← Book details Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 95

Sashe 51

Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Magana d'aya yayi Al'ameen ya fahimci daga can wajen da suke neman license ne, don haka ya juyo ya kalle shi sanda ya ajiye kiran.

"Meye?" Kamaal ya tambaya.

"Dan Allah kar ka raina min hankali Kamaal, just say it!"
Sai yayi murmushi kawai sannan ya juya fuskarsa ya mayar titi.

"An samu license d'in Al'ameen, daga yanzu zaka iya shiga kowacce kotu a Nigeria ka kare Fadeelah."
Maimakon yaji farinciki kamar yadda ya dad'e yana zumud'in hakan, sai yaji yawu ya wuce kwat! cikin mak'ogwaronsa.

Ya juyar da kansa a hankali ya mayar kan tagar gefensa, me ya same shi ne wai yau?

Meke shirin faruwa dashi.

"Al'ameen." Kamal ya kira sunansa da muryar dake nuna mamaki.

"Muyi sauri Kamal, tunda mun samu license d'in ya kamata in had'u da lawyer wad'ancan 'yanuwan nata, Daddy yace jiya ma sun shiga asibitin nama nan."
Daga haka bai k'ara cewa komai ba, kuma akayi sa'a Kamaal din ma bai sake magana ba wanda hakan yayi masa dad'i don ya fi so a barshi da hargitsin cikin kansa kawai.

Sai dai hakan bai d'ore ba, don wayarsa dake kan cinyarsa ce ta shiga k'ara tana nuna wata sabuwar number ce ta k'asar waje, bai yi tunani sau biyu ba yasa hannu ya danna button d'in amsawa.

Magana d'aya ya gane mai maganar, wani kawunsa ne d'anuwan Maminsa, ma'ana daga dangin su Daddy na can washington kenan, ya gaishe shi cikin girmamawa da kuma taraddadin abinda zai biyo baya.

"Al'ameen tun jiya Maminka nata kira baka d'auka ba.

Lafiya dai koh?"
Wane zab'i yake dashi banda k'arya?

Saboda haka kai tsaye yace.

"Bana kusa ne amma insha Allah zan kira ta yanzun nan."
"A'ah kar ka kira ta ma, don baza ta iya d'auka ba.

Dama mahaifinka ne yake ta rashin lafiya tun jiyan aka kaishi asibiti, yau da safe kuma Allah yayi masa rasuwa, sai dai hakuri Al'ameen mu kuma bishi da Addu'a, ka nemi koda jirgin yawo ne in zai samu ka taho a yau, don gobe za'ayi jana'izarsa."
Sau d'aya kawai zuciyarsa ta buga amma ya tabbata Kamaal dake gefensa yaji k'ararta har cikin kunnuwansa!

Habiba ta tafi neman halaka Bintu.

Fadeelah ta shirya tunkarar k'alubalen dake jiranta a Ikara.

Adam zai koma lauyan Bintun da bai gani ba har yanzu?"
Ga license ga kuma rasuwar Mahaifinsa, wanne Al'ameen zai dauka?

BAYAN NA MUTU!

AYSHA SHAFI'EE*
*27*
Daddyna mutum ne mai sauk'in kai Fadeelah, bashi da hayaniya ko kad'an sannan bashi da matsala a komai, wad'annan halayen nasa su suka sa Mami ta samu damar juya gidanmu baki d'aya, amma yanzu girma yazo masa kuma ya dawo gida, don haka abubuwa zasu canja deelah, baki da fargabar komai insha Allah.

Ta tsamo wannan maganar a cikin kanta ne daga d'imbin lokutan da Al'ameen yayi mata maganar mahaifinsa kuma d'aidaiku da zancen ya had'o dana mahaifiyarsa, Bata tab'a ganinsa a zahiri ba amma yasha turo mata hotunansa da kuma nasu tare wanda saboda yawansu har tana ganin ma kamar ta san shi a gasken ne...

Ya Allah!

Bata san yaya Al'ameen yake ji a yanzu ba, ya rasa mahaifinsa, ya rasa Uba a lokacin da ya d'auki fata da yawa na cigaban rayuwarsa ya d'ora a kansa, ya rasa wani jigo na rayuwa dake d'aga darajar mutum a duniya.

Ta san irin wannan yanayin, don a yanzu da kwakwalwarta ta dawo daidai, ta san cewa a baya ta shige shi na sau d'aya ba, ba kuma sau biyu ba.

"Eh, Daddy ma ya biyo jirgin safe d'azun nan."
Muryar Mami Saffiya ta fad'a cikin wayar da take yi da wata 'yaruwarsu Daddyn dake can washington.

"Anyi jana'izar ne?" Ta sake tambaya cikin wayar.

Kafin Fadeelah ta fahimci amsar da aka bata, hannun Aunty Hadiza ya kamo nata a hankali.

"Deelah, yaya kike jin jikin naki?"
Idanunta na k'asa, don bata fiye son yawan d'ago kanta da take jin kamar bulo guda aka jingine akansa ba tace.

"Aunty da sauk'i, babu ciwon yanzu sai dai kawai nauyin da kan yake min."
"Allah ya sawwake, insha Allah shima zai daina kwanan nan...

Ki ajiye duk wata damuwa a ranki kinji?

An riga an samu lauyan da zai kare ki, sun yi magana da Daddyn jiya kafin tafiyarsa, watak'ila yanzu kafin a sallame ki ma ya shigo."
Ba tace komai ba, tayi shiru kawai tana k'ifta idanunta, tunda ta farka a daren jiya, ta fahimci hankalinsu Mami gabad'aya a tashe yake kuma suna cike da mutuk'ar tausayinta, basu san cewa ita kuma su take tausayi a yanzu ba, yadda ta d'ora musu tulin d'awaniyarta a baya alhali babu hakkinsu a kanta, sannan a yanzu kuma tana shirin sawa su fuskanci abinda ko a cikin danginsu bai tab'a faruwa ba sai akanta...

Ita baren da ta shigo cikinsu.

Ta rasa sai zuwa yaushe hargitsin rayuwarta zai barsu su huta.

Ganin bata da niyyar magana yasa Aunty Hadiza ta saki hannunta sannan ta matsa wajen Mami da ta gama wayar.

"Kunyi magana da Baba Habibu?" Ta tambayeta cikin sauti k'asa-k'asa amma duk da haka ta ji ta.

Mami ta d'auke wata guntuwar kwalla da yatsanta d'aya sannan ta amsa.

"Na kira shi d'azu yaya amma yace ba zai sami damar zuwa ba."
Maganar tasa Fadeelah ta dago da kanta da kyar ta kalle ta, saboda haka ne har take hawaye?

Toh fisabilillahi meye laifin Baba Habibu anan?

Bashi da wata alak'a da ita don me zai kashe ayyukansa ya bisu Zariya akan shari'arta?

Ba tun yau ba tasha fahimtar ba'a kullum ne ake samun mutane masu zama da mutum zuciya d'aya irin Mami ba, saboda duba alak'ar fa...

'Yar tsintuwa daga dangin miji zata dinga nunawa kulawa haka?

"...

Amma yace yayi magana da wani abokinsa an sama mana gidan da zamu zauna a can din, ya bawa Abdullahi numbersa idan munje zai karbo mukullin."
"To ai ba wani abu bane Safiyya tunda da Abdullahi ma, sannan gashi d'anuwan nata na can ya samo mata lauya insha Allah ina ganin bamu da matsala, tunda shima Daddyn ba zai fi kwana uku ba ai na san."
A duk maganar Aunty Hadiza, abu daya ne ya dauki hankalin Fadeelah, '... d'anuwan nata na can daya samo mata lauya...' Tunaninta ya k'ulle a lokaci d'aya, waye d'anuwanta a Ikara da zai sama mata lauya, dama har akwai wani sauran mai jin k'anta a Babban gida?

Kafin ta samu wad'annan amsoshin Mami ta k'araso gare ta, ta zauna a kujerar gefe sannan ta rik'o hannunta d'aya kamar yadda Aunty Hadiza tayi.

"Ya kike ji yanzu?" Muryarta na nuna tsantsar kulawa.

"Da sauki Mami, babu wani ciwo."
Ta gyad'a kanta sannan tace.

"Yaya Hadiza ta tafi kiran Nurse a cire miki allurar."
Sai a sannan ta d'aga kanta taga ledar jinin da ake k'ara mata saura kad'an a ciki, kowanne lokaci daga yanzu, inya k'are nata jinin ne zai fara tafiya cikin ledar.

"Al'ameen yaso ganinki kafin ta tafi deelah, babu yadda ya iya ne amma wallahi yayi iya kokarinsa a cikin kwanaki hud'un nan, har license sai da ya samu na shiga kotu yace zai karb'i shariar taki, wallahi ya damu sosai, dalilin da yasa ya dakatar da d'aurin auren kenan, yace kowacce mace na farin ciki ranar aurenta, bai zai so ke kuma ace ba kya cikin haiyacinki ba a ranar.

"Allah ne bai nufa ba kawai Allah ne bai nufi komai kamar yadda muka tsara ba, wallahi abinda suke zargina k'arya ne Mami, ban kashe kowa ba, ban tab'a..."
"Shhhhhh." Mamin tayi saurin katse ta.

"Kar ki sake fad'a min haka Fadeelah, na san baza kiyi kisan nan ba, kuma na san baki yi ba don haka mu rufe babin nan, mu fuskanci abinda ke gabanmu shine yadda za'a tabbatar da hakan a gaban shari'a.

Zaki iya tunawa a cikin 'yan uwan mahaifinki akwai wani..."
Wani wa?

Zuciyarta tayi hanzarin tambaya sanda maganar Mamin ta katse, sai dai itama tana d'ago da kanta tata tambayar ta katse sakamakon bud'e k'ofar d'akin da akayi.

Taji kamar an saka adda an sara tsakiyar kanta mai nauyi a lokaci guda, don babu wani makari tayi IDO DA IDO da mutanen Ikara, mutanen da tsawon shekaru suka shafe a cikin tunani da kwakwalwarta, sai a yanzu cikin sati d'aya kawai komai ya baiyana, komai d'in dake barazanar tarwatsa rayuwarta ta biyu.

Kawu Yahya ne a farko, mutumin da a baya zuciyarta ta riga ta manna masa wani tambari da ba zai tab'a rabuwa da siffarsa ba.

"Allah ya yiwa yaya Bukar rasuwa Saratu, Babu yadda muka iya sai hak'uri, yanzu aka shiga da gawarsa Babban gida...

Wannan ranar, wannan ranar da yazo da labarin rasuwar mahaifinta tsaye daga k'ofar d'akin Inna Saratu, wata rana ce da ba zata tab'a gogewa cikin idanunta ba.

Bayan shi, Kawu Sulaiman ne ya shigo wanda shima ba baya bane tun a da wajen nunawa Innarta kiyaiyarsa.

Fadeelah taji dad'in yadda Mami tayi shiru bata gaishe dasu ba don ba Mamin kad'ai ba idan har itama suna tunanin samun gaisuwarta ne to zasu dauwama inda suke ne.

"Sannunku." Kawu yahya yaga damar yanke shirun.

"Yauwa sannu." Mami ta amsa a hankali.

"Ke." Muryarsa da kauri ta biyo baya, Fadeelah ta d'ago a hankali ta sake kallonsa don ta san da ita yake.

"Kin gane mu?" Ya tambaya.

Sai ta gyad'a kanta ba tare da ta d'auke idanunta daga cikin nasa ba.

"Na gane ku Kawu Yahya Barka da zuwa."
Bai amsa ba sai ya kalli Kawu Sulaiman yace.

"Ai ni na san k'arya ne ace wai ta manta komai, kuma ita k'arya dama ai ba'a yinta kusa da gida ma balle a gidan..."
Ya dawo idonsa gare ta.

"...

Bama zanyi mamaki ba da kin nuna baki sanmu ba, wadda ta tsallake gida tabi duniya meye ba zata aikata ba.

Kinga nan..." Ya d'ago wata takarda a hannunsa.

"Sallamarki ce don haka ki shirya komawa tushenki a yau ki girbi abinda kika shuka, insha Allahu yau sai kwanan kotun da za'a bi mana hakkin mahaifiyar mu a cikinta."
Kai tsaye tace.
Chapter 51 · 0% Book details