Sashe 21
Alaƙar Zuci Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kome na Abba ya sani kuma haka yasa shi kara samun yarda har da na dangi domin idan ba Abba bane ya ce yayi wani abu ba zai tab'a yi ba.
Shima Abba yana ganin kamar dan uwansa ne a tare da shi, domin kaf halin Baban Jama'are Ya Hafiz ya kwashe bai bar kome ba.
Haka na taso da wani mahaukaciyar kaunar Ya Hafiz da fari ni doguwa ce, sannan a yanayin yan gidanmu bamu da irin jikin nan da zaka ga mutum kato, a'a muna da yanayi jikin fulanin Jama'are, sannan gidanmu yanayin kowa daban, yanayin dakin Mama mu fatarmu tana da dan duhu, yayinda dakin Yadiko Fatarsu take da haske, haka yasa idan ka gan mu zaka yi ta mamakin yanayinmu.
Wannan shine labarin dangina da gidanmu.
2015-
June/July.
A karo na uku na lashe musabakar Alqur'ani, na fara shiga tun ina jss 1, sannan wancan satin mun Quiz and prize, na kasa a garin Abuja wanda na wakilci makarantarmu, tare da rakiyar Yayuna.
Allah ya zuba min rawan kai surutu uwa Uba tsokana da son ayi da ni, gashi yau mun yi bye bye da Jss3.
A lokacin ina fama da tashen balaga, wayyo kusan kwaila da rawan kai, haka muka shiga makaranta mu hudu team dinmu, nice a gabansu na juya ina kallonsu ina musu bayanin yadda Abuja yake, sai ji nayi kamar nayi kawo da mutum.
Na tafi kamar xan fadi, na ji an tare ni.
Da yanayin wata gaurayayyen hausa mai mix da fulatancin da ta kama harshe tare da wani guntun fashion English aka ce min, "opps i hope baka ji ciwo ba!" Sai ce min sannu yake, da wani irin murya me sanyi.
A hankali na matsa ina fa
in.
"Ba kome!" Na riko hannun Rumana muka yi gaba sai juyawa suke suna kallonsa, ni kuwa naki juyawa don bana ce ga yanayinsa ba sai dai yadda gabana yake faduwa yasa na yi saurin janye su muka shiga cikin Makarantar.
Bikin yaye dalibai yayi kyau domin nima naci lamban yabo kala uku, a cikin kuwa har da kyautar kudin da na samu, saboda zama na daya da anyi a ko ina.
A wannan ranar mai cike da tarihi har Makarantar Ya Hafiz ya zo ya dauke ni a ranar da ya fara sayan mashin dinsa Simba, tun muna Jss1 kawayena suka san da zancen Ya Hafiz.
Rumah Rabi'u Mai shanu, Hafsah Faruq Babaji, Nafisa Sadi Gital, sai ni Lubabatu Shehu Umar Jama'are, sau dayawa cewa ake sunana yayi tsawo ni kuwa ban tab'a ganin tsawonsa ba.
Wani lokaci shafin
addara tana budewa a rayuwarmu, ba tare da mun sani ba.
Idan da ace wani abun mun rike tow ba makawa da ba zamu manta da shi ba.
Haka muka sha hutu, sannan muka dawo.
A lokacin na dawo da wani irin yanayi na ciwon mara na al'ada.
Sati na biyu da dawowa, da yake ban yi al'adar da wuri ba sai da na shiga aji na hudu, sannan ranar ita ce ranar da na fara, ciwon ciki kamar zan mutu, zufa nake yi tare da jin wani irin zazza
i ya rufe ni, ga ciwon ciki kamar xan yi amai.
Sabon malamin Chemistry da aka kawo mana ya shigo ya fara kiran sunan kowa sannan shi zai zame mana Form master dinmu, a hankali ya fara kiran sunayen mu, har ya zo kaina ya kira sau biyu ban iya d'ago kai ba, sai da ya kara kiran na uku Ruma ta ce mishi.
"Sir tunda tazo gata nan bata da lafiya!" A dan hanzari ya kalle da wurin da ta nuna, a hankali ya karasa wurin ya
an ta
a desk
in a hankali na d'ago kai kafin ya tambaye ni na sheka mishi amai a jikinsa baki
aya, sai a lokacin na zaro idanu ina kallonshi.
"Sorry how are you feeling now?" Shine tambayar da yayi min, kasa magana nayi ina rike da cikina.
Shiru yayi na wani lokaci kafin ya mike ya fita can sai ga yan ss3 sun shigo tare da shi har ya sauya kayan, wata jamfa ce a jikinsa golden yellow, yana shigowa ya ga yadda suke ta irin kyamar tabani.
" Me kuke yi haka?
" Takawa yayi yana kallon yadda suke son taba ni don ni kaina nasan a i mess up, duk aka rasa dabarar da za ayi min sai gashi an buga break, yan class suka fita a dudduke na mike, dawowa bayana yayi zai magana yadda zasu rike ni ya ga hatta hijab dina ya baci da jini!
" Look koma ki zauna!" Haka na koma na zauna ina jin wani irin ciwo ya ce yan matan.
" Ku tsaya ina zuwa!" Haka ya fita can sai gashi tare da Malama Malika ta Jss3, dauke da sabon hijab dal a hannunta ta sallami yan matan sannan ta ce min..
"Lubnah sannu ko!" Gyada kai nayi, ta bani hijab din na saka, sannan ta dauki wancan ta saka a leda, ta riko hannuna muka fita waje, motar Principle aka saka ni, muka wuce gida, ban san ya aka yi ba sai da nayi sati sannan na dawo lokaci na warware, Ya Hafiz yake kawo ni.
Tun daga lokacin Malamin nan ya saka min idanun, sannan shi ya rubuta min note akan duk ranar biyar ga wata, matukar ba jarabawa ba ne ba'a bukatar nazo makaranta idan kuma nazo, na fara zuwa clinic na makarantar na amshi magani da sanatery pad ni sai ya shiga sani jin kunya haka kawai zai saka ni jin na zama yar iska, akwai wani program da kamfanin Always suka yi a lokacin, tabbas sun bamu kyautar pad din, haka na ga mutumin nan yana kallona.
Ni tun a wurin nayi kyauta da shi domin na tsani yadda yake bina da idanu.
Sau biyu na taba kallonsa, idan na Ganshi bana iya d'aga kai na kalle shi domin zubi yake min da gardawan almajirai.
A gefe guda soyayyarmu da Ya Hafiz kamar mu cinye kanmu, haka yasa yan gidanmu suke ta ganin ina gama secondry School za'a aurar da ni, ban damu ba.
Amma kuma zuwa lokacin da muka shiga ss2 mutumin nan ya fara damuna, don ya saka min idanu yadda ni ban zata ba, sannan duk wani abu nawa yana jin sa ne a bakin Ruma ita kuma sai Allah ya daura mata sonshi da ni, ita tayi ta ziga ni har na fara kula shi, amma ba a makarantar ba a gidan Aunty Inna, domin a lokacin Aunty Hindatu tana tare da Ya Hafiz, Nafisa Sadi Gital kuwa cewa tayi na ci ku
insa kawai don mun lura wallahi kamar bai da wayo, duk abinda zance ina so zai bani, kuma bai ta
a jin zafin cire kudi, Yaran Aunty Innah kuwa wani irin kashe musu kudi yake domin ni a wurinsa na ta
a ganin wasu chocolate.
Amir dan Aunty Innah ya cika shekara biyu, nake gaya mishi ai sati na zagayowa sai ga tarkace har da Cake, lokacin Blackberry sai wane da wane ina fama da wata yar Nokia da Ya Hafiz ya kure a daka ya saya min, sai ga Malam Bilal ya kawo min sabuwa dal, ai kuwa Aunty Innah yana kara zuwa ta mai da mishi ya ce shi me zai yi da shi, dukkanmu kallon mai fama da albashi muke masa, bana sonshi domin Ya Hafiz ya cika min raina da soyayyarshi.
Lokacin da muka shiga Ss3 ya gabatar da kanshi a wurin Abba, maganar gaskiya Abba ya amince da shi amma lokacin da ya tambaye ni, kai tsaye na ce ni fa Ya Hafiz nake so, shima kuma Ya Hafiz din ya amince ni yake so, haka da ya kara dawowa Abba ya bashi hakuri tare da gaya mishi an tsayar min da miji domin ya tambayar da yayi min na gaya mishi gaskiya.
Koda na je makaranta na samu sakon yana min fatan alkhairi, Malam Hamza Adam ya kira ni office dinsa ya min..
"Lubabatu gaya min me yasa bakya son Malam Bilal?" Shiru nayi ya rasa yadda zai saka ranshi..
"kin san waye kika yi rejected dinsa kuwa?
Kin san waye shi?
"
Kasa kasa nace mishi.
" Kayan lambu ne da zan tsaya dai ya nuna zan zabe shi.
Ni ina da wnada nake so!" " Wanda kike so kin san waye shi?
" " Dan uwana ne fa!
" Na fada ina
auke kai daga kallonshi.
" Shi kenan Allah ya baku zaman lafiya!" Daga haka na mike na bar mishi office din.
Kafin mu gama makaranta na ji labarin wai ai
an masu arziki ne, Malam Hamza ya gayyace shi bikin Yaye dalibai shine ya zo.
A bakin Ruma naji wacce ta ce min ya bar min sako a wurinta.
" Ki rike na baki sakon da ya bani!
" Tayi ta mamaki.
Haka muka gama makaranta na manta da shi domin ya cikin lissafina, a 2017 muka gama har da Jamb, na kuwa cika ATBU, ba laifi point dina ya ja, suka bani business administration, a shekarar da na fara a wannan shekarar Ya Hafiz ya kawo lefena da sadakina har dubu hamsin, duk da a lokacin sadaki yafi haka amma ba yanke mishi ba, Dangina kowa ya goyi bayan auren Yayuna maza da mata kowa yana san barka, haka yasa bikin ya zama irin na yar gatan nan, gidan da Ya Hafiz zai zauna Haya ce ya kama a fadaman mada, layin gidan Mamar tsohon gwamnan Bauchi Isa yuguda.
Duk wani kayan gata an saka min anyi min auren gata kowa ya sani, shi kanshi Ya Hafiz yasan yadda Iyayena suke kaunata.
Yadda muka fara da soyayyarmu me tsayawa a raina kowa ya ganni sai ya yi maganar aure ya amshe ni, gashi dai nice karama amma ayi min goyon auta ba don na koyi girki a gabansu Mama da Yadiko, haka yasa nayi ta kula da mijina, watanmu uku da aure Ya Hafiz ya kawo min shawarar tunda ina karatu na fara shan maganin hana daukar ciki yana tausayina nayi karama ga kuma karatu, cikin soyayya da kulawa ya bani wannan shawarar, ni kuma na amsa hannu bibbiyu.