← Book details Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 95

Sashe 10

Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Tun ina shekara goma nake amfani da Hijaab a rayuwata kuma ban taba tunanin cewa sai a lokacin da girma ya same ni sannan zaizo ya zame min k'alubale ba."
"Kar ki fad'i haka Mami, komai zai wuce ba zai yiwu ace kowa ne ya d'auki ak'idarsu ba, za'a samu wanda zasu fahimta insha Allah."
"Har zuwa yaushe deelah?

Tambayar da nake yiwa kaina kenan kullum, naje interview masu yawan da Allah kad'ai ya san adadinsu, kuma inada tabbacin cewa ina da abinda suke so, amma a yanzu ba wanda yake son d'aukan mace mai hijaab, kamar shi d'in wani bomb ne da zai iya tarwatsa su."
"Mami ki gwada applying wani kamfanin a matsayin recruiter (Mai talla akan ayyuka) kinga kusan aikinsu gabad'aya a waya ne, kuma mutane suna kira ne da karamci tunda aiki suke nema baza suyi wani abin da bai dace ba, irin wannan aikin kuma kamar suna da religious minorities kamfanin baza su damu sosai ba."
Ta girgiza kanta ahankali.

"Haka ne tunaninki Fadeelah, amma a yanzu ko a bayan gini zaka yi aiki, sai ka bi tsarinsu."
Fadeelah ta ajiye bowl d'in hannunta akan dryer, zuciyarta ta tafi wani tunani ba tare da tace komai ba, Mami bata taba fad'a mata ba amma ita ta san dalilin da yasa ta damu sosai da samun aikin nan.

Ta tsinci hirarsu ne ita da Daddy a wata rana da daddare data fito kitchen d'aukan ruwa, kowa yayi bacci a lokacin sai su biyu a falon kuma sun kashe fitila saboda haka basu kula da ita ba.

Tattaunawa suke akan yadda albashin Daddy yayi musu kad'an wajen tafi da rayuwarsu, kud'in ruwa, kud'in wuta, kudin gida, kudin siyan kayan abinci da abubuwan yau da gobe, sannan mafi girman abun kuma kudin makarantar kowannensu da yake mai d'imbin yawa, a lokacin tana jin yadda suke soke abubuwa da yawa ana hak'ura dasu don a samu a fito da kud'in makarantar kawai.

"Ya akayi kike aikin ke kad'ai?

Ina Zahra?"
Mami data juyo a lokacin ta katse ta daga tunanin data tafi.

"Ta yanke hannunta da peeler ne, shine na k'arasa."
Sai ta girgiza kanta kawai tace.

"Ko kuma bata son yin aikin ba, ta yaya peeler ke yanke mutum."
Bayan ta gama goge kwanukan ta jera su a dryer, sannan tabi ta falo inda Daddy ke kallon news, su Zahra na daga can study suna homeworks d'insu itada Iman, Faruk kuma na kan dining yana danna wayarsa, ta wuce zuwa d'akinta zuciyarta d'auke da wani irin nauyi.

Shawarar data yanke tare dasu Melissa a kwana biyu da suka wuce ne ke tantama a ranta, sun yanke cewar baza ta tab'a kiran Adam da sunan lesson d'in Maths ba, don basa son kowacce irin alaqa ta had'a su dashi, kuma itama ta rantse in har ta hanyarsa zata iya sanin maths sai dai ta mutu a dak'ik'iya.

Toh amma meye amfanin rantsuwarta a yanzu? meye amfanin rantsuwar data san zata cutar dasu Mami ne, tunda suna iya bakin kokarinsu wajen ganin sun bata ilimin da bai zama dolensu akanta ba, ita kuma tana gefe tana shirin watsa musu k'asar kunya a ido koma abinda yafi hakan, tunda ya zasu ji a lokacin da aka gaya musu kud'in maimata aji zasu k'ara biya mata har na tsawon shekara daya?

Sai kawai ta kwanta akan gadon ta dukunkune jikinta, zuciyarta na gaya mata cewa kar ta sake ta soma bin shawarar da kwakwalwarta ke bata don baza su iya jurewa ba, ba zasu iya
jurewa mu'amala da mutumin da suka tsana ba, amma sai kwakwalwarta ta hasko mata ranar da za'a kafe sunanta b'aro-b'aro a jerin masu maimaita aji, watakila ma sunanta kad'ai za'a saka...

Toh taya zata iya kallon idanun Daddy a ranar? kuma ta yaya zata iya cigaba da sakewa da Mami tare da tambarin wannan laifin a fuskarta?

Sai tayi k'arfin hali ta mik'e ta jawo jakarta, a aljihun gefe ta rab'a paper da Mr.

Hawkins ya bata, wani waje da ba zai rik'eta sosai ba, amma duk da haka a lokacin sai da zuciyarta ya gaya mata cewar jakar ta k'ara nauyi.

A hankali ta zaro ta, idonta ya manne akan number da kuma sunan dake jiki, Sunan wanda zuciyarta ta tsana fiye da duk wata halitta mai numfashi a doron k'asa, sai gashi yanzu a cikin hankalinta tana shirin kai kanta gare shi, bisa dalilin data kira da sunan abinda yafi kaddara!

A hankali ta kwafe number cikin dial log na wayarta, sannan ta tsira mata ido kamar tana so ta tsince guda d'aya daga ciki ko hakan zaisa kiran ya tafi cikin wata lambar daban, kuma mai lambar ya amince shine mai koya matan.

Me su Romilda zasu ce in suka ji me take shirin yi? wane irin tunani zasu yi akanta?
zuciyarta ta rad'a mata amma sai kwakwalwarta ta goge hakan, Ba zata iya raunana fatan su Mami akanta ba.

Bayan kusan rabin awa cikin muhawara kwakwalwarta tayi nasara.

Hannunta yayi dialling number.

Sai dai kiran ba shiga ba ya katse, ta sake dannawa kusan sau uku amma ya dinga katsewa a hanya kafin ya kai ga shiga, watakila itama wayar tata bata goyon bayan wannan al'amarin ne.

Kiyi hakuri ba yadda zamu yi ne, ba zan iya b'ata ran su Mami ba.

Ta ayyana tana kallon screen d'in, kamar kuwa taji abinda tace wannan karon sai kiran ya shiga a take, kuma k'ararsa ya shiga bugawa tare dana zuciyarta, kamar a irin lokacin da dalibi ke kokarin binciko sakamakon jarabawarsa.

"Heelllooo..."
Tsigar jikinta ta mik'e yar! har zuwa tafin k'afarta, Muryarsa a lalace take kamar wanda ya amsa cikin bacci, ta kalli agogon gefen gadonta, karfe tara da rabi... ta yaya mutum zaiyi nisan bacci a wannan lokacin?

"Mhmmmm...."
Muryar ta sake fad'a a hankali jin anyi shiru, wannan karon sai da ta matsar da wayar kad'an don ji tayi kamar numfashinsa zai busa ne a cikin kunnenta.

"Naga kamar bacci kake yi, wani lokacin."
Ta daure ta fad'a sai dai bata sauke wayar k'asa ba.

"Nahh, ina jinki." Ya fad'a cikin wani lallausan turancin daya kwanta a sautinsa.

Taji kamar ta katse kiran kawai amma muryar Mr.

Hawkins ta amsa a cikin kanta.
...ina baki shawara gwara ku fara da wuri, don jarabawa na kan hanya.

Ta san in har bata yi maganar a sannan ba, zata k'ara b'ata lokacinta ne don a yanzu haka ma an shafe kusan kwana uku da Mr.

Hawkins ya mata maganar.

"Na tashi..." Muryarsa ta sake fad'a mata a hankali cikin speaker wayar kamar wanda bai gama wartsakewa ba, taji kamar taja tsaki amma sai wata zuciyar ta gargad'e ta.

Ba yanzu ya kamata ta fara kwance d'aurin data tanada ba.

"Sunana Fadeelah Malik."
Ta fad'a kuma tayi shiru shima yayi shiru, me yasa zata yi shiru kamar tana jira ne yace wani abu game da sunan.

"Nice wadda Mr.

Hawkins yace zamu.." Sai tayi saurin canja hakan.

"... zaka min lesson na Maths."
Shiru ya biyo baya sannan muyarsa ta sake
fitowa a hankali.

"Oh...

Yarinyar!." Ya
fad'a alamun kwakwalwarsa ta tuna masa.

"Na gane, zan kiraki gobe a makaran..."
Dib! ta kashe wayarta.Ta fahimci abinda yake nufi don haka bata ga amfanin sai ya kai k'arshe ba.

Ta wullar da wayar gefe sannan ta jawo jotter ta, zuciyarta cike da nauyi ta rubuta.

Alhamis, 9:36 pm.

Na karya alkawari, saboda sadaukarwa.

Ta mik'e ta shiga toilet, tayi alwala sannan tayi sallar Isha'i, tana idarwa ta nufi wajen alon zanenta, kusan wata guda kenan zanen dake kai bata k'arasa shi ba.

Zanen gida ne a cikin daji mai yawan bishiyu da shuke-shuken fulawoyi, a gabansa akwai wata fadama kwantacciya, zanen yayi kama da lokacin da akayi ruwa aka d'auke, Daga can gefe akwai wajen da babu komai, ta rasa a baya me tayi tunanin zanawa a wajen don yana da fad'i sosai amma ta kasa tunawa, sai kawai ta yanke shawarar zana dutse wanda zai zama kamar ana hango shi daga can nesa ne.

Ta d'auko pallette (Abin zuba kaloli) ta cakud'a Acrylic kalolinta akansa sannan ta d'auko sababbin brushes, tunda wanda tayi amfani dasu sun dad'e a bushewa bata wanke ba.

Ta saka siririn glasses d'inta sannan ta maida hankalinta kacokam! wajen zana hoton dake cikin kanta.

Zane, wani abu ne da ta tsinci hannunta nayi tun farkon sabuwar rayuwarta, bata da sanin cewa tayi shi a baya ne ko kuma taga ana ayin, ta san dai kawai ta samu hannunta da son zana taswirar abubuwa da yawa wanda take son fito dasu daga cikin kanta.

Dalilin da yasa Daddy ya kaita wata painting school ta tsawon wata biyu kenan kafin shigarta makaranta, kuma a yanzu haka ta sayar da zanenta guda uku wad'anda aka kai kantin Daddyn, Grocery store d'in da ya bud'e a gaba dasu kad'an.

"Nayi zaton kince fad'uwar rana zaki zana anan wajen."
Muryar Zahra ta fad'a tsaye daga step d'in k'ofar d'akin, a lokacin tayi kusan minti talatin tana zana rabin dutsen.

Ta juyo ta kalle ta sannan ta dawo da ganinta kan zanen, kuma hakane, faduwar rana shine yayi daidai a wajen tunda yanayin kamar na yamma ne.

"Wallahi na manta ne, bari in gyara."
"A'a ki barshi..

Dutsen ma yayi.

Kinga sai a kasa gane wane irin yanayi ne a wajen, yamma ko safiya?"
Da ta sake kallo kuma sai ta ga hakan ne, ta girgiza kanta da murmushi tace.

"Rana ta farko da kika fadi abu mai amfani."
"Ko kuma rana ta farko da kika bar zuciyarki ta fahimce ni ba."
Sai tayi murmushi kawai ta juya ta cigaba da zanenta.

"Da gaske kike?"
Romilda da Melissa suka had'a baki wajen fad'a, idanunsu a zare da tsantsar mamaki, Fadeelah ta damk'e rigarta ta baya yadda baza su gani ba.

"Da gaske nake, ba yadda zanyi bani da wani zab'i bayan hakan, ba zan iya b'ata ran su Mami ba."
Melissa tayi tagumi da duka hannayenta biyu sannan tace.

"Bayan duk k'okarin da muka yi don kar mu shiga hanyar mutanen nan, sai a yanzu da muke ko kike ganin kin kusa cimma hakan zaki b'ata komai?"
Romilda ta girgiza kanta, cikin turancinta mai cakud'e da spanish tace.
Chapter 10 · 0% Book details