← Book details Alaƙar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 86

Sashe 86

Alaƙar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Duk ganinta da kake ka zata tana da aure kai ka ce ina taimaka maka da labarin zaman da take duk tura maka da nake baka duba ba?

Har labarin mutuwar aurenta da jinyar da tayi da barinta Bauchi na tura maka ta email dinka!" Dafe goshinsa yayi yana fa
in..

"Innalillahi wainnalihir rajoun Innalillahi wainnalihir rajoun, innalillahi wainnalihir rajoun.

Da na ga baka samu lokacin min reply ba na turawa Alhaji ELYakub da yake tab'a tambayata maganar ka da Lubnah na tabbatar masa da gaske ne domin a lokacin gani suke kamar gamo ka yi ba da gaske ba ce." Mai da kanshi yayi ya kwantar da shi a saman kujeran yana jin wani irin sara mishi da yake yi.

"Wannan karon dole ka tsayawa kanka, fight for yourself, domin ina jin cewa kamar zata koma hannun dan iskan gaye nan." Bude idanun yayi akan Malam Jamil ya ce mishi." Yaushe ka ji zata koma?" "Tun kwanciyar babansu a Lagos, Matata Yayarta kawar Yayar Lubnah ce, take cewa Mamansu ta ce da ta koma gara ga gawarta." Ware idanunsa yayi akan Malam Jamil, kafin ya ce mishi.

"Ku tashi muje!" Rike hannunsa Malam Hamza yayi ya ce mishi.

"Ina son ka bi kome a hankali, in sha Allah sai inda karfinmu ya kare ba zamu kara barinka, ka rasa ta ba a karo na biyu." Zama yayi yana sauke ajiyar zuciya, idanunsa sai wani kyalli suke.

Malam Jamil yake bashi labarin wahalar da ta sha ji yayi kamar ya bude idanunsa ya ga Hafiz no wonder ya mishi wannan dukar ranar sashe kishi da takaici suka kwashe shi yayi daidai kenan, yana zaune har wurin daya da wani abu suka fita zuwa masallacin suka yi sallah sannan suka dawo suka zauna daga nan ya bawa Yaran Malam Hamza barka da sallah na dubu hamsin, haka suka wuce dutsen tanshi, wurin karfe biyu da wani abu sakamakon unguwa ya cika dakyar suka gano gidan, sai da ya kira Mama ya gaya mata gashi nan a kofar gidan ta tura Hashiya ta shigo da su, lokacin da suka shiga parlourn Abba ta kai su, ta gaya mishi ga Shugaban Lubnah daga Lagos ya zo musu barka da sallah.

Koda suka shiga Alhaji yayi dattako domin yayi ta mishi tambayar da kure hankali, yadda yake bashi amsa tare da fadar waye shi, yasa baki
aya ya nutsu.

"Yanzu me ya kawo ka Bauchi?" "Nazo zumunci da kuma gaisawa da abokan arziki da aka zauna." Shiru Abba yayi kafin ya ce mishi.

"Kamar shekarun baya ka zo nan kai da wadannan abokan naka ko idan ban manta ba?" "An yi haka Alhaji shekaru goma da wani abu;" gyada kai yayi yana kallonsu, duk da ba shi bane ya bada amma amma kuma sai ya ga yadda suka zo wancan lokacin da kuruciya yau dashi sun zo da shekarunsu.

"Masha Allah;" nan suka yi ta hira amma shi bai ce kome ba har aka fara shigo da abincin Abba ya bar musu parlourn.

Present
Mikewa nayi xan bar parlourn ya ce min.

"Me yasa kika boye min baki da aure?" Tambayar ya zo min a wani irin bazata, "ka sani ko tana da wani dalili?" "Which dalili zata boye min bata da aure?" Zubawa kofar parlourn idanun nayi kafin ns cigaba da tafiya.

"Baki gaya min dalili ba?" "Ka tambayi Alhajinku yafi ni sanin dalilin haka!" Ta kowa yayi bayana kafin ya zagayo gabana yana mai zuba hannunsa dukka biyu.

"Na zata idan wani zai boye min kome ba zaki aikata haka ba?

Me kika dauke ni?" "Malam Bilal ka yi bincike!

Kada ka yanke hukuncin da sauri haka." "Jamil" sai kuma yayi murmushi ya juya ya fita, wani irin abu na ji ya tsaya min a raina, ba zan iya barinsa ya tafi haka na, lokacin da na biyo bayanshi na samu Hafiz a harabar gidan, suna kallon kallo tsakaninsa da Bilal.

"Sir ka tsaya mu yi magana." "Me yasa zan tsaya mu yi magana!"
" Ka saurare ni Please!"
"Ashe da gaske abinda ake fada min yana faruwa da gaske ne, kwartonki kik..." Ganin Hafiz nayi a can kasa kamar zai tashi amma saboda yadda ya sha bugu.

"Kaci zarafina zan dauka, ba yau na sha jin kazaman kalamai daga bakin mutane ba, amma ita din kaunata idan bana nan xaka yi yadda kake so amma ina tare da ita ni kamar inuwa nake mata ka kiyayye kalaman ko na rufe ka har abada."
Tashi yayi yana fa
in.

"Idan har ina raye aure sai dai ki ga ana yi Lubnah ki dawo rayuwata idan ba haka ba wallahi sai dai kowa ya rasa."
"Na rasa gane kai wani irin jahili ne, amma a yau zan gaya maka abinda ka sani ba.

Har abada ba zan tab'a komawa rayuwarka ba.

" Kallon CEO nayi a hankali na kai hannuna tare da rike rigarshi.

" Tun daga lokacin da na hadu da shi yake bawa rayuwata kariya ka koyi yadda ake mutunta mutum.

" Na fada tare da sake rigar na juya cikin gida hawaye na zuba min.

"Lubnah!!!!" Dukkansu biyu kira sunana a lokaci guda................

Alhamdulillahi anan na gama book 1 waye zata amsawa
(In sha Allah ranar Monday zan cigaba abubuwa dayawa na tara a gabana don Allah ku bani hutun idan na fara in sha Allah sai na gama zan tsaya amma yanzu ina son na hutawa nima bana jin dadi ga Yarana ma haka basu da lafiya amma zuwa ranar Monday in sha Allah zan dawo da karfina da abubuwa dayawa da ba zaku manta da shi ba Team Lulunhafiz da Team Lunanturaki)
SummaryInformation
DocumentSummaryInformation
WpsCustomData
24048RN6CG
TECNO LD7
WPS Office
Normal
Default Paragraph Font
Normal Table
No List
Calibri
Calibri
SimSun
Times New Roman
Times New Roman
Light
Light
DengXian
Cambria Math
Cambria Math
!%),.:;>?]}
$([{
_GoBack
13ee42a34c0e4685a26af75d46817e4f
Chapter 86 · 0% Book details