Sashe 9
Alaƙar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ina ga ko yadda ya musu bayani ba haka suka dauka ba, amma zan tambaye shi ko nice ban fahimci yadda suke ganin laifina akan fitowa da nayi ba tare da izininsa ba, domin a sanima da izininsa na fito zuwa gidanmu, a hankali na fito daga dakin Babanmu, a bakin kofar muka hadu da Jalilah yar rikon Yadiko ce, amma yar uwarmu ce sosai, sai dai Jalilah ni da ita bama ga maciji saboda kawai kowa da abinda yake tsammani a tare da shi.
Ni dai ban san me na mata ba, amma tare muka taso, zuwa yanzu dai auren Jalilah uku, tana zawarci sannan yan uwarmu ce na kusa sosai domin Mahaifinta kanin Baba ne, mahaifiyarta kanwar Yadiko, a sanina Jalilah kawar Ya Hafiz ce, kuma kawar Matarsa domin tun aurensu suke tare.
Kallo daya tayi min ta dauke kai, nima na dauke kai kamar ban san tana wurin ba.
Dakin Yadiko na nufa na ce mata.
"Yadiko zamu tafi!" "Tow Allah ya kiyaye hanya, sannan ki daina fitowa ba tare da izinin Mijinki, baki san kin girma ba ne." Ni dai bance mata cin kanki ba, har ta gama magana na wuce dakin Mama na hada kayana.
Ina hada kayana sai ga Ya Umar ya shigo da sallama, murmushi nayi na zauna.
Sai da ya fara gaida Baban Bauchi da Yadiko, sannan ya shigo ya samu su Hajiyarsu Ya Hafiz ana ta surfa abinci, kallona yayi yana murmushi ya ce min.
"Auta shi ne baki karaso makama ba?" Murmushi nayi na ce mishi.
"Ina wuni Ya Umar!" "Lafiya lau!" Kafin ya rufe baki Mama ta tab'e baki ta ce mishi.
"Ai fitowa tayi ba da izinin Mijinta ba!" Kallona yayi yana murmushi ya ce mata.
"Tsakanin da Allah auta ta wuce sai ta nime izinin zata zo gida nan, kada ki manta Hafiz dai a gidan nan ya taso haihuwarshi ce ba ayi ba, sannan na biyu idan Auta ta tawo babu izininsa meye ribarta?
Kayyasa Mama Hafiz da Lubnah dukkansu Yaran gidan nan, kuna nazari kafin yanke hukunci gudun kada a tsaya a gefe guda!" Da yake sunan Ya Umar sunan Baba Malam ne wato Kakanmu bata iya ko d'aga mishi murya ta ce mishi.
"Mai sunan Baba Malam!" "Mama maganar Allah nake gaya miki kafin Hafiz ya auri Lulu mu ne muka fara auren Yaran wasu, yanzu saboda yadda Habibah ta samu wuri wallahi idan zata fita sau dari bai wuce ta gaya min sau biyu ba, mu Yaran wasu muka musu adalci sai mu namu ne ba zasu samu adalci ba?
Mama ita yarinya ce baki
aya shekaru tara ake nima da aurenta idan kuka tsannanta mata bata da inda ya wuce nan ku sani shi Hafiz namiji ne, hmm kayya.
Lulu kina son wnai abu ne?
" Da zumudi na mika mishi takardan da nazo da shi.
Budewa yayi sannan ya ce min.
" Ok akwai ma a gidan nan kamar jiya aka yanka abokina dan liti zai zo ya saya.
Fita yayi ina jin yadda Yadiko take gaya mishi abin da ya faru, itama nan gaya mata gaskiya yayi ya saka Ya Sani ya cire min kajin, duk wannan abin da ake Hajiya kunya ce ta kamata bata iya magana ba, sai sunkuyar da kai itama Mama sanin cewa Ya Umar ya daure ta da jijiyarta yasa bata yi magana ba, a can parlourn Baba naji yadda Ya Hafiz yake fa
a shi da Ya Umar, koda yake Ya Umar ya gaya mishi magana daya ya ce mishi.
"Ka gama duk abinda zaka yi, wa'adin Allah gaskiya ce, ni da kai mun san kome!
" Ba sai Ya Hafiz ya fusata ba, ya mike tare da sallama yana fa
in.
" Na hakura da Lubnah tunda ban muku adalci ba!
" Nan Baban Bauchi ya dirkowa Ya Umar fada yake kamar zai cire bakinsa, har da cewa.
" Idan kuka kashe mata aurenta ko bayan raina ne ban yafe muku ba.
" Murmushi Ya Umar yayi ya ce musu.
"Ni ba zan kashe mata aure ba, ai ita mace baka ce mata kaso aurenta ki zo mu zauna wannan wani lamari ne da Allah yake shirya faruwansa!
Ka yi hakuri Baba idan na
ata maka rai!"
Ko amsa masa sallama Baba be yi ba ya bar gidan, haka Baba ya zauna da Ya Hafiz yayi ta bashi hakuri, har da kiran Hajiya ya bata hakuri wai ta bawa Ya Hafiz hakuri.
Abin bai yi dad'i ba, domin haka muka baro gidan zuciyata ba dad'i.
Kaina a sunkuye a cikin motar.
"Ban da rashin mutunci irin na Yaran Salamatu don an rufa muku asiri an yi muku alfarmar auren yarku sai ku saka min d'a a gaba?
Wallahi kun yi asarar!" Haka Hajiya take fada,
shi dai bai ce kome ba, zuwawa yanzu ya fara jin wani irin yanayi a tattare da shi, "Hajiya don Allah ki mana shiru!" Yadda yayi magana a karfafe zaka
auka ba ita ta haife shi ba, jin yadda ya daka mata tsawa yasa ni na sha jinin jikina na koma gefe da jikin kofar, har muka iso Tambari, na bude motar na fita tare da
aukar kayan da nazo da shi, kaya sosai aka hada min Mama da Yadiko wai kada na tashi hankalina.
Bayan na shigar da kome na wuce zuwa part dina na saka kome a muhallinsa, sannan na wuce zuwa kitchen na daura ruwan zafin na zuba a flast, kafin na fito a kujeran Parlour na hango shi.
"Zo nan!" Ya ce min, na taka a hankali jikina yana rawa domin nasan irin wannan kiran babu alkhairi a cikinsa.
Durkusawa nayi a gefen kafarshi ina me sunkuyar da kaina.
Shiru ne ya ratsa parlourn kafin ya ce min.
"Me kika gayawa Umar?" D'ago kai nayi da sauri ya tsinka min mari, sai da naji wani irin shuuu a kunnena, baki
aya kaina ya fara min irin wannan ciwon da yake min tare da juyawa.
Rike fuskana nayi da kaina.
"Tambayarki nake!" Tsoro da tashin hankali, ya hana ni magana kara rufe fuskana nake ina girgiza kai.
"Tambayarki nake?" Ya kara zuba min wani irin gigitaccen mari da yasa ni zama da duwawuna, nace mishi.
"Wallahi ban fadi kome ba, ka yarda da ni." Na fada ina fashewa da kuka, haka yasa take ya kyale ni, ya bar parlourn anan na cigaba da kuka har dare ya raba na wuce daki na kwanta, haka nayi kuka har na godewa Allah, kwanciyar da nayi har na fara barci ya shigo ya bani wata magani na amsa na sha, ko minti goma ba ayi ba na fara jin kaina yana wani irin juyawa a hankali na kwanta.
Daga nan ban kara sanin me ya faru ba, sai da asuban fari na tashi na shiga wanka, bayan nayi wanka na fito duk yadda naso na tuna mai ya faru na kasa, sallah nafilla nayi na wuce zuwa kitchen, ja daura abinda zan daura sannan na fito zuwa dakin nayi , bayan na idar na koma na fara aikin abin karyawa karfe bakwai saura na nufi bangarensu, na taso Yusrah amma yarinayr nan tayi ta min ihu har da wani abu kamar tana dambe da ni, ihun da take min da kuma yadda nake jin wani abu me karfi a kaina yasa na daka mata tsawa.
"Don Allah tsaya na miki wanka!" Wannan abin na mata yarinyar nan ta fasa ihu, sai ga kowa ya shigo ban dakin, ba tare da wani bincike ba ya Hafiz ya rufe ni da duka, kamar zai kashe ni, saboda karfin azabar duka zubewa nayi akan gwiwata hancina yana zuba da jini.
"Tashi ki mata wanka!"
asa tashi nayi ina kife a wurin, koda ya d'ago ni, sai komawa nayi na kwanta sharaf kamar an jika tsuma, abinda ya saka hankalinsa ya tashi amma saboda rashin imani ya ce min.
"Wallahi idan baki tashi ba, na taso sai na kara taka ki, jaka juya wacce bata san darajar haihuwa ba"
"Gara ka gaya mata dai, ban da rashin mutunci ki saka yarinya a gaba da azaba, ke ina danginki gani suke ana cutar da ke!"
Sai dai duk abinda suke yi bai saka na motsa ba, anan suka fahimci fa babu numfashi a jikina, abinda ya firgita su har Tijjani ya shigo yana fa
in.
"Yanzu kana ganin daidai ne abin da ka yi?
Kana tsammanin yadda Umar yake kallon idanunka zai kyale ka ne idan ya ji abinda ya faru?
Kana abu kamar mahaukaci yarinyar nan kana amfani da ita yadda bai dace ba, ba fa Ubanta baya sonta ba ne a'a alfarma ya maka saboda Abbanmu, ka sake aka gano yadda kake azabtar da ita wallahi ka ji na gaya maka, ba ruwan kowa da kai ne ka fara waye ne ya fara.
Kuna ganinsa zai kashe musu yar mutane bayan kace jiya ka mare ta, yau kuma ka kara rufe ta da duka.
Ji yadda take sume ni dai ina shaye-shaye amma wallahi na fi karfin dukar mace kamar yadda kake yin nan ai abin ya koma jahilci kuma!", daga haka ya fita zai gashi da ruwan gora mai sanyi yana zuwa ya samu fuskata ya zuba min, ajiyar zuciya na sauke ya ce min.." tashi ki koma part dinki, Yarinyar idan baza du shirya yarsu ba, to su barta ko na kira Baban Jama'are yau wallahi na gaji da iskancinka Hafiz na gaji da muguntarka idan kayi wasa sai na gayawa Abbanmu!
" Sanin cewa dan shaye-shaye ne bai da mutunci zai aikata.
Dakyar na tashi na nufi hanyar fita, tunda na shiga parlourna, rufewa nayi na kwanta a saman kujeran parlourn nayi ta kuka ina jin kamar zuciyata zata buga, na rasa gano laifin da nayiwa Ya Hafiz.
Zuwan Kabiru na bude mishi kofa nayi na zuba mishi abinci nace ya je yau ba aiki.
"Aunty me ya same ki?" "Ba kome!" Shiru yayi kafin ya ce min.
"Aunty ki yi hakuri kin ji, akwai abinda nake son na kawo miki idan kin amince sai na kowa miki!" Gyada mishi kai nayi nace mishi.