← Book details Alaƙar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 86

Sashe 13

Alaƙar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abin da basu sani ba ita Jalilah Ya Hafiz take so kamar tayi hauka, duk aurenta uku da tayi ta kasa zama a gidan aurenta ne domin tana da yakinin wata rana ya Hafiz xai dawo gare ta.

Haka abin ya cigaba da tafiya ba dad'i, a lokacin Ya Hafiz ya tsiro da wani hali shi da Matarshi.

Abinda suke mun ba kome ba ne, sai nuna min da suke ni rayuwata bata da amfani, domin ido da ido ya ce min.

"Lubnah baki da amfani a rayuwata, amfaninki kalilan ne, idan aka cire amfanin rashin amfanin yafi yawa, kin ga wallahi ko bukatarki na dabi'ar da namiji bana ji, ke kanka dube ki, yanzu ace na sake ki waye zai aure ki?

Wallahi babu namijin da zai tab'a sha'awar aurenki domin baki da wani abin burgewa mace sai kace saniyar hu
a!

" Ire-iren wa
annan maganar da yake gaya min ya haifa min da wani irin yanayi.

Yana yawan gaya min cewa a yanzu dangi ma basu bukata na, babu wanda ya damu da ni, itama Hindatu don kudina da yake hannunta ne, idan babu ba zata kara kula ni ba,haka muka cigaba da jin kamar ba ni da wata amfani a rayuwar Ya Hafiz.

Tunda ban haihu da shi ba, bani da wani abun da zai burge kowa.

Ni kaina nasan be zama dole wani ya bukaci ni a rayuwarsa ba.

A hankali na dinga jin kamar ni din ba kowa ba ce bani da sauran amfani.

A haka watan azumi ya karato, ba zata Baba yayi mana, ya biya mana umara ni da Yayuna.

Sai dai me?

Ya Hafiz najin haka yayi ta kunci da bakin rai tare da rigima da fitina kala-kala, karshe dai ban san yadda aka kare ba Baba ya ce ya cire sunana a cikin masu tafiya yayi replace da Jalilah.

Wani irin bugawa zuciyata tayi kamar zata fito, a hankali na kama dariya ina jin kamar ni daya ce bani da amfani a duniyar nan, haka watan azumin nan suka yi shi a can ni ina gida, a lokacin na kara koyan yadda xan bawa kaina nishadi.

Sai na fara tunanin sana'a bayan sallah, wanda shima a wunin sallah ya ce ba zan je ba.

A Jama'are zamu yi sallah, nan ma na amince muka tafi.

Muna dawowa nazo da madaran kuka.

Na fara sayar da kankara da Pure water, ta nan bai hana ni ba.

Sai dai ya daina bani kudin cefane.

A hankali na kara har da zobo da kunun aya da fresh milk.

Haka su Aunty Hindatu da Aunty Innah suka zo min gidan, wuni da Yaransu nayi ta hidima gashi bana iya zama idan nayi baki abu ba abu ba sai dariya.

Haka suka yi ta kuka a daki, wunin da basu yi ba kenan.

Wani abin da na fahimta shine Ubangiji ya saka albarka a kayan ruwa, domin lokacin sallah layya, nayi ciniki har na ji tsoro, ana kawo min ruwan pure water har gida ake sauke min rabin mota, a lokacin da Ya Umar yazo gidan ya dauke karamin firji din a ranar aka kawo min babba deep freezer, wnada nake zuba jakan pure water ashirin ga kayan sanyina a gefe.

Yadda kudi suke shiga da fita yasa Ya Hafiz ya fara tashin hankali na fara kudi xan rena shi, idan nayi abinci bana saka nama a wadace ai da can ba haka nake ba, nayi ta bashi hakuri ashe zai zare min tallafi da yake ne, domin ya daina kawo abinci gidan.

Haka dai na kara tsayawa a tsaye sai Allah ya yaye mun dariyar da nake, sai dai duk niman da nake ina bawa Ya Hafiz ne domin bayan na cefane da nake yi kudin kusan shi nake bawa.

Maman Na'ilah ita ce ta tambaye ni aron kudi, na ji tsoro ban iya bata ba.

Karshe kamar wacce ta matse ni na gaya mata ai kudin wurinsa yake, zuba min idanun tayi kafin ta ce min.

"Lubnah da hankalinki kuwa?" Shiru nayi kafin ta cigaba da cewa..

"wacce irin soyayya kike yiwa mijin nan naki ne?

Kin san mun san kece kike dauke da hidimar gidan?" "Ba kome ai dan uwana ne." "Na ji ba wannan ba, daga yau zaki na kawo dubu uku akwai adashe da muke yi zaki shiga ai zaman tare ta wuce haka, ga yayarki nan wata siririya muna haduwa a asibiti ba karamin taimako take min ba, don Allah ki na kawo kudin!

" " In sha Allah!" Na fada tun daga ranar ban yarda na kai mata ba, domin kamar wanda aka gayawa Ya Hafiz, kullum sai ya kirga abinda nayi yasan na kudin da yake ciki, idan ya dawo zai tambaye ni.

Haka zan dauki kudin cinikin na bashi na mishi lissafin abinda aka kashe, ita Matarshi bata kome ni ce dai akansu, haka dai muka ta mikewa abin ba dad'i, kwatsam aka tashi wani biki, Aunty Innah ta kawo min aikin Kunun aya da zobo, domin suma ina bayarwa a kai musu har gida, a lokacin aikin zai min yawa na shiga gidansu Maman Na'ilah na roka su zo su tayani.

Haka muka yi aikin dasu.

Sannan ka zo aka dauka, washi gari muka sake yi sai da muka yi kwanaki uku muna aikin kafin aka kawo mana kudin aikin naira dubu hamsin, na dauki 20k na basu talatin, Maman da tazo ta kwace ashirin din ta tafi da shi, ban san me yasa matar nan take min karan tsaye ba, amma naji haushi, wasa wasa sai ga Mamansu Na'ima ta saka ni a gaba da amsar kudina ko ina so ko bana so zata dauka, haka muka yi ta fama da ita daga baya da kaina nake tura mata kudin ma, ta daina zuwa.

Ban san manufarta ba amma tabbas ta wani gefen tayi min abinda jinina suka gaza min.

Haka watan azumi ya kara zuwa, ita ta bani shawarar na ajiye kayan za
i na koma sayar da
ara.

Ba sai ya Hafiz yayi tsaye ya ce bai yarda ba.

Sai dai idan zan sayi generator, na ce mishi.

"Ya Hafiz tow ka ba Ni a cikin kudin wurinka mana!" Ai kamar ya rufe ni da duka.

"Ba zan bayar bada wutar gidana kike amfani." A lokacin na rasa yadda xan yi ina jin kunyar amsar kudin wurin Maman Na'ilah, sai na kira Ya Sani na tambaye shi nawa ne kudin generator?

Tunda sune suke sayarwa.

Ashe nayi wayar a kusa da Ya Albashir, sai cewa yayi me zanyi da shi?

Na gaya mishi gaskiya washi gari sai ga Mikano daidai da zata dauki freeze na har da karin freeza.

Nayi ta godiya aka turo masu aiki suka min aikin tsaf na sauka akan wutar gidan Ya Hafiz shima dai ai yana morar generator tunda kowa yasan watan azumi a lokacin nepa suka tadda iskancinsu, ga lokacin ana wani irin agazarin rana.

Duk yadda xan fada farin cikin da nake ciki, kamar na boye ne.

Ganin duk yadda zai
ullo min ina toshe hanyar don bana son muna rigima, ba sai ya tsiro da fitinar cewa sai dai na kama haya dakin da nake ina biyan kudin wata wata da ruwan da nake tarawa a wajen shima ina biya.

Haka na amince na ce nawa xan biya?

" " Duk wata dubu goma!

" Shiru nayi kafin na ce mishi.." tow Ya Hafiz ba ragi ne?

" " Sai dai ku fitar min da kayanki a gidana!" " Shi kenan!

" Haka na amince ai ba wani abu ne, haka nayi ta niman kudi ya Hafiz yana amsa da sunan nashi, da sallah yayi nayi musu
inkin sallah don ya ce min hakkina ne nayi musu tunda ai ina samu, nayi mishi nayiwa Yaranshi da matarshi da Yan'uwansa na tura har Jama'are aka kai musu, har da Baban Jama'are nayiwa Baba Malam ne ko da wasa ban mishi ba, ai kuwa na sha zagi ya kira Baba ya gaya mishi, Hafiz ya bani kudi nayi musu kayan sallah amma naki, haka Ya Hafiz ya fada.

Sannan ya kara da cewa har su Mama da Yadiko nayiwa, amma a ku
ina a lokacin sai da na kwashe kome nawa na sayar har da dan kunnen gwal dina, tow bani da kudin ina sana'a kudin na hannunsa.

Bayan sallah ina cikin azumi sitta shawal, na fara sauraron karatun Malam Albani Zaria, akan khulu'i wanda ban tab'a jin kalmar ba sai yau.

Ba dai na kara nutsuwa ina sauraren dalilan da suke kawowa ayi shi..
*08130269641*
[12/4, 10:51
AM] Firdausi Salis: *ALA
AR ZUCI*
Ramlat Abdulrahman Manga
Mai_Dambu
PAID BOOK
TAKWAS
Wato akwai wani abinda hankalinmu baya kai sai wani dalili mai girma ya shato shi cikin rayuwarmu, ban tab'a nazari akan khulu'i ba, amma kuma me yasa na damu?

Me yasa nake son sani akanshi?

Kawai sai naji abin bai min na cigaba da nazari akai ba, kawai zan cigaba da zama da fahimtar iyayena.

A bangaren Ya Hafiz kuwa nadan wata rana zai dawo yadda muke zai kaunace ni sama da baya, amma kuwa zai yi haka.

Bayan sallah da sati uku.

Weekend
Ina aikin hada zobo na dauke tukunyar fresh milk, koda yake ya jima da na sauke amma da yake yana da wuyar sha'anin, sai na ta saka idanun akanshi saboda Yaran nan da zarar na sauke tukunyar fresh milk sun ta kara kaina akai kenan, har sai na hada na basu.

Hankalina yana kan zobo wanda nake ta saurin ha
awa.

Sai naji an tab'a murfin tukunyar, da sauri na juya Yusrah ce rike da kofi ta bude tukunyar fresh milk din zata har ta saka kofin ta dibo da yake na juya mata baya, a matu
ar razane na kalle ta ina fa
in.

"Gaskiya Yusrah bakya jin magana maza rufe min ki mai da kafin na zo wurin." "Ba zan mai da ba." Ta fada tana kallon cikin kwayar idanuna, abin da ya bani haushi da takaici yanzu ta kone Iyayenta su ce na konata.
Chapter 13 · 0% Book details