← Book details Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 95

Sashe 14

Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta yaya za'ace don kawai yaga takardunta ne zai yanke hakan, shi kad'ai ransa? kuma har yana fad'in taje tayi shawara ta samo matsalarta, sai yanzu sosai ta fahimci rainin hankali k'arara a cikin zancen.

A baya tayi kokarin goge tunani irin nasu melissa a cikin kanta amma a yanzu kwakwalwarta ta fara gano ingancinsa, dole ne akwai wani dalilin da yasa ya kawo kansa cikin rayuwarta, akwai wata manufarsa daban da yake son cimma, kuma tayi wa kanta alkawari in har da ita yake tunanin amfani yayi koma me yayi niyya to sai dai su rasa damarsu su duka biyun!

Da haka ta k'arasa k'ofar gidan nasu, ta tsaya a barandar ta danna door bell dake gefe.

"Aunty deelah! kin san su waye suka zo?"
Iman ta fad'a da k'arfinta sanda ta wangale k'ofar.

"Su waye?" Ta tambaya sanda ta shigo ciki tana kokarin cire takalminta.

"Aunty Miryama dasu Haneey!

Kuma kin san me? wai sun dawo nan gabad'aya."
Gabanta ya fad'i a lokaci d'aya, ta juyo da sauri ta kalleta.

"Nan ina?"
"Nan garin mana, anjima ma zamu je muga sabon gidansu!

Dad'i nake ji sosai...

Haneey tace tana da games d'in su Moana da yawa kuma har da..."
Daga nan corridor d'in tana iya jiyo muryoyin mutane dake ta tashi daga falo, Aunty Miryamah 'yar uwar daddy ce ta dangin mahaifinsa dake zaune a garin Vegas ita da mijinta Balarabe da kuma 'yayansu guda uku duka mata.

Fatimah, Sa'ar Zahra guda d'aya, sai wadda ta girmi Iman Aysha da kuma sa'ar Iman d'in Haneefa.

A farkon zuwanta k'asar nan, lokacin Aunty Miryaman da 'ya'yanta sun zo hutu,
matsalar da ta fara samu daga wajenta ne, don ba irin fad'a da maganganun da bata yi ba, akan rik'e ta da Daddyn yace zaiyi, ta dinga ziga Mami Saffiyya da shawara kala-kala akan kar ta yarda da zamanta sai da Daddyn da kansa ya taka mata birki sannan tayi shiru.

Ta fahimci ita macece da bata tab'a son wani ya rab'e ta ita da 'ya'yanta, don duk shirin da suke da Mami Saffiya ma, su Zahra basu cika zuwa gidanta ba don ko sunje d'in ba wata kulawar kirki suke samu ba.

Ta k'arasa cikin falon jikinta a sanyaye sanda Mami Saffiya ke fad'in.

"Har kin dawo deelah, nayi zaton sai nan da awa d'aya."
Aunty Miryaman dake zaune a gefen Mami ta juyo jin hakan, tana sanye cikin doguwar riga bak'a ta abaya, ta had'e girar sama data k'asa kamar mai shirin lailayo zagi.

"Eh, Mami bamu fara ba tukunna sai jibi."
Ta fad'a muryarta a hankali sannan ta tsugunna har k'asa ta gaishe ta.

"Lafiya." Bakinta ya motsa kad'an ba tare da wani sauti ya fito ba, sai ta juya gefen Mami tace.

"Dama har yanzu wannan yarinyar tana nan? kinyi kokari wallahi Saffiya kinyi k'okari!"
A baiyane yake tun da bata tab'a b'oye kiyayyarta ko a gabanta ne kuwa.

Fadeelah na ganin yadda Mami ta d'anyi murmushi alamun bata ji dad'in hakan ba, sai ta mik'e da sauri tayi hanyar d'akinsu amma kafin ta isa kunnenta ya jiyo mata Aunty miryaman na fad'in.

"Kuma har yanzu tana fama da wannan ciwon haukan?"
Ta rufe k'ofar da sauri sanda kowannensu ya d'ago ya kalleta.

Zahra da sa'arta Fatima nata danne-danne cikin Ipad dinta yayin da Iman ke nunawa Haneey stickers d'inta na cartoons, d'ayar Aysha na daga can jikin zanenta tana kallo.

"Kin fara lesson d'in?" Zahra ta tambaya lokacin da Fatiman ta maida kanta kan abinda suke yi, ba tun yau ba ta fahimci dukka 'ya'yan halinsu d'aya da mahaifiyarta, Aysha ce kawai mai d'an saukin kai a cikinsu.

A baki su 'ya'yan musulmai ne, amma a d'abia da tarbiyya basu da banbanci da 'ya'yan turawa, akwai layi mai kauri tsakaninsu da 'ya'yan Mami.

"A'ah Zahra, sai jibi tukunna."
"Amma ko waye ya raina miki hankali wallahi, zaman da kika yi a banza kenan?"
Murmushi kawai tayi ba tare da tace komai ba, don a yanzu zancen Aunty Miryamah ya shafe na Adam a cikin kanta.

Ta ajiye kayanta sannan ta shiga band'aki tayi wanka, har ta shirya ba wanda ya kula ta a cikin 'ya'yan itama bata bi kansu ba ta saka doguwar riga mai k'aramin hannu sannan ta d'aure gashinta cikin bun.

Har zata fita a haka, ta tuna da Aunty Miryama saboda haka ta d'auko hijaabinta ta zura.

Sanda tazo wuce su ta falo, kanta na k'asa saboda haka bata ga irin banzan kallon da Aunty Miryaman tabi ta dashi ba.

Tana shiga kitchen ta cire hijaabin ta fara kokarin had'a tea don haka kawai taji bata sha'awar cin abinci.

"Fadeelah."
Mami ta kira sunanta sanda ta shigo kitchen d'in.

Da murmushinta ta juya ta kalle ta.

"Dan Allah kar ki saka zancen Miryamah a kanki ya dame ki, tun farko bata fahimce ki bane amma na tabbata tunda yanzu sun dawo kusa damu komai zai gyaru insha Allah."
"Insha Allah Aunty, ba komai." Ta fad'a da murmushi ba tare da ta tabbatar da abinda ta fad'a ba, don daga yanayin Aunty Miryamah bata tunanin ko tunda aka haife ta suke tare zata tab'a sonta.

A hakali ta juya ta cigaba da kokarin zuba sugar da take yi a cikin madara.

Sanda ruwan zafin dake cikin kettle ya tafasa take zubawa, lokacin taji motsi a bayanta, tayi zaton Mami ce saboda haka bata juya ba har ta gama had'a tean ta.

"Uhmm... ina kike ganin zan ajiye wannan?"
Da wani irin sauri ta juyo jin muryar namiji a bayanta.

Ai kuwa karaaf! idanunta suka shiga na cikin wani saurayi
daga bakin k'ofar kitchen d'in, yana tsaye hannayensa rik'e da manyan ledojin siyayya.

Kallo d'aya tayi masa idanunta suka gano mata wani irin tsantsaren kyau da kamala.

Fararen idanu tas! d'an siririn hanci a tsaye masu k'ananan k'ofofi na shak'ar iska kawai, gira mai kauri, dogwayen gashin idon da har inuwarsu ake gani akan fatarsa, d'an siririn leb'e dake tsakiyar wani kwantaccen saje... sai a lokacin kuma ta tuna irin rigar jikinta sai ta juya baya da sauri ta lalubo hijaabinta ta zura, kanta cike taf da mamakin WAYE SHI kuma me yake yi a tsakiyar kitchen d'insu.

Sai dai muryar Aysha data shigo a lokacin, ta amsa mata dukkan tambayoyin a cikin jimla d'aya.

"Ya Al'ameen kazo inji Mommy zamu tafi yanzu."
Sai k'afafunta suka k'ame cike da tsananin mamaki, wannan d'an Aunty Miryaamah ne?

Tayi zaton ai Fatima ce babbar 'yarta, ya akayi bata tab'a ganinshi ba?

Taji k'arar sanda ya ajiye ledojin akan counter kitchen d'in sannan muryarsa ta biyo baya, wata husky murya mai zurfi da kuma kwarjini, wadda ta fito da zallar matsayinsa na namiji.

"I'm sorry, kiyi hakuri na ganki a haka."
BAYAN NA MUTU!

AYSHA SHAFI'EE
Tana tsaye daga bayan wata had'addiyar mota hannayenta rike da ledojin siyayyar nan wad'anda ta rik'o bisa umarnin Mami a lokacin da suka rako su Aunty Miryaman dake shirin tafiya.

"Toh shikenan idan ya dawo zamu yi maganar dashi, kince ma kuna buk'atar wata motar ta kai yara makaranta ko?"
Mami ta fad'a sanda suke cigaba daga tattaunawarsu daga bayan motar nan, wadda a cikinta yaran Aunty Miryamah ne dasu Zahra da zasu je su gano sabon gidan da suka tare.

Yana zaune daga mazaunin direba, ya saita mudubin gefensa yana kallonta tsaye daga gefen su Mamin, headphone ne a kunnensa wanda k'arfensa na sama yabi ya nutse luf! cikin sumar gashin kansa irin ta jinsin larabawa, a karo na biyu data kai idonta cikin mudubin suka had'a ido sai ta koma bayan Mami a hankali ta kare kanta.

A cikin zuciyarsa, tunani ne fal! na son sanin ina Mami ta samo wannan 'yar kamilalliyar budurwar da kuma sanda tazo, tunda shi dai ya san ko a wajen 'yan k'annensa bai tab'a jin zancenta ba duk kuwa da yana yawan ji suna hirar su Zahra, ya k'ank'ance idonsa kad'an yana hango gefen fuskarta ta tsakanin fuskar Mamin data tsaya a bayanta, haka kurum yaji yana da interest na son sanin wacece ita.

"Goben idan kin shigo sai muje mu siyo curtains d'in."
Aunty Miryama ta fad'a sanda ta zagaya can gaba zata shiga motar, har Mami tayi gaba tabi baya
nta sai kuma ta juyo tace.

"Deelah wannan a booth za'a saka su...

Al'ameen bud'e mata booth d'in."
Aunty Miryama da bata kai ga shiga motar ba ta juyo tabi ledojin hannun Fadeelan da wani irin kallo, kamar tana shawarar fasa amfani da kayan ciki ne tunda hannayen wadda tak'i jini sun tab'a.

Har zata yi magana sai fitowar Al'ameen ta katse ta.

"Button d'in yak'i dannuwa daga nan, bari in gani..."
Ya rufe k'ofar motar, ya zagayo baya daidai inda take tsaye, yayi mata murmushi mai nuna alamun sannu sanda ya danna mukullin motar, booth d'in ya shiga d'agawa da kansa.

Bata ce komai ta shiga k'ok'arin had'a bakin ledojin don ta saka, sai ya sunkuyo da hannunsa k'asa ya karbi na hannu d'aya, muryarsa mai zurfi kamar maganad'isu ta ratsa cikin kowanne senses na jikinta.

"Ban tab'a ganinki a gidan nan ba...

Zan iya tambayar yaushe kika zo?"
K'amshin sassanyan turarensa ya busa a hancinta sai ta sakar masa ledojin cikin hannunsa ba tare da ta shirya ba, haka kurum taji ta takura a gabansa.

"Last year." Kwarjininsa yasa ta amsa hankali ba tare da ta d'ago da kanta ba.

"Fadeelan last year, ya akayi ba wanda ya tab'a fad'a min kinzo?"
Ta d'ago da kanta da sauri ta kalle shi jin ya ambaci sunanta, tunda take bata tab'a jin wanda ya fad'i harafan sunan daidai kuma yayi mata dad'i kamar shi ba, idanunta suka shiga cikin nasa farare tas! sai dai bata yi wani nisa ba muryar Aunty Miryama daga baya ta finciko ta.

"Baza ta iya sawa bane?"
A tsorace ta juyo ta kalli gaban motar,
Mami na amsa waya yayin da Aunty Miryaman ke tsaye a jikin k'ofar motar ta had'e girar sama data k'asa tana kallonsu, sai dai shi bai saurareta ba don sake sunkuyowa yayi ya karb'i na d'aya hannun nata ya saka a booth d'in.

Sai ta juya da sauri ta koma hanyar cikin gidan idanunta na kallon yadda tafin hannunta yayi ja saboda nauyin kayan.

"Mommy wacece ita?
Chapter 14 · 0% Book details