ta kalle shi, a zamansu kaf! inda tana rik'ewa zata iya kirga adadin sanda daya kira sunanta kuma dukkansu a lokuta masu mutuk'ar muhimmanci ne, saboda haka maimakon taji sauki
sai hakan ya k'ara nauyin ajiyar zuciyar tata, ta maida kanta jikin glass ta langwab'ar a hankali yayin da tayar ta cigaba da motsawa.

Minti biyar kawai ya isar dasu gida mai lamba d'ari uku da ashirin kamar yadda yake rubuce a hannunsu, sai dai me?

K'ofar gidan cike take da motoci da kuma mutane sannan ga kid'a na tashi daga cikin gidan.

"Bibty biki suke yi." Bakinta ya furta a hankali tana kallon gate d'in gidan.

"To ko zamu koma gobe ma da...?"
Ta katse shi ta hanyar girgiza kanta.

"Inaga wannan lokacin shine daidai, in har zata je wancan bikin, wannan ma baza ta kasa zuwa ba..."
Ta juyo daga kallon gate d'in ta kalke shi.

"...zan iya ganinta ba tare dana tambayi kowa ba."
Har yanzu hannunsa tana rik'e da hannunta ya d'aga mata kai.

"Haka ne sweetum, kina shiga zaki ganta insha Allah."
Sai ta juya ta kalli su Afra dake kwance a bayan motar sunyi bacci, kafin tayi magana ya riga ta.

"Kije kawai, har ki dawo na san baza su tashi ba."
Yana iya jin yadda hannunta ke rawa kafin ta zarw shi daga cikin nasa sannan ta bud'e k'ofar motar ta fita,
fitar ta dake gaya masa cewa zamansa da ita ya fara tangard'a kenan,
don bai san me zai faru ba in har ta k'arasa fahimtar abinda yayi mata.

Sadiya ta kafe idanunta kan Bintun da take kallo babu ko k'akk'autawa, gani take kamar an sa sanda ne an ture duk sauran mutanen dake tururuwa a rumfar, fuskar dai Bintun dake ta dallarawa cikin hasken camera kawai take iya gani yayin da mamaki ke rarakarta inda take tsaye.

Me zai kawo Bintu nan?

Ta yaya ta canja rayuwa ta samu duk wad'annan DANGIN?

Har zata yi aure cikinsu?

Ta yaya suka karb'eta?

Su san ko ita wacece?

Su san me tayi?

Ita ta manta da nata dangin kenan?

Ta manta dasu?

Ta zata tayi nisan da har baza su iya ganinta ba?

"Lalle yarinya k'arshen shirinki yazo, ana yi miki bikin barin duniya ne."
Ta furta a hankali sanda ta juyawa rumfar baya sannan ta zaro wata 'yar qurqurar wayarta da niyyar kiran wad'anda zasu datse wannan al'amarin ba tare da b'ata lokaci ba.

Tayo gaba a hankali don samun wajen da zata iya jin kiranta sosai ba tare da karar kid'an dake tashi ba.

Tazo daf! da hanyar gate d'in ne ta bangaji wata mace don yadda idanunta suka rufe da zumud'i da kuna rud'ani yasa bata ko ganin gabanta.

"Dan Allah yi hakuri." Muryar matar ta fad'a sai dai bata ko bi ta kanta ba tayi gaba da niyyar wucewa.

Cak!

K'afafunta suka tsaya sanda muryar tace.

"Aunty Sadiya!!!!"
Sai da sunan ya fito sannan ta fahimci rawa muryar keyi, da sauri ta juyo don ta san kaf! garin Abuja ba wanda ya santa da Aunty Sadiya,
wannan lak'abi ne da 'ya'yan yayye da k'annenta ke kiranta dashi a can Ikara.

Fuskar Mairo ce ta hau k'aru akan ta Bintu da ta cika tunaninta, Mairo wadda ta gudu da saurayi tsawon shekarun da suka dad'e da goge ta cikin lissafinsu a Babban gida.

Mairo dai yayar Bintu!

Mairo da Bintu 'ya'yan Amina 'yar gudun hijira.

BAYAN NA MUTU!

AYSHA SHAFI'EE
Godiya mai tarin yawa ga yadda kuke bani sharhinku akan labarin nan, kuma kuke jimirin jiran k'ok'arina mai cin lokaci.

Ina rok"on Allah ya faranta muku da dukkan farin cikin duniya.

Sadiya ta ki'fta idanunta kusan sau ba adadi amma fuskar dai Mairon dake tsaye a gabanta bata canja ba, tana tsaye itama tana kallonta da dukkan wani ma'anar tsoro na duniya kamar bata yarda cewa ita d'in take kallo a gaske ba.

"Mairo?

Ke nake gani?

Dama nan kuka gudo ke da 'yaruwar taki?

Ke kika zo kika d'auke ta tun wancan lokacin?

A tunaninku kun tsira?

Kun zata alhaki baya bibiya?"
Muryar Mairo na rawa kamar hannayenta tace.

"Aunty Sadiya wace 'yaruwar tawa?

Bintu kike nufi?

Tare kuke anan?

Ai nima ita nazo nema."
Sadiya ta girgiza kanta.

"Ai babu sauran wata yaudarar ku kuma yanzu,
tas! na gane abinda kuka shirya, bak'in cikinki ya kashe mahaifiyarki shine kika lallab'o kuka had'a baki da Bintu kuka kashe mana tamu mahaifiyar don kuna tunanin ita ta jawo muku komai ko?

Sannan kika d'auketa kuka gudo nan da tunanin kun tsira kenan har abada?

Waya gaya muku laifi na kwanciya Mairo?

Abuja har nisan duniya ne tsakaninta da Ikara da kuke tunanin zaku k'are rayuwarku asiri a rufe?

Kunyi zaton..."
Kamar yadda dutse yake a k'ame waje d'aya babu alamun fitar iska ko numfashi a jikinsa, haka jikin Mairo ya sandare tun daga lokacin da Sadiya ta furta..

'... bak'in cikinki ya kashe mahaifiyarki..'
Komai ya d'auke cak! daga kwakwalwarta, duniyar ta tsaya mata a lokaci guda ba tare da ta fahimci sauran abinda muryar Sadiyan ta cigaba da fad'a ba balle hayaniyar wajen.

Abinda take haskowa daban ne a cikin kanta...

Innarta ta rasu?

Yanzu babu Innarta a duniya?

Tun tsawon wane lokacin?

Da gaske ne rabuwa dasu da tayi ne sanadin mutuwarta?

Me yasa ta rabu dasu d'in?

Me yasa ta bar iyayenta masu tsananin sonta a lokacin?

Yadda Innarsu ke shan gori da tsangwamar 'yanuwan Baba musamman akansu shine har ta iya gudowa ta barta?

Yadda Baba ke mutuk'ar sonta har ya dage wajen bata ilimin da ba kowacce d'iya ke samun irinsa a Ikara ba shine har ta iya gudowa ta barshi?

Saboda Sadiq kawai?

Wane alkhairi ta samu tare dashi ne ma tsawon lokacin nan banda 'ya'ya kawai?

Da wace zuciya tayi shawarar hakan a baya?

Da gaske ne Innarta Amina ta rasu..."
"Wallahi Tallahi billahil azeeem..." Muryar Sadiya tayi sa'ar dawowa cikin kanta.

"...

Sai an kwatar mana hakkin Mahaifiyarmu akanku Mairo, sai an kashe ku kamar yadda kuka cire Imani itama kuka kasheta,
waya sani ma ko harda had'in bakinku aka kashe Yaya shima...

Wanda ya kashe Uwa meye a ciki don ya kashe Uba?"
Wace ce kuma aka kashe?

Sannan waye Yaya?

Babansu kenan?

Mairo ta tambaya cikin kanta, shima ya mutu?

Ta yaya?

Baba ya mutu...

Sai dai wannan karon Sadiya bata yarje mata dogon tunani ba taji ta finciki hannunta da k'arfi sannan ya shiga janta suna ratsawa ta cikin mutane da kuma teburan dake barbaje a wajen, bata san ina zata kaita ba don idanunta a hargitse suke bata ko iya kama siffar mutanen dake wajen balle ta san inda suke nufa!

Fadeelah ta had'iye yawu a makogwaronta sanda hasken camerar ya sake dallare fuskarta, kumatun ta har zafi suke yi saboda yawan murmushin k'aryar da take yi tana kallon mai hoton, wani dunk'ulen abu ne mulmulalle a k'asan mak'ogwaron nata, wanda duk sanda mutanen dake zuwa d'aukan hoton suka ce.
Chapter 45 · 0% Book details