← Book details Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 95

Sashe 28

Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Dama duk me suka sani sauran 'yan class d'in, ke dai bari ai za'ayi decoration d'in da ba'a taba yin irinsa ba a..."
Duk hirar da suke hankalin Fadeelah baya kansu, tunda ta idar da sallar la'asar ta nemi guri ta kwanta don ranar bata da lectures ko daya, sai dai baccin da take ganin kamar tana jinsa yak'i zuwa ko kad'an, saboda haka ta lalubo takardun lesson d'inta da Adam ta shiga bitar kowacce question d'aya data riga ta haddace ta.

A jikin wata tambaya guda d'aya idonta ya gano wasu kalmomi da suka sa kwakwalwarta tunani.

Da sauri ta mik'e zaune tana k'ara kallon rubutun kafin ta d'ago ta kalli Zahra.

"A ina mukullin store yake?"
"Yana jikin k'ofar d'azu na rufe." Ta bata amsa tana tand'e bakinta da take sawa janbaki.

"Yawwa Aunty deelah nima zan duba wani abu da nake tunanin na saka a cikin kayanki muje tare."
Iman ta fad'a sanda ta biyo bayanta ta nufi hanyar k'ofa.

Cikin k'aton kwalinta na store d'in tayi ta bincikawa har sai da ta d'auko tsohuwar jakarta ta makaranta da take amfani da ita a America.

Hannunta na rawa ta zuge wani d'an k'aramin zip a gefe ta zaro wata siririyar takarda, takardar da tun daga ranar data ajiyeta bata k'ara tunawa da ita ba sai yau.

Ta warware ta da sauri sanda tsararren rubutun jiki kamar an buga shi ya baiyana.

Ya jikin naki?.

Aka rubuta daga tsakiyar paper sai daga can gefe kuma.

Mr.

Hawkin's yana nemanki.

A hankali ta kara ta da rubutun Adam na paper lesson d'insu... kamar an tsaga kara, iri d'aya sak!

Kenan Adam ne ya rubuto mata paper a lokacin? a ranar data koma makaranta bayan rashin lafiyar da tayi? ya akayi ya san bata da lafiya? tun a lokacin ya san matsalarta kenan?

Shi yasa ya tambayeta tun sanda zasu fara lesson d'in nan? shi yasa ya nemi jotarta don ya nuna mata ya san me take ciki?

Ta rufe idonta a hankali tana tunanin wane irin mutum ne shi daya iya mu'amala haka? waye zaiyi ta binta a hakali ta laluma haka?

"Aunty Deelah Id card d'in waye wannan?"
Muryar Iman ta fad'a a kusa da ita, ta bud'e idonta a hankali sannan ta karbi id card d'in da take nuno mata.

WASHINGTON STATE BAR
1111 East Main street, Suite 819
VA 2356-4318
Barrister Adam Steve
Status: Active
ID Number: 54217
Issued: 01/08
A gefen duk wannan bayanin, Hoton Adam ne cikin wata bak'ar suit, gashinsa da kullum yake a barbaje yanzu a kwance yake luf! cikin wani hadadden style, sannan yana da wani kwantaccen saje daya had'u ya zagaye da gashin baki wanda ya k'arawa kamaninsa mutukar kyau ba kamar yadda ta sanshi a makaranta ba, abu d'aya daya tabbatar mata da cewar Adam d'in data sani ne a hoton shine wad'annan lumsassun idanun nasa!

Bakinta ya furta sunan da kwakwalwarta ta kasa fahimta cike da rud'ani.

BARRISTER ADAM STEVE?!

Adam lauya ne?!
_!!!_
_Labarin dai yana ta warware wa!_
_Muna ta gangarawa!_
_Mun kusa kaiwa inda komai zai kwance gabad'aya!_
BAYAN NA MUTU!

AYSHA SHAFI'EE
Ayyiryiryiriiiiii!

Ayyiryiryiriiiiii!

Wata dattijuwar mata rangad'a zankad'ed'iyar gud'ar data cika kaftanin d'akin, duk kuwa da d'imbin hayaniyar matan da suka cika falon suna ta d'aga wasu tsantsara-tsantsaran kayayyaki daga cikin jerin akwatunan dake gabansu.

"Wallahi kaya sunyi mutuk'ar kyau masha Allah, Allah ya sanya alkhari nawa suka bayar kuma kud'in d'inki da cefanen?"
Wata k'awar Haj.

Halima matar Baba habibu ta tambaye ta sanda suke duba akwatin kayan shafe-shafe.

"Dubu d'ari cif! ai wallahi munga kokarinsu, don da farko dubu talatin muka tanada tukuici sai da aka cika ashirin."
"Sun cancanta gaskiya, a sabon ma'aikaci ai yaron yayi bajinta ba kad'an ba, akwati goma fa."
"Goma kam! ni yanzu jigilar na Saifudden kawai nake hangowa, ba had'a lefen ba taronsa kamar wani bikin ne."
"Haba hajiya ku da abin gabad'aya na cikin gida ne, ku zaku had'a abinku fa ku karb'i kayanku."
"Ke dai bari, abinda kake rainawa shi yake zuwa ya baka tsoro."
Daga gefensu haj.

Saddika matar Baba sani tace.

"Ai mu ya kamata mu fad'i haka ma ba ke ba, tunda a lokacin komawa gefe zaki yi ki bar mana hidimar."
Da dariyarta ta amsa mata.

"Ke da har yanzu baki fad'i matsayarki ba, ni dai ina gaya miki ne gwara ki zab'a tun yanzu kar abu yazo ya cakud'e miki ki rasa inda zaki yi.."
"Babu zancen cakud'ewa don zan iya, kowanne b'angare ina nan, ni ta amarya ce kuma ta ango."
Suka yi dariya gabad'aya ta cikin surutun dake tashi a d'akin, ko'ina ka duba mutane ne dai ke ta d'aga kaya daga wannan akwati zuwa wannan, yayin da daga can kitchen su Mami ne da Aunty Hadiza, matar kawu Isma'il da kuma wasu daga cikin 'yan uwansu makusanta ke hidimar raba irin snacks d'in da aka sallami dangin ango dasu ga mutanena cikin gidan.

A d'aki na k'arashe daga benen gidan, Rahma ta bud'e k'ofar band'akin da k'arfinta.

"Wallahi na dad'e banga 'yar iskar amarya irinki ba, kina nan kina waya ana k'asa ana bidirin kawo kayanki."
Aseeyah ta d'ago daga wayar da take yi ta kalle ta.

"Zuwa zanyi in taya su ko me?"
"Ai abinda ya rage baki yi ba kenan, ko ni duk rashin kunyata barin gidan zanyi wallahi."
"To sai gani ni kuma na dame ki a rashin kunyar."
"Ai baki burge ni ba, da kin sani da suka shigo zuwa zaki yi ki gaishe su, ki tsugunna kiyi godiya in sun tashi tafiya kuma ki taka musu zuwa mota."
Fadeelah dake gefe cikin kwalliyarta kamar kowa a gidan, tayi murmushi kawai tana jinsu hannunta na kan wayarta da take browsing wani assignment na makaranta.

"Kin san Allah in su Mama suka san kina gidan nan sai ranki ya b'aci."
"Toh ta yaya zasu sani, sai dai in ke ko munafakan yaran nan ne zasu gaya musu..."
Ai kuwa kafin ta rufe baki, su Sahla Sameera da Zahra suka banko cikin d'akin, da sauri Rahma ta rufe k'ofar, a yanayin kwalliyarsu wani zai zata ranar ake d'aurin auren.

"Mutane 'yan naci ne wallahi, sun k'i su matsa ma muga komai." cewar Sahla.

"Ni wallahi 'yan k'auyen nan da Hajiya ta gaiyato tsoro nake kar a samu masu sata, dan yaya Rahma baki ga yadda suke kallon kayan nan ba wallahi."
"Kowanne fa sai sun kalle shi sau uku-uku."
Zahra ta karb'ewa Sameerah.

"Dama a yanzu manya ya kamata su fara gani, ku da za'a bar abin a gidan ma ai har sai kun gaji da gani in dai kaya ne."
"Mun d'ebi na d'iba ba kuma." inji Sameerah.

"Eh dole, tunda ku za'a aura me zai hana ku d'iba.

Fatima ta shigo d'akin a lokacin hannunta rik'e da tray d'in snacks.

"Kun san me yake faruwa kuwa?

Mami Hauwa ce fa tazo yanzun nan."
"Wacce?"
Rahma da Sameera suka had'a baki wajen tambaya.

"Wacce kuka sani in ba ta Kaduna ba? wallahi yanzu direba ya sauke ta gata can a falo ana gaisawa."
"Kai! wallahi Aseeya kin ciri tuta, kawo lefe ba biki ba matar nan ta tako k'afa tun daga kaduna tazo? fito-fito kiji sabon labari."
Fadeelah ta amsa sanda ta nufi inda Fatima ta dire tray d'in nan, ta d'auki samosa guda d'aya sanda su Sameera suka nufi k'ofar band'akin suna fad'in.

"Dama wai tana nan...

Yaya Aseeya Mami cewa tayi fa kin fita... in gaya miki akwati set goma... kinga wani lace a cikin kayan kuwa..."
Fatima tace.

"Ku kwantar da hankalinku mana, in dai kaya ne sai kun ture, wani ma na hanya."
"Kayan wa kuma?"
Fadeelah ta tambaya.

"Wai baki san yaya Saifudden ne zai auri Rahma ba? har fa ana shirin kawo kud'i."
Mamaki ya kama Fadeelah, ashe shi yasa kwanaki da zasu je gidan Baba habibun tak'i binsu, da kuma sanda ta ganshi a kitchen ya tambaye ta Rahman, ita fa har yanzu bata iya maida hankali kan sha'aninsu, sai dai ta saurari iya abinda ta tsinta kawai don Mami ma yanzu ta rage hira da ita samun su Aunty Hadiza da Aunty iyami a kusa.

Ta jinjina kai a hankali, mamaki take yadda hali biyu mabanbanta suka had'u, shi miskili mara magana Rahma kuma wayayyiyar mace mai surutu da rawar kai, lallai wani had'in sai Allah.

"Kema Deelah kamata yayi kawai a had'a ki da Rahman ki fito mana da ango musha biki... ko ranar nan wani abokin Yaya Yusuf sai da yayi min zancenki."
Cak! tunaninta ya tsaya, don yau ne rana ta farko da wani mahaluki ya d'auko kalmar aure ya danganta ta da ita, saboda damuwar kowa a kanta na rashin lafiyarta ne da son jawo ta cikinsu, hatta Mami kuwa... tunaninta akanta kullum na samun lafiyarta ne kawai, sai taji kamar ta zama mutum kamar kowa ne da Fatiman ta fad'i hakan.

Duk da cewa kuwa har ga Allah bata son d'orar da rayuwarta a haka, bata son saka kanta a wata sabuwar rayuwa da guntulallen asalinta iya na yanzu, tafi son ace itama ta koma cikin 'yanuwanta kamar yadda su Mami suke yanzu, tana son samun irin wannan farin cikin da annushuwar da take gani a idanunsu duk sanda suka je gidan Hajiya Amarya.

Ta tauna samosan hannunta a hankali sanda hayaniyar gidan ta k'ara rud'ewa sakamakon wata dank'areriyar sark'ar gold da aka gano a cikin d'an kit d'in kayan lefen.
i ta mik'e ta koma kusa da jakarta, ta zaro Id card d'in Adam, ta kalli wad'annan lumsassun idanun nasa da suke kama da yana d'aukanta a hoto ne duk sanda ya kalleta, da murmushinsa dake maqalewa a gefen lebb'ensa d'aya, da kwantaccen gashinsa daya taho har ya rufe gefen idonsa, taji kamar ta mik'a hannu ta ture gashin ta kalli idon nasa sosai, idon tayi kewa tsawon shekara guda da d'oriya.

Don a yanzu ta riga ta gama lissafawa cewa kewar Adam take, shi yasa ta kasa cire shi daga ranta tsawon wannan lokacin, shi yasa komai k'ank'antar abu yake tuna mata dashi, shi yasa a ranar data rasa magazine d'in nan ranta ya sosu.
Chapter 28 · 0% Book details