← Book details Alaƙar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 86

Sashe 26

Alaƙar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Baba ina son matata, sharrin shaidan ne wallahi ban yi haka don na cutar da ita ba."
Matsowa yayi gabana domin yanzu yasan tabbas za a raba shi da Lulu Kuma wannan zai kara hankad'o wasu abubuwan da ya aikata wanda haka yana fitowa kowa sai ya kusan tsine mishi "Luluna ki yi hakuri ki amince mu koma zamanmu!" Yadda yake roko da magiya zaka rantse ba shi ya gama cika baki idan ya sake ni sai na rasa majingina ba.

Yadda ya gigice da Babanshi ya kara daka mishi tsawa Kakanmu Baba Malam ya ce mana.

"Ku tashi ta koma dakinta."
"Gaskiya ba zata koma ba, domin yanzu haka Lubnah tana ganin likitan
walwa ne, saboda damuwar da take da shi ya shafi
walwarta kowani lokaci zata iya haukacewa!" Inji Aunty Innah, kallona kowa ya koma yi cike da mamaki sai lokacin da hawaye yake zuba min.

"Tabbas a yanzu haka ranar Monday zata ga babban likitan
walwa anan Bauchi muna saka ran idan ya ganta zai daura ta akan magani!" Inji Ya Umar,
Zare idanun Mama take zuciyarta yana wani irin bugawa.

"Wani irin likitan
walwa kuma?" Inji Yadiko, .

"Kamar yadda kika ji Yadiko zamu mai da ta ganin likitan
walwa, domin dole ta ga likita Lubnah da muka bashi ba ita ba ce wannan, idan kun kalle ta da kyau wannan bata da sake koma me yake damunta ba mu da dauka lokaci ya kure da zata kara." Ya Ado ya fada yana kallon agogon hannunsa, Baban Bauchi cikin isa irin nashi ya ce mana.

"Idan kuka kashe mata aure ba dai gidana ba, kuma zan zare ku a cikin zuriar ta." "Kai sake ta, sannan na rungume Yaran Yaya Usman a madadin nawa, wallahi idan baka sake ta ba sai na maka Allah ya isa." Cikin fushi Hajiya Asiyah ta ce mishi.

"Dalla sake ta, me za ayi da Macen da bata haihuwa me zaa yi da Macen da bata da amfani."
Cikin fa
a Yadiko ta ce mata.

"Kike fadar haka Hajiya Asiya?

Kike fadar haka Hajiya Asiya?

Rashin haihuwar waye sanadin mata haka?

Ke Lubnah waye ya kawo miki maganin hana daukar ciki?" Kaina wani irin sarawa yake, hayaniyarsu saka min kaina juyawa yake.

Kallon bakinsu nake domin motsinsa nake gani bana jin me suke cewa baki
aya.

Lumshe idanuna nayi na bude a hankali, tare da dafe kaina.

Jijiga Aunty Hindatu da nake kusa da ita tayi, na koma zan zube ta riko ni.......
*08130269641*
[12/4, 10:51
AM] Firdausi Salis: *ALA
AR ZUCI*
Ramlat Abdulrahman Manga
Mai_Dambu
*Littafin nan na kudi ne akan 1500*
*1500 ne, Nijar kuma 600 CFA 5921536136 ramlat Abdulrahman Manga Moniepoint or 0472282105 ramlat Abdulrahman Manga Gtbnk ko Nijar 98 04 67 67my Nita*
Domin tura shaida wannan number. +234 703 513 3148 ko wannan 08130269641
Posting Arewapen da Telegram
SHA BIYAR
Wannan sumar ya haifar da abubuwa dayawa, domin Mama ta tsaya a gefena tsawon wunin da nayi a gadon tana tare ni.

Tashin hankalin da Ya Hafiz ya shiga abin har ya wuce tunanin kowa.

Abu kamar wasa sai gashi lamarin ya wuce yadda ake tsammanin domin hajiya take kara jagula take al'amarin ta hanyar da aka yi wani rikici a cikin family akan aurena, sai da ta kai an rabu gida biyu wasu suna ganin kamar naki Ya Hafiz ne saboda Yan uwana sun zuga ni, Yayinda wasu suke tare da ni saboda ciwon da yake jikina suka ce ai tunda ya yarda da ya aikata ,sai gashi haka ya kawo rabuwar kuma kowa ya amince da a rabun, banda Abba da ya kafe shi da Baba Malam sai na koma.

Wasa wasa har tsawon kwanaki uku ina asibiti, yau Mama ta shirya tare da fa
in.

"Zan tafi karbo takardanki, na gaji da ganin yadda kome yake faruwa shi Babanku ya dage ni ma kuwa ina tare dake babu wanda ya isa miki dole!" Gyada kai nayi ina mai cigaba da kwanciya, nasan cewa ina cikin tashin hankali, amma a kasan zuciyata ina jin kamar ban mishi adalci ba, anya Ya Hafiz ya cancanci haka?

Bayan fitar ta sai ga Abba ya shigo, wani irin tsoro ne ya cika ni nayi baya ina zare idan, zama yayi.

Gyara zama Babanmu yayi yana kallon yadda nake zaune a wurin guda, tunda ya shigo dakin, ya ga na kurawa window din idanu.

"Lubabatu!" Ya kira sunana, a hankali na juyo ina kallonshi.

"Nasan lafiyarki lau me yasa kike bawa Yan uwanki da mijinki wahala!" Kura mishi idanu nayi ina kallonshi.

Turo kofar dakin Ya Ado da Ya Umar suka yi a tare, "me yasa kike bawa zuciyar kowa wahala?" "Baba bata da lafiya ka bar wannan maganar idan mun dawo ayi ta!" Inji Ya Umar da yake yana da zafin rai sosai.

Rike shi Ya Ado yayi yana girgiza mishi kai.

"Lubabatu Y'ata ce, akan me kuke kokarin shiga tsakaninmu?"
"Saboda ka fifita zumunci akan Rayuwarta, ka rabata da Mahaifiyarta kada tazo ta ga halin da take ciki.

Ka nisantata da kowa nata, Abba idan ka sake ta mutu a wannan yanayin Allah sai ya nuna maka iyakar...." Tass ya tsinkawa Ya Ado mari, a zuciye yayi waje." "Abba zan koma gidansa!" Juyawa yayi yana kallon yadda nake murmushi.

"No Lulu kada ki mana haka." "A'a zan koma Ya Ado, zan koma saura me ya rage a rayuwata?

Farin ciki sai dai wasu su yi, amma ni na san nayi hannun riga da shi, Ya Ado na gode sosai ka ce likita ya sallame ni kawai na koma dakina."
Hankad'o kofar aka yi da karfi Mama ce tsaye tana huci.

"Ba zaki koma ba, kin gama aurensa daga kotu muke ga takardanki."
"Salamatu" "Sai me?

Uwarshi ta kai kotu me ya rage?

Ai dama albarkacin zumunci ne zaku kashe min Y'a Uwar da tafi
arfin Mijinta zaka yi tsammanin zata bar Lubnah ta zauna ne?

An bashi kudin wanke muni me ake bukata?"
Shima kamar wanda aka wurgo shi ya ce mana.

"Wallahi ban sake ta ba."
"Kotu ta sake ta!" Inji Mama tana kara kallonshi.

"Kaci albarkacin Ubanka, da sai na saka an maka abinda baka zata ba, Lubabatu kuwa ta haramta maka.

Adamu kasan yadda zaku yi da ita zaman Bauchi ya kare kuma ka kuma kusantar inda Lubabatu take sai na saka an wulakanta min kai, idan kana jin rashin kunya da fitsara wannan cikin ta haifa min, lauya, magatakarda, Soja, da sojar kasa da na sama sun fika kwaya da tijara ahir dinka."
"Wallahi ban sake ta ba, ina son Matata kuma babu wanda!

Ya isa raba ni da ita Baban Bauchi kana gani sun raba ni da Matata!" Ya dawo gabana ya ce min.

"Luluna kina ganin sun raba mu?

Luluna ki ce wani abu, ni ne Ya Hafiz dinki.

Dube ni ni ne Hafiz
inki!" A hankali na zare hannuna a cikin nashi, zuciyata tana wani irin bugawa na ce mishi.

"Alhamdulillahi Ubangiji da ka samar min yanci!

Ka je na yafe maka kai da Karimcy ka je na bar muku kome na cikin gidan hatta suturata na yafe, Alhamdulillahi Ubangiji na gode maka!" Sai a lokacin na samu damar fashewa da kuka.

Kuka nake da dukkan zuciyata.

Cikin irin haukar da ya saba ya ce min.

"Idan baki dawo gare ni ba.

Wallahi haka zaki kare rayuwraki babu namijin da ya isa kallonki!" Cikin fushi Mama ta ce mishi.

"Ai kai ba Allah ba ne muna nan zaka ga tayi aure kuwa wallahi sai tayi, ka fita kafin na kira a ci mutuncinka." "Lubnah ki dawo?

Wallahi ki dawo ko kuma kina ji kina gani ki kare rayuwarki a wulakance!

" Dariya Mama tayi tana fa
in.

" Alhaji ka ji abinda danka yake fa
a?

Ka ji yadda yake ihu bari na nuna mishi nima ina da fitsararru irinsa, ta leko waje tana fa
in.

"Kai Adamu zo kayi min waje da wannan
an iskan ka nuna mishi yadda ake rashin kunya!" Ba Ya Ado ba baki
aya Yayuna maza suka yo dakin wani irin daukar amarya suka mishi, zuwa waje suka ajiye shi..

"idan ka sake zuwa inda Lubnah take gara ka kira kanka gawa domin sai munci Ubanka shege mara kunya dan iska!"
Suka kore shi sannan suka dawo a lokacin Abba ya mike tsaye, kin yi yadda kike so da Yaranki ku je na sallame ku ke da ita Yar so dinku!" " Alhamdulillahi Masha Allah, na gode katuro min takardar da wuri domin ina gama idda zan yi aure in sha Allah!

" Ashe maza ma na da kishi, cak Abba ya tsaya ya ce mata.

" Uban waye ya ce zaki yi aure a shekarunki nan?

" " Allah mana ya ce nayi koda ta dauki kwarinka!

" " Kai Adamu ka gaya mata wallahi na dawo da ita kuma kada ta wuce yau bata koma dakinta ba, ita kuma kanwarku ba dai gidana ba.

" Yadda Abba ya nuna baya bukatar ganina yasa min wani irin kunci, a hankali Mama ta d'ago hannu zata tab'a ni nayi maza na kare kaina, tare da cewa.

"Don Allah ki yi hakuri!" Sake baki kowa na dakin yayi suna kallona har shi Abba da bai fita ba, juyowa yayi yana kallon yadda na kare fuskana.

"Lubnah meke damunki!

" Inji Ya Ado da ya tako gabana, " babu!

" Na furta a hankali ina kallon Mama da itama mamaki ya kusan kashe ta.

" Hafiz yana dukanki ne?" Rufe bakina nayi ina kallon Abba.

" Gaya min dukarki yake yi?" Fadawa jikin Mama nayi na rufe idanuna, sake magana yayi ma kame-kame Mama ina ajiyar zuciya.

" Wai a haka za a mai da ta wurinsa!

Umar muje Bauchi a mai da ita asibiti she need treatment domin basu yadda ya dauka yana azabtar da ita ba.

"
Kiransu Aunty Innah da Hindatu aka yi aka ce zaa koma Bauchi saboda mota daya aka dauko, a ranar aka bar Jama'aren, karfe tara na dare muka isa Bauchi, kai tsaya asibiti aka wuce da ni.
Chapter 26 · 0% Book details