← Book details Alaƙar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 86

Sashe 29

Alaƙar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da na ji labarin na tausaya mishi amma idan na tuna yadda yaso kashe ni sai naji shi ba abin tausayi ba ne da ya samu wuri kashe ni zai yi da kwanaki na, gara da Allah ya yakin ce min shi da an barni da halina tabbas da na mutu.

Kwatsam ina zaune Aunty Innah ta nima min aikin koyarwa, wai ko dai rage min zaman da nake na kadaici, matata kuwa da Ya Hafiz ya rike sun karba aka sayar aka sauya min wata yar karama mai kyau, haka na fara zuwa aiki da ita.

Bana shiga rayuwar kowa bana iya d'ago kai kalli mutum, asalima maza tsoro suke bani domin kallon Ya Hafiz nake su.

Malamai mata ma sama-sama muke gaisawa.

Haka na cigaba da aikina yaran bani da matsala da su, musamman da suke
anana.

Ina koya musu math, yadda na samu nutsuwa a yar wannan lokacin yasa hatta Yaran sun san bana son tashin hankali.

Bana son magana bana son hayaniya.

Sai Allah ya bani sa'a akansu yadda ko tari basu min nima da na fahimci sun fahimci halina, sai nake saya musu yar choco-choco ina bawa masu
arin cikinsu, ina son Yara ina son ganinsu cikin farin ciki da walwala.

Haka yasa yaran idan na shiga ajin sai su yi shiru kafin su mike su gaishe ni, sai na musu alama da da hannu suke zama na cigaba da musu karatu, kasancewar makarantar private ne sai Allah ya taimaka duk ranar Alhamis ina fita da su, PE physical education, saboda Yarar juma'a manya ke fita.

Yau da ya kasance Alhamis na isa Makarantar da wuri, nayi parking sannan na wuce staff office nayi sign sannan na nufi hanyar aji sai ga daya daga cikin malaman makaranta ya ce min.

"Mrs Jama'are kina headmistress tana kiranki!" "Ok na gode!" Na juya na wuce office din, ina shiga da sallama idanuna ya fad'a cikin na......
*08130269641*
[12/4, 10:51
AM] Firdausi Salis: *ALA
AR ZUCI*
Ramlat Abdulrahman Manga
Mai_Dambu
*Littafin nan na kudi ne akan 1500*
*1500 ne, Nijar kuma 600 CFA 5921536136 ramlat Abdulrahman Manga Moniepoint or 0472282105 ramlat Abdulrahman Manga Gtbnk ko Nijar 98 04 67 67my Nita*
Domin tura shaida wannan number. +234 703 513 3148 ko wannan 08130269641
Posting Arewapen da Telegram
*Last Free pages*
SHA BAKWAI
Wani irin faduwa gabana yayi wnada ya saka ni ji kamar na juya da gudu, me ya kawo Ya Hafiz inda nake aiki?

Me ya kawo shi?

Abinda zuciyata take ta tambayata kenan jikina yana rawa a hankali.

"Shigo mana Malama Lubnah!" Ya fada yana murmushi, wani irin kuka ne yaso min, na shigo ina gaida headmistress, "Auta kin tashi lafiya!" Kasa nayi da kaina ina fa
in.

"Alhamdulillahi Aunty Barakah." "Masha Allah, ga sabin dalibai ne aka kawo miki sai kuma Malam Hafiz yace yana son yasan Malamar domin dai fada mata yadda zata kula da Yaran " "tow!" Na fada muryana yana rawa.

"Yawwa Madam na gode, ga Yaran Aliyu Hafiz Aliyu Jama'are, Asiyah Hafiz Aliyu Jama'are ." "A'a tsaya ba sai kai ne Ex dinta!" Inji Headmistress, murmushi yayi irin wanda ya saba yaudarar mutane da shi, ya ce mata.

"Madam ba wani Ex raba mu Dole suka yi amma nasan Luluna tana sona!" "Aunty Barakah zan tafi Class idan ya gama ya kaai yaran!" Na aro jarumta nayi waje kafin ta samu damar sake wani Magana, ina tafiya amma bani da nutsuwa duk wnada ta ganni musamman yadda nake kallon office din Aunty Barakah zaka fahimci a tsorace nake, haka na isa ajin yaran suka gaishe ni na amsa tare da zama ina sauke numfashi, daya daga cikin Yaran da suke me suna Munir ya kawo min ruwa da gudu, ya mika min.

Murmushi nayi na nuna mishi nawa, murmushi yayi na ce mishi.

"Je ka zauna na gode!" Komawa yayi ya zauna na fara kiran sunansu, ina cikin kiran Ya Hafiz ya iso class din, tare da Yaransa ni dai ban d'ago kai na kalle shi ba, haka na cigaba da aikina ina kiran sunan Yaran.

Yadda yazo ya min rumfa a kaina ya janyo min wani irin tashin hankali da tsoro uwa Uba jikina wani irin rawa yake.

"Luluna, nayi kewarki ina bukatarki sosai ina jin kewar kome naki, ina jin kewar can
asarki me jekewa jabga!" Wani irin mikewa nayi jikina yana wani irin rawa.

Na fara ja da baya, yana takowa har sai da ya kure ni a bangon.

" Ki dawo ko kuma na saka miki abinda zai saka ki dawo dole!" Yadda yayi magana yasa ni durkusawa a wurin tare da toshe kunnena.

A tsorace hawaye na zuba min ashe ina murna na rabu da shi ashe zai dawo innalillahi wainnalihir rajoun, Ya Allah me nayi da zafi haka, fita yayi ya bar Yaran suna ta min dariya, ni dai ban kula ba bayan fitarsu na ji kaina yana amsawa da dariyarsu, daurewa nayi na fara koyarwa a lokacin Yaron nan ya fara kuka, wato Yasir, kuka irin me d'aga hankali sai ji nayi kaina kamar zai fita shi dai a kai shi Yusrah.

Ranar Yaron nan da ya saka ni a gaba da kuka, sai da naji kamar zan yi hauka.

Haka ya Hafiz yake zuwa yayi ta min rashin mutunci, idan ta kama kamar dai rufe ni da duka a gaban jama'a, da yake gaya musu ya mayar da ni, yan uwana suka zuga ni, a hankali sai damuwar da na rabu da ita ya fara dawowa, na kasa fadawa kowa domin ya tabbatar min duk ranar da aka kira shi aka mishi magana wallahi zai dauke ni a nime ni a rasa wannan yasa Ya Hafiz ya sake dawowa Rayuwata, kamar zan yi hauka rashin mutunci sai wanda ya karu.

A hankali na fara kin zuwa aikin sai dai na kwanta idan kuma zan fita zan tafi wurin Aunty Hindatu ko aunty Innah, idan suka tambaye ni me yasa ban tafi aiki na sai naki basu amsar tambayoyinsu.

Ranar dai Headmistress ta kira Aunty Innah tace kusan sati biyu ban zo makaranta ba, Aunty Innah tayi ta fada ta kira Ya Ado ta gaya mishi, kai tsaye ya ce mata.

"Lubnah ba zata ki zuwa makarantar ba, akwai wani abu da yake faruwa.

Ta je zan tura Sani ya bi bayanta ya kuma yi min bincike idan da wani abu ya gaya min."
Haka ta kira ni ta ce na shirya na tafi, kuka ne ya zo min tsoro da fargaba ya cika ni, domin kullum sai kira ni da barazanar sai ya dauke ni ko ya kashe ni kowa ya rasa, tunda naki na zo makarantar.

Haka yasa na shirya ina kuka na tafi, ina isa wurin parking na fita daga motar sai gashi, yadda ya juyar da ni yayi ta kifa min mari, Malamai maza suka zo ya daka musu tsawa tare da kwatar key motar ya bude zai saka ni, Ya Sani ya rufe shi da duka, wani irin dambe suka kama yi, na shiga motar na rufe kaina ina kerma.

Dole Headmistress ta kira Aunty Innah tare da gaya mata abinda yake faruwa, ita kuma ta kira Ya Umar daga muda lawan suka nufo makaranta lokacin an samu an raba fadar da kyar, Ya Sani yana fa
in.

"Kai uban waye ya tsaya maka a Bauchi shege bagidaje, ka kuma taba Lubabatu sai na karya maka hannu."
"Wallahi idan ina raye Lubnah ba zata tab'a samun peace of mind ba, matu
ar ina numfashi, sai dai ta ga wasu mazan da idanu, amma wallahi babu namijin da ya isa samunta, gara ta kare rayuwarta a matsayin karuwa!" Zuwan Ya Umar da Yan sanda yasa aka kama ya Hafiz ni kuwa Aunty Hindatu tana zuwa a hankali na saka kafa na fito, wani duhu ne ya lullube min ganina, a wurin na zube sumammiya.

Daga nan ban kara sanin me ya faru ba, sai bayan wani lokaci, na farka na ga Yadiko tana zaune suna hira.

"Yar iska munafuka ta koma wurin Uwarta ban isa ba, ni ina nan ina tausayin Jalilah ashe ita ta gaya masa har inda Lubnah take, kai hatta number Lubnah munafuka ita ta bashi, nayi mamakin ashe duk abinda yayi ta faruwa tana sane da ita Hafiz yake hada baki a cutar da ita me Lubnah tayi mata?

Ai Sani ya so zane ta, na ce ya kyale ta ta ji Allah zai mata sakayya mene ne a cikin duniyar wanda Lubnah bata gani ba, Allah yasa haka ne mafi alkhairi, zaman Bauchi ya kare itama Lubnan ta bar Bauchi hala wani arzikin ne yake nimanta!" Inji Yadiko tana fada kallon yadda na tashi a hankali, ina kuma zan tafi?

Na gaji na gaji da rayuwar da nake ji nake kamar rayuwata tafi bu
atar mutuwa da wannan rayuwar, na rasa yadda zan yi da kome baya min dadi, sai da nayi alwala na fito na gabatar da sallah azhar da asar, ina idarwa Yadiko ta tura min abinci, kallon abincin nake ina kallonshi kamar naga sabon abu, haka nayi ta kallon abincin.

"Ci abinci Auta!" Haka na dauki cokalin na dibi jollop din macaroni na kai bakina, ina ci hawaye na zuba min.

"Ba zan hana ki kuka ba, domin lokacin da kika so fahimce ki mun kasa fahimtar ki, yanzu kuwa da muka fahimce ki ba zamu hana ki kuka ba." Haka yasa na dan ture abincin na cigaba da kukana, shigowar Ya Tahir yana waya.

" Yawwa gata ta farka bari na bata.

" Mika min wayar yayi, na dauka ina shashekar kuka.

" Lulu" " bana son sunan nan" na fada a sanyayye.

" Lily fa!

" Sauke kukan nayi a hankali na ce mishi" Ya Ado!" " Na saka Innah su hada miki kayanki, in sha Allah zan miki booking flight nan da yan kwanaki, am sorry bana nan amma nasan Attahiru da Umar da Sani sun yi duk abinda zan yi, Lily i promise you in sha Allah daga lokacin da kika dawo wurina ba zaa ki sake samun wani threat daga wani ko ayi bullied dinki ba zan tab'a bari ba.
Chapter 29 · 0% Book details