← Book details Alaƙar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 86

Sashe 38

Alaƙar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da ya cire shi a key ya tsaya yana kallon hotonsu na kuruciya, suna dariya ya danne bayan Turakin.

Murmushi yayi sannan ya cigaba da.

Lalubar wayar har ya zo kan number shi wanda ya rubuta Introvert.

Wayar har ta gama ringing ba a dauka ba, sai can aka turo mishi sako da number.
*Ya suke?*...........
[12/4, 10:51
AM] Firdausi Salis: ASHIRIN DA BIYU
Daga wannan babu wani sakon, har leka bayan wayar Ubaid yayi ko zai ga sauran sun makale, amma ina iya su kenan kalma biyu, harufa hudu?

Wato shi dai ba zai tab'a sauya ba.

Cikin fushi shima ya tura masa da Ash'ar.

Tunda ya tura ya kai minti goma a wurin ba reply ai yasan ko sama da kasa zasu hadu ba zai dawo mishi da sakon ba, idan yayi sa'a gobe ma da zai kara tura mishi abu daya ne zai sake turo mishi.

Sake kiran layin yayi ya danna mishi busy.

Takaici ya saka shi wucewa gidan ya samu Hajja da Alhaji ELYakub sun koma hiransu, mika mishi File din yayi ya ce mishi.

"Wannan sune sakon da ya bani, sannan da farko ban fahimci yadda sakon yake ba, sai dazun nan na fahimci sakon." A hankali ya fara warware mishi bayanin da Turaki ya turo mishi, shiru yayi yana mamakin yadda, kome yake tafiya ba tare da saninsu ba.

Sannan wani abin da ya bashi tsoro yadda aka karkata da ku
i ta wani hanyar da bai dace ba.

"An samu masu hannu a cikin lamarin?" Bude baki Ubaid yayi zai magana aka turo kofar, Alhaji Mudansir ELYakub Kumo ya shigo cikin wata danyen Wagabari dark blue, yayi ya wani irin daukar fatarshi.

Sai wani shaki yake kamar dare kwana sha hu
u, duk wanda ya ganshi yaga wanda arziki ya zauna mishi, cikin isa da kasaita ya samu wuri ya zauna cikin girmamawa ya gaida iyayensa.

A hankali ya mai da hankalinsa wurin Mahaifinsu da ya ga ya tattara nutsuwarsa ga Ubaidullahi.

"Yanzu ka mai da mishi sakon kace yayi duk abinda yake ganin ya dace, sauran kuma zan dauki mataki in sha Allah ba zan bar kome ya tafi a haka ba." Wani irin harara Alhaji Mudansir ELYakub ya watsawa Ubaidullahi ya cigaba da sauraren maganarsu da ba fahimtar inda suka nufa yake ba, tunda kusan a dunkule suke maganar.

Mikewa yayi don ya fahimci a al'amarin duniyar nan matukar maganar Turaki ne tow dattijon Mahaifinsu baya sauraren kowa kuma baya fahimtar kome idan har da a furta sunan Turaki a gabanshi ko a gefensa.

"Baffa zan leka kamfani."
Kallonshi Hajiya Dadda tayi ta ce mishi.

"Saurin me kike yi da ba zaki zauna ta gama magana ba?

Ban san me yake ciwon ranki idan kika zo ki ka ga ana magana akan Turaki sai ki tsirfo da wani hali." Daga haka bata kara magana ba, ta dauke kamata kamar ba ita tayi maganar ba, kunya ce ta sa shi komawa ya zauna.

Burinsa ya fita waje ya jira Ubaid yaji wani abu suke shiryawa.

Bai gama wannan nazarin ba sai ga Alhaji Mujitafa, wanda suke kiranshi Auta.

Cikin girmamawa ya gaida Iyayen nasu sannan ya kalli Ubaida ya ce mishi.

"Second love, kai ne da sassafen nan?" Gyada kai yayi yana murmushi ya ce mishi.

"Uncle Auta barka dai." "Barka second love, ina wancan Introvert din ya shiga ne?

Na kira bai dauka ba." Kunshe dariya Ubaid yayi yana kallon Uncle Auta da yake
ara duba wayarshi.

"Duba ai ba zai gaza turo maka sako ba!" Dubawa yayi yaga sakon.

"Sorry im busy!" Tsaki yayi ya ce musu.

"Baffa na gaji da halin Turaki." Make shi Hajiya Dadda tayi cikin wannan rikitaccen hausar nan nata me juya mace namiji , namiji mace ta ce mishi.

"Kin ci gidanku, mara kunya in gaji da halinta, wani hali ne da ita banda halin kwarai, ita yaron nan Turaki mutumin kirki ce, kowa yasan tana da kirki amma bakin halin zeenatu da yayiwa Turaki sharri, ina da tana nan da nata iyalin, wai yaron dan uwanku kenan kuka juya mata baya ke Auta da nake gani a mutumin kirki amma kike cewa kin gaji da halinta.

" Matsawa can yayi yana jin zafin yatsun hannunta.

" Daddah kece kika bawa Turaki dama yayi yadda yake so, Fisabiilillahi me ya nima ya rasa.

" " Abubuwa dayawa.

" Inji Alhaji ELYakub Kumo ya fada ya ce mishi.

" At teenage ya rasa Uwa da Kannensa, sai Jasminah itama don ba yadda ta iya da shi ne, tunda su biyu suka rage, tunda ta zama yar amshin shatar zeenatu, koda yake uwarta ce ba yadda ta iya amma a gefe guda ina ganin laifinka ne, Mudansir.

" " Baffa ni kuma?" Ya nuna kanshi da muryanshi a shake, " Eh kai;" shigowa wasu matan alfarma suka yi tare da wani shima babba a cikin gidan.

" Daddy!

" Ta kira sunansa.

Kallonta yayi yana mai mika mata hannu ta zauna a kusa da shi, tana kallon Alhaji ELYakub Kumo ta ce mishi.

"Baffa ina kwana?" " Lafiya lau Fadima." "Barka da safiya Kawu?" " Barka dai Munir!" Shigowar wata hamshiyar mace parlourn cikin wani uban ado kamar zata biki da daya daga cikin yan matan nan da suka je salon, nunawa yarinayr wurin zama daya yarinyar tayi.

" Badar ga wuri!

" Wani yatsina fuska tayi, tana kallon gefen da mahaifiyarta ta zauna.

Itama nan ta zauna.

Kallon zuri'arshi yayi babu bare a cikinsu dukkansu ahalin Kumo ne, kuma masu hannun jari a kamfanin KUMO properties nigeria agency, kamfani ce fa take sayan duk wani kadara da gwamnati zata yi gwanjonsa, kamfani ne da banku suke binta, ba iya nan ba akwai wasu iyalan nan, domin kuwa lissafin a bayyane take.

Su waye KUMO properties nigeria agency?

Alhaji ELYakub Kumo, dan asalin Gombe ne da ya fito daga garin kumo, ba fulatani ne da ya gaji arziki daga iyaye da kakanni domin su ke da sarautar Sarkin Fulani Kumo anan lagos sarautar ce da ita ta Sarkin Fulanin lagos., dogaye ne masu matsakaicin jiki yayinda matan cikinsu suka kasance sirara iyayen suka kasance yan chubbys.

Alhaji ELYakub yana mata daya Hajiya Fadime, wacce suke kiranta da Daddah.

Ita ta haifi Yara shida maza uku mata uku.

Marigayi Alhaji Haris shi ya fara bada shawarar kafa kamfanin KUMO properties nigeria agency, amma har yanzu sana'arsu ta gado sayar da shanu da madara basu fada ba domin bude wani kamfani aka yi na sayar da madarar shanu da namar shanu.

Kasancewar Alhaji ELYakub da girmansa ya fada harkan boko, domin lokacin da ya auri Dadda bai gama secondry School ba, tun yana Yaro dan shekaru goma sha uku yake kad'a shanu daga Gombe to lagos, a cikin gwangwaro.

Haka yasa wani bayarabe ya bashi shawara ya fara karatu domin Allah ya mishi baiwar iya sarrafa kudi, gashi tun yana wannan shekarun turanci ya zauna akan harshensa.

Kusan fulanin zamanin da akwai zuciya haka yasa yana dawowa ya fara makaranta, shekara daya yayi a primary ya tafi secondry School, yana da shekaru ashirin cib ya gama secondry School, a wannan shekarar aka auren mishi yar baffansa Daddah.

Zamansu yayi albarka domin kuwa kuwa an haifi Harisu wanda shine Babba,sai Mudansir, Khaulatu, Sameerah, sai Ramatu kafin Uncle Auta wato Mujitafa.

Kamar yadda suke su shidan haka kowane a wurin halinsa daban, Alhaji ELYakub ya
gina kansa da matsayin da yake ta hanyar sana'ar sayar da shanu daga Gombe zuwa Lagos, kafin wani abu ya faru a gabansa, wani mutum ne ake bi bashin banki, su kuma banki suka zo kwace kadarorin mutumin lokacin duniya tana kwance, a take suka fara kwashe kayan sanin cewa suna tare da bayaraben for while sai ya tambayi kudin da ake bin mutum banki ta fada mishi, cikin ikon Allah sai ya gwada biya, tare da maida wa mutumin kayanshi idan Allah ya hore mishi ya biya shi.

Shi dai da farko bai dauki haka a matsayin wani babban al'amari ba.

Bayan an bashi shawarar ya dawo Lagos da zama ai zai fi yana sakawa ana kawo mishi dabbobin daga arewa, ace duk bayan sati biyu yana hanyar Lagos, a lokacin ya ha
a degree dinsa na daya zuwa na biyu, ga shi idan ya ce yana da iyali
aryata shi ake domin a lokacin ya cika shekaru talatin a duniya, haka ya nime gida a alaba rago, ya kawo Daddah da Yaranta, dama can ko a Gombe Yaran suna karatu domin Daddah tana haihuwar kunika ne, yaran kusan kansu daya idan ka cire Harisu da ya fi su tsawo, tunda suka dawo Lagos sai rayuwarsu ta kara inganta, idan aka samu jajjirtaccen namiji akan ilimin Yaransa, tow baki
aya dauke kome yake yi, haka Alhaji ELYakub ya kasance, ya tsayawa Yaransa musamman harisu da ya kasance mai zuciyar neman na kai, domin shi ya fara bada shawarar Daddah ta fara sayar da fura da nono lokacin bai wuce shekarun sha biyar a duniya ba, da ya gama secondry yana jami'a shi ya fara gayawa Mahaifinsu madadin kudin da yake biyawa mutanen da suka shiga matsala da banki yayi Register da lasin domin ya fara sayan kadarorin mutane, idan ka biya kudinsu ka dauki kayanka, a yanzu an cigaba, shi anan kasar turawa da yake karatu haka suke yi, domin shi a can Rasha ta tafi karatunsa bayanshi babu wnada ya samu wannan damar domin sun dauki irin rayuwar karya da son a san su din wasu ne, Uncle Auta ne ka
ai yayi karatu har zuwa Nijar, da yake shi din na.

Musamman ne, Allah ya ha
a jininsa da dan uwansa Harisu, Haris yana da abokai guda biyu, Jibrin Mahaifin Ubaid, sai Abbas, abokai uku nan sun taso cike da kaunar juna da adalci idan ka cire Uncle Auta a cikinsu wnada ya kasance Yaro ne.

Jibrin Mahaifin Ubaid, dan Kanwar Alhaji ELYakub ne, ya dauko shi ya kawo shi gidansa tun suna Yara, shi kuma Abbas dan abokin Alhaji ELYakub ne, mahaifinsa ya rasu Maraya ne, wanda dangin mahaifinsa suka kwashe dukiyarsa suka watsar da shi.

Haka Alhaji ELYakub ya ha
a su da nashi.
Chapter 38 · 0% Book details