← Book details Alaƙar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 86

Sashe 71

Alaƙar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nasan duk tsiya ranar Alhamis zan koma sai nake ji kamar kada na koma na ji dadin gida, a kwanakin da nake gida ne naji Ya Ado yana cewa zai mai da Abba gida an sallame shi.

Sai da suka yi kwanaki a gidan Ya Ado, domin yace ba zai mai da shi gida ba, sai ya nutsu.

Kullum muna tare ina zuwa na gaishe shi domin a daya gefen gidan ya ajiye su, na zauna ina karanta mishi karatun Alqur'ani, ranar da zan koma aiki na je dakin na zauna ina fa
in.

"Yau naji zaku tafi ni kuma zan koma aiki, Allah ya kai ku lafiya, a gaida mutanen gidan." Har na gama maganar da nake bai amsa min ba, duk dama baya wani kula ni.

Haka na fito ina jin wani irin nauyi a raina, a harabar gidan na sami Baban Jama'are da Baba Malam, sai Ya Hafiz da Rufa'i.

Sama sama na gaida iyayena maza na wuce wurin Motar Ya Ado na shiga ko Rufa'i yanzu na daina bashi fuska domin na fahimci shi yake bawa Ya Hafiz wani bayani a kaina.

Ina tsaye a wurin ina wasa da wayata.

"Luluna!" Banza nayi kamar ban ji shi ba fitowar Ya Ado ya ke ce min.

"Auta muje na sauke ko na dawo domin yau akwai inda xan je zan kuma ajiye su Abba a airport shi da Yadiko da Rufa'i, su Baba kuma xasu bi motar kasuwa.

" " Tow ba kome!" Na shiga gaban motar na zauna." Ado kun raba ni da Matata!

" Ya fada yana kallon yadda na dauke kai.

" Luluna ki dawo gare ni!" " Wanda muka yi a baya ma Allah ya yafe min!" Daga haka muka bar gidan, a hanya Ya Ado ya sake murmushi.

" Bakinki ya fara magana!" Shiru nayi ban ce kome ba.

Ya ajiye ni inda zan samu motar Garej, ina fita kuwa na samu motar minti talatin da biyar muka isa na biya tare da sauka na cigaba da tafiya a kafa.

Horn da naji a bayana, juyawa nayi na ga motar Jasminah ne, ta tsaya tare da sauke glass din ta ce min.

"Shigo!" "A'a na kusan isa fada mata ina murmushi.

" Shigo dai mu karasa!" Ta fada tana bu
e min kofar ta ciki, shiga nayi a hankali ina murmushi.

" Na gode!" Na daura jakata a cinyata.

"Kawai don oganki baya nan sai ki lafe a gida?" Murmushi nayi nace mata." Ai shi yace na zauna!" Jingina kai tayi kar muka isa cikin kamfanin a tare muka shiga na isa inda zanyi sign na wuce, " Sai yau kika gadamar zuwa?" Juyawa nayi na kalleta sannan na ce mata.

"Oga ne ya ce na zauna a gida tunda baya gari." Sai suka shiga kallon juna irin mamakin nan waye aka tab'a bashi wannan damar haka sai ni?

"Karya ne Oga ba zai tab'a baki wannan damar ba." "Stella me ya kawo wannan maganar?" Jasminah ta tambaye ta, "Ma gani nayi zata yiwa oga karya!" "Ta miki kama makaryaciya ce?" "No Ma!" Ta fada, daga haka ta ce min.

"Ki tafi office dinki!" "Tow!" Na ce na wuce abuna, ban kara tsayawa ba, ganin da gaske zan wuce sai wata take cewa.

"Me kika fi sauran mala'ikatan!" Ban kula su ba, na wuce zan hau elevator, "ya daina aiki!" Wucewa stair nayi na fara haurawa a hankali, dama ai haurawan ba sabon abu ba ne.

Ina isa office din na samu tarin aiki, na bude table tap din, na fara aiki kamar yadda na gani, na shigar da bayanai, na tura mishi office
insa, na turawa Taj da Jasminah, sai karfe biyu na samu kaina.

Yana zaune duk yan uwan babanshi sun taru ana son dalilin kwatsamawa Khamis mari da Lubnah tayi, yadda yake shan fruit hankalinsa kwance, sai da ya sha ya koshi, ya mike yana fa
in.

"Daddah ke da Dattijo ban san dalilin kiran da kuka min ba, gashi nazo babu wani bayani sai tambayar da ni dai nasan da yarinyar bata mare shi ba, sai na karya mishi hannun da ya tab'a da shi, tsalle tsallensa ya tsaya inda yake da iko idan ya shigo wurina ya tab'a min ma'aikta!" Mikewa yayi bayan ya gama daure takalminsa, ya dauki jacket dinsa ya saka yana mai kallon Uncle Auta ya ce mishi.

"Wallahi sai na kwashe mishi kayan aiki!" Daga haka ya fita abinsa bayan ya saka Black prada a idanunsa ya nufi waje.. har ya fita sai ya dawo ya ce musu.

"Yaran da kuka turo min na mai da su Office din Uncle Mudansir ina ga zasu dacewa da can!" Daga haka ya yi tafiyarshi idan kana niman hayaki fidda na koko to Bilal ya kai wannan matakin wai sun zo gaban Alhaji ELYakub amma bai hana yayi yadda yake so, kuma ba yadda suka iya.

Don ya zame musu kadangare bakin tulu a karka, a kar tulu.

A barka ka b'ata ruwa.

" Baffa kana ganin abinda yayi ko?" Mikewa Uncle Auta yayi yana fa
in.

" Me ya aikata?

Ni ban ga wani abin da yayi ba.

Ku jawa Khamis kunne ya san limit
insa." Daga haka ya juya ya fita, " ka godewa Allah da ita yarinyar tana wurin, shi din yasan darajar jini da ace bata wurin daga abinda ka yi ta fita tow wallahi inda zaka yi fitsari na sai an daura maka leda!

Kayi kazamtarka a idan aka baka dama banda inda yake karewa domin mutuncin kansa.

" Inji Ubaid, sannan ya fita daga cikin gidan.

Wa
annan mutane biyu sun yi kaurin suna wurin kare Turaki.

Karfe uku da wani abu suka shigo, bata nan bai wani damu ba.

Haka ya wuce Taj yana bin bayansa koda ya shiga office ya samu ta ajiye mishi printing din da ya da ce duk wani abinda ya dace tayi.

Cire jacket din yayi taj yana me amsa ya rataye mishi ya ce mishi." Oga na ga ta gama aikin saura ka
an ne?" Tsayawa yayi yana kallon aikin da tayi.

" Daga ina aka turo wannan abin?

" Ya d'aga wani bunch na white paper, wanda har da pin
insu tayi.

Dauka Taj yayi ya fara dubawa.

" Oh My God!

Daga office din Badr ya fito ba sakon nan ba ne?" " Kira ta" ya fada a hasale, fita yayi da sauri yana zuwa ya samu har lokacin bata dawo ba.

Shi kuwa sai cira yake ya
an zauna a gaban table
insa tare da harde hannu a kirjinsa yana kallon kofar.

Yana jin wayarshi yana ringing amma bai dauka ba, asalima dauke kai yayi yana kallon kofar.

Taj kuwa haka yayi ta bi yana nimanta, bai same ta ba sai da ya fito waje ya hangota rike da ledar abinci da kuma daya ledar kamar abu ta sayo mr muhimmanci, a hankali take takawa.

Murmushi nayi lokacin da na ga taj yana jirana, amsar ledar yayi tare da cewa.

"Me kika aikata haka?

Na bar miki kome amma kika yi shirme haka, yau Allah ka
ai zai kwace ki, domin Oga yana can yana jin rigima a ransa.

Hadiye yawu nayi na ce mishi."Me ya faru?" "Muje!" Hannu ya kai zai dauki daya ledar nayi baya da shi.

"Wannan dai!" Na fada ina murmushi, amma ni daya nasan yadda nake ji, a hankali nake tafiya saboda zuwan al'adata bazata, kuma nasan yau da gobe zan shiga wani irin tasku ne.

"Don Allah ki yi tafiya da jikinki." Kamar ance na d'ago kai, yana tsaye yana kallona, da sauri na sunkuyar da kaina ina tsoronshi sosai.

Lokacin da na shiga, cikin building na kamfanin sauran abokan aikin sai dariya suke min, ni ban kula su ba.

Haka na wuce na shiga elevator.

Lokacin da na shiga jingina bayana nayi da jikin elevator, baki
aya naji kamar xan yi amai.

Haka muka fita har zuwa kofar office dina, daga shi har ni Dan tsorace muke shi yana tashi ya shiga da ledar hannunsa, nima kuma haka na shiga da na hannuna tare da dunkule shi, kasancewar pad ne a ciki.

Ajiye ledar yayi ya dauko min takardun ya ce min.

"Mene ne wannan?" Ba tare da kome ba nace mishi.

"Sakon da ka bar min na yi printing dinsa shine nayi na turo mishi." "Ba shi bane ina wanda na baki?" "Kamar Ya?

Ban gane ba!" Na fada a hankali, ina cizon bakina.

"Na bar miki akan table
inki fa!" "Ni iya shi na gani wallahi azim ban ga kome ba sai su!" "Tow ina kika je?" Ogan ya jefa min tambayar, kaina a sunkuye nace mishi..

"abinci na je sayowa!" Na fada ina rike ledar hannuna da kyau.

"Babu a kamfanin ne?" "Bana son na kamfanin ne!" Sai a lokacin ya zuba min idanu.

Kaina a sunkuye, "ko karfe nawa zata kai i don't care daga kai har ita ku hada min aikina ina jiran ku!" Daga ya shuri takalminsa ya bar mu a office din.

Haka muka fito na kalli Taj nace mishi..

"kayi hakuri!" "Ba kome dauka aka yi domin na Ajiye miki."
Shi kuwa yana fita ganinsa ya fito babu jacket dinsa yasa yan mata dayawa binsa da idanu, ga wani tafiyar da yake ya zuba hannu a cikin aljuhun wandonsa, can tsohon office din ya nufa, yana shiga ya hadu da Badr.

Zuba mata sirrintaccen idanunsa yayi cikin wani irin tsinannen kallo me cike da tsana da b'acin ran ya ke bin ta da shi, juyawa tayi ba musu ba tare da ya ce mata bani abinda kika dauka ba, ta wuce ya tsaya a wurin ma'aikata sai gaishe shi suke yana amsawa, Alhaji Abbas da yaji labarin yana wurin ya fito da sauri.

"Yallabai shigo mana!" "I'm ok da nan!" Can sai gata nan dauke da takardun, nuna mata hanya yayi ba musu ta wuce ya cigaba da tafiya yana latsa wayarshi.

Har office dinsa, kamar yadda ta shiga ta dauka haka ta dawo da shi cike da kunya. ,harde hannunsa yayi a kirjinsa.

"Ke ina wasa da ke?" "Am sorry sir!

Ba zan kara ba ayi hakuri." Ta shiga bashi labarin.
Chapter 71 · 0% Book details