← Book details Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 95

Sashe 16

Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Har a lokacin bata iya fahimtar komai ba daga cikin muryoyin dake ta hawa da sauka a cikin kanta ba, sai wani irin jiri da ya mamayeta ta dinga jin kamar zata yi amai, tana iya ganin yadda mutane ke ta juyowa suna kallonta da tunanin gudu take yi ko tafiya, amma wannan bai dame ta ba neman inda zata fake kawai take yi.

Daga can wani gefe idonta ya hango mata hanyar wani waje mai tarin bishiyu, bata da lokacin tunanin inda ya fishi saboda haka ta durfafi wajen har tana tuntub'e.

A k'asan wata bishiya ta zauna ta duk'unk'une jikinta bakinta na furta tarin addu'o'i kala-kala.

Abubuwa da yawa suka fad'o daga cikin jakarta dake yashe a gefe.

"Baki kalli wayarki kafin ki shigo ba ko?"
Mami Saffiya ta tambaya sanda Fadeelah ta k'arasa cikin falon.

"10 missed call deelah hankalina ya tashi baki d'auki waya ba, naje har clinic d'in ance kinzo kin tafi, titi-titi duk inda na san kina zuwa naje ban ganki ba."
Sai ta ajiye jakarta akan kujera kai tsaye tace.

"Mami bayan na fito ne kaina ya shiga juyawa shine na sami waje d'aya na huta, amma yanzu naji sauki komai ya tafi."
"Ya salam!

Kinga abinda nayi ta gudu kenan, yanzu yaya kike ji?

Ta yaya kika iya dawowa gida?"
"Ya tafi ai, na samu waje na huta bana jin komai yanzu."
"Toh shikenan, bari in kira Miryamah in gaya mata baza mu samu zuwa ba, d'azun nan Farouk ya tafi dasu Zahra."
"A'ah Mami, wallahi naji sauki, muje kawai ko mun zauna ba abinda zanyi ai."
"Kin tabbata?"
Ta d'aga kanta a hankali.

"Toh shikenan, jeki ki shirya sai mu tafi."
Bayan ta fito daga wanka, tana nad'a hijabinta a gaban mudubi, Fuskar Al'ameen ta haska cikin kanta.

Ya salam! wai meke damunta ne?

Tana da tarin abubuwa a gabanta, Al'ameen kamar tsakuwa ne sabuwar haihuwa a cikin kanta, me yasa tunaninsa zaiyi girma ya dame ta a d'an k'ank'anin lokaci?

Ta danne k'arshen hijaabin da pin, sannan ta jawo wayarta cikin jaka da niyyar fita wajen Mami dake jira a mota, sai dai vibration na alamar shigowar sak'o ya katse ta a daidai k'ofar d'akin.

A lokaci d'aya, zuciyarta ta fad'o har dandaryar k'asa sanda tayi arba da number da sak'on ya fito ta cikinta, star ce guda d'aya tal! kamar yadda tayi saving number ADAM da ita, ba shiri ta bud'e sak'on sai dai abinda ta gani yasa zuciyarta data fad'i k'asa ta rugurguje har garinta.

Jotter ki tana wajena, in case zaki nema baki gani ba!
_A ina Adam ya sami jotter ta?_
_Kenan yanzu ya tabbatar da ciwonta da take b'oye masa?_
_Ya lesson d'insu zai kasance a yanzu da babu Dr.

Florence a gefenta?_
_Me yake shirin faruwa a kanta game da Al'ameen?_
BAYAN NA MUTU!

AYSHA SHAFI'EE
"So, kin shirya yin magana?"
Raunanniyar muryarsa ta fad'a yana kallonta daga tsallaken teburin dake tsakiyarsu, ya riga ya gama yi mata bayanin cewa ya tsinci jotar ta ne a k'asan wata bishiya dake gefen gidansu, ya karanta kuma ya fahimci tana fama da matsala ciwon kwakwalwa ne.

Takaicin Fadeelah d'aya ne a lokacin, na yadda jotar
bata d'auke da bayanin tsanarsa ko d'aya kamar yadda ta rubata a ta baya, idan har k'addara ta kaita har gefen gidansu ta yar da ita, ya kamata k'addarar ma tasa ya fahimci yadda ta tsani mu'amalarsu.

Saboda haka rashin rubutawar da bata yi a wannan ba yasa zuciyarta ta cika fal da k'ulli-k'ulli na haushin yadda bai ga ainihin tunanin zuciyarta game dashi ba, ta rasa wanne kuma daga k'ullin zata fara kwancewa.

Adam ya ciji k'asan lebb'ensa kad'an sannan ya juya gefe, bata san yaya yake jin wannan kallon da take masa bane, bata san yaya yake jin kamar idanunta na d'aure shi tsam! da jijiyoyin jikinsa ne ba.

"Akwai wani abu da ake cewa sirri, wanda na tabbata ba'a addinina kad'ai ba duniya gabad'aya ana girmama shi.

Me yasa ka bud'a min sirri na?"
"Saboda na tambaye ki kin k'i fad'a min, kuma dole sai da sanin abinda ya shafi sirri zamu iya yin komai, don haka akwai wani abu da ake cewa sadaukarwa ma a duniya don abubuwa su tafi daidai."
"Abinda nayi a baya kenan, shi yasa har ki ka ganni anan."
Kamar ya fahimce ta sai ya gyad'a kai kawai tare da rufe idonsa kad'an sannan ya fad'i abinda ya naushi kwakwalwarta.

"Leelah kina fama da 'Memory loss' right?" (Gushewar tunani)
Bata ce komai ba don bakinta ya k'ulle, ta cigaba da kallonsa kawai ba tare da ko kiftawa ba.

"Ba zan tambaye ki me ya faru ko a wani stage kike ba, don na riga na sami abinda nake nema, na samu amsar da yasa kwakwalwarki take hargitsewa wajen gane Maths."
Sai ta rage kaifin kallon da take masa, mamaki ya sirku a cikinsa.

"Akwai wata cutar kwakwalwa da ake kira 'Dyscalculia' tana faruwa ne idan an haifi mutum da ita ko kuma idan kwakwalwa ta bugu, ta samu ciwo ko kuma tayi rauni da yawa.

Nakasa ce da take dakushe b'angaren dake iya rik'e adadin abu, gane numbobin, sanin duk wani abu da zai had'a da lissafi ko kuma number-based operations.

Abinda na fahimta shine Memory loss d'inki ne ya jawo miki wannan cutar, shi yasa baki da matsala a sauran subjects d'in sai Maths kad'ai, da ace science kike karantawa kina yin Physics, dole ne a shima ki samu irin wannan matsalar.

Kuma zaki iya ganin cewa a asibitin ki basu gaya miki haka ba saboda basu sani bane, Dyscalculia ciwo ne kamar memory loss ba'a iya ganinsa sai dai alamunsa, kuma ke ba wata mu'amalar lissafi dake had'a ki da likitanki don haka ba lallai ne ya fahimta ba."
Fadeelah ta rasa wani irin yanayi take ji a lokacin da kasalalliyar muryarsa ke wannan bayanin, Mamaki?

Haushi? ko kuma rashin yarda da abinda ya fad'a?

Kamar ya karanci tunaninta kuwa, sai ya janyo wata hadadd'iyar tablet d'insa ya turo gabanta, a fuskarta shafi ne dogo dake d'auke da tambarin Sunan da ya gama fad'a yanzu.
*Dyscalculia*
Sai ta girgiza kanta game da maido
masa da tablet d'insa.

"Ni ban yarda ba, sai na tuntub'i likitana tukunna."
Ya d'aga kafad'unsa kad'an idonsa baya kallonta.

"Bani da lokacin jiran amsar likitanki leealah, kwanakin da zamu yi abin nan a k'aiyade suke, so ni zan koya miki yadda zaki yarda da hakan."
Kafin ta sake cewa wani abin, ya turo mata wata blank paper da biro akanta.

"Zaki iya rubuta min dukkan abubuwan da kike so a jiki?

I mean hobbies d'inki, duk wani abu kike jin dad'i in kina yinsa."
Bata d'auki paper ba, kuma bata bar kallonsa da idanunta da yake jinsu kamar wani gaushi a jikinsa ba.

"Idan baki rubuta ba ina da hanyar da zan sami amsata, kinga wancan karon ma dana tambayeki baki fad'a ba."
"Idan banyi niyyar rubutawa ba, magana ko barazanarka ma basu isa su canja min ra'ayi ba."
"Naji, rubuta."
Ya fad'a hankalinsa a kwance, ta ja tsaki a k'asan numfashinta sanda ta jawo paper ta shiga rubutawa.

Maganar da ya fad'a bayan ya gama karanta abinda ta rubuta ya kwance dukkan wani k'ulli dake zuciyarta.

"Good, zamu fara gobe."
Wannan wane irin yawo da hankali ne?

Tabbas yanzu ta k'ara yarda akwai dalilin da ya shigo da wannan mutumin cikin rayuwarta, dalilin kuma daya kamata ace ta fuskance shi don ta san yadda zata kare kanta in har yana tunanin ruguza mata rayuwa ne.

Da yamma gari yayi luf! kamar ana shirin samun saukar ruwa, Mami, Zahra da Iman sun tafi saloon a lokacin, Daddy bai dawo daga aiki ba, daga ita sai Farouk a gidan wanda ke can d'akinsa shi da wasu abokansa suna kallon ball.

Ita kuma tana daga kitchen tana girkin da Mami ta bar mata ta k'arasa, Basmati rice ce da miyar waterleaf wadda tasha nama.

Bata dad'e da yin wanka ba don bayan ta dawo daga makaranta ta shafe fiye da awa d'aya tana zaune tana yiwa Mami mitar cewa ita bata tunanin wannan extra lesson d'in da take yi zai amfane ta komai.

Kamar kullum doguwar riga ce a jikinta mai hannu iya gwiwa peach colour, ta nad'e kanta da mayafi kalar light brown, ranta cunkus da haushin da Adam ya bata, da kuma yadda ya d'auki jakarsa ya riga ta fita daga library d'in, a gefe kuma ga ihun abokan Faruk da ya cika gidan sanin da suka yi cewa Mami bata nan.

Tana k'ok'arin rage wutar miyar, falon ya karad'e da sautin k'ararrawar da aka danna daga waje.

Ba tare da tunanin kowa ba, ta isa k'ofar ta bud'e ta, wannan siffar tasa mai tsananin kyau sanye da k'ananan kaya farare ta baiyana a gabanta ba tare da wata katanga ba, sai taji kamar shi d'in fatalwa ne da in ta rufe idonta ta sake bud'ewa zata ga babu shi.

"Zaki iya gaya min me yasa Fadeelah bata amsa sallama?"
Muryarsa mai zurfi ta amsa a cikin kanta.

Sai ta d'an matsa baya kad'an alamun ya shigo sannan ta amsa sallamar da tunaninta bai bari taji ba.

"Nayi zaton ko ba kya amsa sallamar wanda baki sanshi bane tunda last time ma baki amsa ba."
Ya fad'a ba tare da ya shigo d'in ba, bata ce komai ba sai ya mik'o mata ledojin hannun sa biyu.

"Rik'e min wannan in d'ebo sauran."
Bayan motarsa dake bud'e ya koma ya d'ebo wasu kusan guda biyar sannan ya rufe motar, tana tsaye a bakin k'ofar har ya shigo ya tsaya dab! da ita sannan ya tura kofar ta baya da k'afarsa.

"Me kuka dafa yau yunwa nake ji Allah."
Kalmar 'Allah' ta fito a had'e da wata madda a mulmule, kafin ta amsa ihun abokan Farouk daga can d'aki ta karad'e falon, da ido yayi mata alamar me ake yi?

"Abokan Farouk ne suke kallon ball."
Ya tab'e baki kad'an, ta matsa daga kusa dashi sannan tace.
Chapter 16 · 0% Book details