← Book details Alaƙar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 86

Sashe 50

Alaƙar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

" Kallonta nake, " har yau baki yarda kina da goyon bayansu ba ne, baki sani ba ko?" Hawaye ne ya zubo min, gyara zama tayi tana juyawa akan kujeranta ta cigaba da cewa.

" Me yasa Ahmad ta daina zuwa?" Shiru nayi ina kallonta na zata ko don an mishi magana ne, girgiza kai tayi tana kallona kamar tasan abinda yake raina ta ce min.

" Kina tsammanin Barista ya hana shi zuwa?

A'a ni na gaya mishi ya rabu da ke, a halin yanzu ba namiji kike bukata ba, kanki kike bukatar you need tow love yourself." Cigaba da kallonta nake, ta mike tana mai isa gaban frij ta dauko min ruwa ta ajiye min tana fa
in.

"Har yau baki san yadda zaki kwanci kanki ba, har yau baki san yadda zaki yi fada don kanki ba, yaushe kike tsammanin zaki iya zaman aure bayan nasan wacece matar Ahmad, ya zo nan ya gaya min kin ki kula shi nace mishi ai ke yanzu baya ga kanki bakya bukatar
arin wani a rayuwarki.

Sannan idan ya nace ya aure ki rayuwarki ta baya zaki koma, me yasa muna janyo ki present zamu mai daki past dinki?

Daga lokacin da kika fara sanin ciwonki, a lokacin zaki fara tantance waye yake kallonki da idanun basira waye yake kallonki domin biyar bukatar kanshi, ni na gaya mishi ba zai iya gina soyayyarshi yadda ya dace a tare da ke ba domin zuciyarki a rufe yake.

A duk lokacin da irin wannan abin ya faru ana bawa masu irin matsalarki lokaci ne, don haka kina da lokaci ki cigaba da kula da kanki da lafiyarki.

Sai me kuma?" Shan ruwa nayi kafin na gaya mata yadda muka yi da likitoci biyu.

Murmushi tayi tana fa
in, " na gaya miki dole ki shiga ajin motsa jiki, kina cin abubuwan da na hana ki ci, har yau baki ware abinda zaki ci don lafiyarki ba, da kin kula da haka da tuni wata Lubnah ake magana ba wannan ba."
Sai na ji kamar nayi knocking heart dina tare da bude kofar ta ce min farka Lulu.

" Yes dole ki fara motsa jikinki, ki biya ku
i a unguwarku ai akwai inda ake motsa jikin, sai ki fara ina son na ganki nan da wata biyu." Kallonta nake ta yi cike da mamaki.

" Kina nufin.

Idan nayi zan samu lafiyar jikina?

Amma kuma ai kunya nake ji wurin za ayi ta kallona." Na fada kaina a sunkuye.

" Kina jin kunya ko?

Kada a miki dariya, bari na ha
a ki da wani yaron da na sani sunan Wasim!" Gyada kai nayi ina wasa da yatsuna, har ta kira Yaron ta gaya mishi, ashe a unguwar yake ta bani number wayarshi.

Sannan na mata sallama na dawo gida, bayan na yiwa Ya Ado bayani ya ce gobe zai tafi har wurin da kanshi ya ga yadda Gym din yake, haka muka kwana ina ta addu'a Allah yasa kada na samu matsala da kowa Allah yasa na kasance jaruma wacce zata iya daukar duk wata matsala, wurin karfe tara na gama shirin zuwa makaranta Ya Ado ya kira ni ya ce min.

"Ki je zasu baki wasu tips and abincin da zaki ci, sai ki amsa idan kin dawo muje a saya ko?" "In sha Allah zan amsa kafin na tafi." Na fada ina shiryawa, bayan na gama na fito na nufi titin unguwar da kafa, na je shagon babba ne na gaske.....
[12/4, 10:51
AM] Firdausi Salis: 32
A hankali nake tafiya ina kallon mutanen da suke wurin karti ne majiya karfi, sai yan mata yan gayu masu kyau da su, sai na ji na muzanta, gasu gwanin ban sha'awa yadda suke wani yauki zaka fahimci yan gayu ne da basu son tara kitse, wannan yanyin ya dauke kin dan kwarin gwiwa da nake da ita, a hankali na isa ciki tare da tura kofar sai aka bude ta ciki.

"Lubnah ko?" Gyada kai nayi ina mai kallon cikin wurin yadda kowa yake rayuwarsa.

Wasu suna motsa jiki wasu kuma suna hira can gefe da aka saka wani abu kamar labule mata ne a zaune suna yogo.

A hankali nake bin wanda ya min magana, wani office ya bude mana, wata kyakkyawar bakar mace cikin shigar kamala da mutunci zata iya kaiwa arba'in amma yadda take kula da jikinta ba zaka
auka ta kai arba'in ba, da murmushi ta kalle ni.

"Lulu!" Ya kira sunana, sai na ji na samu nutsuwa da ita, na gaida da ita murmushi tayi ta ce min.

"Adam ya ce min wai auta zai kawo?" Sai na rasa a ina na santa, kurban tea dinta tayi tana mai ajiye min wani kofi a gabana.

"Baki sani ba don tun kina yar yarinya muka bar Bauchi!" Zama nayi ina gyad'a mata kai.

"Sunana Nuratu Abdulfatahi kin tuna gidansu Kafaya?" Sosa kai na fara ina kallon kasa na tuna gidan har yau ana kiran gidan da sunan.

"Nice Kafaya." Sai na ji kamar an yantani daga wani yanayi na musamman, muryanta na ji a kaina tana tura min cup of tea din.

" Lokacin da Dr Dijah Bala tayiwa Wasim magana ban san cewa ke ce ba, da nace kawai ki zo, sha kada ya huce " dauka nayi na kurba ba sugar sai kamshin kayan kamshi, da lemon tsami.

Da kamshin ganyen tsamiya.

" Tea din ganyen tsamiya ne, yana taimakawa.

" Ta fada tana murmushi, haka na sha sannan ta cigaba da cewa." Adam yazo wai biya miki, kawai aka turo min shi OMG kin san rabona da Bauchi shekaru ashirin kenan fa yau ga sai dan Bauchi kuma
an unguwarmu, dan abokin Babana." Murmushi tayi kafin ta sha tea din nima rashin sabo yasa na sha ka
an.."Bayan rasuwar Babanmu muka dawo nan, Mamanmu ta cigaba da kula da mu har na samu miji nayi aure kasancewarmu Yarbawa da aka haifa a cikin arewa sai muka taso da dabi'ar yan arewa bamu manta da yarenmu ba." Shiru tayi tana kallon yadda nake kallon tea din.

" Kada ki damu zaki saba da shi." Ta fada tana murmushi, "Na auri wani dan uwana kuma kabilata, sai dai zamanmu bai yi dad'i ba haka muka rabu da dakyar shima ba ni ce na nime saki ba, mun haifi yara biyu da shi, kamar yadda kike gabana haka nima na kasancewa.

" Sunkuyar da kai tayi ina ganin yadda take dauke kwallar da yake zuba mata, haka na rabu da shi na cigaba da rayuwa, sai Allah ya ha
a ni da wani dan kasar ghana yazo nan yana kasuwanci ya koma, wani abu da ya faru shine yadda aka yi ta cin zarafina da kibar da nake da shi." Ta kalle ni yadda nake kokarin toshe bakina, saboda kukan da yazo min.

"A lokacin kaf narasa wani wanda zai dafa min ga tsohon mijina da yake yawan d'aga min hankali, haka Mr Anwar wanda ya kasance bako a cikin mu, shi ne mutum na farko da ya fara kallona a matsayin mutum mai daraja, duk da an san cewa mijina shi ya sake ni don kanshi amma sai da aka yi ta hango gazawata da nuna min halayyata ce bai da kyau domin tunda ya sake ni bani da hali mai kyau ne, haka na cigaba da taimakon Mr Anwar ya gaya min cewa dole na rayu domin har na fara fama da ciwon damuwa, a irin haka na rasa Yarona karami a wani ruwan saman saboda ya je wurin Babansa, a hanya dawowa ya fada cikin lambatu, sai da na ji ina ma da nice na mutu, sai mace da take tare da ni, Mahaifiyata ta ka
ai ta fahimci yadda nake rayuwa, hatta yan uwana sai da suka na tsani kaina na ji bana kaunar kaina.

Wannan yayiwa tsohon Mijina dad'i bani da zabi dole ya cigaba da abinda yaso.

"
Turo kofar aka yi wata matashiyar budurwa ta shigo tana fa
in.

" Momma!

Daddy yana ta kiranki fa!" Daukar wayar tayi tana fa
in.." Tuba nake Sarkin da yake mulkar zuciyar Kafaya!" Ban san me ya faru ba sai ga tana dariya tana fa
in." Idan ka sake na kama ka zaka sha wuya!

" Fita yarinyar tayi tana fa
in." Momma baku girma ke da Daddy;" ta jima kafin ta katse wayar ta ce min.

" Sorry Mijina haka yake baya iya minti talatin bai ji muryana ba." Murmushi tayi sannan ta daura da cewa.

" A lokacin na rasa kowa dai Mr Anwar shi ya tallafe ni da shawara da yadda zan tsaya domin har rasa aikina nayi, shi da kanshi ya bude min shagon saloon na fara Allah ya saka albarka a shekara daya na samu damar komawa makaranta, shi ya kara bani shawarar na rage jikina, ina cikin haka sai ya bijiro min da soyayyarshi, duk yadda naso kauce mishi haka ya shiga duk inda xan ji maganar mutane, yayi min hidima da ba xan iya tsallake bu
atarshi ba, a lokacin na tsaya da kafata da taimakon shi na san wacece ni, bai ta
a nima na da wani fasikanci ba, sai dai gina ni da yayi da soyayyarshi wanda ya saka na fahimci kaina na fahimci ashe nima mace ce, tunda ni na bukaci mu yi aure idan har da gaske yake, bayan wannan yarinyar da take waje, Nasiba, sai Abdullahi da Hafsa, da na haifa da shi.

Sannan shi ya kara tsaya min har na bude nan ina aiki da ma'aikatan gidajen kurkuku na jahar nan, a can na hango Mijina Babansu Nasiba, kinsan me yasa na baki labarin nan?" Girgiza kai nayi, ina share kwalla murmushi tayi ta ce min." Saboda ki gane kafin ki zo nima ban gina nan domin niman kudi ba, sai da labarina ya gina min nan, asalin nan Labarina ne ya gina min shi
addarata tana da nasaba anan, a duk lokacin da aka kawo sabuwar daliba abu daya nake tambayar me ya kawo ta me yasa ta zo?
Chapter 50 · 0% Book details