← Book details Alaƙar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 86

Sashe 18

Alaƙar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ki yi hakuri kin ji kome zai wuce wata rana zaki ga kamar mafarki ne kin ji ko?" Murmushi nayi mata nace mata.."Nagode!" Haka ta mana sallama ta tafi, wurin karfe takwas sai ga Mama da Abba, tsoron ganinsu yasa na rikice ina mai niman hanyar da zan gudu ban daki, amma ba hali shigowar Ya Ado da yaga yadda jikina yake kerma ya zo inda make ya zauna tare da kwantar da kaina a kafad'arshi.

"Shiiiiii!" Yake furtawa a hankali, yana matse hannuna rintsa idanuna nayi hawaye na zuba min, a hankali a kafad'arshi.

"Tow Yar gata, yar kwai ko nace yar gwal!" "Hajiya Shehu idan kana son tayi aman
walwarta sai ka gyara wuri ka zauna domin ina ga haka ya dace da ku kai da Yaya Salamatu;" jin haka yasa shi kallon Umma ya ce mata.

"Aminatu amma kin san abinda tayi bai dace ba?" "Ai rashin dacewar yasa zance maka kai ka tab'a tambayarta me yake faruwa a rayuwar aurenta?

Yanzu yar gurin kishiyata da muka aurar bariya a lokacin
a ina cewa saboda ita na fari ce uwar ta watsar da batunda mijin nan yayi ta cutarta ba a sani ba karshe sai da ya dauko mata lalura yarinyar nan ta rasu a wurin haihuwa bayan ciwo ya cinye ta ita da abin cikin ina lokacin da yar take kawo karar koranta muke?

Sauyin Lubnah yayi yawa.

Shirunta cuta ce ga rayuwarta ko ku shiga lamarin ko kuma muna nan daku zaayi kukan mutuwarta.

Da yake Allah ya bata wani mugun jiki ne da baya bayyana tashin hankali da wata ce ta kare tas sai kashi da hakora rakwacan!

" Kasancewar Umma Aminatu abokiyar wasarshi ce ita kanta Mama Abokiyar wasan Abba ne domin su Ya'yan mace, shi kuma
an namiji.

Haka yasa ta hana shi magana kuma akwai mutuntawa a tsakaninsu domin Mijinta da ya rasu aminin Abba ne, cikin nuna damuwa ta ce mishi.

"Nasan da Madaki yana raye da shi zai dauki lamarin Lubnah da muhimmanci, gaskiya abin ba dad'i duk da har yau bata ce mana uffan ba, shiru idan yayi shiru mace idan ta tashi mutuwa aman jini take yi saboda lokacin da ya dace tayi magana an rufe mata bakinta." Ambaton Madaki yasa Abba ya juya yana fa
in." Kai anan zaka lalace ba zaka koma aikinka ba!" "Zan koma ina son na ga yadda al'amarin zai kasance ne!" Juyawa Abba yayi ya zuba masa idanu kafin ya harare shi.

"Kada ka sake ka lalata mata aure domin ba zan dauki haka a matsayin kuskure ba." Shi dai bai ce kome ba har ya janye ni a jikinsa ya rako Abba da yake Mama zata zauna da ni.

Har ya dawo ya samu ina karyawa, ban yi magana ba, amsar nashi abun karyawa yayi yana waya da Aunty Zakiya har da mika min na gaishe ta daga haka nayi shiru na cigaba da karyawa.

Mama ta fara magana a hankali.

"Shi rayuwar aure dan hakuri ne." "Ai kuwa idan irin na Lubnah ne kabari ne wurin zamanta kawai domin daga alamu kun fifita zumuncin uban yaron akan Yarku!" Jin haka Mama ta rufe Umma da Fada itama Umma ta hau sama suka rikito ashe itama yar bala'i ce, daukar airbon din nayi na saka a kunne na, na fara
arin kunna karatun Alkur'ani, sannan ba kure karar, yadda ba zan tab'a jin muryansu ba.

Haka ce ta faru kuwa, sai abin ya zo min da sauki har suka gama hayaniyarsu ban san me ya faru ba don Ya Ado yana gefena har barci ya dauke ni.

Gyara min kwanciya yayi, bai kashe karatun ba ya cigaba da yi.

Karfe daya na rana na farko a lokacin wai Mama ta tafi da na tambayi Umma Aminatu sai tabe baki tayi wai tana fa
in..

"taga ni da lauya munki bin bayan shegen Yaron nan shine ta yi zuciya Allah yasa ta daka da kafa har Dutsen tanshi idan tana da zuciya." Wanka nayi nazo na gabatar da sallah, ina addu'a Ya Hafiz da Baba Malam suna shigowa, wani irin bugawa kirjina yayi wanda ban san lokacin da hawaye ya zubo min ba.

Gaishe Baba Malam Umma Aminatu tayi tana kallon Hafiz da yake kallona cikin jin dadi.

"Kaso daga gidanka a wuce da ita dungulbi ko?" Take ya gyara fuskarshi yana kallon Baba Malam..

"yanzu ba wannan ba yaushe da a sallame ta ne ta koma dakinta.

Na kashe wannan maganar domin na samu Usmanun na gaya mishi na kashe zancen nan har abada a bashi matarsa Allah ya taya shi riko!

"
Kaina a kasa har aka turo kofar yana kara jaddadawa an kashe maganar, Ya Umar ya ce mishi.

" Magana dai bata mutu ba, sai yq gaya mana inda ya kai mata da duk abinda ta mallaka.

" " Umaru ina magana kana magana da nuna min abinda na isa da shi!"
Gyara tsayuwa Ya Hafiz yayi yana kallona, kafin ya ce musu.

" Gata nan ku tambaye ta yadda tayi da dukiyarta?

Har shaidu ina da shi, yarinyar nan Alhaji nayi hakuri da ita yarinyar da ta bada jinginar gidanta kawai don a bata kwaya ta sha, meye ne ban mata ba?

Kayan sawanta ta ha
a ta sayar kome nata ta sayar wallahi na rantse da wanda rayuwata take hannunsa yarinyar nan ba karamin bashi ta cillani ba, Alhaji kasan yadda nake kaunar Lubnah amma ni yanzu idan yan uwanta suka ce ba zata zauna da ni ba, zan iya hakura da ita ba gaji!

" Yadda na kafe ya Hafiz da idanun yasa ji wani abu me daci ya cika min wuyana.

Ban san yadda aka yi duk soyayyar da nake yiwa Ya Hazif ya dawo kiyayya ba, shin dama ba soyayya ba ce to idan ba soyayya ba ce mece ce nayi mishi?

A sanina dai na kaunace shi, nayi mishi biyayya na wulakanta kaina na boye ka
an daga cikin miyagun halayenshi, kura mishi idanu nayi ban iya magana ba, haka akayi ta rikici ni dai har lokacin ban ce kome ba, kuma bana son na ce kome, haka suka tafi ashe bayan barin asibitin babban rigima aka yi da Baba Malam wanda ya tilasta Abba cewa daga asibiti idan aka sallame ni a wuce da ni gidan Mijina.

Ba zan mutu ba sai naga karshen Ya Hafiz haka yasa koda na warke aka sallame ni ban cewa kome daga abinda yake faruwa ba, haka suka yi ta bina akan na musamman abinda ya fada karya ne nace musu A'a ai gaskiya ya fa
a, wannan abin da nayi ya fusata yan uwana, haka suka mai da ni dakina, tunda na fahimci an gyara min dakin an saka min sabin kayan dakin, sai na tsaya a kaina da zuciyata dole na kwaci kaina a hannun Ya Hafiz, amma ta ya?

Shine ta hanyar shigar da shi kotu amma kuma idan na kai zancen kotu ya familyna zasu dauki al'amarin, sai na kara jin na shiga wani irin damuwa mai danne zuciya.

Hankalina yayi azabar tashi.

Bani da hanyar da zan iya yakince Ya Hafiz a rayuwata sai na ji bani da wani kwarin gwiwa, tunda na dawo kuwa iskanci da cin zarafi sai da yafi na baya, gori kuwa ina shan shi, tun ina dauke kai har ta kai da idan na rama sai ya dake ni, haka yasa na kara shiga wani irin kuncin rayuwa, domin kuwa Ya Hafiz ya saka Abba haramtawa kowa zuwa inda nake, haka yasa babu wnada ya san halin da nake ciki, sau biyu ina faduwa a ban daki.

Haka zan farka na ganni dauke da karin ruwa.

Faduwar da nayi na biyu ranar Maman Boy ta shigo ta ga na fadi suka kama ni suka kai ni daki, suka yi ta min fifita dama ya dake ni kenan ya fita shine na fadi, itama Karimah ta fita abinta.

"Har ga Allah lokaci yayi da zaki samawa kanki Yanci idan kika kai shi kotu kudin wanke muni zaki biya!" Shiru nayi ina nazarin maganar, bayan fitarsu.

Ina kwance na kira Ya Ado.

"Ya Ado!" Amsa min yayi kafin ya ce min..

"na'am Auta!"
"Ya Ado idan nace zan rabu da Ya Hafiz Abba zai hana ni wurin zama!" "Are You ready!"
*Wannan littafin na kudi ne*
*08130269641*
[12/4, 10:51
AM] Firdausi Salis: *ALA
AR ZUCI*
Ramlat Abdulrahman Manga
Mai_Dambu
SHA
AYA.

Kamar yana gabana na gyad'a kai ina jan hancina.

"Lubabatu kin shirya rabuwa da Hafiz ko baki shirya ba?" Sai na ji tambayar ya zo min a wani irin rude, ban san lokacin da na fashe da kuka ba, na rasa meke min dad'i shin mai yayi zafi da zan kashe auren.

" Abba zai kore ni!" Ina jin yadda ya sauke numfashi ya ce min.

" You're not ready!" Ya kashe wayar.

Haka na cigaba da kuka na rasa yadda zan saka kaina, haka na wuni suku-suku har dare yayi ban daura abinci ba, ko da Ya Hafiz ya dawo ganin babu alamar na daura aninci sai bai ce kome ba, ya fita ya sayo abinci ni kuma ko kallo bai ishe ni ba, ina da sauran kayan tea shi na sha na kwanta.

Tun daga lokacin wani irin kunci da kasala ya shige ni, a daddafe nake ibada da alamarun gidan wanda ya dauki idanun ya zuba min, ina kiyaye lafiyata domin duk bayan sati biyu ina zuwa ganin likita wanda su Mama ba su sani ba, haka muka ci gaba da zama, ba ana haka Azizat matar Ya Tahir ta haihu, kiri kiri ya hana ni, zuwa.

Nima kuma ban damu ba, ana gobe suna Ya Tahir ya zo gidan da kanshi, ya same shi tunda ya ga Ya Tahir yayi ta kame kame.

"Nace ai ta je ita ce!" "Ko dai kai ne baka yarda ta je ba, Hafiz mun fa san halinka!" " Wallahi Attahiru ba haka ba ne, kasan yanayin ne yanxu tana zuwa ta ga su Inna da Hindatu, zasu zuga ta ai." Murmushi Ya Tahir yayi ya ce mishi.

" Yaushe zaku bar gidan nan an kusan shekara biyu kenan a gidan nan?" Shiru yayi yana kame kame kafin ya ce mishi.
Chapter 18 · 0% Book details