Sashe 69
Alaƙar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Auta babu ruwanka na kawo Batul ce ya bata aiki kamar yadda aka bawa kowa aik." Shiru yayi yana kallon yadda take ta hayagaga, mikewa Boss yayi ya kalle ni, da sauri na nufi wurinsa naga yana kallon duk wani abu a wurin sai da na dauka na saka mishi a jakarshi, kome sai da na tattara, sannan na raka shi waje, tare da jiransu har suka fita na ja office din na rufe ina jin suna masifa tare da bin stair domin yaki tafiya yana bakin elevator din.
Sai da na gama na riko jakarshi muka nufi elevator din tare, haka muka fito tare na kai mishi jakarshi motar, sannan na nufi main entrance na kamfanin na tafi kayi sign kafin na hada kayana, na fito a gajiye.
Motar kamfanin da aka ware na mala'ikan shi na shiga aka kai mu har inda zamu shiga motar unguwar, minti goma sha biyar na samu motar unguwar, na shiga.
Na gaji tun kafin na isa nake jin barci ina isa wanka na shiga nayi da ruwan zafi sannan nayi Alwala sallah Magariba da Isha, Abinci ma yau daki Ya ado ya kawo min yana murmushi.
"Auta yau na ganki da CEO na KUMO PROPERTIES NIGERIA AGENCY!" Murmushi nayi nace mishi" Ya Ado kafana yana ciwo na gaji sosai." " Allah ya kawo miki miji nagari yadda ba zaki jima ba kin yi aure!
Bari na kira miki su Adil su miki tausa.
" " Na gode sosai!" " Ina babu matsala a wurin aikin?" Girgiza mishi kai nayi, ya fita can sai ga Yaran don ma mun sallah isha, haka suka yi ta min tausa abincin da ban ci ba kenan barci yayi gaba da ni.
Duk yadda suka yaso ya kamata da laifi ko na wani abu sai ya lura bata da matsala, haka yasa shi kara saka idanun yadda suka yi kome ba tare da saninsa ba, haka zai ci taransu.
Bayan sallah isha ya shirya cikin kananun kaya ya nufi can family house
insu tare da Tajudeen, koda suka isa fita yayi Tajudeen ya dauki wani kwali ya bi bayanshi, har cikin gidan.
Inda ake jiranshi.
Da sallama ya shiga Daddah ta mike tana murna, rungume shi tayi tana fa
in.
"Turaki ko baki da lafiya ne?
Naga har yau baki Maganar aure?
Haka zaki cigaba da zama?" Sai a lokacin duk wunin da suka yi da yarinyar nan bai ga ta dauki waya ba, abin ya bashi mamaki tow ina Mijinta ko ta kashe wayarta ne?
To ina ruwansa?
Wannan personal life dinta ne.
A hankali ya sakarwa Daddah murmushi.
Haka suka hadu familyn baki
aya aka fara cin abinci.
"Baffa ka tambaye shi me yasa yau ya fita da mace akan aiki me muhimmanci?" Kallonshi Alhaji ELYakub yayi amma ganin kamar ko a jikinsa, ya kuma zubawa Alhaji Mudansir idanun yana son jin dalilin tambayar, amma gogan yana cin abincin a nutse kamar ba shi ake magana akan shi ba.
"Eh Baffa sabuwar dauka ce bata goge kamar Badr ba akan me zai dauke ta, sannan idan har aikin zai dauke su ba ga Mimi da Badr ko Batul ko Hanif ba?
Irin wannan aikin me muhimmanci taya za a janyo bare a cikinsa."
"Sata na samu yarinya take aka ce na danne ta, ai gara na dauki bare idan na danne ta xan bata kudi zata yi shiru da bakinta " ya kai hannunsa tare da jan baki kamar zip.
Ba yawwa ba dad'i, kallonshi suka yi tayi suna mamakin wannan bakar maganar.
"Tow Turaki me yasa baka dauke su aiki ba?" Murmushi yayi bai kara magana ba sai da Uncle Auta ya amsa.
"Basu fa turo bukatar haka ba, idan aka ce kowa alfarma za ayi mishi ai kuwa ba za'ayi aikin da ya dace ba, idan har aiki suke so su je Hamma Babba ya dauke su!"
"Wannan wacce irin magana ce!" Tauna kashi Turaki yayi da karfi sai da suka yi shiru.
"Duk me son aiki ya tura shaidar bukatar haka, babu wata alfarma kowa nima yake!" Inji Alhaji ELYakub yana kallon Turaki.
Murmushi yayi tare da gyada mishi kai, ai kuwa haka suka gama cin abincin tare da kawo korafi kamar zasu mutu amma Turaki tun maganar farko bai kara magana ba.
Haka aka tashi a taron cin abincin.
Masu aiki suka kwashe kayan da aka zuba abincin.
Haka suka dan bude hira wanda korafi ya fi yawa, amma gayen nan ko a jikinsa kusan duk bayanin da suke yiwa kakanshi shima bayan jikanshi yake bi, abin har mamaki yake basu, sai wurin tara suka bar tashi zasu tafi ya ce musu.
"Da kuke maganar mace ina gurbin Mrs Thomas ta maye?" Yadda yayi maganar baki
aya sai suka yi shiru, haka ya fita daga cikin gidan, Uncle Auta da Ubaid, shi kuma da Taj.
Haka suka nufi unguwarsu.
Bayan tafiyarshi ne suka saka Ubansu a gaba da roko har sai da ya amince da batun sauran jikokin su fara aiki a kamfanin.
Wato jiya na gaji yau ma a tsaye saye na karya, ina gamawa na shiga mota ina duba abubuwan da suka faru jiya, domin abinda Driban ya gaya min kenan ina tattara abubuwan da aka yi zai taimaka min.
Karfe bakwai da arba'in yayi min a kamfanin, Ya Ado sai dariya yake min yana fa
in.
"Da alamu boss
inki yana da zafin kai!" "Ya Ado ba zaka gane ba ne." Dariya yayi kawai, har na isa office dinsa.
A rufe dawowa kasa nayi na zauna na cigaba da zaman jira, dayawan ma'aikanta sun same ni ne a kamfanin, sai ya zamana ana ta gulma.
Karfe tara ya iso, karban jakar hannun driban nayi ina tambayarshi.
"Yau me ake da shi?" Mika min table tap din yayi, na ce mishi.
"Thank you!" Har muka shiga elevator, shi ogan yana gaba mu muna baya, office dinsa muka shiga, na ajiye jakar a kan table din na koma gefe na fara duba abinda ake da shi, babu fita akwai ganawarsa da masu saka hannun jari, yara zasu zo daga wata gidan marayu zasu gana da shi, haka nayi ta tattara kome ina sakawa a littafina, sannan ka mikawa Driban tables din.
Ya kai ya ajiye sannan muka fita da driban ya nuna min inda zasu tattauna.
Abin sha muka kawo aka jera sannan muka fito.
Wurin sha daya suka shigo bakin, ni da driban muka tarbe su har inda zasu yi meeting din, ina mai musu iso, kafin na haura sama na same shi.
"Sir sun iso!" Kallona yayi ya ce min.
"Bakya ganin ina aiki ne?" Yadda yayi maganar kamar a tafashe yake, "kayi hakuri!" Na fada ina kallon kasa haka ya gama abinda yake ya dauki top dinsa ya saka sannan ya kalli laptop din na tafi da sauri na dauka, na rufe tare da bin bayansa, kamar zan kifa haka na bishi a cikin elevator ma ina kaf-kaf da da laptop din, haka muka sauko a lokacin na ga wasu team na yan gayu sun iso kamfanin, na bi bayanshi har inda ake meeting ina Kai mishi na juyo zan fito ya ce .
"Have sit!" Juyawa nayi na kalle shi naga ba ni yake kallo ba, bakinsa yake kallo, zama nayi aia fara meeting, kallonshi nayi ta yi yadda yake magana da turanci da kuma France sai Russian haka yana nufin yaji yare, can kuma naji ya koma harshen Germany, ba sai ga bakin suna tafa mishi tare da mika mishi hannu alamar alakar ta kullu......
[12/4, 10:51
AM] Firdausi Salis: 48
Duk da sun ji dadin tarban da ake amma haka sukai ta jan da hira.. tare da da nuna mishi bukatarsu, mutumin nan dan renin hankali ne, maganar ma da kyar yake yin hayaniyar da ake yi ne yasa shi kallona, na mike zan fita daya daga cikin bakin ya kai hannunsa zai tab'a ni ya mishi magana da da Russian, da sauri ya janye hannun da sauri yana mai bashi hakuri, nima kuma yana mai bani hakuri.
Ina fita waje na samu rigima ake tsakanin driban da Yan gayun nan.
Na tambaye shi ya gaya min shiru nayi domin suna tabbatar suma suna da iko da kamfanin.
"Ok ku kira baki su tafi sai ku shiga!" "Uban waye ya baki damar gaya maka magana haka?" Inji wata yar zafin kai, komawa gefe nayi fitowa yayi da bakin take suka yi tsit kamar basu suke ihu ba, kallonmu yayi da driban muka rufa mishi baya.
Har inda motarsu take.
Sannan muka dawo dawo a hankali yake yiwa Driban magana yana gama magana muka shiga kamfanin.
"Duk sun shiga halinsu, saboda irin kallon da naga yana wulla musu sai na ji dadin haka ko ba kome shi din jarumi ne akan kome, minti goma da shigarmu ya saka aka kori Yaran zuwa daya building din.
Wurin karfe daya sai ga Yaran nan, haka suka shigo suna ta murna, ban yi mamaki ba amma kuma yadda yaran suke murnan ganinsa kamar dama can sun sanshi.
Mika min musu hannu yayi suka rungume shi.
Kallonsu nayi yadda yake hira da murna..
"Wadannan Yaran marayu ne, tun lokacin Maman oga kamfani ta sayi filin gidan marayun, suka yi ta rokon arziki a bar musu filin tow kasancewar filin yana under Christian sai ta basu, tare da cewa ita me zasu bata.
Saboda adalcin da ta musu shine suka amshi Muslunci, bayan rasuwarta Baban oga ya rike su da kula da su, haka yasa koda ya rasu shima sai aka cigaba da kula da kamfanin ko bai je ba, haka zai yi video a turo da fadar sunansu, sun sanshi sosai domin ko sabon baby aka kawo za a tura mishi ya saka mishi suna, hatta sunan gidan Marayun sunan Mahaifiyarshi ce."
Gyada kai nayi, wunin ranar akan Yaran nan muka yi shi, ni kan tafiya sallah nayi da na tafi ban dawo ba sai La'asar, tunda na dawo kallo daya yayi min bai kara magana ba.
Driban yake tambaya ta dalilin zaman da nayi nace mishi ai na tsaya Sallah la'asar ne.
Wurin cin abinci Driban ya ja ni muka tafi, shi kuma muka barshi da Yaran da suka ci nasu.