Sashe 6
Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shima kuma ya tsani ire-irenta saboda suna saka hijaab, suna sallah, suna azumi, sannan basa cin fiye da rabi na kalar abincinsu... ko kuma a saukak'e kawai ace saboda su d'in Musulmai ne!
A lokacin da ta k'addara ta kawo ta k'asar America ana dab! da fara zab'e na sauyin Shugaban k'asa ne, kuma takurar da akewa musulmai ko kad'an bata kai haka ba sai a yanzu da canji yazo na sabon d'an takarar daya lashe zab'en, canjin daya tab'a kowa, kuma ya tab'a rayuwar duk wani musulmi dake cikin k'asar America.
Saboda tun kafin hawansa ya fito kiri-kiri ya nuna kiyaiyarsa ga Musulmai ya kuma dad'a k'arfafawa wanda suke da akida irin tasa hakan, sai ya zama musulmai suna fuskantar tozarci a fili kuma har ta kai ma ana shirin hana wasu musulman dake waje shigowa k'asar.
Kuma suma kamar kowanne musulmi a k'asar suna fuskantar wannan k'alubalen don a kwanakin baya har wasu sun daki Zahra a cikin motar makaranta saboda ta saka baki wajen hirar siyasar sabon shugaban k'asar da akeyi.
Gashi kuma a satin daya wuce an kori Mami Saffiyya daga wajen aiki saboda tace ba zata bi ka'idar sabuwar shigar da suka sanya na cire hijaab ba.
Allah ya sani komai nata YA MUTU a baya, amma zuciyarta na rik'e da son addininta, tana mutuk'ar samun nutsuwa a cikinsa, don ta tabbata ba zuwanta gurin likita ko magani ne ya tallafi kwalwalwarta a baya ba, k'arfin imanin da take dashi game da addininta ne.
Sai gashi a yanzu da cikin makarantar nan ya zama waje d'aya da take iya sakewa bayan cikin gidansu
shima za'a takura ta a cikinta.
Mutumin da a yanzu ta tsana fiye da kowa a makarantar yana cikin kungiyar dake shirin datse walwalarta.
Don me yasa kuwa baza ta damu ba?
"Toh don me yasa zaki damun?"
Romilda ta fad'a daga gefenta tana tauna sandwich d'inta cikin baki, Suna zaune a cafteria ne bayan fitowarsu daga class na uku a ranar, commerce.
"Naga dai bamu kad'ai ne musulmai a makarantar nan ba, saboda haka bamu kad'ai zasu takurawa ba."
Ta fad'a cikin turancinta mai cakud'e da yaren Spanish.
Fadeelah ta juyo ta kalle ta.
"Shine matsalar, don kawai bamu kadai za'a takurawa ba sai kice kar mu damu? bamu san me suka shirya ba? ba mu san k'ank'anta ko yawansa ba da zamu ce ba zai shafe mu sosai ba."
Melissa dake tsallaken teburin da suke zaune ta gyara zaman dogon gashinta zuwa bayan kunne sannan tace.
"Deelah, kome suke shiryawa ni na san hukumar makaranta bata san da zaman k'ungiyarsu ba, don haka za'a taka musu birki da zarar sun fara."
Turancinta a kwance yake fita ba irin na Fadeela dake a warware kona Romilda mai cakud'e da yarenta ba, don ita haifaffiyar baturiyar America ce kuma ba musulma ba, amma duk da haka k'awancensu na tafiya daidai kasancewarta mai saukin kai da kuma fahimta.
Fadeelah ta buga kanta cikin hannayenta tare da yin ajiyar zuciya.
"Kamata yayi kawai ace na yaga fastocin nan a lokacin da na gansu."
Romilda ta girgiza kanta.
"A'ah Deelah, a dai yanzu gwara da baki fara ba, gwara da baki yi abinda zai sa ya fara lura dake ba balle har mu shiga cikin lists d'insu don ko kin yaga zasu sake yin wasu ne."
Ta sake yin ajiyar zuciyar tana d'ago da kanta.
Ta san cewa shi bai santa ba, baima tab'a lura da ita ba a cikin d'imbin matan da suke cikin makarantar, Amma ita zuciyarta ta dad'e tana bidirin tsanarsa, tsana irin wadda d'an adam ke yiwa annoba!
"Kin je kiran Mr.
Hawkins kuwa?" Romilda ta katse shirunta, a hankali ta girgiza kai.
"Me ya faru?" Mellisa ta tambaya.
"Faduwa nake yi a komai na Math, makina yayi k'asa da yawa.
" Ta bata amsa muryarta a hankali.
"I'm sorry, ya kamata ki same shi gaskiya, ki gaya masa irin ciwon kwakwalwarki na san zai baki wani aikin ne da zai d'ago ki."
"Zanje." Ta amsa.
"Insha Allah." Ta k'ara akai.
"Mun tab'a zancensa bai zo ba kuwa..."
Muryar Romilda tasa ta wulk'ita da idonta gefe kuma a lokaci d'aya hoton fuskarsa ta shigo cikin ganinta.
Adam Steve, Saurayin da yafi kowanne tashe da d'aukaka a makarantar saboda dalilai biyu, fasahar kwakwalwarsa da kuma tsananin kyawunsa wanda ya had'e cikin kammani irin na Africa da kuma mutanen k'asar Turkey, tsananin kyawun da ya jawo masa girman kai da kuma tarin d'abi'u na d'agawa wanda baya hana d'aukacin matan makarantar suji kamar su bauta masa don kawai ya kula su.
Yana tafe rik'e da lemo cikin wani taku na tak'ama da kuma Izza, Dylan babban abokinsa na d'auke da tray din abinci a gefensa yana masa magana, amma shi in banda lemon ba komai a hannunsa don ba wanda zai iya bada shaidar ranar da aka ga yaci wani abu a makarantar, kafin a ganshi a cafteria d'in ma aiki ne.
Tana iya ganin yadda yawanci fuskokin mata ke binsa da kallo kamar yaune rana ta farko da ya shigo makarantar, da kuma yadda wasu ke cije lebbensu kamar suna hana kansu ihu ne saboda mahaukaciyar kwakwalwarsu na gaya musu cewa shine k'arshen burinsu.
Sai dai duk wannan hank'oron nasu yana bajewa ne a iska, Adam bai tab'a kula d'aya daga cikinsu ba kamar yadda aka san duk wani saurayi mai irin qualities d'insa nayi,
mata da yawa sun sha yarfa kansu wajen masa shishshigi don baya tab'a damuwa da kowa sai tarin abokansa da suke harkar karatu tare, mutane sunce yana da wani bak'in tarihi ne game da mata, amma abinda fadeelah ta sani shine bak'in tarihinsa bai hana shi yad'a tozarci ga addininta ba.
"Inaga ina da abinyi fiye da zama anan." Ta fad'a tana d'aukan jaka da wayarta ta bar teburin.
"Baki ci abincin ba..."
"Bana jin yunwa, sai na ganku a aji."
Daga cikin cafteria a mik'e office d'in Malamin Maths d'insu ta nufa, Mr.
Hawkins.
"Ina ganin ya kamata ki samu wanda zai dinga koya miki wani karatun daban a gida, makin ki ya b'aci da yawa, in zaki cigaba a haka bana tunanin zaki iya kaiwa gejin da ake nema wajen cigaba zuwa wani ajin."
Zuciyarta ta buga a cikin ramin k'irjinta, ta yaya zata maimata ajin da take tsawon shekara guda, ta yaya ma zata kalli Daddy tace masa rashin k'ok'arinta ya kai har ta maimaita aji?
"Zanyi iya k'okarina sir, zan dage in dinga ganewa, watakila in ka bani wani aikin naje nayi zan samu k'arin makin."
"Yaudarar kai kenan, ina fada miki ne ya kamata ki nemi malamin da zai dinga miki wani karatun a gida, sai ki iya samun maki mai kyau nan gaba amma a haka, ba zaki iya kaiwa inda ake so ba."
Ta d'anyi shiru tana murza 'yan yatsunta, ita ta san Daddy ba zai iya d'auko mata wani malami ba a yanzu.
Kuma ta san in har ta amsawa Mr.
Hawkins to ta yaudari kanta ne ta guntulewa kanta samun wata hanyar da zai iya kawowa ta taimake ta, saboda haka tace.
"Kayi hakuri sir, Babana ba zai iya d'auko min wani malami a yanzu ba."
"Saboda me?"
Yayi tambayar da zuciyarta ta san zata biyo baya, sai dai har ta bud'e baki zata yi magana k'ofar office d'in ta bud'e bayan bugu d'aya kawai da akayi.
"Ance kana kirana... sir?"
A cikin sakan d'aya kawai tunaninta ya tsaya cak!
Don a cikin sakan d'ayan kawai wannan muryar ta shiga kunnenta, muryar wanda ta tsani had'uwa dashi, wanda
zuciyarta ke gudunsa kamar irin gudun da bawa ke yiwa Shaid'an.
Me ya kawo shi nan kuma bayan ta yiwa kanta katanga dashi daga cafteria?
Sai kawai ta d'auki jakarta tace da mr.
Hawkins ta gode sannan tayi hanyar k'ofa.
Ta rik'e numfashinta sanda tazo gifta shi, ko kad'an bata k'aunar ta shak'i kamshin turarensa wanda ta haddace shi a gefen lokarta.
Sai dai abinda bata sani ba shine alkalami ya riga ya bushe akan k'addararsu, Office d'in Mr.
Hawkins shi ya zama jigon mafarin k'addarar dake jiransu a gaba!
****
"Bayan duka kuma abin ya kai har ga zagi?
Daddy ya kamata muje makarantar nan, ba zan zauna kowa ya dinga takura musu don kawai wani dan isk** shugaban k'asar su ya basu damar...
Mami Saffiyya ta fad'a cikin fad'a tana ajiye bowl din miyar dankali akan dining table inda suka taru gabad'ayansu suke cin abincin dare.
"Kar ki k'arasa, yaran nan suna jinki." Daddy ya fad'a yana tauna abincinsa.
Zahra wadda ke zaune a gefensa, ita ta gama k'orafi akan wani d'an ajinsu dake zaginta, amma kamar ba akanta ake maganar ba, hankalinta ya tafi wajen raba abincinta da nikak'ken naman da aka had'a.
"Da gaske nake, bana tunanin shirunmu zai sa rashin mutuncin nasu ya ragu.
" Ta sake fad'a sanda taja kujerarta ta kusa da Fadeelah ta zauna.
"Kana jin me nake fad'a kuwa?"
"Kowacce kalma, amma ba inda za kije, dole ne mu k'ara hakuri don makarantar yara ce k'anana, ba zai yiwu muje fad'a dasu ba, in har abun ya k'ara yawa ne sai ayi reporting."
Ba haka taso ba amma ba yadda zata yi, sai ta miko masa plate d'in salad tana fadin.
"Amma dai ko kiran malaminsu ne ya kamata ayi, don su san ba tsoronsu muke ji ba."
"Karki damu, abincin nan yayi dadi da yawa...
Kin iya girki.!"
Sai murmushin dad'i ya maye gurbin fushinta.
Fadeelah na zaune a gefenta tana tauna abincinta a hankali, tunani take a cikin kanta in har yara k'anana zasu fara nuna kiyaiyarsu ga yara irinsu musulmai, me yasa take ganin hakan ba zai faru a makarantarsu ba? zuciyarta ta cika da d'aci sanda fuskar Adam ta shigo cikin tunaninta, wani mutum guda d'aya da ta tsana fiye da kowa, bata sani ba ko a rayuwarta ta baya akwai wanda ta tsana irin hakan, amma BAYAN TA MUTU, shine halitta na farko da taji bata sonsa, kuma bata sonsa har cikin zuciyarta.
"Do you know what the boy even said...?" Muryar Iman ta fad'a cikin kunnenta.
"Iman, Hausa!" Mami Saffiya ta katse ta.