Sashe 73
Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Na san kai ba bahaushe bane d'an nan, da watak'ila ka san karin maganar dake cewa 'Alhaki kwikwiyo ne, dole ne yabi mai shi, irin wannan ranar na dad'e ina gujewa Habiba."
Adam ya gyara zamansa a hankali, kafin tsohon ya sake tambaya.
"Kai waye a wajen Habiba?
Ban tab'a ganinka ba."
"Ni d'an k'anin mijinta ne, ba'a garin nake ba har ka tafi shi yasa bamu tab'a had'uwa ba."
Tsohon ya sake gyad'a kansa sannan yace.
"Ni na san shari'ar nan baza ta tab'a mutuwa ba sai anyi ta, an samu yarinyar da ta gudu ne?"
Adam ya gyad'a kansa.
"Eh ta dawo."
Tsohon ya girgiza kansa.
"Daga Habiba har yarinyar sun fad'a tarkon wani mai sharrin ne, anyi amfani dasu a cimma wani burin."
Da sauri Adam ya tare shi.
"..
Ban gane abinda kake nufi ba."
Tsohon ya juyo ya kalle shi sosai.
"Ko waye ya turo ka kaje ka gaya masa ba Habiba ce ta kashe Hajiya Balaraba ba."
Adam ya had'iye yawu shima yana kallonsa sannan yace.
"Zan iya sanin abinda yasa kace hakan?"
Kafin ya amsa, ya juya ga d'ansa dake gefe ya fad'i wani abu da Adam bai ji ba, d'an ya mik'e da sauri ya kama kafad'unsa, ya mik'ar dashi zaune sosai sannan ya koma ya zauna.
"Ita Habibar da ta turo ka wajena na tabbata ta gaya maka sana'ata a Ikara kafin kazo nan, don haka na saba da ita ne ta hanyar yawan siyan magungunan gargajiya da take yi a wajena.
Ana gobe za'a yi wannan rasuwar, tazo wajena da bayanin abinda kake nema yanzu, tace tana neman taimakona da in sayar mata da sassak'en wata bishiya da yake kamar guba idan mutum yaci shi, da farko bata shaida min me zata yi dashi ba sai da na matsa mata taga da gaske ba zan bata ba har sai naji dalilinta tukunna, sannan ta gaya min cewa ta yanke shawara ne kawai zata kawar da Hajiyar daga duniya don ta samu damar mik'e k'afa a gaba tayi komai yadda take so babu mai hana ta.
Ba tun a ranar ba Habiba ta saba sakin jiki ta fad'a min duk sirrinta saboda ina biye mata a dukkan ra'ayoyinta.. saboda haka na san duk irin matsalar dake tsakaninta da Hajiyar.
Ta gaya min a lokacin cewa taje wajen malamai da yawa, amma dukkanin ayyukan da akayi mata babu wanda yaci akan hajiyar, don haka k'awarta ta gaya mata in har ta samu wannan sassak'en tasa mata a abin ci ko sha, to nan take zata mutu.
Sai dai a wannan ranar, ban biyewa mata kamar yadda na saba ba, na gargad'e ta da cewa abinda take shirin yi mai girma ne, kisa ba k'aramin abu bane da zata yi ya wuce kamar sauran shirinta, amma duk iya k'ok'arin da nayi wajen ganar da ita, bata saurare ni ba ta ajiye min mak'udan kud'in da basu tab'a shiga tsakanina da ita ba tace lallai in bata.
Ganin kar in rasa kud'in a wannan lokacin yasa na amsa mata sannan nayi mata alk'awarin kawo mata sassak'en har gida, washegari kuwa na sami wani sassak'en da bashi da tasiri ko kad'an naje na kai mata a matsayin wanda take nema, saboda har a lokacin zuciyata bata bani cewar in sa hannu a kisan mutum ba."
Adam ya gyad'a kai a hankali sanda tsohon ya kawo nan, bai sani ba ko a duk duniya kaf akwai sunan abinda ke faruwa a cikin kansa a lokacin, don bashi da wani kokwanto tsohon gaskiya yake fad'a, ya yarda da maganganunsa irin yardar da zai iya tsayawa a gaban ko waye ya tabbatar da hakan, amma ta yaya wannan al'amarin ya faru?
In har ba Habiba ce ta kashe Hajiya ba to waye?
A lokaci guda kwakwalwarsa ta shiga hasko fuskokin 'yan Babban gida d'aya bayan d'aya, kamar a sannan za'a nuna masa wanda yake nema.
"Zaka iya yi min dukkan tambayoyin da kake so yanzu."
Muryar tsohon ta katse shi, ya maido da idonsa kansa, sai a sannan ya lura cewa ashe bai ma yi masa tambaya ko guda d'aya ba amma ya sami fiye da rabin amsoshin da yake nema.
"Me yasa duk ka gaya min wannan zancen kai tsaye?" Ya yanke shawarar fara yi masa tambayar da ko 'ya'yansa dake zaune zaso sani.
Tsohon ya k'ara yin murmushi kamar mutumin dake cike da raha sannan ya kai hannunsa ya yaye bargon da ya lullub'e inda k'afafunsa suke, sai dai me?
Wajen fayau yake babu k'afafun, balle cinyoyi, sai alamarsu kawai daga can k'ugunsa wanda ke nuna alamun yankewa akayi.
Adam ya d'ago daga kallon wajen ya kalle shi.
"Naga ishara mai tarin yawa daga Allah d'an nan, baka labarin halin da na shiga da irin wahalar dana sha kafin in iya k'arasowa nan abu ne mai tsaho, don haka ba kai ba, ko waye a yanzu yazo neman wani bayani daga wajena, wallahi zan gaya masa abinda na sani komai munin irin rawar dana taka a ciki kuwa."
Kamar yadda sama-sama suke gane abinda yake fad'a, shima ba kasafai Adam ke gane kowacce kalma ta cikin hausar sa ba, amma yana iya fahimtar abinda yake nufi, don haka ya gyad'a kansa a hankali kafin ya sake yin wata tambayar.
"Idan har abubuwan da ka gaya min duka gaskiya ne to waye yayi kisan kenan?
Tunda labari ya dad'e da fita cewar Hajiyar ta mutu ne sanadiyar gubar data ci."
Sai da ya maida bargon ya rufe jikinsa sannan yace.
"Wanda ya taki zance akan zance ya kuma taki sa'a akan sa'a."
Adam bai fahimta ba, kuma fuskarsa ta nuna alamun hakan.
"Ina nufin wanda ya san duk abubuwan da Habiba ke k'ullawa kuma yaji zancena da ita."
D'akin ya d'auki shiru na wani lokaci, tsakanin shi da tsohon babu wanda ya sake magana, da alama kowannensu da irin tunanin dake faruwa akansa, tunanin Adam bai wuce na jiran tsohon ya k'arasa masa abinda yake nema ba, don ya yarda in har ya san duk wad'annan abubuwan, to abinda ya rage ma ba zai shige masa duhu ba.
Zuwa can tsohon yayi ajiyar zuciya sannan yace.
"Sule yaje wajena a wannan ranar bayan fitar Habiba."
Sule.
Sule.
Sule!
Adam ya zana sunan a cikin kansa da manyan harafai, sai dai waye shi?
A Babban gida yake? anya ya tab'a ganinsa kuwa?
"Amma bani da tabbas akansa don sai bayan awanni da fitarta sannan yazo, kuma abinda ya kawo shi ba sabon abu bane, dama yazo neman maganin
ciwon mahaifiyarsa kuma nace ya dawo a ranar."
"A ina ya same ka?" Adam ya tambaya kai tsaye.
"A cikin gidan da nake zaune inda nake ganin mutane."
"Ka tashi ka barshi shi kad'ai a lokacin?"
Bai amsa ba sai da ya d'ago ya kalle shi.
"Idan kana tunanin ya d'auki sassak'en gubar ne to ba abu me mai yiwuwa ba, babu wanda ya san inda nake ajiye magunguna na balle har a gansu, sai dai in nine na fito dasu."
Adam ya girgiza kansa.
"Ba tunani nake ya d'auki gubar ba, tunani nake yaga maganin a lokacin da ka fito dashi zaka kaiwa Habiba a matsayin gubar, kuma ya gane ba gubar bace."
Sai da tsohon ya bud'e baki cike da mamaki sannan ya gyad'a kansa.
"Kwarai sanda ya shigo ina dab da fita, don magariba ta k'arato kuma so nake in shiga Babban gida a lokacin da maza suka tafi masallaci, mata kuma ke d'aki suna sallah, don haka na fito da maganin yana ajiye a gefena."
Adam ya gyad'a kansa.
"Kuma kana da tabbacin kuma babu wanda ya ganka a lokacin da ka shiga wajen Habiban?"
"Ina dashi, na tabbata babu wanda ya ganni."
"Akwai..." Adam ya bashi amsa yana kallon fuskarsa.
"...
Don ba Habiba ce ta turo ni wajenka kamar yadda kake zato ba, wani ne daban wanda ya ganka a lokacin da ka shiga."
Ga mamakinsa sai kawai tsohon nan ya bushe da dariya a maimakon murmushin da yake yi.
"Na fahimci kai lauya ne tun shigowarka nan yaro, kuma ba lauyan dake kare Habiba ba, A ina wannan yarinyar ta samu gatan mai d'auko mata lauya kamar kai?"
Adam ya girgiza kansa.
"Ba shine abinda ya kawo ni ba, so nake ka gaya min da gaske babu wanda ka gani a lokacin da zaka shiga wajen Habiba?"
Tsohon ya sake girgiza kansa.
"Hanyar shiga b'angaren Habiba a can k'arshen Babban gida yake, don haka ba waje ne da mutane suka fiye yawan zuwa ba, in banda Anna dake zaune a wajen da wuya kaga wani a hanyar."
"Anna...
Anna, wacece ita?"
Kalmomin har karo suke wajen fitowa daga bakin Adam.
Tsohon ya sake dariyar data zame masa jiki.
"Kar kasawa kanka wani fata, Anna mahaukaciya ce, ba abinda take ganewa balle tayi maka amfani."
Ba fata kad'ai ba, Adam ji yayi zuciyarsa ta d'auki k'addarar shari'ar kacokam!
Ta maida kan Anna mahaukaciya.
Dukkan wannan rikicin ya fara ne daga Babban gida, an kashe Hajiyar a cikin Babban gida, An d'orawa Bintu sharrin kisan a Babban gida, an shigar da k'ara kotu daga Babban gida, ya baro Babban gidan ya taho wannan luluk'in bincike....
Ashe watak'ila AMSAR na dai cikin BABBAN GIDAN!
"Wacce hanya ce zata yi mana sauk'in fita titi?"
Ya tambayi Jamil bayan komai ya kammala tsakaninsa da mutanen Mimbiri, ya gama da tsohon nan, yayi sallama da maigari har kuma sun saki Sa'id d'in da aka tsare a fadar Maigari.
"Komawa hanyar Abuja yanzu tafiya ce mai nisa kuma hanyar bata da kyau, daga nan yafi kusa da Keffi, gwara ku fita keffin sai ku d'auki hanya ta titi ku koma yafi sauki."
Hakan suka yi kuwa, Jamil yayi sallama da wan mahaifinsa sannan yabi su har wata mararraba da ta d'auki hanyar fita k'aramar hukumar keffin daga nan shi kuma ya sami motar da zata koma k'auyensu, suka rabu bayan Adam yayi masa alkhairin da yake ganin zai koma k'auyensu ne a matsayin attajiri!