Sashe 39
Alaƙar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Lokacin da suka dawo gidan ba karamin wulakanci suke sha da Mudansir ba, domin kiri-kiri yake nuna musu sun zo cin arzikinsu ne, Jibrin yana da zuciya sosai haka yasa ya daina zama a gidan, don yana jami'ar Lagos a can yake karatu yake zaune sai weekend da yake shigowa, Abbas dai yake nanike Mudansir idan Harisu baya nan, domin yana da bala'in kwadayi da son abin duniya.
Lokacin da Harisu ya dawo sai gashi tare da wata yar kasar habasha, amma haifaffiyar kasar rasha, mai suna Annah.
Kasancewar Alhaji ELYakub bai hana kowa yadda yake so ba, haka ya amince da abinda dansa yake so, amma da sharadin idan ya gama ya samu lokaci zai aura mishi yar dangi, bai ki ba shima Harisu ya gayawa Annah tana sonshi, haka yasa ta amince, Ubanta mai kudin gaske ne a rasha da Habasha, don kusan da yardan Iyayenta suka tawo gani take idan Harisu ya dawo ba zai tab'a aurenta ba, Annah ba fara bace asalin kalar fatarta na an Ethiopia ne, shi harisu ne ma Faris sosai domin shi ya dauko fatar Daddah don ita farin fatarta har wani jajja ya
e.
Irin tarban da suka yi Annah yasa abin ya bawa yan uwan Harisu haushi, amma Jibirn ya goya mishi baya, satin su biyu suka tafi har can rasha aka basu auren Annah, sai dai tunda aka yi Auren yan uwansa suka tsangwami Annah saboda ita bata sallah, haka yana basu haushi bayan sun manta cewa Addini ya bawa maza musulmai damar auren auren Ahalul kitab.
Wani ikon Allah annah tana shigowa sai ciki, wannan cikin ya saka mata kwadayin abubuwa musamman fura da nono, sai tuwon dawa, wanda kusan abincin Alhaji ELYakub ne, haka suka hadu suka yi renon cikin har ta haifi danta, namiji Masha Allah.
Lokacin da sako ya isawa danginta, sun zo domin farin ciki.
Ranar suna ta ce ta bar addininta na Kirista ta koma addinin Muslunci, yaro ya ci suna Bilal wanda Jibirin ya ci Turaki domin a lokacin sunan yaron aka kara bunkasa kamfanin KUMO properties nigeria agency, aka kara fadadda shi, a lokacin Jarin Alhaji ELYakub yayi kasa, sai da Annah wacce sunanta ya koma Nana Aishatu, ta tafi har rasha ta nimo kudi, a wurin mahaifinta iya mata uku ya haifa.
Annah Aisha ita ce Babba haka yasa da tazo da bukatarta basu hanata ba, ita ce mutum na farko da ta fara saka hannun jari a Kamfanin, kafin Bilal ya cika shekara biyu a duniya Kamfanin KUMO properties nigeria agency yayi wani irin bun
asa.
[12/4, 10:51
AM] Firdausi Salis: 23
Irin bun
asa da ba a tab'a kawowa ba, kasancewar ko a can rasha ita take ji da kamfanin mahaifinta, sai Harisu ya ce a bata wani bangare na kasuwanci a kamfanin yadda zata iya jagoranta, duk abinda zai yi sai ya fara da iyayensu sannan ya kawowa abokinsa Jibrin shi yake bashi shawara.
Rike kamfanin da Annah A'ishah tayi ya kai kamfanin wata irin matakin nasara, a lokacin ta samu cikinta na biyu, tana kuma jagorantar kamfanin, kafin ta haihu bankin First suka fara kulla Yarjejeniyar kasuwanci, wnada idan aka samu matsala na bashi su zasu fara tuntuba, domin babu kamfanin a kasar nan sai su ne suka fara jagorantar shi.
Shekarar Turaki biyu da wata goma aka haifa mishi Yakub wanda suka kiranshi da Baffa, wani irin kaunar Yaran suke kamar su boye su.
Daddah kuwa soyayyar duniya ta daurawa Turaki, sonshi take kusan tun yaye ta rike musu da taki basu.
Sai a lokacin Mudansir ya koma makaranta, suma matan da suka fara maganar karatu Alhaji ELYakub ya ce sai dai su yi aikin mazansu.
Khaulatu dama suna soyayya da Abbas, Sameerah kuma tana tare da wani dan Kano da yake nan Lagos, ELYakub yaso Jibrin ya auri Ramatu amma yaki domin ya riga Harisu aure, matar ce dai take Gombe, itama tana da Yaro Ubaid wanda kusan wata uku ne tsakaninsu da Bilal Turaki.
Ita Khaulatu tana cikin wani gidan da Alhaji ELYakub ya basu ita da Abbas, haka tayi ta fama itama dai ta koma boko damuwarsu shine matsayin da Aisha da harisu suke kai su samu, sai dai irin wannan matsayin ana samun shi ne ta hanyar da ta halatta, haka suka sakawa ransu kyashi da hassada, wanda yasa suka kasa gaba suka kasa baya.
Abin haka yayi ta tafiya har zuwa da ta yaye me sunan Baffa, sai ga wani cikin.
Murna a wurin harisu da su Daddah abin ya wuce sanin kowa, haka aka haifi wannan karon namiji, a take yayiwa Yaron huduba da Jibrin suna kiranshi Aydin, bayan wannan Yaron bata kara haihuwa ba, sai bayan shekaru goma, ta haifi Fadime.
A lokacin KUMO properties nigeria agency ya kai matakin da sai da aka bude mishi branch a Kano Fatakwal da Abuja.
Annah Aisha itace baki
aya CEO na kamfanin yayinda Haris yake vice President na kamfanin wanda ya janyo idanun yan uwansa ya tsaya akansu.
Kusan rabin dukiyar kamfanin 65% na Annah da Yaranta ne, 5% na masu saka hannun jari ne, 20% Na ELYakub ne 10% na Harisu.
Annah bata yi duhun kai ba duk yaran ta raba musu hannun jarin musamman Bilal Turaki, wanda ta bashi 25% na hannun jarin.
Saboda shi yana karatu a King Abdul Aziz International school Riyad tare da Ubaidullah Jibrin Kumo, haka yasa bai wani san damuwa ko tashin hankali ba, yana aji biyar na secondry School, bayan sun kawo mishi ziyara, Allah ya musu rasuwa baki
ayansu Ita Annah Aisha da Kannensa.
Kuma ba a gaya mishi har sai da ya gama karatu suka dawo gida aka gaya mishi a lokacin ya zo ya samu Mahaifinsa da wata mace ba Mommy dinsa ba, kamar yayi hauka don yaji ya tsani.
Haka yasa shi yayi fushi ya koma wurin kakaninsa, har izuwa lokacin Ubaidullah bai rabu da shi ba, domin da zai koma Rasha tare suka tafi a can suka cigaba da karatunsu, kaf duniya babu wnada ya fahimci Bilal Turaki sama da Ubaid, yasan halinsa yasan shi sama da sanin da zaka yiwa wani a duniya.
A lokacin da Annah Aisha zata rasu a cikin kwanakin ta ha
a kan hannun jarin baki
aya ta tattarawa Bilal Turaki, domin tana jin wani strange abu yana bibiyarta, haka yasa ta ha
a kome ta tura Rasha wurin iyayenta da yan uwanta.
Bayan haka Haris da ya auri Zeenatu itama tana zuwa ta samu cikin Jasminah a burinta namiji zata kara haifa sai aka yi rashin dace ta haifi Jasminah, wacce suka daurawa jigon 20% na hannun jarin Haris zai bar mata.
Shi kuma kamar wanda aka gaya mishi ya raba hannun jarin ya sakawa Ubaidullah 5%.
Bilal 5% Hajiya Zeenatu da yarta 10% sai abin ya fisgi hankalinta akan me za a karawa Bilal a kuma bawa Ubaidullah da bai zama kome a cikin KUMO FAMILY GROUP ba.
Shi kuwa ya ce ya yanke.
Tsakanin Alhaji Haris da Annah Aisha shekaru shida chib wanda ya tilastawa Bilal Turaki dawowa Nigeria, shi kan Ubaidullah ya jima da dawowa gida domin har yayi aure da zuri'arshi.
A lokacin rasuwar Mahaifinsa ne ya zo gobe tun suna Yara sukan zo bikin sallah karamar Sallah da babbar sallah.
Haka sai yasa Kumo Family group matan suka saka buri akan magajin KUMO properties nigeria agency, domin ya ha
a degree dinsa na farko yana da shekaru ashirin cib a duniya.
Wannan rashin da yayi duk da yana jin zafin mahaifinsa, ya kara pushing dinsa gefe ya saka shi kara zama wani irin mutum me murdaden hali.
Da manya da yara na Kumo Family group kowa shakkarsa yake, bayan gefe guda gasa suke da juna.
A lokacin abinda Alhaji ELYakub yayi shine bawa Bilal Turaki kujeran mahaifiyarsa, kasancewar ita ce mafi yawan hannun jari wanda a yanzu Bilal yana da kashi 70% na hannun jarin KUMO properties nigeria agency, sai dai haka kawai ya juya ya koma inda ya fito, ya cigaba da karatunsa.
Bai kara dawowa Nijeriya ba sai rasuwar Alhaji Jibirin Kumo,.
A lokacin yana da shekaru talatin da wani abu a duniya, akwai ciwon da yaji da yasa shi tattarawa ya koma Germany wurin Ellina, Kanwar Annah Aisha, tana auren wani magajin garin Berlin, anan ya cigaba da aiki da babban Cibiyar nukiliya ta Germany.
Yan mata dayawa sun yi kuka akan Bilal Turaki, amma shi ko a kwalarsa.
Bai damu da kowa ba a duniya sai mutane hudu, Alhaji ELYakub, Daddah, Uncle Auta da Ubaid, haka a wurin kakaninsa na Uwa yana sonsu.
Turaki mutum ne da baya shiga rayuwar kowa, baya kuma da rawan kai irin na yaran masu ku
i, duk da gadon da yake da shi Bilal niman kudi yake kamar ba attajirin da aka tara mishi ba, an ta
a hira da shi.
Aka tambaye shi me yasa yake niman kudi bayan yana cikin manyan matasan Nigeria masu arziki, budar bakinsa ya a cikin muryansa mai sanyi da dadin amo, ya ce musu.
"Wancan dukiyar ba Bilal yayi faffutukar tarawa ba, dukiya ce da mutane uku suka tara idan nayi amfani da shi akan kaina na zama cima zaune idan na nima da kaina zan iya rike kaina da kuma duk wnada zai zauna a gefena." Idan bilal yayi magana mai tsawo haka yana nufin yana son maganar ce.
Kai ko a cikin abokai ne yana iya ware kansa, ya koma gefe yana abinda yaga zai iya.
Yana iya daukar nauyin abokansa ayi shagali amma shi zaka hango shi can gefe yana wani aiki abinsa.
Idan kana son ganin asalin Introvert tow Bilal ne, domin ko lokacin da ya fara soyayya Ubaid da Alhaji ELYakub suka sani, haka da yarinyar tayi rejected dinsa, sune suka san me ya faru.
Da abin ya faru sai da yayi kusan kwanaki uku kafin ya tattara ya bar musu kasansu.
A lokacin Alhaji ELYakub yaso ya je har wurin dangin Yarinyar ya nuna musu jikanshi ba talaka ba ne, amma ya ce mishi..