← Book details Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 95

Sashe 64

Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

'Yan Babban gida suka sami abinda suke so, farin ciki ya rufar musu ganin cewa suke da nasara a kowanne zama da akayi, hankalin Kawu Ibrahim ya tashi ya zama kusan kullum yana zarya tsakanin Ikara da Zaria wajen Adam, Mami ma ta k'ara rud'ewa gani take a kowanne lokaci za'a iya yankewa Fadeelah hukunci akan shari'ar nan, ita kanta Fadeelah duk sanda aka shiga zaman kotun ta kalli fuskar 'yan Babban gida taga yadda kowannensu ke murmushin jin dad'i sai zuciyarta ta sare, don hatta Habiba yanzu ta fara goge tashin hankalin kan fuskarta ganin yadda shari'ar tafi karkata gare ta a kullum.

Sai itama ta fara tunanin cewa sa'a na hannun kowa, rayuwarta tare dasu Mami zai iya kasancewa shine lokacin hutunta kawai a duniya, komai zai iya k'arewa a wannan gab'ar a yanke mata hukuncin da zai kawo k'arshen rayuwar tata.

Akwai zaman da akayi wanda Kutama ya dinga kawo hujjoji harda hotunan gawar Hajiyan ga Alkalin, hankalin mutane ya nutsu aka dinga ganin kamar a ranar za'a kawo karshen shari'ar saboda yadda komai ke fitowa fili...

Amma Alkalin ya juya zaton kowa da sake d'aga k'arar zuwa wani lokacin, da alama yayi amfani da rok'on Adam na tun farko cewar kar kotu ta yanke hukunci cikin gaggawa.

Sai dai duk wannan abin da akeyi, hankalin Adam a kwance yake tsaf don shi kad'ai ke iya k'arfafawa Kawu Ibrahim gwiwar cewar ya kwantar da hankalinsa shima, Kutama yana barazana ne kawai da abinda bai sani ba.

Aunty Hadiza, Fatima dama kuma Abdullahi duk sun koma a lokacin, don haka Daddy da a dole ya nemi hutu a asibitinsa shi kad'ai ke kwantar da hankalin Mami data kafa ta tsare cewar ba zata koma Abuja ba sai an gama shari'ar nan, tana zaune a garin har lokacin kuwa da aka d'age shari'ar da hutun sati biyu, su Zahra ma sunzo amma har suka tafi basu samu ganin Fadeelah ba don an dad'a saka tsaro sosai akan ganin nata.

Abinda ya dad'a d'aid'ata rayuwar Mairo kenan wadda har a lokacin take wajen Kawu Ibrahim, kullum tana gidan bata taba fita sai ranar da za'ayi zaman kotu, ta toshe kunnenta kuma ta hakura da duk wani zagi da maganganun da ake fad'a mata a Babban gida, ta karb'i rayuwar a yadda tazo mata hannu biyu ta manta da Sadiq da wasu 'yanuwansa, 'ya'yanta ne kawai kan fad'o ranta lokaci zuwa lokaci tana jin kewarsu, amma duk da haka a ranar da Sadiq ya shafawa idonsa toka ya d'ebo 'yanuwansa har cikin Babban gida da sunan biko, bata ko kalli 'ya'yan ba balle shi.

Kawu Ibrahim kawai suka samu ya saurare su a duk fad'in gidan, kuma shima bai basu wani fata ba don yace sai abinda ita ta yankewa kanta tukunna, saboda laifin Sadiq ya riga ya fito k'arara su kansu 'yanuwan nasa a yanzu sun san ya aure ta ne bisa rashin sanin iyayenta, amma da yake da kud'insa a k'ugu sai hakan ya zama kamar ba laifi ba kowannensu ya rik'a sunkuyar da kai wajen nemar masa bikon.

Tawagar biko na biyu daya kawo ta mata ce, wadda hakan ya had'a har da yayar mahaifiyarsa, suka zo da dad'in bakinsu, don har magiya sun had'ata da ita suna gaya mata halin da 'ya'yanta ke ciki amma daga k'arshe tashi tayi kawai ta k'ulle kanta a band'aki har suka gaji suka tafi.

Ta riga ta yiwa kanta alkawarin cewa sai ta tarwatsa rayuwar Sadiq kamar yadda ya tarwatsa tata itama.

Sai ta hargitsa shi ta raba shi da duk wani sukunin rayuwa, sai dai hakan zai zo ne a gaba don yanzu ba ta shi take yi ba ko kad'an, ta 'yar'uwarta take.

Duk da har yanzu basu yi wani had'uwar kirki da ita ba amma hankalinta a tashe yake kamar kowa, kowa d'in da bai had'a da jama'ar Babban gida ba, wad'anda a gaban idonta suke kafa hira ana rahar yadda shari'ar ke kai musu, don hatta labari ya fara yawo a cikin gari cewa an kusa yankewa Bintu hukuncin kisa itama, saboda a wannan d'an tsukin Kutama ya firfito da hujjojin da ko alk'alin ya fara gamsuwa dashi.

Yadda hankalin kowa ya tashi haka ma na Fadeelah ya fara rawa ganin yadda komai ya karkata d'aya bangaren, hakan yasa ta ture komai ta tambayi Adam d'in a wata rana da yaje ganinta.

Saboda kamar k'aida ya mayar da zuwa dubata cikin kowanne sati, har ya zama itama ta kan k'irga kwanakin da zasu kai ga zuwan nasa saboda ta sami kayan amfani...

Zaman cikin kurkukun bai canja daga komai ba, amma rayuwarta a cikinsa ta canja dalilin kulawar da take samu daga Adam, bata da matsalar abin ci a yanzu ko ko na abin sha, sannan bata ko ciwon kai balle zazzabin saurayen da basa damunta a yanzu, magungunan komai tana dasu hatta vitamin C wannan, Adam ya canja mata komai ya kuma sauk'ak'a mata zaman wajen, hakan ya k'ara masa matsayi sosai a idanun su Mami har ma da Kawu Ibrahim a duk ganin da zasu yi mata ranar zaman kotun, amma ita a ranta ta yarda cewa yana kyautata mata ne kawai don amfanin kansa, saboda yayi ya rabu da shari'arta kamar yadda ya fad'a.

"Kin manta me na fad'a miki?" Lallausar muryarsa ta tambaya maimakon ya bata amsar abinda ta tambaye shi d'in.

Yana zaune daga kujerar tsallaken teburin data raba su, hannunsa rik'e da wata 'yar karamar jotter da yake d'iban bayanin wani abu da ya tambayeta game da Hajiya mai rasuwa.

Tun zamansa a wajen sau d'ay
a ta kalle shi, a yanzu wani irin kwantaccen saje ya fito a kowanne gefe na fuskarsa, hakan ya fallasa mata cewar yawan aiki ya rage masa lokacin kula da kansa, hasken d'akin kuma ya k'ara fito da bak'in wannan gashin nasa da yake a taje kullum, a lokacin taji kamar ta tasho taje tasa hannu ta barbarza shi ya koma kamar yadda yake lokacin had'uwarta dashi, sannan ta d'auko mudubi ta haska masa kansa a ciki, watakila hakan zai sa ya bud'i baki ya gaya mata cewa shine dai Adam d'in da ta sani a da.

"Tun kafin a fara komai na gaya miki cewa mutanen nan sun tara isasshiyar shaida a hannunsu, so bai kamata kema ki biyewa mutane a tunaninsu ba, wannan duk barazana ce kawai lauyansu yake yi akan abinda suka bashi, na kusa gyara masa tunaninsa."
Ya fad'i hakan ne a hankali yana lumshe idanunsa, wani irin bacci ne a idonsa tun lokacin da muryarta ta fara yi masa bayanin daya tambayeta, gajiyar da yake ciki ta salallab'o ta rufe shi don ya manta yaushe rabonsa da bacci a cikin kwana biyun nan da shari'ar ke shirin dawowa hannunsa, tsabar yawan aikin da yake yi da kuma had'e- had'en bincikensa yasa ya ture bacci daga cikin priority list d'insa..

Ya riga ya zama addicted da yawan aikin dake gabansa shi yasa rashin baccin ma baya damunsa.

Fadeelah ta cukwuikuye ledar kayayyakin da ya kawo mata, sannan tace.

"Kana tunanin za'a k'ara wata guda ana cigaba da shari'ar?"
Ya sake lumshe idonsa.

"Komai yana hannun Allah, amma a yanzu da shariar zata dawo hannuna...

Ba zan ja da nisa ba, zan fito da komai a d'an k'ank'anin lokaci insha Allah."
"Me kake nufi da shari'ar zata dawo hannuka?"
"Lauyansu ya gama fito da duk shaidunsa, yanzu turn d'inmu ne, mu zamu yi leading shari'ar."
Yadda ya furta kalmar 'Mu' d'in ta fito kamar lokacin da suke tutorial d'in nan ne, sannan ya bada ma'ana kamar ita dashi sun zama team a yanzu.

Ta rasa tunanin cewa Adam ne zaiyi leading shari'ar ya sata jin sassauci a zuciyarta ko kuma yadda ya had'e shi da ita cikin jimla guda ne.

Tunaninta ya shiga lalube kan wane irin shaidu zai gabatar amma muryarsa ta katse ta...

Muryarsa da ta saba da ita a yanzu.

"Mu cigaba?" Ya tambaya.

Sai ta sake cukwuikuye hannun ledar sannan ta cigaba da abinda take gaya masa kafin tayi tambayar data katse su.

"Bayan haka, akwai ranar da Inna Saratu ta aike ni Babban gida in kaiwa Hajiya goro, bani da wani wayo a lokacin sosai amma ban so zuwa ba, saboda ko tare da ita muka je a gaban idonta ma masu zagina da habaici Allah yayi yawa dasu.

Mutum na farko dana fara gani kafin in kai b'angaren Hajia Aunty Sadiya ce, ta fito da tulin wankinta tana yi tana biyo wasu wak'okin hausa, tana ganina tace inzo in tayata wai ba don kar na mata jagwalgwalo bama da ta bar min gabad'aya..."
Adam saurarenta kawai yake yi amma baya fahimtar ma'anar abinda take cewa, jin muryarta yake kamar sarewar dake busawa a hankali tana kwad'aita masa baccin da yayi kewarsa tsawon kwanaki biyu.

"...Sai muka fi kusan awa guda muna yi kafin ta saka ni in shanya mata, daga nan na hadu da Aunty Saratu matar Kawu Nura kafin k'arasa wajen Hajiyar, ta aike ni can Kasuwar rana in siyo mata kayan abinci, tafiya mai nisa ce tsakanin nan da kasuwar ga rana, ga k'ank'ata ta, amma bata duba komai ba ta tura ni, na tafi na b'ata don ban gane hanyar dawowa ba sai kusan yamma, hankalin Aunty saratu ya tashi akayi ta nema na.

Masu neman nawa sun tafi ni kuma na dawo na shiga na kai mata, kuma ko a jikinta tace in ajiye nan k'ofar d'akinta.

Daga nan nayi wajen Hajiya, ina ta sauri inje in kai mata goron dake k'ulle a jikina kafin wani ya sake ganina, hakan yasa naci karo da Yaya Sule a zauren shiga wajen nata, ya danno wani zagi sanda ya damk'o wuyana ya d'aga ni har sama..."
Jin yadda take ta bayani ba tare da yace komai kamar da farko ba yasa ta d'ago da kanta ta kalle shi, mamaki ya dirar mata a lokaci d'aya sannan ta zare ido tana kallonsa...

Ya jingina kansa baya kad'an da kujerar da yake zaune, ya karkata fuskarsa, ya rufe idonsa, dogwayen gashin idon sun bi sun kwanta luff akan junansu sannan numfashinsa na fita a hankali...

Bacci yake yi!
****
BAYAN NA MUTU!
Chapter 64 · 0% Book details