← Book details Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 95

Sashe 38

Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ka wanke kowanne biyar, iya kyan da suka yi, iya yawan kudinka."
Da sauri ta zare yatsunta daga cikin nasa sannan a gajarce tace.

"Ina zuwa."
Da haka ta juya ta barshi da mai hoton suna cinikin rabon da Allah ya kawo masa.

Bata yi nisa ba taci karo da Fatima wadda ke ta faman zarya daga nan zuwa nan saboda ita kanta adadin mutanen gaiyarta daban ne.

"Faty Mami nake tambaya kinga inda suka yi?"
"Gasu can wajen amarya suna d'aukar hoto, me za'ayi?"
"Al'ameen ne zai bata sak'o kafin ya wuce gida, wai ba dad'ewa zaiyi ba."
Da murmushinta tace.

"Yarinyar nan zaki biyani fa wallahi plan d'ina yayi aiki, kice har bibiyarki yake ko'ina."
"Bafa saboda ni yazo ba, na gaya miki Mami tace ya bari sai anyi bikin sannan ya tafi."
Kafin ta amsa mata, Aunty iyami daga can wajen ta shiga d'ago musu hannu, don duk 'yan gida masu irin ankonsu suna ta zuwa ana d'aukar hoto da Amarya da ango wanda sai fara'a suke dukkaninsu cikin shigar brown kaya da suka dace da kwalliyarsu.

"Mami, Al'ameen ne yake nemanki, yazo yanzun nan."
Fadeelah ta fad'a cikin hasken flasher sanda suka jeru gabad'aya ana d'aukar hoton, ta san a wannan lokacin ne kad'ai Mamin zata saurareta, ganin ana d'aukar hoton ma wasu daga can na d'ago mata hannu.

Ai kuwa da kyar ta samu ta had'ata da Al'ameen d'in da ya dad'e a tsaye yana jiranta bayan dawowarsa daga wajensu Ya Abdullahi.

"Mami kayan da kika ce in taho dasu ne daga gida, suna nan a cikin booth, kuma ni yanzu zan juya."
Cikin alamu na rud'ewar biki Mami Safiyya tace.

"Yawwa to ai ga ma Fadeelah a kusa, kuje ki karbi muk'ullin motar hannun Farouk, a kwashe kayan a saka a cikin booth d'insa, plates ne da za'ayi amfani dasu gobe da safe na manta ba'a tafi dasu ba."
Da haka bata k'ara cewa komai ba ta juya ta koma wajensu Aunty iyami.

"Kin san inda Farouq d'in yake?" Al'ameen ya tambaya.

Ta girgiza kanta tace.

"Ai Farouq ma baya cikin wajen nan, tun d'azu suka fita, gashi kuma tace kayan na amfanin gobe ne."
Ya cije lebbensa kad'an alamun tunani.

"Kawai muje wajen, duk motar da zata koma can gidan sai a saka kayan a ciki."
Da hakan suka sami wani direba daya d'ebo wasu mata daga can gidan bikin suka kwashe kayan gabad'aya aka saka a motar tasa.

"Gobe zan koma fa."
Al'ameen ya fad'a sanda ya mik'o mata fakitin wasu cokala na k'arshe a cikin kayan, ba don ta riga ta mik'o hannunta ba, watakila daya sake su ne a k'asa saboda yadda maganar ta shammace ta.

"Zaka koma ina?" Tambayar ta fito kai tsaye ba tare da tantancewa ba.

Sai yayi murmushi kad'an, hannunsa akan murfin booth d'in dake bud'e.

"Garinmu mana, ko kin manta d'azun nan ma ki gama min gorin na saka kayanku."
Mamaki bai barta ba, ta had'e hannayenta sosai ta rik'e cokulan.

"Amma nayi tunanin Mami tace sai bayan bikin tukunna."
"Flight d'ina na yamma ne, saboda haka zan sami d'aurin auren da safe, ai shine k'arshen bikin koh?"
Saboda shirme sai ta girgiza kanta tace.

"Akwai kai amar..." Kan ta k'arasa ta hango shirmen nata saboda haka tayi saurin had'e zancen da cewa.

"Mami ta sani kuma?"
"Ina zan saka Mami a wannan lamarin, Daddy ne kawai ya sani amma ita sai goben tukunna idan taga babu yadda za'ayi kinga sai in tsira."
"To amma me yayi zafi haka?

Saurin me kake yi?"
Ya d'anyi shiru wannan karon kafin yace.

"Mamina ta matsa in koma can d'in ma, beside ai ban ma yi sauri ba in kin duba kwanakin dana k'ara bayan gama aikina, sannan hutuna ma ya kusa k'arewa."
Zuciyarta tayi tsalle sannan ta hantsila a lokaci d'aya jin sunan Aunty Miryamah daya kira, itafa ta riga tabi shawarar Fatima ta cire ta kwata-kwata daga kanta a yanzu,shi yasa take iya yin komai ba tare da fargaba ba.

A idonta ta hasko da za'a iya nuna haska mata duk abinda ya faru tsakaninta da Al'ameen a cikin d'an lokacin nan, ta tabbata ba abinda zai hanata kashe ta sannan ta had'a ta binne ta tare da duk wata shaidar kisan!

Ta had'i yawu ya zarce makogwaronta wajen kokarin b'oye damuwarta sannan a hankali tace.

"Allah ya kaimu goben, Allah kuma ya kiyaye hanya."
Shikenan fa!

Komai ya kai k'arshe, shirmen da zuciyarta ta d'ora ta akai har ta janyo Fatima cikin wautar tata duk ya k'are a yau, duniya ta koya mata wani b'angare na hankali, ta fahimci ba'a kodayaushe ne Allah ke azurta mutum da dama har sau biyu ba dole ne ka girbi abinda ka shuka a wasu lokutan.

Al'ameen ya riga ya barta kamar yadda wannan shekara d'ayan ta horar da ita, babu kuma wata dabararta da zata dawo dashi.

"Kin tuna ranar dana fara ganinki?"
Muryarsa ta katse ta daga ramin tunanin data rufta, ta d'aga ido ta kalle shi hannunsa d'aya na rik'e da murfin booth d'in yana kokarin rufe shi, sai itama kwakwalwarta ta tuna da ranar, a can Washington sanda suka rako su da kaya ranar dawowarsu garin na farko.

Har ya sunkuyo da hannunsa ya karb'i ledojin data rik'o sannan ya wannan muryar tasa mai d'auke da maganad'isun data ratsa ko'ina a jikinta ta fara janta gare shi.

"Kusan shekara d'aya da rabi kenan yanzu, gashi zamu sake rabuwa a daidai jikin mota, don na san ba lallai ne gobe in ganki ba, Allah kad'ai ya san sai kuma yaushe k'addara zata sake had'a mu."
Baza ta tab'a bari yaga rauninta ba, saboda haka ta tsaida fuskarta sosai sannan ta d'anyi murmushi.

"Hakane, ina fatan Allah ya sake had'a mu cikin alkhairi."
"Ameeeen." Yaja kalmar wajen amsawa.

Kuma da kalmar da jan, da muryarsa dama wannan lokacin su suka dasa aya mai kauri kan shirmammiyar hanyar da take ganin ta fara nasara da ita wajen dawo da wannan damar da ta riga ta tankwabe a baya.

BAYAN NA MUTU!

AYSHA SHAFI'EE
Kwana nawa mutum ke d'auka ne wajen saita kwakwalwa da zuciyarsa ta dawo daidai game da wani abu daya rasa?

Watakila babu wani takaimaiman lokaci, ya danganta da iya yadda mutum ya d'auki wannan abun da muhimmanci kawai.

Shi yasa a kullum Fadeelah ta tashi da wannan nauyin zuciyar da kuma kumburin idon da ta fitar da kwalla d'aya ko biyu cikin dare, sai ta tsaya a gaban mudubi ta tambayi kanta sunan wanda take yaudara?

Don in ba yaudarar kai ba ta yaya za'a ce har tsawon sati biyu da tafiyar Al'ameen wai ta kasa cire damuwarsa akanta?

Farko,
banda kyautatawa tafi kowa sanin babu wani abu kuma daya faru tsakaninsu, na biyu ko a
rabuwarta dashi na farko bata damu kanta sosai haka ba, na uku, su kansu 'yan gidan dake da dangantakar jini dashi sun gama kewarsa sun shiga harkokinsu, sai ita karan kad'a miya kawai wadda ta riga ta gama shuka masa rashin kyautatawarta a can farko.

Ta jawo tawul daga cikin wata drawer da suke jera su ta fad'a band'aki a wata safiyar da ta gama irin wannan nazarin, ko Fatima data taimaka mata wajen 'yan dabarunta ta riga ta dad'e da gaya mata cewa tayi hakuri kawai Al'ameen babu abinda yake ji game da ita tunda har ya iya tsallake k'asar da tsawon sati biyu bai ko nemeta a waya ba.

Tayi wankan had'e da wanke gashinta sannan ta fito d'aure tawul d'in a jikinta da wani kuma k'arami akanta.

Safiya ce irin ta asabar da kowa ke gida sannan bata da lectures,
don haka bata damu da fita can falo da wuri ba ta shiga shirinta a tsanake, sanda take binciken neman wani man kwakwa a cikin kayanta ne hannunta ya d'ago wata 'yar mitsitsiyar purse a can k'asa da tayi ajiyar id card d'in ADAM a ciki.

Da sauri tasa yatsunta ta sake tura ta can cikin drawer sannan ta danne ta da wasu tarin littattafai, Tun lokacin da ta yarda zata biyewa Fatima su gwada sa'arta kan Al'ameen ne ta d'auki wannan matakin, ta tattara duk k'ok'arinta ta tura azababben tunanin Adam dake cinyeta a kullum can baya cikin kanta, tayi wa kanta nisa da duk abinda zai dinga tuna mata dashi don ta san cewa zuciyarta ba zata tab'a tsayawa waje d'aya ba in har zata cigaba da tunanin bad'ini akan zahirinta.

Ta yarda cewa Adam ya riga yayi mata nisan da bai kamata tayi ta tauye kanta tana k'arewa a tunaninsa ba, tunda hakan ba zai amfane ta da komai ba saima dakushe wasu abubuwan a rayuwarta, don Allah ya sani duk sanda take tunaninsa, wani irin abu ne ke tsagawa cikin b'argo da ruhinta ya kuma tab'o har cikin zuciyarta.

Ta rufe idonta a hankali tana jin makamancin hakan na shirin ratsata.

"Aunty deelah, wani irin wanka kika yi wai?

Tun d'azu nake shigowa baki fito ba."
Muryar Iman ta fad'a kuma ta katse ta sanda ta murd'o k'ofar d'akin ta shigo.

Ta juyo ta kalle ta.

"Har da wanke kai nayi, me ya faru?

Mami ta fita ne?" Don ta san ba zai wuce abinci take nema ba.

"A'ah bak'i akayi Mami tace in kira ki kizo gaishe su, 'yanuwan su ya Al'ameen ne kuma harda Daddynsu a ciki, baki ga kayayyakin daya kawo min ba daga Haneefa."
Sai idanunta suka zare a lokaci d'aya,
'yanuwan Al'ameen kuma?

Daga ina haka a safiyar da ko azahar bata k'arasa ba?

"Iman me suka zo yi?

Me ya faru?"
Da mamakin rashin fahinta itama ta tambayeta.

"Gaishe da Daddy fa suka zo yi, ko kina tunanin wani abu ne ya faru?"
Kafin ta amsa ta kara cewa.

"To ni dai naga suna ta fara'a, in ma mutuwa ce bana tunanin ita akayi."
Sai itama tambayar da tayi ta bata dariya, ta juya kawai ta cigaba da shirinta, Al'ameen d'anuwansu ne fa, me yasa don DANGINSA sun zo zata yi tunanin wani abin?

Sai dai me, bata je koina a shirin ba,
Mami ta bud'e kofar d'akin ta shigo fuskarta d'auke da wani abu kamar fara'a kamar kuma mamaki sannan ta sallami Iman kai tsaye daga d'akin ta samu gefen gado ta zauna.
Chapter 38 · 0% Book details