← Book details Alaƙar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 86

Sashe 23

Alaƙar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Uwar da ta haife ni ta tsame Hannunta a kaina, Mahaifina ya watsar da ni, a koda yaushe nayi kuka Ya Hafiz xai nuna min ai ba kome ba ne, saboda kawai dan karamin mistake ai ba wani abu ba ne can babba da zai saka ni damuwa, Ya Hafiz Dan uwana ne tunda da Baban Jama'are da Babana uwa daya Uba daya, sannan Ya Hafiz ya boye munannan halayenshi ya bayyana kowa kyawawan halaye da Dabi'u, babu wanda zai ga ya Hafiz ya zata yana da mugun hali.

Sai dai kowa yasan mai kyau kuma yasan mara kyau, idan da ni ce Ya Hafiz ba zan taba saka shamaki a tsakanin zuciyoyin da suka yarda da ni ba.

Amma sai ya lalata min rayuwata da future dina da kuma duk wanda zai kalle ni ya tausaya min, sai ya cusa min kin kaina da rashin accepting kaina.

Ya danna min tsoron duk wani d'a namiji da kuma duk wanda zai kalle ni a matsayin mace, ya nuna min cewa ni ai ba mace ba ce.

Ya kuma gaya min cewa kaf duniya da zuriar Baba Umar Jama'are babu wanda zai ganni ya ji sha'awar zama da ni ko kaunar zama da Ni.

Bayan ya ga bani da amfani ya cigaba da ajiye ni domin a ga yadda yake namijin
arin kula da rayuwata.

Ba zasu fahimci waye shi ba, sannan idan zasu shekara dubu ba zasu tab'a gano waye Ya Hafiz ba hawainiya ne shi mai sauya launi daga wannan zuwa wancan.....
*08130269641*
[12/4, 10:51
AM] Firdausi Salis: *ALA
AR ZUCI*
Ramlat Abdulrahman Manga
Mai_Dambu
*Littafin nan na kudi ne akan 1500*
*1500 ne, Nijar kuma 600 CFA 5921536136 ramlat Abdulrahman Manga Moniepoint or 0472282105 ramlat Abdulrahman Manga Gtbnk ko Nijar 98 16 12 40 my Nita*
Domin tura shaida wannan number. +234 703 513 3148 ko wannan 08130269641
Posting Arewapen da Telegram
SHA UKU
HAFIZ
Da farko bai zata zai haukace akan tafiyar Lubnah ba, bai ta
a kawowa a ransa tana da amfani har haka ba sai da ya wuni yana bibiyar dangi da yan uwa ko ta je wurinsu, amma babu labarin kai ko a mafarki babu labarin Lubnah haka yasa hankalin kowa ya tashi ban da yan dakinsu da sun san mafarin.

Yadda Ya Hafiz yake playing victim sai ka rantse da Allah, ba shi yake yi sanadin barinta gidan ba, aikuwa Washe gari sai ga Baba Malam, shi da Baban Jama'are da Hajiya Asiyah,Goggo Alti da Goggo Uwani sai Goggo talatuwa.

Hankalin kowa yayi bala'in tashi, rayuka sun b'aci.

Tambayar da Baban Jama'are da Goggo Alti suka mishi ya sake cillashi cikin wani tashin hankalin.

"Me ya ha
a ka da Lubabatu da har ta dauki wannan matakin?" "Wallahi na rantse da Allah ban mata kome ba, kishi yake janta." "Yarinyar da magana ma bai dame ta bane zata yi kishi har na fitina?

Hafiz kasan ina da labarin abinda kake aikatawa!?" Inji Mahaifinsa, take Baba Malam ya rufe shi da fada.

"Ya ana cikin wannan tashin hankalin zaku kara mana da wani.

Ku barshi da ji da damuwar da yake damunsa ba a kara masa wani ba, gaya min me kuke son cewa." Goggo Alti ta ce mishi.

"Baba Hafiz munafiki ne, ba kan Lubnah ba hatta Sirajo sai da Hafiz yayi sanadin barinsa shagon Shehu, yanzu haka ya koma wurin Babana yana zaman shagon, Allah ya gani tunda ka yi sanadin da Babana ya bar shagon na fara tunanin ya kuke zaune da Lubnah kowa yasan yadda kake nunawa ka damu da ita bayan kuma kai ne shaidanin da kake rabata da duk wani farin cikinta, Shehu da kanshi ya kira ni yana gaya min ya kori Sirajo ina laifin ya ce min na ja mishi kunne, bayan abinda Sirajo ya sani gaskiya ne, Ali ka ganshi idan akace min zai dafa mutum ya ci zan yarda domin munafiki ne na gaya muku gaskiya.

" " Alti ina magana!

" " Baba dole fa mu fadi gaskiya domin Lubnah ka
ai ba zata iya fadar abinda take ji ba, azzalumi mugu hatta dukiyarta sai da ya lalata mata ya kwashe maha'inci, kai akanka ba ka bar kanka na balle wani haba don Allah wacce irin rayuwa kake yi ne haka?

Wacce irin manufa kake so ne?

Ina tausaya maka Shehu yaranka da ka watsar ka ce basu tausayinka wata rana su zasu dafa maka domin.

Wannan munafikin ya hmm!

" Tayi murmushi mai ciwo, tsoro ya kama Ya Hafiz haka dai aka tashi zuciya ba dad'i.

Mama ita kanta yanzu ta fara tsoron kada wani abu yake faruwa Lubnah ta bar musu Bauchin, take hankalinta ya dawo kan Lubnah bayan Goggo Alti tayi mata tas, ta ce mata.

" Idan baki tsaya mata ba, wallahi zaki kashe yarki shi Shehu bai da asara haka Hafiz bai da asara gara ki tsaya mata kafin lokaci ya kure mata."
Wannan maganar ya rikita Mama da Yadiko, don haka tayi ta addu'a Allah yasa Lubnah tana hannu na gari, wasa wasa sai da aka kwashe kwana biyar babu labarin Lubnah, haka ya kara fusata Abba wato Baban Bauchi, wanda kai tsaya ya tara Yaranshi da suke Bauchi ya ce ko su dawo da Lubnah ko kuma ya sake Mama, kuma ta bar mishi gidansa wallahi zai aikata, abinda yasa yayi haka faduwar da Hafiz yayi a kasuwa, aka kai shi asibiti akace jininsa yayi azabar hawa, ba sai ga Hafiz ya fadi ba.

Abin kamar alamara, sanin cewa Lubnah yake bukata yasa Abba ya fadi haka, shiru Umar yayi kafin ya ce mishi.

"Gobe idan Allah ya kai mu zata dawo abin bai kai har ha..." Tass Mama ta wanke shi da mari ta kara wanke shi da mari.

"Dama kasan inda take kayi shiru!" "Dukkanmu mun san inda yake ni na bata kudin motar na kaita tasha!" Inji Ya Tahir, ba sai yadiko ta rufe shi da duka tana kuka ba, abin fa ba karamin al'amari bane, haka yasa a ranar suka kira Almu shi kuma ya ce ayi hakuri ranar juma'a zai zo.

Domin Lubnah ma ya kaita 44 ganin likita bata da lafiya.

Da wannan aka kashe case din sai ta zo, kasancewar kowa ya gama jin ranar da zasu sake haduwa tunda ranar talata aka yi zaman.

Lubnah
Tun daga ranar da na isa gidan ban kara samun damuwa ba, sai dai rashin lafiyar da nake a tsaye, bana cin abinci sosai.

A lokacin da Ya Almu suka kai ni asibiti na ciro takarda asibitina na nuna musu.

Kallona Likita yayi ya ce mishi.

"Kanwarka ce?" "Eh likita." Basu takarda yayi ya ce yaje yayi test yana jiranmu, haka muka tafi aka yi min test din sannan na zauna zaman jiran, idan mutane na magana sai nayi ta jin maganar har cikin kwanyana yana wani irin ciwo.

Haka yasa ina karban result din na kai mishi.

Shiru yayi ya ce min.

"Akwai ciwon kai?" Gyada kai nayi ya gyada kai yana mamaki ya ce min.

"Akwai test din da zan baku sai dai ina ga kamar a Kano ake yi ban sani ba ko an samu asibitin da suke yi anan din." Bamu hoton
walwa yayi muka tafi Ya Almu ya kai ni aka min, sannan na dawo kiran wani likita yayi ya zo, yana mai gaya mishi case
in.

Kallon Ya Almu suka yi kafin suka ce.

"Officer maganar gaskiya, kanwarka akwai wani sanadarin da yake sakata jin ciwon da take ji, na farko akwai drug din da take sha ta daina wanda ya ke hana wancan sinadarin aiki sosai, na biyu abin ya tab'a mata
walwa da yasa take jin ciwon kai
, a takaice dai Mentally healthy dinta ya tabu, sannan tana fama da rashin lafiya resilant, daga yadda take gabanmu kawai dai saka ka fahimci tana fama da kanta, amma zan bata magani!" Anan ya Almu ta gaya musu ai ina ganin likita a Bauchi, take suka ce zasu so ganin record dina, shiru Ya Almu yayi kafin ya ce musu, "daga Bauchi take idan aka ce sai anyi haka zai iya daukar lokaci!" Haka suka yi shiru suka kallona, kafin daya likitan ya ce mishi.

"Ko zaka samu wani da yake da alakata da ita akan matsalar." Tunawa yayi da Aunty Innah, don haka ya kirata ya gaya mata abinda yake faruwa.

Shiru tayi ta ce ya bawa likitan wayar, ya mika mishi suka gaisa kafin suka shiga tattaunawa da yake abu na masu ilimi da sanin ya kamata, na wane da wane,a fagen da kowa ya kware.

Maganar da suka yi da Aunty ya sakawa likitan tabbaci da hasashensa.

Sannan ya tambaye ta maganin da nake sha, ta gaya mishi sannan ya canza min wasu magungunan.

Ya kalli Ya Almu ya ce mishi.

"Yana da kyau ta ga asalin likitan
walwa da na zuciya." Shiru yayi kafin ya cigaba da cewa.

"Cikin fahimtar da nayi duk da ban duba
angaren zuciyar ba yana da kyau a san da zuciyar na da matsala ko babu." Sun jima suna magana wanda rabin maganar ba fahimta nake ba, bayan mun bar asibitin Ya Almu ya mai da ni gida, tunda muka isa na zauna a parlourn don shi ya umarce ni na zauna ya kawo min ruwa da magani ya bani na sha.

Sannan ya ce min.

"An samu matsala a gida, ranar juma'a zan mai dake gida kin ji!" Gyada kai nayi ya cigaba da cewa.

"Zamanki a daki bai da amfani kin ga Saliha bata nan, ki zauna a parlourn kafin ta dawo.

Akwai abinci." "Yaya tafi zan kula da gidan!" "Are you sure?" Gyada kai nayi ina mai kallon gefe.

Amma idanuna kwalla ne yake taruwa a hankali.
Chapter 23 · 0% Book details