Sashe 61
Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ai ni na san za'a zo nan kallonka kawai nake dama, ace har ni zan maka tayin abu ka fara kawo min qabli da ba'adin Allah yace Annabi yace, ub*n waye bai san Allah ba, kai rayuwar nan fa ina gaya maka yanzu ko ita kanta ibadar sai da kudi take tafiya, yanzu dai kalle ka, kaine shegen a ajinmu mai cinye komai, ni kuma irin masu nane muku don mu samu na assignment d'in nan, amma wani ya shigo yanzu wallahi cewa zaiyi almajirin gida na ne kai.
Ya b'ata rai a lokacin gami da jan tsaki.
"Ba sai ka zage ni ba Yusif na san duk wannan abin daka lissafa, yanzu dai ka gaya min in zaka taimake ni ko a'a, don gashi yamma har ta fara yi kuma ban koma na kai musu komai ba."
Yusif ya sake kyalkyalewa da sariya kafin yace.
"Ni na isa in ki taimakonka, amma dai ya kamata ka fara sanin cewa d'an adam baya d'aukewa wani talauci ko?"
"Na sani."
"Yawwa kwaro, dad'i na da kai ganewa yanzu zan baka abinda zai ishe ka zuwa gobe sai ka dawo muyi magana, tunda kace yamma tayi."
Minti uku bayan hakan, Yusif ya fito daga d'akin dake jikin tamfatsetsen falon da suke ciki rike da 'yan bandir na sababbin kud'i fil!.
"Dubu hamsin ne wannan kwaro, kaje ka sai muku abinda zaku ci zuwa gobe sai kazo muyi magana a nutse, tunda naga duk hankalinka yayi gida yanzu."
Daga lokacin da yasa hannunsa ya karb'i kudin nan, daga wannan lokacin ya tashi daga Sadiq d'in da mahaifinsa ya mutu ya bari, ya koma Sadiq d'in da zai iya bin kowacce hanya don faranta ran mahaifiyarsa, saboda washegari kuwa goma a gidan Yusif tayi masa, wanda shi bai fito ba sai wajen sha biyu na rana tukunna.
"Kana ji ko kwaro, na yanke shawarar taimakon ka ne saboda irin naka taimakon da kayi min a makaranta, shi yasa zan fad'a maka wannan sirrin da ko Uwata bata sanshi ba.
Ka san inda zaka samo mace mai kyau?"
Yayi sororo yana kallonsa.
"Mace mai kyau kuma Yusif?"
"Kwarai ita zata zama jarinka."
"Ban gane ba."
"Yawwa kwaro, ba wani abu ne mai wuya ba, wata k'ungiya ce ake shiga da farko, ba wai ta tsafi bace ko ta wani abu, su kawai jinin hailar Mace kyakkyawa suke bukata na watanni tara kawai, idan har na kai ka, ka amince zaka yi, to zasu baka rabin wasu mak'udan kud'i ne daga ranar da ka kai musu na farko, sannan zasu baka k'arashen a ranar da ka kai musu na k'arshe, daga nan ka gama dasu Kwaro, sai dai kayi ta cin dukiyarka da tsinke ka shiga kasuwancinka ka cigaba da habb'aka."
Yayi shiru yana juya zancen.
"Ba dai ce min zaka yi akwai haramun a ciki ba?"
"Da wannan Yusif, tunda bamu da tabbacin me suke yi da jinin nan, idan wani abu ne da zai iya cutar matan fa?"
"To ina ruwanka? da ka gama da ita sallamarta kawai zaka yi ta koma inda ta fito, in ma mutuwa tayi ruwanta...
Kawai dai sai kayi taka tsan-tsan ne a zaman naku kar kaje a samu matsalar haihuwa."
Ya sake yin shiru.
"Kwaro kar kasa fa inyi nadamar gaya maka zancen nan."
"Ba haka bane Yusif, a ina zan samu Mace mai kyau yanzu?
Yanda nake a talaka na?"
"Tambaya mai kyau, don ka san sai sun ganta ma k'iri da muzu, sannan za'a yarda a fara harkar da kai...
Yanzu kawai k'auye zamu je inda za'a sami irin fulanin nan, mu juye zuciyar wata yarinya kawai ta rabu ma da 'yanuwanta ta biyo ka kamar yadda nima nayi, azo kawai a fara harka, da ta gama amfani ka sallameta ta koma garinsu."
Ya sake yin shiru yana lissafi a cikin kansa.
"Ba wahala fa kwaro, ni zan ranta maka kudin da za'a kaiwa malami yayi asiri in mun samo yarinyar, sannan zan dinga gaya maka yadda duk wata zaka kai musu jinin nata, da yadda zaka fara fito da arzik'inka a hankali har ka sami wata sana'ar da zaka kafu akanta in ma aikin gwamnatin ne ka samu yadda zaka gujewa zargi.
Ka san ina sonka Sadiq shi yasa na bud'e maka cikina haka, in ba haka ba kai baka isa kaji wannan ba wallahi."
Bai ce dashi komai ba har a lokacin, shiru kawai yayi yana lissafi cikin kansa, lissafin da a k'arshe yaje ya dawo ya kuma yarda da kautacciyar hanyar da Yusif ya kwad'aita masa, hanyar da ta had'o da k'addarar Mairo cikin rayuwarsa, don a washegari tafiya ta kama shi Ikara zuwa janaizar matar wani aminin mahaifinsa, inda anan yaga Mairo wadsa ta dace da dukkan wata siffa da Yusif ya zayyana masa.
Babu jimawa suka yi asirin nan da shi da Yusif suka je duka binne a wani kabari cikin k'auyen Talfa, kuma Mairo ta rabo mahaifarta ta biyo shi, Yusif ya ranta masa isassun kudin daya aure ta dasu a lokacin bisa cewa mahaifiyarsa da 'yanuwansa da yayi bata da iyaye, sai wata mata kurum da ya biya ta zauna a wajenta har akayi bikin.
A wata na farko kuma ya d'auki jininta ya kai wa shugabbannin k'ungiyar da Yusif ya sanya shi cikinsu, kuma a wannan watan ya fara rik'e makudan kudin da bai taba mafarkin irinsu a rayuwarsa ba.
BAYAN NA MUTU!
AYSHA SHAFI'EE
"Kinga abinda nake gaya miki ko Salame?
Shi yasa nace dake ki d'auke ni mu tafi can k'auyen 'yar uwar nan taki inda ba mai sanin inda nake, amma kika kafe cewar wai hakan ne zai jawo a zarge ni, to yanzu gashi na zauna d'in ma amma ban fasa shiga zargi ba."
"Kalli nan kiga Habi, zamanki anan fa ba mai d'orewa bane, naji su Yahya suna magana da lauyan zasu san yadda za'ayi a fitar dake, kuma hakan shi zai sa ki gane cewar gwara zaman naki, da kin gudu yanzu su Yahyan zasu tsaya miki haka ne?"
Habiba juyar da kanta gefe ga barin kallon Salame.
"Wallahi wajen ne babu dad'i Salame, ga sauro, ga duhu, ga makewayi had'e da inda kake ciki, ga d'an banzan wari, ga fargaba sannan ga babu mai taimaka min haka zan ta kama bango ina kokarin mikewa.
Abu d'aya dake sawa inji dama-dama shine in na tuna kince min aikin malamin nan yana hanya, sai inyi tunanin ko yau ko gobe asirin nan na iya ci."
Salame ta nisa.
"Ni kaina tunanina kenan don baki ga yadda ya dad'a tabbatar mun cewa jinkirin da aka samu da niyyarsa ne ba kafin in yarda, ina gaya miki kwanan nan baturen nan zai d'ebi kunya ya koma inda ya fito, don har sunan lauyan naku sai da na fad'a masa ya bashi sa'a.
Habiba ta girgiza kanta.
"Layaunsu dai Salame, don na gaya miki asirin Niger tuni ya fara karyewa, tunda aka kawo ni fa banda su Sadiqu ('ya'yanta) a babban gida ba wanda ya lek'o ni."
"Kar ki damu ai zaman duniyar kenan Biba, ba yadda za'ayi komai ya tafi maka daidai in mun d'and'ana wuya yau, gobe dad'i zamu fantsama cikinsa don tabbas ance bayan wuya sai dadi."
Salame ta fad'i hakan ne da kokarin kaucewa fitowar dariyar k'etar da
zuciyarta ke aunawa Habiba tun shigowarta wajen, idan ta kalli duk yadda ta fita haoyacinta ga idanu kwal! a waje, sai kuma ta
hango kud'inta dubu d'ari da hamsin cif!
A cikin sif d'inta ta gida.
Yo ni mahaukaciya ce kamar ke Habi zan d'auki kudi irin haka in kaiwa inda babu tabbas d'in nasara?
Ko da nasarar ma ni na tara irinsu ne da zan
kaiwa wani mak'iyin Allah k'aton banza ya lafe?
Ke dai da baki yarda da lamarin ubangiji ba yi ta sa rai!
A can wani d'aki na ganawar bak'i dake cikin kotun kuma Mami ta kalli Fadeelah tace.
"Ba yadda bamu yi ba amma wallahi sun hana mu shigowa da waya, Al'ameen yana ta son magana dake tun safe yake ta kirana."
Ta fad'a rik'e da hannun Fadeelan.
"Fatima ma tana waje ita da Abdullahi, tun safe muke tsaye anan baki ga da yadda aka bar mu muka shigo ba sai da Abdullahi ya basu kud'i tukunna, shima suka ce wai mutum biyu ne kawai zasu iya ganin naki, amma kowa yana gaishe ki Deelah, daga kan su Zahra har su Aseeyah ba wanda baya kira yaji me ake ciki, Hajiya Amarya ma ta damu sosai wallahi."
Jin yadda muryarta ta fara rawa yasa Fadeelah ta mik'o d'aya hannunta ta damk'e nata da duka biyun.
"Mami dan Allah... dan Allah ki rage damuwar nan insha Allah komai warware, Allah zai dube mu, Allah yana bayan mai gaskiya a kodayaushe."
Muryarta a tsaye take kyam, tsayen dake nuna cewar ba zuciyarta kad'ai ba, hatta ruhinta ya dad'e da karb'ar al'amarin nan, don tayi duk wata damuwar data zarce tunanin d'an adam ta zarta har ta kai mak'urar da komai ma yanzu kallonsa kawai take, an dad'e da k'ure malejin da hankalinta zai tashi akan wani abun.
"Tabbas haka ne..." Cewar Aunty Hadiza.
"Allah yana ganin komai Safiyya, sannan ga wannan lauyan shima yana iya kokarinsa, za'a yi nasara insha Allah."
Adam.
Fadeelah ta furta sunan a ranta, Allah ya sani bayan dogaronta ga Allah, ta gutsira wani b'angare na fatanta akansa, duk da cewa reto yake yana lilo don bata gama yarda dashi ba har yanzu, amma wani b'ari na zuciyarta ya fara yarda cewa ya san abinda yake yi tun daga zaman kotun da akayi, akwai wani abu game da yadda yake bin komai a nutse da kuma irin maganganun da yake gaya mata.
Ya Allah!
Yake gaya mata?
Yaushe ta ma ta k'arasa ganinsa tun bayan ranar da za'a fara shari'ar.
Mami tasa hannunta d'aya ta d'auke kwallar da ke shirin taruwa a idonta.
"Haka ne insha Allah komai zai zo ya wuce." Ta d'an shak'i numfashi kad'an sannan ta cigaba da cewa.