Sashe 82
Bayan Na Mutu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sanda take raka Mairo bayan gari ta had'u dashi, da sanda Mairo bata fahimtar komai in ba kalamansa ba... ta gane shi sarai da sunan mutumin daya zama farkon hargitsa rayuwarsu.
Daga cikin sauran k'ofofin motar da suka bud'e, mata uku da maza biyu suka fito, a hannun d'aya daga cikin matan wani abu ne daya zuk'e duk fushin dake shirin tasiri a zuciyarta, wani d'an farin yaro tas! da kammaninsa ke baiyana cewa jinin Mairo ne sannan rik'e a hannun d'aya daga cikin mazan, yarinyar da bata wuce shekaru biyar ba sanye cikin wasu milk kaya masu kyau!
Fadeelah taji kwalla ta cika idanunta a take, taji dama tana da iko da lokaci a sannan, da ta dawo da rayuwar baya lokacin da innarsu ke raye, ta hasko mata wannan lokacin don taga 'ya'yan Mairo, 'ya'yan da rabo ya rantse akansu ya zama dole ta tsallake mahaifarta a wancan lokacin don su zo duniya, sai kawai ta k'arasa gurin matar dake rik'e da Muhammad ta karb'e shi.
Mairo tayi zaman dirshan kan gadon Aunty Hassanah tana sak'e-sake a ranta, ta san cewa a wata guda daya wuce zuciyarta ta yanke mata cewa bata damu da mijinta ba, ta d'auki kudirin yanke duk wata alak'a dake tsakaninsu ta kuma yi alk'awarin cewa zata yi nesa da duk wani abu daya dangance shi, amma ganinsa kawai da tayi yanzu ya tuna mata da cewa Sadiq ne fa!
Wannan Sadiq d'in da taso fiye da komai a rayuwarta, d'an bafulatanin nan da tun gani na farko da tayi masa a bakin rijiyar da suke zuwa d'ebo ruwa taji zuciyarta ta fad'a duniyarsa...
Ta rufe idanunta
a hankali tana tuna banbancin yadda ta barshi da yadda yake a yanzu, kammaninsa sak! suke dana mutumin da yayi nesa da kwanciyar hankali.
Ya tara gemu har da gashin baki, gashin kansa babu taza sannan daga takalmi har hular kansa basu dace da dogwayen kayan daya sanya ba...
A baiyane yake cewa rashinta ya tab'a shi ta kowanne b'angare don kammanin fuskarsa ma kad'ai sunfi kama dana mara lafiya.
Sai dai duk da haka, ta san ko kad'an halin da yake ciki bai kamo k'afar irin halin da ita ya sakata a ciki ba.
Sallamar Mairo ta katse tunaninta, tana d'ago ido kuwa zuciyarta dake da rauni ta sake karyewa ganin Muhammad rik'e a hannunta, shima ya rame kad'an sannan yayi d'an wuya.
"Afrah tana wajen sauran, gasu nan sun shigo falo."
Fadeelah ta fad'a tana k'ok'arin mik'a mata Muhammad d'in, sai dai me yana had'a ido da ita ya juya kansa sanann ya fara kuka alamun ba zai je ba.
"Kaga fa, mominka ce." Cewar Fadeelah, amma maimakon ya fahimce hakan sai ma k'ara tsallara kukan da yayi ya shiga zillewa yana k'ara k'ank'ame jikin Fadeelan, sai kawai itama ta juyar da kanta gefe ta fara hawaye, dama ta sani cewa alhakin Muhammad ba zai barta ba, ta yakice shi daga jikinta a sanda lokacinsa bai kai ba, don haka dole ne yayi zuciya da ita.
Tayi saurin goge hawayenta sanda Aunty Saratu tayi sallama, biye da ita Zakkiyya ce da k'annen mahaifiyarsu su biyu, ta zamo daga kan gadon sanda su suka zauna akai.
Afrah na ganinta kuwa ta janye hannunta daga cikin na Zakkiya ta fad'a jikinta tana fad'in.
"Mommy Oyoyo, mommy oyoyo!"
Karo na farko tun bayan rabuwarta dasu itama ta rungume 'yarta sannan ta cusa kanta cikin wuyanta ta shiga gaishe su.
"Lafiya k'alau Maryam, ya hakuri kuma?" Suka had'a baki wajen amsa mata.
"Alhamdulilah." Muryarta ta fito a hankali.
Aunty Saratu ta nuna Fadeelah tace.
"Ga k'anwarta nan, wadda aka sallama daga kotu."
Mairo tayi shiru tana saurarar rad'ar da Afrah ke mata yayin da suke barka da kuma yiwa Fadeelah jaje.
"Mommy kullum sai nace Daddy ya kawo ni wajenki amma sai yayi tace min sai gobe, kuma nace masa ya yanke farcensa yace wai bai iya ba sai kin dawo zaki yanke masa."
Tayi kokarin maida kwallarta sanda yarinyar ke tambaya.
"Momy yaushe zaki dawo?
Zaki dawo?"
Har kusan yamma Muhammad bai yarda yazo wajenta ba, harkarsa kawai yake kuma duk wanda zai d'auke shi zai yarda amma banda ita, zuciyarta duk tabi ta cunkushe sannan Aunty Hassanah kuma tayi ta binta da kallon 'Me na gaya miki?'
Sauk'in da ta samu d'aya ne da su Zakkiyan suka tashi tafiya anan suka barsu da yake dama da kayansu aka zo, kuma kamar lokutan baya Sadiq bai nemi ganinta ba haka su Aunty Rabi ma basu yi mata zancensa ba, gaisuwar da suka zo don ita kawai suka yi suka tafi.
Afrah na mak'ale da ita duk inda tayi, amma Muhammad a wajen Aunty Hassanah ya kwana don daga baya Fadeelah ma k'in yarda da ita yayi, watakila ya gano kammanin ta da mahaifiyar data wullar dashi ne.
Washegari Juma'a Saminu yazo mata da wani labari bakinsa a washe kamar gonar auduga, cewar a jiya Kawu Ibrahim yayi magana da Sadiq har kuma yace dashi yazo wani satin ranar laraba tare iyayensa.
Mami bata gaya musu ranar da Kawu Ibrahim yace suma su zo ba, amma bayan ta shaidawa Fadeelah, sai dukkaninsu suka yarda cewa rana d'aya ne da sanda su Sadiq zasu zo.
Zatonsu ya kara tabbata ne da daddare lokacin da Aunty Hassanah ta dawo daga b'angaren iyayen Said, tace dasu mahaifiyar Said d'in tayi waya dashi yace mata da jibi zasu zo amma Kawu Ibrahim yace su zauna jikin Adam ya k'ara warwarewa tukunna ranar laraba sai su zo.
Haka kowannensu ya kwana a ranar da tunanin wane irin taro za'ayi RANAR LARABA?
LARABA, TA BAWA RANAR SA'A!
Adam ya gyara zamansa kad'an ya jawo hannun rigar Said dake gefensa, sannan ya mik'a wuyansa saitin fuskarsa yace.
"Nawa ka ciro a Atm d'in?"
"Dubu d'ari kamar yadda kace, wai kud'in meye?"
"Ban sani ba, jiya ne ya kira ni a waya yace in taho da 50k."
Har Said zai sake magana magana k'ofar falon ta Kawu D'anjuma ta bud'e, mata suka fara shigowa d'aya bayan d'aya suna zama a d'aya b'angare na d'akin, idan har Adam zai iya rik'ewa to a b'angaren da suke zaune, kusan duk wani namiji babba daya mallaki hankalinsa a Babban gida yana wajen.
Bai rayu tare dasu ba amma zai iya tabbatar da cewar ba'a tab'a irin wannan zaman daya had'a da kowa da kowa a gidan ba har kuwa da mata.
Kawu Ibrahim ya riga ya gaya masa cewa zama za'ayi na gidan gabad'aya saboda haka tun da suka taho a hanya daman ya shirya samun hayaniyar mutane, ilai kuwa abinda ya tarar kenan, da wad'anda suka je duba shi asibiti dama wad'anda basu sami damar zuwa ba haka suka yanyameshi kowa na fad'in yaya ya k'ara ji da kuma fad'in cewa ya rame.
Ya kai hannu ya tab'a wuyansa kad'an, shi kansa ya san ya rame don zazzab'in da yayi mai zafi ne, kwana biyu baya cikin haiyacinsa bacci kawai yake yi a k'asan allurorin da ake masa, bayan ya farka kuma jikisa yayi nauyi da yawa don haka ya rasa k'arfi mai yawan da har yanzu bai dawo daidai ba.
Ya d'ago da idonsa ya sauke akan k'ofar da matan keta shigowa ciki, jiran shigowar Fadeelah kawai yake don ko bayan ya farfad'o daga tasa rashin lafiyar, tunani yake idan nata idanun sun farfad'o, so yake yaga ta koma daidai kamar yadda take a baya, so yake tayi jinyar zuciyarta a d'an k'ank'anin lokaci ta kuma warke, baya fatan ace ta rik'e komai a ranta don in har ta cigaba da wahalar da kanta, shima zai cigaba da wahala ne da tunanin halin da take ciki.
Daga bayan yayarta Maryam, Fadeelan kuwa ta shigo sanye da wani dogon hijabi kalar coffee daya rufe jikinta ruf! in banda fuskarta data haska cikin duhunsa.
Fatansa ya karb'u sanda suka had'a ido...
Ya hango wani kyalli da rabon daya ganshi a idanun nata tun sanda suka rabu a America sannan kuma kalarsu ma ta daidaita, sai kawai ya samu kansa da yi mata wani guntun murmushi, labari mai dad'i shine itama ta mayar masa kafin ta nemi waje ta zauna.
Fadeelah ta sunkuyar da kanta k'asa bayan ta zauna, rabonta da shigowa d'akin nan tun zamanin baya a wannan ranar data canja akalar rayuwarta, ranar data gudu daga Babban gida, ranar da Kawu Ibrahim ya ceto ta daga hannun su Salisu dake mata dukan mutuwa, sannan ranar da a cikin d'akin nan dai kowa ke mata kallon wadda ta kashe mahaifiyarsu.
Bayan gyara da d'akin ya samu babancin wancan lokacin da yau shine...
A yau ita d'in wankakkiya ce mai 'yanci, babu wanda ya isa yayi mata kallon raini balle har a sami mai d'aga hannu akanta, haka kuma gaskiya ta fito ta wanke ta tas daga zargin kisan da aka d'ora mata.
Ta rufe idonta a hankali sanda muryar Kawu D'anjuma ke umartar Kawu Bashir daya bud'e taron da addu'a...
Gani take kamar a yau ne komai ya faru, kamar a safiyar yau Hajiya ta rasu kuma a yau d'in aka gano cewa Sule ne ya kashe ta ba ita ba.
Tabbas tsakanin hak'uri da rashinsa d'an tak'in kad'an ne!
Sai ta sunkuyar da kanta a hankali tsakiyar cinyoyinta, bata son wani ya hango kyallin kwallar dake shirin taruwa a idonta, don ta fahimci kusan kowa hankalinsa na kanta.
Ta gefen idonsa Adam ya hango sanda ta sunkuyar da kanta fatansa wani tunanin take ba kuka ba, ya cigaba da kallonta har lokacin da aka shafa addu'ar, a sannan ya lura da yawa daga cikin matan sun tsura masa ido ne kuma sun san Fadeelan yake kallo, don haka yayi saurin sunkuyar da kansa ya koma kallon k'afarsa dake tankwashe.
Kawu Bashir ne ya fara magana akan zumunci da kuma muhimmancin 'yanuwantaka, yayi bayani mai tsaho kafin Kawu Danjuma ya karb'a, sai dai mafi yawan bayaninsa na neman yafiya ne kan abinda yayi, kuma ko a muryarsa kowa zai fahimci cewa da gasken ne yayi nadama, kalamansa na k'arshe da suka yiwa Adam dad'i sune inda yace.