← Book details Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 95

Sashe 35

Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A wannan lokacin alak'ata da Maria kawai shine duk abinda nace mata muyi zata yi, amma ta daina min magana da kuma sani a harkokinta,
laifina take gani cewar na rabota da wajen da Ahmad yake, nima kuma ban damu ba saboda hankalina na kan yadda zamu daidaita rayuwarmu kawai, sai dai hakan bai yiwu ba saboda rashin lafiyar da muka fara a lokacin, Maria ce ta fara fama da wasu irin kuraje k'anana masu k'aik'ayi da suka feso a bayanta kafin daga baya su fara bin kowanne b'angare na jikinta, daga nan nima suka fito min a fuska sannan hannaye da duka jikina.

Ba tare da wani b'ata lokaci ba kuwa mai gidan cin abincin ya kore mu, muka je asibiti anan aka shaida mana cewar basu tab'a ganin cuta irin wannan ba, babu wanda yayi mana zancen biyan kud'in magani suka ce dole mu zauna don a bamu taimakon gaggawa, nayi tunanin da zuciya d'aya suka yi hakan, ashe tun kafin zuwanmu an riga an sanar da kowanne asibiti a kewayen cewa da zarar mun zo a kama mu.

Maria ce ta binciko wata takarda a d'akin da aka zaunar damu, wadda aka buga ta da sunanmu cewa mun gudo daga sansanin sojoji ne d'auke da wata cuta ta annoba da zamu iya shafawa mutane ko a iska ne don haka a sanar da hukuma da zarar an ganmu, anan muka fahimci dalilin da yasa sojojin nan suka damu da nemanmu.

Mun gudo daga asibitin cikin sa'a kuma mun sha wuyar b'oyewa mutane kafin mu had'u da wata tsohuwa wadda ta tausayawa Maria saboda tsohon cikinta ta sauke mu a gidanta, cikin 'yan kwanaki kuwa ciwonta yayi tsanani sosai har nakud'ar haihuwarka ta kamata, a cikin wannan ciwon Maria ta rik'e hannuna ta rok'e ni da in kula da abinda zata haifa kuma in shaida masa asalin mahaifinsa don kar ya k'are rayuwarsa irin tamu.

Kwananta biyu cikin tsananin ciwon kafin ka fito duniya,
a ranar kuma hukumar asibitin nan suka gano inda muke aka shaidawa sojojin dake nemanmu.

Maria bata ko shura ba bayan fitowarka ta mutu saboda tsananin wahalar da tasha, Na san cewa idan har na gudu a lokacin nan to neman mu ba zai tab'a k'arewa ba, amma idan har suka ganni tare da gawar Maria,
kai zaka iya tsira daga nemansu, hakan yasa na rok'i tsohuwar nan data d'auke ka ta gudu don mu d'auke hankalinsu daga kanka.

Ganina da kai na k'arshe kenan, sanda tsohuwar ta lullub'e ka cikin wani zani ta fita da kai ta k'ofar baya, ba tare ko anyi maka wanka na farko a duniya ba.

Wani abu dana tabbatar in cewa ko ka rayu a wannan lokacin dole hakan ya haddasa maka wani ciwon, don kazo duniya ne cikin wani irin hargitsattsen yanayi.

Ba wai hawaye ba, kuka ne sosai ya taho cikin idanun Adam, amma sai ya girgiza kansa alamun A'ah,
komai ya riga ya wuce, ya shud'e tare da lokaci mai dad'ewa, don haka koya zubar da hawayen babu amfani a yanzu,
yasa yatsansa guda d'aya ya d'auke guntuwar kwallar da taru a gefen idonsa...

Ashe asalin ciwon kwakwalwarsa kenan, shi yasa iyayensa na can suka kasa gaya masa dalilin da ya haddasa masa shi, tunda sun same shi ne tare da ciwonsa.

Tsaya, ta yaya ma suka same d'in?

A hankali ya maida idanunsa kan guntun rubutun daya rage ya cigaba.

Bayan sojojin nan sun kama ni an kuma binne gawar Maria,
sai na fahimce cewa ashe suna neman mu ne don kar mu shiga cikin mutane mu yad'a musu ciwon ba wai don su kashe mu ba, aka kaini wani babban asibitin sojoji inda ake warkar da sauran 'yan sansanin namu, wanda kowannensu ya girgiza jin mutuwar Maria, sai dai ba wanda na bud'i baki na shaidawa cewa ta haihu kafin ta mutu, watanmu biyar a asibitin cikin kulawa kafin a sallami kowannenmu da d'imbin kud'i a matsayin ladan wahalar da muka yi a sansanin yaki.

Ranar da zan bar cikin asibitin nan,
na ziyarci d'akin adana hotuna na sojojin nahiyar, a cikin hotunan fursononin da suka sadaukar da rayuwarsu a wajen y'akin, naga hoton Ahmad.

A wannan lokacin ne kuma duk kukan rashin k'awa kuma 'yar'uwata dana tara tsawon watanni biyar ya b'alle daga idanuna, Maria taso Ahmad da zuciyarta guda kuma taso musu rayuwa mai kyau a gaba, amma hakan bai yiwu ba, ni d'in da ban tsara komai ba, ni na rayu kuma na sami tarin dukiyar da zan iya yin komai da ita a lokacin.

Naji cewa zan iya bayar da komai har kuwa da rayuwata a lokacin in da wani zai iya canja k'addarar Maria da Ahmad.

Ya dawo musu da rayukansu, sannan ya sanya nutsuwa da kwanciyar hankali a rayuwarsu ta yadda komai zai tafi kamar yadda Maria ta tsara a mafarkinta.

Bayan barina asibitin, na koma gidan tsohuwar nan na nemeta don in karb'e ka ka girma a wajena, amma abin mamaki babu inda ban shiga ba amma ban ga matar ba,
sai a lokacin na gane gangancin da nayi,
na dank'a ka a hannun wadda ban sani ba, sai dai wane zabi nake dashi a lokacin?

Shekaruna goma tsakanin birni da wannan k'arami garin ina neman bayani akan wannan tsohuwar amma ban samu ba, sai a cikin shekara ta gama sha biyu ne na sami labarin mutuwarta daga wani mutumi a cikin garin,
yace min shekaru hudu baya, mota ta kad'e ta a gefen titi kuma ba wanda ya ganta da wani yaro k'arami.

Sai na shiga bin gidajen marayun dake wannan yankin ko ta kaika can ne, amma ban same ka ba saboda haka na k'addara cewa ka mutu,
kuma k'uncin yayi min yawa saboda haka na tattara komai nawa na bar k'asar, na komo Ingila na bud'e wata sabuwar rayuwar da ban tab'a jin dadinta ba saboda na k'addara cewa in har na sami dad'in rayuwa ban yiwa k'awata adalci ba wadda ta mutu cikin k'unci.

A yanzu cikin kwanakin nan ne nake yawan mafarki da Maria rik'e da kai hannunta lokacin data haife ka, hakan yasa na fara tunanin cewa baka mutu ba kenan, saboda haka na cigaba da bincike akanka har zuwa yanzu da nake rubuta wasik'ar nan,
na kudirta a raina cewa idan har na same ka zan shaida maka labarin iyayenka dalla-dalla fiye da yadda yake a rubuce yanzu, idan kuma bamu had'u ba, na tabbata a dunk'ule wannan zai ishe ka sanin komai, don idan har na mutu da nauyin da mahaifiyarka ta bar min, na tabbata ba ita kad'ai ba ko waye yaji labarin nan ma ba zai yafe min ba.

Idan har wasik'ar nan ta isa gareka d'an Maria, inaso ka san cewa mahaifiyarka tace in shaida maka ita bata da dangi amma ka nemi 'yanuwan Babanka a can k'asar Nigeria a wani gari mai suna IKARA!

Asalin sunansa shine Ahmad Muhammad.

Adam na kaiwa daidai nan a karatunsa wata takardar check ta zamo ta fad'o gefen k'afarsa, a hankali ya mik'a hannunsa ya d'auko ta, idonsa ya gane masa zunzurutun ku'di cikin adadi na dalar k'asar ingila.

Da sauri ya sake juyawa ya karanta layi d'aya daya rage a jikin wasik'ar.
...

Idan har na mutu, dukiyata gabad'aya taka ce d'an Maria, idan kuma har ba'a same ka ba, na sadaukar da komai ga gidajen marayu da tsofaffi marasa DANGI irina da mahaifiyarka.

A hankali ya ninke check d'in ya ajiye shi a gefe, abinda yake gabansa yanzu ya tabbata mutuwa ce kawai zata iya tsada shi, labarinsa bai k'are ba, hasali ma yanzu komai ya fara, a take yaji zuciyarsa tayi fiffike ta yiwa garin IKARA tsinke!

Ko kun tuna cewar Bintun da muka fara had'uwa da ita a farkon labarin nan daga IKARA take?

Wane k'ulli ne labarin nan ke shirin kwancewa?

Insha Allah next update zai zo kafin ranar Lahadi.

BAYAN NA MUTU!

AYSHA SHAFI'EE
Dangi anata taro...

Ko'ina d'aukacin masoya,
Aure ake na manya, lallai amaryar fa
tayi dace...
...

Angonki ya kasance mai hak'uri da tausasawa.

Kamar yadda wak'ar ke fad'a, k'aton hall ne wajen cike da dangi na birni da k'auye, b'angaren amarya da kuma b'angaren ango, kowa yazo don shaidawa da kuma taya murnar auren Aseeyah da Angonta mai suna Idris Makama.

Duk inda ka duba mutane ne cikin kwalliya da farin ciki,
gashi wajen yasha had'adden decoration tunda bayan kamu da akayi a jiya, wannan itace walima guda d'aya tilo da aka za'a gabatar sai kuma gobe Asabar a d'aura aure, ayi yini sannan a kai amarya baki d'aya.

Lokaci ne irin wanda Amarya da Ango basu dad'e da isowa ba, M.c ya rik'e su a tsakiyar fili yana tsokanarsa kala-kala sannan kuma yana kiran dangi su zo su nuna musu kara ta hanyar lik'i, adai lokacin kuma masu rabon abinci sun fara aikinsu na kawowa tebur-tebur, don haka banda hayaniya da kuma k'arar kid'a,
wajen a cakud'e yake da zirga-zirgarsu da kuma ta masu gajen hakurin cewa ba'a kawo abincin wajensu ba.

Fadeelah na zaune a wani tebur daga can gefe cikin k'awayen Fatima da suke ta hirarrakinsu suna d'aukar hoto, irin ankon jikinsu shi itama ta sanya, anyi mata d'inkin doguwar riga mai simple design data zauna b'am a jikinta, telan su Fatima da bai san awonta ne ba yayi dinkin,
don haka sai rigar taso ta matse ta daga sama,
sai ta d'ora light pink mayafi irin kalar ashoken dake kanta.

Ita bata san k'awayen Fatiman da take zaune cikinsu ba kuma ba zata iya shiga cikin hirarsu ba saboda haka tayi shiru kawai tana kallon hada-hadar mutanen wajen, a cikin zuciyarta kuma dad'i take jiwa Aseeyah sosai, yadda ta kasance 'yar cikin dangi masu yawa da k'aunarta haka, gani take Aseeyah ta riga ta gama samun rabin nasarar rayuwa irin wadda ita take nema a yanzu ido rufe.

Allah ya riga ya karrama d'an Adam da rahamomi da yawa, a ciki kuwa harda sanyashi da yayi cikin mutane masu irin jinsinsa da ake kira da DANGI, ta dad'e da fahimtar cewa duk wata d'aukaka da nasarar da mutum zai samu a duniya in har baya cikin danginsa, to wallahi ko meye zai tashi a banza ne.
Chapter 35 · 0% Book details