← Book details Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 95

Sashe 56

Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ya mai shari'a, Bintu bata aikata laifin nan ba, bata kashe kakakarta ba kuma ba kuma bata tab'a samun ra'ayin kashe ta ba, wasu sunyi amfani da damarsu akanta ne sun isar da niyyarsu ta kashe kakar tata, wanda a gaba cikin wannan shari'ar zan fito da hakan insha Allah, saboda haka da muryar adalci nake kira da kar kotu tayi saurin yanke hukunci ga yarinyar da bata da laifin komai."
D'an wannan tak'aitaccen bayanin ya gamsar da Alkalin wanda har haka yasa ya gyad'a kansa sau d'aya sannan ya juya ga Kutama.

"Masu shigar da k'ara zasu cigaba?'
"Kwarai ya mai girma mai shari'a kamar yadda na fad'a a baya, akwai tarin hujjojin da zai sa kowanenmu ya yarda cewa wannan yarinyar dake zaune fuskarta na nuna kammani irin na salihan mutane, kwararriyar mai kisa ce ..."
"K'orafi ya mai shari'a."
Muryar Adam ta katse bayanin kutama.

Alkali ya gyad'a kansa.

"K'orafinka ya karb'u, bai kamata mai zargi ya tabbatar da abinda shari'a bata yanke hukunci akansa ba."
Kutama ya duk'a kansa kad'an sannan yace.

"Ina sanar da kotu cewa akwai hujoji na mutane da kuma abubuwa wanda zasu tabbatar da zargina, amma kafin in fara kawo komai, ina son kotu ta fara da mutanen da kisan ya faru a kewayensu don muji ta bakinsu."
Alkali ya gyad'a kai yana kallonsa.

"Zanso in kira shaida ta farko, Sadiya Muhammad wadda k'anwa ce ga mahaifin ita Bintun da ake zargi da kisan."
Daga cikin masu saurare, Sadiya ta mik'e ta taho wajen tsayuwar masu shaida.

Magatakarda yace.

"Ki fad'i sunanki kuma ki fad'i kowacce kalma dalla-dalla don za'a rubuta."
Cikin muryar dake shaida zumud'i Sadiya tace.

"Sunans Sadiya Muhammad, k'anwa ga mahaifin Bintu marigayi.

S-a-d-i-y-a M-u-h-a-m-m-a-d.

Kotun ta d'auki shiru a lokacin da ake rantsar da Sadiyan kafin ta k'araso ta tsaya.

"Sadiya ina son ki shaidawa kotu kina da aure ko baki dashi?" Kutama ya fad'a tsaye a gabanta.

"Bani da aure a halin yanzu, amma a baya nayi aure sau biyu na fito."
"A shekarun baya, lokacin da Bintu take tare da Hajiya kina gidan ko bakya nan."
"Ina gidan don ba'a fi shekara da mutuwar aure na ba a sannan."
"Hakan na nufin kin san irin alak'ar dake tsakanin Hajiya da Bintu kenan?"
"Kwarai na sani."
"Zaki iya fada mana wani abun?"
"Tun tasowar Bintu dama bata son Hajiyar mu, bisa tarbiyar da mahaifiyarta ta d'ora ta akai na k'in mu dangin ubanta saboda mun nuna cewa bata da asali sanda aka tashi auro ta, don hakan ko bayan da iyayenta suka mutu rik'onta ya dawo wajen Hajiyar da wannan akidar ta taho a ranta, kuma aka sami akasi Hajiya bata maida ita makarantar bokon da take zuwa ba saboda BABU ta yau da kullum.

Sai wannan abun ma ya k'ara d'arsa tsanar hajiyar a zuciyarta, shi yasa mamakina kad'an ne lokacin da aka ce ta kashe Hajiyar tunda tun a baya dama ba wata cikakkiyar tarbiyya ce da ita ba."
Fadeelah na daga can gefe idanunta kyam akan Sadiya, tana sauraren yadda take had'a karya da gaskiya waje guda tana tada wani sabon labari.

"Ta wace hanya kuke zargin ta kashe Hajiyar?"
Sadiya ta girgiza kanta.

"Ba zargi muke ba ai ranka ya dad'e, a cikin damun kokonta ta saka mata guba, tunda kowa ya san cewa tunda ta dawo gidan nan itace mai dama mata koko a kowacce safiya."
Kutama ya gyad'a kansa da murmushi yace.

"Kotu ta gode da wannan gudunmawar taki kwarai malama Sadiya."
Sai ya juya b'angaren Adam yace dashi.

"Your witness.."
Adam ya d'anyi shiru idanunsa na nazarin Sadiya daga inda yake kamar zai taso sai kuma ya girgiza kansa yace.

"Bani da tambaya akanta."
Hakan ya bawa kowa mamaki, Alkali ya kalle shi yace
"Baka da tambaya Barrister Adam?"
Ya sake girgiza kansa yace "Babu ya mai shari'a."
Da wani irin murmushi na k'eta kutama ya juya yace.

"Ina so kotu ta bani dama in gabatar da shaidata ta biyu ya mai shari'a."
"Kotu ta baka dama."
Kutama ya juya baya yace.

"Zan so in kira Sule wanda yake d'a ga wan Mahaifin Bintu."
Sule ya mik'e daga cikin mutane ya k'araso gaba, ya fad'i sunansa aka rantsar dashi sannan ya k'araso gaban Kutama.

"Sule, me zaka iya shaidawa kotu game da rasuwar Hajiya?"
Sule ya gyara tsayuwarsa sannan yace.

"A safiyar da Hajiya zata mutu ni ta bawa sak'o cewa in gayawa Bintu ta kai mata kokonta, kuma bayan ta had'a ta kai mata har gubar tayi aiki a jikinta, mu muka fara shiga d'akin dani dasu Salisu, sannan mu muka d'auke ta muka kaita har asibiti inda aka shaida mana cewa guba taci mai k'arfin gaske tayi sanadiyar mutuwar tata."
"Sule, a lokacin da kaje gayawa Bintu ta had'a kokon Hajiya me take yi?"
"Wankin kayanta take yi, kuma wankin ma da kyar ta karbe shi a ranar don har saida nasa baki sannan ta d'iba."
"A baya dama haka take yi?"
Sule ya girgiza kansa.

"Ko kad'an, ana bata zata tashi tayi."
Zuciyar Adam ta tabbatar masa da wani tunani a lokacin.

"Hakan na nufin a ranar bata yi niyyar wankin bane saboda ta riga ta shirya..."
"K'orafi ya mai shari'a." Muryar Adam ta katse kutama.

"Mai zargi yana kokarin bawa mai shaida sabon ra'ayi."
'K'orafi ya karb'u, lauya ya kiyaye."
Kutama ya sunkuyar da kansa sannan ya koma ga Sule.

"Sule a lokacin da kuka shiga d'akin, Bintu tana ciki?"
"Kwarai tana ciki don a gaban gawar ma muka same ta kuma idonta babu alamun tashin hankali balle hawaye."
Sai a lokacin da Sule ya fad'i haka ne sannan Fadeelah ta fahimci ma'anar kalaman Adam na d'azu.
...kar ki bari duk abinda zaki ji daga bakin mutane ya raunana fatanki na samun nasara, baki da laifi don haka insha Allah zaki kub'uta."
Kutama ya juya ga Alk'ali.

"Ina fatan kotu ta fahimci abinda hakan ke nufi, Bintu bata tab'a tunanin cewa wani zai shigo kafin ta tabbatar da mutuwar Hajiya har taje ta fad'a ba, shi yasa suka same ta a wannan yanayin na rashin alhini."
Ya juya ga Salisu yayi masa godiya sannan ya juyo ya kalli Adam yace.

"Your witness..."
A karo na biyu, Adam ya girgiza kansa sannan yace.

"Bani da tambaya akansa."
"Yayi kyau Barrister Adam, Dama gaskiya d'aya ce kuma a koina ba'a iya kalubalantarta."
Wannan maganar tasa kotun ta rud'e da hayaniya jama'a, Kutama ya jira har akasa surutun ya sassauta sannan ya kira shaidansa na gaba.

Habiba.

Da kyar ta taso tana dogara sandanta aka rantsar da ita sannan ta tsaya.

"Hajiya Habiba, zaki iya gaya mana meye matsayinki a Babban gida?"
"Na'am?" Muryarta ta amsa a cikin kotun, Kutama ya sake maimaita mata tambayar a hankali.

"Ni matar wan mahaifinta ce."
"Ance mahaifin nata yana da yayye da yawa harda wanda ba uwa d'aya suke ba, shi wanda kike aure yaya alak'arsu take da mahaifin nata?"
"Uwarsu d'aya, shine d'a na biyu a wajen marigayiyar."
Ya gyad'a kansa alamun fahimta.

"Habiba kina a ina safiyar da Hajiya ta rasu?"
"Ina b'angarena ban ma fito da wuri ba sakamakon d'ana k'arami bashi da lafiya a lokacin, sai daga can naji hayaniya na lek'a aka ce dani wai Hajiya ce ta rasu."
"Me kika yi bayan nan?"
"Na tafi can b'angaren Hajiyar inda akace Bintun na can kuma ita ta saka mata guba a kokon data sha."
"Ance a ranar Bintu ta zarge ki da cewar ke kika had'a kokon ba ita ba."
"Wallahi k'arya take min ranka ya dad'e, na gaya maka ma ni ban ma fito da wuri a ranar ba kuma..."
"Kwantar da hankalinki Habiba, ai kowa anan yasa k'arya take miki, so nake kiyi tunani ki gaya mana shin akwai wani abu daya tab'a had'aku ne da har kike ganin zata iya dora miki wannan laifin."
"Eh ranka ya dade kowa ya san Bintu yarinya ce mai rashin kunya, to ni kuma a lokuta da yawa ina yawan kwab'arta akan hakan, kamar yadda dai marigayiya take k'okarin nusar da ita abubuwa a kullum, watakila saboda haka ne bayan ta kashe hajiyan, ni kuma ta nemi d'ora min wannan laifin."
Kutama ya gyada kansa.

"Na fahimta, bayan haknan akwai wani abu da zaki iya k'ara mana game da abinda kika sani?"
Habiba ta girgiza kanta da sauri.

"Allah ya sani ranka ya dad'e, ni ban fiye shiga harkar mutane ba, kowa zai min shaidar hakan, saboda haka ba zan iya cewa komai game da ita ba."
"Na fahimce ki Malama Habiba, na kuma fahimci irin abinda kike ji a yanzu, sharri bashi da dad'i musamman k'azafi irin wannan na kisa.

Kotu ta gode sosai da wannan gudunmawar taki."
Ya juya ya kalli Adam.

"Your witness..."
Ga mamakin kowa sai ya mik'e a hankali ya karaso gaban Habiban da zuciyarta ke dukan casa'in- casa'in kamar ta na shirin fasowa daga kirjin nata ne a kowanne lokaci.

"Habiba.."
Yadda ya kira sunanta da wannan malalaciyar muryar tasa yasa wani abu ya tsarga mata har k'asa, taji tana k'okarin sakin fitsari a tsayen da take.

"A yadda rahoton yake babu wanda ya san Hajiya ta rasu har sai da aka kaita asibiti, ta yaya ke daga jin hayaniya kika lek'o akace miki Hajiya ce ta rasu?

Sannan waye ya gaya miki?"
Habiba ta tsure ta rasa me zata ce, don ita har ga Allah ta manta ma ta fad'i hakan, to zancen da ba gaskiya ba.

Kotun tayi shiru, kowa ya tsira mata ido jiran amsa, ganin haka yasa kutama ya mik'e da sauri.

"K'orafi ya mai shari'a, Lauya na k'okarin tursasa...

"K'orafi bai karb'u ba."
Alkali ya katse shi tun kafin ma ya k'arasa, sai ya koma ya zauna zuciyarsa cike da haushi.

Adam ya lumshe idonsa akan Habiba sannan ya sake cewa.

"Ya akayi kika san Hajiya har ta riga ta rasu a lokacin bayan ba wanda ya fad'a miki ma dalilin mutuwar, sannan waya ya shaida miki cewa ta rasun?"
Habiba bata da mafita sai wata k'aryar saboda haka ta hadiye wani tarin yawu a bakinta sannan tace.
Chapter 56 · 0% Book details